← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 85

Sashe 30

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mintuna tana kallo Tayi nisa a kallon series film d'in da take kallo taji motsin foots step daga b'angaren mazan gidan nasu ta juyar da kanta tana kallan direction d'in da take Jin foots step d'in.yayan nasu ta gani yana saukowa Hakan yasa tai saurin d'auke kanta daga kallansa ta Maida kan TV harya k'arasa saukowa downstairs d'in.ganin zai gif tata zaiyi hanyar dining yasa tai saurin cewa. "barka da safiya yaya". Ta fad'a cikin ladabi.batareda Afeef ya juyo ba bare ya kalleta ba ya ansa mata .ya k'arasa dining d'in yaja kujera ya zauna Yana zube wayoyinsa kan table d'in. Ammie ce ta sauko downstairs d'in cikin shiga ta Alfarma ta k'araso falon tana kallan Huda tace. "Ina HUYAAM d'in? badai har yanzu Bata tashi daga baccin ba?...." Ta fad'a tana kallan Huda. Afeef Dake dining Yana cin abinci ya d'ago da kansa ya Kalli Ammie Jin abinda take fad'a sai Kuma ya Maida kansa ya cigaba da cin abincin.Huda ta juya tana kallon Ammie tace . "Eh Bata tashi ba".ta fad'a tana kallan Ammie. Ammie ta sauke numfashi tace . "Ya Allah! Ni kan bansan ya Zanyi da yarinyar nan ba Agidan nan akan k'in yin breakfast da wuriba, ni damuwa ta D'aya kartai ta bacci kuma Bata ci abinci ba banason Wani ciwon ya kamata ta". Sai Kuma ta kalli Huda tace. "Jeki taso ta maza yanzu".Babu musu Huda ta Mik'e Afeef ya bita da kallon gefen ido azuciyarsa yace wato yarinyar nan har yanzu Bata daina wannan baccin nata ba kenan ya lura tunda yazo gidan nan kullum haka ake fama da ita.tuna ninsa ya katse ne lokacin da Ammie ta kalle shi tace. "Ka fito kenan?...." Sai a lokacinYa d'ogo ya kalli Ammie da sexy eyes d'insa ya gyad'a mata kai kamar Wani k'aramin yaro Hakan yasa Ammie tace. "Aishikenan" sai Kuma tace. " k'arfe nawa yau d'in zaku fitan". yace. "k'arfe shad'aya ne in Sha Allah". Ammie ta Jin jina kai tace. "Allah ya kaimu, Kai wannan bama hutu kazo ka aiki kazo Yi ai".yay murmushin da Bai shirya ba Wanda yay masa bala'in kyau Amma baice komai ba.huda ce ta dawo falon tana kallan Ammie tace. "Na tashe ta tak'i tashi Ammie".ta fad'a tana kamae Zatai kuka... Ammie ta sauke numfashi tace. "Bata tashi ba da kika ce Huda? Na rasa ya Zanyi da Huyaam akan wannan baccin nata a gidan nan ni damuwata ma shine ta tashi taci abincin kar ulcer ta kama mun ita, badan haka ba tai ta baccin har sai ta ga dama ta tashi". Afeef dai Yana jinsu baiyi magana ba Ammie ta kalli Huda tace. "Wai Huda Bakice mata nice na Aiko kiba? kema fa nasan halinki Huda zuwa zakiyi kiyi mata ta k'arfi ita Kuma ta biye miki tak'i tashi". Huda tace . "Wallalhi Ammie babu abinda nai mata zuwa nai kawai na tashe ta nace kince ta tashi baccin ya Isa haka". Ammie ta sauke numfashi tace. "To ki koma yanzu kice nace lallai lallai ta tashi tun Kafin na shigo da kaina na sameta".Huda tace. "to" har tai gaba Afeef da yake cin abincin sa batare da ya d'ogo ba yace cikin husky voice. "Kije kice ta tashi injini".ya fad'a Yana cigaba da cin abincinsa kamar bashi ne yay maganar ba.huda ta juya ta haura stairs bayan ta ansa masa da to...Koda Huda ta shiga d'akin HUYAAM har lokacin tana a yadda ta barta tana kwance cikin lallausan blanket d'in ta,ta lullub'e duka jikinta dashi sai sauke numfashi take a hankali tana baccinta cikin kwanciyar hankali.Huda ta haura saman gadon ta d'age bangon tana kallan Huyaam tasa hannu ta fara Tashinta Huyaam tai juyi ta Bud'e idonta kad'an, sukai Ido hud'u da Huda ta yamutsa fuska tace . "Wai ke Dan Allah meye hakan ke idan Baki katse mini bacci ba arayuwar ki bakyajin Dadi wai?...." Ta fad'a tana Wani tura Baki gaba.huda ta sauka daga saman gadon ganin ta tashi tace. "Bani d'in bace da kika Raina Yaya ne yace ataso ki ko Kuma yazo da kansa". Ai Jin haka yasa Huyaam tai saurin mik'ewa zaune tun Kafin Huda ta k'arasa kaiwa zancen,ta sauko daga saman gadon tana zare ido tace . "Dan Allah fa da Gaske kike ko Kuma wasa?..." Huda na gimtse dariyarta tace . "Wallahi da Gaske nake ko kin d'auka wasa nakeyi". HUYAAM ta d'auki hularta tasa ta kalli Huda kamar zatai kuka tace. "Dan Allah kice masa na tashi yanzu zan fito". tana fad'ar haka tai hanyar toilet ta shige ta kullo k'ofar.Huda tai murmushi tana cewa ga tsoro kuma ga tsiwa ta fice daga d'akin ta Sauka downstairs ta tarar da har Afeef d'in ya fita ta samu Ammie Zaune kan kujera ta k'arasa wajen ta tace. "Ammie ta tashi, Ina kuma yayan yake?..." Ammie tace. "Yanzu ya fita".Huda ta sauke numfashi ta koma wurin zamanta ta zauna. K'arfe uku Saura na Rana, Hajiya Lubabatu ce tare da Salima Wacce suke zauna a d'akinta saman kujerar Dake a d'akin tana kallan salima tai k'asa da murya tace. "Salima Abinda yasa na k'iraki Nan ba Wani abun bane ba illa kisan yadda zakiyi kijawo hankalin Afeef zuwa kanki ya zamto Babu wacce yakeso sai ke Nima zan tayaki ta bayan fage idan Allah yaso ya yarda,Dan san samu na ace ana gama bikin su Bahijja zan cen naku za'a fara".ta fad'a tana kallan yanayin salima...Salima ta sauke numfashin farin ciki Dan d'aukar ta wata maganar hajiya Lubabatu zatai mata ba wannan ba tace cikin farin ciki. "Wallahi mama kamar kinsan abinda yake Raina kenan inason Yaya Afeef so bana wasa ba Amma wallahi Bai tab'a yimin k'wakwk'waran Kallo ba Dan kwata kwata tunda yadawo gidan nan wallahi sau D'aya na ganshi Shima daga nesa ne lokacin sun dawo tare da Mai martaba Kuma duk lokacin Danaje sashensu sai na tadda baya Nan jiyama a islamiya Dana tambayi Zarah cewa bana ganin ya Afeef tace mun ai baya zama kullum suna fita tareda da Mai martaba ne Kuma idan suka fitan sai Dare suke dawowa". Ta fad'a kamar zatai kuka .Hajiya Lubabatu ta gyara zamanta ta k'ara tai k'asa da murya tace. "Eh nasan da wannan, sannan ke Kuma meye damuwarki da Wani kallo Kinga indai akan wannan ne karki Wani damu Dan Baya kallanki tunda ba ke kad'ai yeke yiwa haka ba .Kuma shi namiji D'an lallab'awa ne saboda haka mu bishi a hankali da sannu komai zai dai dai ta karki Wani ta-da hankalinki akan Hakan, sannan batun Kuma baya zaman gidan nan duk Mai sauk'i ne tunda idan suka fitan ba kwana suke ba duk mun dare suna dawowa gidan ai da sauk'i".salima dai kallanta Kawai takeyi Sai kuma ta k'ara gyara zama tai k'asa da murya tace. "kina jina bari nai miki wata dabara Mai zai Hana kije sashen nasu da daddare na tabbatar lokacin duk inda yake ya dawo Tunda ai ance da daddare yake dawowa ko?..." Salima ta gyad'a mata kai.hajiya lubabatu ta k'ara gyara zama tace . "To abinda nake so Dake shine idan kiga je b'angaren nasu ko an tambayeki mai ya kawoki kice kinzo gaida shine,sannan Kuma Zaki Mai godiyar tsarabar Daya kawo muku...." Ta fad'a tana kallan Salima. Salima tai Jimm sai Kuma tace. "Amma mama kinsan fa ko mutum yaje baya Wani bashi attention d'insa idan kai Sa'a nema ya ansa gaisawar ka".ta fad'a kamar zatai kuka. Hajiya Lubabatu ta Bat'a Rai sai Kuma tai k'asa da murya tace. "Yo ke in Banda abunki Salima Ina ruwanki da Wani Shan k'amshinsa indai keda kike nema aiko hantararki Yaya ki jure wata Rana sai labari labarin ma baza'a jiba, kuma zaki ce nina fad'a miki, kinsan Allah Salima da kansa zai sauko kedai kawai abinda nake so Dake shine ki bishi a hankali mudai burinmimu shine ya soki kuma ya aureki shikenan wata Rana sai kinyi mamakinsa zakice na fad'a miki" ta fad'a tana sakin fuskarta.salima ta rausayar da kai tace. "shikenan mama Allah yasa, anjima da daddaren naje ni". Hajiya Lubabatu tace. "Yauwa ko kefa kiyi kwalliya tajan hankali kije ki sashen nasu". Salima tace "to" sallamar da sukaji da Muryar wanda sukaji yasa Hajiya Lubabatu cewa. "Tashi muje Aziz ne karya fara NEMA na.daga haka duk suka mik'e Salima ta fita daga d'akin Hajiya Lubabatu tabi bayanta...... ___________ Da yamma bayan sallahn magrib Aziz chiroma ne tsaye a Wani k'aton mall Yazo yin siyayya Yana tsaye gaban wasu rings na gold masu bala'in kyau da tsada sai Wani walwalin haske sukeyi ya d'auki Wani Mai Dan Karan kyau Wanda yake ganin zaiyiwa Huyaam kyau ya d'auka mata dai dai size d'inta duk da ba sani yayi ba gassing kawai yayi sannan Kuma ya d'aukawa Huda ma irinsa Amma design d'in ko wanne daban sannan ya bar wajen ya k'arasa wajen dogayen riguna nan ma ya d'aukar musu guda biyu iri D'aya ita da Huda sai Kuma ya d'aukarwa su Ikleema ma da safna da Aziza dukansu kowa set D'aya sannan ya bar wajen ya k'arasa inda ake saida chocolates nan ma ya d'aukar musu package package kala kala masu bala'in tsada da Dad'i sannan ya bar wajen ya k'ara wajen payments bayan ya gama duk abinda zai Siya... fitowa yayi daga cikin Mall d'in gabad'aya D'aya daga cikin workers d'insu ne ya rakoshi da kayan daya siya d'in ,boot d'in motar ya Bud'e mutumin ya zube masa kayan aciki sannan ya rufe ya sallameshi ya karasa ya Bud'e driver seat ya shiga ya ta-da motar ya bar wajen direct Wajen Wani abokinsa ya tafi dayake ta doka masa K'iran tun d'azu...... Wajen k'arfe 9 saura na dare gama yin dinnersu Kenan suna Zaune a falon k'asa Huyaam na mak'ale kusa da ya Zarah wacce ke nuna mata abuba wayarta Huda Kuma tana nunawa muneefa yadda zatai homework d'in da aka Basu a school,Ammie Kuma tana d'akinta Bata Dad'e da Shiga ba taje yin abune .sallamar da akai daga k'ofar falon ne yasa suka juya suna kallan Mai yin sallamar harta k'arasa shigowa falon.ansa mata sukai harta k'arasa ta Zauna kan kujera Huda na kallonta tace . "sannu da zuwa ya Salima".Salima na murmushi ta ansa mata hakama Huyaam da muneefa duk suka gaida ta lokaci D'aya, nan
Chapter 30 · 0% Book details