Sashe 5
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Emir palace kano state* Wajen k'arfe shida dai dai na yamman Ranar, Wata k'atuwar mota ce nagani ta tunkaro Wani babban gate Irin na gidan sarauta motar k'irar family car ce sabuwa dal da ita . tun kafin motar ta k'araso naga wasu dogaraye Wanda suke Zaune abakin gate d'in gidan daga waje Wanda ak'allah zasu kai kusan su shida sai police guda hud'u Wanda da dukan alamu sune suke tsaron gate d'in.mutane biyu daga cikinsu naga sun mik'e cikin sauri suka wangale k'aton gate d'in gidan, adai dai lokacin motar ta iso bakin gate d'in gidan direct ta kutsa kai ta shiga har cikin gidan yayin da fadawan nan suka cika wad'anda ke cikin motar da kirari tare da saukowar su lafiya. A babban compound d'in gidan motar tai parking .Wani dogari na gani ya fito daga gaban motar cikin sauri inda yay saurin zuwa ya Bud'e bayan motar Wanda naga yaran gidan ne gabad'ayansu sanye da uniform na islamiya a jikinsu Wanda da dukan alamu daga islamiyar aka d'aukosu. yara mazan ne wad'anda ke seat d'in farko suka fara fitowa daga cikin motar cikin shigar uniform na islamiya kusan su hud'u Wanda a shekaru a k'alla zasuyi 12 years haka,sai da suka gama fitowa sannan naga Yara matan suma sun fara fitowa , Wad'anda sune k'ana nun cikinsu,su su hud'u ne suma Wanda a shekaru a k'alla zasuyi 8 years haka D'aya ce kawai take 12 years Acikinsu.bayan sun gama fitowa sai yayunsu 'yan mata Suma su hud'u Wanda duk Sa'an nun juna a shekaru zasuyi 17 years haka , bayan sun gama fitowa sai yayansu suma su hud'u biyune manyan cikinsu wadda suka fisu dan sune manya Wanda a shekaru zasuyi 24 haka sai sauran biyun Wanda su Kuma ashekaru zasu 22 haka , gabad'ayansu sun gama fitowa wasu sun cikin gajiya Dan naga sai Wani ya Mutsa fuska suke alamar gajiyawa atare dasu .bayan sun gama firfitowa kowa ya nufi part d'insu dayake gidan Irin K'aton gidan nan ne Mai d'auke da sashe daban daban Wanda a k'alla zasuyi guda biyar agidan, sashe biyu suna b'angaren dama sai sauran sashe ukun Dake nan b'angaren hagu. Wanda ke b'angaren Daman part na farko naga wasu daga cikinsu sun nufa su_su biyar suka nufi part d'in Wanda su Hud'un mata ne sai namiji guda D'aya,yaran sune agaba macen da namijin kenan, namijin Yana rik'e da Hannun k'anwar tasu Mai suna muneefa wacce itace autar su sai shi Mai suna muneeb. Daga bayansu kuma yayar suce Wadda itace Babbar cikinsu Mai suna zarah sai K'annanta Wanda suke bi mata suna bayanta D'aya na rik'e da D'aya ajikinta da dukan alamu d'ayar Babu lafiya ne Wanda Sa'an nun juna ne . Ta juya Ganin da tana bayansu,ganin basa sauri yasa tai gaba.ta tsaya tana kallan wacce ke rik'e da d'ayar tace cikin fad'uwar gaba . "Huda! meya samu HUYAAM d'in naga kin rik'ota?...."ta fad'a tana kallan HUYAAM wacce idonta ke lumshe. Wacce aka k'ira da Huda ta d'ogo tana kallan wacce tai maganar tace cikin Damuwa. "Wallahi ya Zarah tun muna class tace min kanta na ciwo,to sai yanzu Kuma da muka dawo gida muna sauka sai naga tana k'ok'arin fad'uwa shiyasa na rik'ota".ta fad'a cikin damuwa. Wacce aka k'ira da Ya zarah ta k'araso da sauri cikin fad'uwar gaba Dan tana tsoron ace ciwon k'anwar tasu ne zai tashi ta Mik'awa Huda Jakar Hannunta tace. " rik'e min bari na kamata". ta fad'a tana k'ok'arin rik'o HUYAAM daga jikin Huda..Babu musu Huda ta karb'a ta had'a ta rik'e musu jakan kunan duka ukun.ya Zarah tai gaba tana rik'e da HUYAAM Huda Kuma tana binsu abaya. Da suka shiga falon babu kowa sai k'arar AC data fan sai k'arar TV dake tashi da sautin karatun Al'qur'ani Mai girma daga bakin Wani babban malami a k'asar nan.direct sama Huda ta haura zuwa d'akinsu rik'e da bags d'in nasu Dan ta ajiye musu .ita Kuma ya Zarah d'akin Dake nan downstairs Wanda shima yake a mazaunin nasu Duk da Basu fiye zama acikinsa ba sai lokaci zuwa lokaci yasa ta nufi Dan takai HUYAAM tunda tasan ba lallai ta iya haurawa sama A wannan yanayin da take ba.tana shiga d'akin ta k'arasa har gaban gadon ta zaunar da HUYAAM akai wacce idonta har sun kad'a sun koma JAA daga farin da suke ada. ya Zarah ta kalleta ganin kwanciya take son Yi tai k'asa da murya tace cikin Damuwa da lallashi. "Sannu HUYAAM! bari na Baki magani in yaso sai ki kwanta d'in".ta fad'a tana kallanta da tausayawa. Huyaam ta k'ara lumshe idonta Amma Batai magana ba.hakan yasa ya Zarah ta fita daga d'akin ta tafi kitchen Dan d'auko mata ruwa. Tana fita Huda ta shigo d'akin ta k'arasa har saman gadon wajen HUYAAM Dake kwance ganin kamar bacci take yasa ta juya ta tashiga toilet d'in d'akin Dan d'auro alwala tunda K'iran sallahn magrib akeyi .Babu dad'ewa ya Zarah ta dawo d'akin da gorar ruwa a hannunta ta tafi gaban lockan Dake gaban mirror ta jawo na tsakiyar ta d'auko Wani k'aramin box ta Bud'e ta d'auko park d'in PCM ta b'alli guda biyu sannan ta Maida ta rufe ta dawo gaban gadon inda har Huyaam ta kwanta ta zauna tana k'ok'arin d'ago Huyaam zuwa jikinta tace . "Tashi Huyaam kisha maganin".ta fad'a tana kallan Huyaam bayan ta d'ago da ita.da k'yar Huyaam ta yadda tasha maganin nan . Saida Zarah ta tabbatar da ya maganin ya D'an tsirga mata sannan ta taimaka mata ta kwanta. tana k'ok'arin Tashi Daga saman gadon kenan aka Bud'e k'ofar toilet d'in d'akin Huda ce ta fito daga cikin toilet d'in tana d'igar ruwa alamar ta d'auro alwala ya Zarah tana kallanta tace . "Yauwa Huda ki zauna da ita bari naje Nima nai alwalan" ta fad'a tana kallan Huda. Huda data d'auko darduma a inda suke anyiwa tana k'ok'arin shimfid'a darduma Dan yin sallahn tace. "To ya Zarah!, da sauk'i ai jikin nata ko?.ta fad'a tana kallan HUYAAM wacce ke sauke numfashi. Ya zarah juya itama tana kallon Huyaam d'in kafin tace . "Eh nadai Bata maganin Tasha"Huda ta gyad'a kai daga haka ya Zarah tabar d'akin. Ya zarah tana yin sallahn magrib ta dawo d'akin Dan K'ara duba jikin Huyaam d'in ta Tarar da Huda ta fito daga toilet rik'e da HUYAAM wacce da dukan alamu ta tai maka matane tayo alwala itama, Huda ta zaunar kan daddumar dake shimemfid'e nan tsakiyar d'akin. Ya zarah ta k'araso cikin d'akin tana kallan Huyaam tace . "Sannu HUYAAM jikin da sauki kenan",sai kuma ta Kalli Huda tace." sallah zatayi ne?..."Huda tana k'ok'arin sakawa HUYAAM hijab Ajikinta tace. "Gatanan dai cewa tai nakaita toilet zatai alwala"ta fad'a tana matsawa daga gaban HUYAAM bayan tasa mata hijab d'in Dan Bata dama tai sallahn. Ya zarah ta sauke ajiyar kafin tace. "Allah ya sawake tunda kina tare da ita bari naje".Huda tace. " Shikenan".daga haka ya Zarah tabar d'akin. Bayan sallahn isha'i gabad'ayansu suna zaune a dining gabad'ayansu tun daga kan ya haidar har zuwa kan muneefa suna dining suna yin dinner muneefa Dake kusa da Ammie ta Kalli ya Zarah tace . "Ya zarah Inasu ya HUYAAM naga bangansuba?..."ta fad'a tana kallan ya Zarah . Ammie itama kallab ya Zarah tai tana jiran ansar da zata bawa muneefa Dan itama Ammien tambayar Dake ranta kenan tun d'azu muneefa ta rigata,ganin Bataga yaran nata ba bayan kuma ba haka suka sababa indai suka dawo daga islamiya ko boko tofa sai sunje har Inda take sunce sun dawo bayama HUYAAM itakan tana da k'ok'arin wannan . Ya zarah Dake juya abincin gabanta Wanda Bata kai ga ciba tace cikin Damuwa . "Suna nan,HUYAAM ce Bata da lafiya kanta ke mata ciwo Shiyasa Basu fito ba". ta fad'a tana k'in kallan Ammie wacce ta zuba mata ido. Take gaban Ammie ya Fad'i Jin abinda Zarah ta fad'a sai kuma ta Dake tace. "Amma shine babu Wanda yazo ya fad'amin acikinku?,bayan kunsan cewa bana wasa da duka jinyanku musamman ma HUYAAM kinsan Bata da lafiyar Amma shine kika kasa fad'a min Zarah"ta fad'a cikin b'acin Rai. Ya zarah ta marai raice tana kallan Ammie tace."ai Ammie na Bata magani fa"ta fad'a tana kallan Ammie. Ammi tace. "Rufe min Baki babbar kawai kinsan Bata da lafiyar Amma kika kasa fad'a min".ya Zarah tai shiru ta sunkuyar da kanta k'asa . Muryar Ammie taji tace. "Tun yaushe ne kan nata ya fara ciwon?...."sai a sannan ya Zarah ta d'ago tace. "Huda tace tun suna aji har muka dawo". Ammie tace. "Yanzu tana Ina?.." Ya zarah tace. " Suna nan d'akin downstairs tare da Huda"tun kafin takai k'arshe Ammie ta mik'e ta nufi hanyar d'akin jikinta a Sanyaye gabad'aya sai Suma suka Mik'e suka bi bayan Ammie. Ammie tana tura k'ofar d'akin ta Tarar da Huda suna kokawa ita da HUYAAM a Saman gadon bil hakk'i da gaskiya sun Zubo da pillows d'in Dake saman gadon k'asa gabad'aya sun jik'e sharkaf da zufa sai kace Wanda sukai gudun tsere fuskar Huda tayi jaga jaga da hawaye da sauri Ammie ta k'araso ta rik'o HUYAAM wacce gashin kanta ya bar baje saman kanta ta kamota kamar wata mahaukaciya tana cewa . "Subhanallah Meya faru Huda?..."ta fad'a tana k'ok'arin rik'o HUYAAM Dake San k'wacewa daga rik'on da tai mata. Huda tace tana huci. "Ammie wai dole saita fita kuma fa Bata da lafiya"ta fad'a kamar zatai kuka. Ammie ta kalli HUYAAM wacce har lokacin idonta Yana rufe tana k'ok'arin k'wacewa daga rik'on da Ammie tai mata tace cikin sanyin murya. "HUYAAM! Ina zaki?.. HUYAAM tai shiru batai magana ba Kuma Bata fasa k'ok'arin k'wace kanta daga rik'on da Ammie tai mata ba.Nan Ammie ta Gane ba ita bace ba, take ta fara Yi mata addu'o'i HUYAAM ta k'ank'ame Ammie tana cewa. "Ammie kaina , Ammie kaina ki rik'emin zai fashe , Ammie zan Mutu"ta fad'a tana rusa da Wani Irin ihu. Take Ammie tai Saurin rufe mata Baki tana K'ara mannata da jikinta tace Cikin damuwa. "Innalillahi wainna ilaihi rajiun Baza ki mutuba HUYAAM in Sha Allah sannu" ,ta fad'a tana tufa mata addu'o'i har lokacin.itadai Huyaam sai jujjuya kanta take tana kuka ganin haka yasa Ammie ta dubi Huda tace cikin Damuwa . "jeki d'akina