Sashe 80
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
jikin pres d'in kayan gimbiya Aysha tana zab'ar mata kayanta da zata sa da Wanda zata buk'ata Idan sukaje can Egypt d'in.knocking k'ofar akai bayan wasu seconds aka turo k'ofar aka shigo lokaci D'aya.Anam ce ta shigo d'akin sanye da uniform d'in islamiya a jikin ta da dukan alamu daga can ta dawo.ta k'araso shigowa har cikin d'akin bakinta d'auke da sallama , Anty Amina ta ansa mata tana cigaba da aikinta.Anam ta ajiye Jakar Hannunta Wacce take ta islamiya nan Saman kujerar dake d'akin.ta nufo Anty Amina ganin tana had'a kayan Maminta a box ta ce "Anty Ina Mami zata? Anty Amina tana cigaba da abinda take ta ce "Egypt" Anam tai murmushi ta ce "harda ni za'a? Anty Amina ta ce "a'a Banda ke" Anam tai shiru lokaci D'aya Jin ba da ita za'a tafi ba" juyowa Anty Amina tai tana kallan ta Sai Kuma ta sakar mata murmushi ta ce "Da wasa nake miki daughter Dake mana za'a Hajiya inna ta ce wa za'a barwa ke idan muka tafi muka barki ai k'afar ta k'afar ki" ta fad'a tana murmushi.ai sai Anam ta washe Baki ta ce "yeh! I love inna" nan ta ta fara murna Jin da ita za'a" Anty Amina ta ce "to jeki cire uniform d'in tukunna" juyawa Anam tai ta wuce wajen press d'in kayanta ta Bud'e ta d'auki wata doguwar riga marar nauyi sannan bar wajen ta nufi Wani D'an corridor Dake nan cikin d'akin ta fara cire uniform d'in ta sauya zuwa na gida sannan ta fito ta daga ciki ta k'araso cikin d'akin ta haye Saman gadon inda gimbiya Aysha take ta zauna nan kusa da ita tanai Mata magana kamar wacce zata ansa mata. ita dai gimbiya Aysha binta kawai take da ido.mik'ewa Anty Amina tai bayan ta gama had'a kayan ta ajiye box d'in a gefe inda nata trolling kayan yake tana kallan Anam ta ce "ki zauna tare da ita bari naje na gano Idan sultan ya had'a kayan nasa" gyad'a mata kai Anam tai ta ce "to Anty" daga haka Anty Amina ta fita daga d'akin bayan ta k'ullo musu k'ofar..Anam ta Maida hankali tana cigaba da yiwa Mamin ta zancen da take mata duk da tasan ba ansa mata zatai ba Amma Kuma ita tana Jin Dad'i aduk lokacin da take yiwa Maman nata zance..... ____________ Aziza ce ta shigo b'angarensu da gudu tana dafe da Kuncinta tana kuka kamar ranta zai fita, tana ihun mommy na makance. Fulani Salamatu da take d'akinsu su Ramla ta taje kwantar da walida ta fito da sauri jin ihun Aziz wacce kamar ranta zai fita.take k'irjinta ya buga da k'arfi Jin abinda aziza ke cewa na wai ta makance.tuni ta nufeta da sauri ganin ta zube a tsakiyar falon har lokacin ihun kuka take. D'agota Fulani Salamatu tai cikin tashin hankali tana tambayar Aziza da lafiya? Aziz ta kasa magana sai ma Wani Irin kuka da take tana k'ok'arin shid'ewa.ai tuni hankalin Fulani Salamatu ya K'ara tashi ta ce cikin rawar murya "Aziza ki fad'a min Mai ya faru Maiya sameki? Da k'yar Aziza ta iya cewa "mummy yaya ne" ta fad'a tana kasa k'arasa zancen saboda Kukan Daya kufce mata.fulani Salamatu da duk hankalinta ya gama tashi lokaci D'aya tsabar rud'ewa tama kasa Gane wanne yayan Aziza take nufi ta ce "waye Kuma wani Yaya?" Aziza ta ce "ya Afeef mana" Fulani Salamatu ta ce "to Mai Yay miki? Aziza ta ce "marina yayi sannan yay ta ball dani" fulani Salamatu ta ce "Mai kikai masa yay miki wannan zalincin haka? Aziza ta ce tana sheshshek'ar kuka "Akan Huyaam ne wai Dan mum had'u a hanya nafito daga b'angaren su ikleema zan wuce ta gaban b'angaren su ita kuma sun fito ita da Huda ko Ina zasu ban sani ba kawai ta harare ni Nima na rama sannan na wanka mata Mari Ashe yayan Yana bayansu kawai ya fusgoni ya wanka min Mari har Sau uku sannan ya dinga Ball dani" ta k'arasa fad'a tana fashewa da gunjin kuka" fulani Salamatu dai kallanta kawai take tun lokacin da take Bata labarin har ta kai k'arshe. lokaci D'aya fuskar Fulani Salamatu ta sauya zuwa B'acin Rai Jin Afeef ne wai yaywa 'yarta haka ya kumbura mata duka fuska Kuma wai akan HUYAAM.bata ce komai ba saboda Tama kasa furta ko da kalma D'aya ce ,nan ta juya ta nufi sama zuwa d'akinta, Babu dad'ewa ta dawo da mayafi a ahannunta. Aziza ta mik'e ganin mommynsu ta d'auko mayafinta da k'yar ta ce "mummy Ina zaki? Fulani Salamatu ta juyo ta ce "zuwa Zanyi wallahi yau komai zai faru Saidai ya faru na gaji da cin zalin da yake Miki Aziza akan wata can zai Yi miki wannan marin ya kumbura miki fuska Bai tsaya nan ba shine harda yay ball Dake saboda ya riga da ya Raina min hankali sannan Babu Mai d'aukar mataki akai daga uwarsa har shi kansa Mai martaba saboda zalinci sannan ace ni Kuma bazan Yi magana ba ko Kuma na d'auki mataki ba, wallahi zuwa Zanyi nayi Abinda ran kowa zai Baci a gidan nan harshi kansa mai martaban sai dai yau ya sakene" tana fad'ar haka ta juya ta nufi k'ofa. Aziza batai gigin binta ba saboda karta je ta k'ara jawa manya Afeef ya K'ara mata Wani Marin.... Gabad'aya su Ammie suna zazzaune a falon Mai Huyaam sun kallo kawai sukaga an Bud'e k'ofar falon da k'arfi anshigo har k'ofar tanayin k'ara.mik'ewa sukai gabad'ayansu da sauri ganin yadda aka han kad'o k'ofar aka shigo da mamakin waye?Amma Banda Ammie wacce ke zaune tana kallon Mai shigowar, ganin Fulani Salamatu ce ta shigo tana huci kamar wata zakanya yasa Ammie mik'ewa tsaye itama cikin nutsuwa tana kallon fulani Salamatu Wacce ke mata mugun kallo tare da sauran yaran. Amma Sai Ammie ta basar tana murmushi ta ce "sannu da zuwa fulani" Wata muguwar hararar Fulani Salamatu tai mata kafin ta ce cikin hargowa "Kinga ga alamun zama ne ya kawo ni Maryam? Nace Kinga alamun zamane ya kawomini Maryam? zuwa nai gunki ba gun mahaukacin d'anki da idan haukarsa ta Motsa yake dakar min 'ya ba. Amma kafin nan bari na fara ta Kansa Ina yake? Nace Ina yake shi marar mutuncin? Ta fad'a tana dube dube a falon kamar Wanda zata ganshi.ganin baya nan yasa ta ce da sigar warning"nazo ne na tuna masa matsayin wannan a golar yarinyar nan agidan nan da yake fifita ta akan Aziza idan har shi ya manta to ni bari yau na tuna masa" ta fad'a tana nuna Huyaam.a tare Ammie dasu ya Zarah da Huda suka kalli HUYAAM wacce fulani Salamatu ke nuna ta da yatsa.itako Huyaam Kallan fulani Salamatu kawai take tana nazarin zancen ta.Ammie ta juyo tana kallon Fulani Salamatu gabanta na Wani Irin fad'uwa lokaci D'aya Jin zancen da fulani Salamatu tazo musu dashi yau a b'angaren nata.da k'yar Ammie ta iya had'a kalamanta ta ce "Fulani Mai kike fad'a Haka ne, waye matsayin su ba D'aya da Aziza ba Agidan nan? Fulani Salamatu mata tai Wani murmushi Jin abinda tazo dashi ya fara karyar wa da Ammie zuciya ta ce "wacece Kwa idan ba Agolar gidan nan ba ko akwai wata Agolar ne bayan ita wacce aka fifita ta akan 'yar gidan har ana Neman akashe 'yar masu gida akan ta" sai Kuma ta Wani tafe hannu ta ce "Au mantawa nai,Ashe fa har yanzu Baku fad'a mata ko ita wace ce a gidan nan ba ko? Da aje a kashemin 'ya akan agola gara ni nazo na fara sanar mata da matsayinta Agidan nan" ta fad'a tana kallan Huyaam.Ammie da ranta ya fara B'aci lokaci D'aya Irin Wanda bai tab'a B'aci ba ta ce cikin tsawar da batama San taiwa Fulani Salamatu ba "Fulani Mai ya faru haka ne da zaki zo kinayin wad'an nan magan ganun marasa tushe a gidan nan Dan Allah? Ta fad'a tana kallanta.Fulani Salamatu zata K'ara magana kuma Ammie tasan ba alkhairi ne zai fito daga bakin ta ba yasa ta ce "Dan Allah kiyi shiru muje b'angaren ki muyi maganar" Fulani Salamatu tai Wani murmushi ta ce "Babu inda zani agaban kowa Za'a yi wannan maganar.wato bakya son yarinya tasan matashin tasan ko wacece ita a gidan nan bane kome?To idan Baku fad'a mata yanzu ba yaushe kuka shirya fad'a matan, ko sai anzo Neman Auren ta tukunna? Ta fad'a tana kallan Ammie ido cikin ido ganin ta kasa magana.Su dai su yay zarah kalllan Fulani Salamatu kawai suke gabansu na fad'uwa suna k'ok'arin fahimcitar inda zancenta ya dosa ganin Ammien su tayi shiru tak'i magana hakama Huyaam da duk take cikin compused d'in zancen Fulani Salamatu.ganin duka yaran sun rud'e sannan itama kanta Huyaam d'in Bata fahimci zancen taba yasa fulani Salamatu ta Kalli HUYAAM ta ce "Kinga yarinya bari na fad'a miki Abinda ake ta b'oye b'oyen fad'a miki shekara da shekaru,ke ba 'yar gidan nan bace ba agola ce.Fulani Maryam da Mai martaba ba su suka haife kiba kamar yadda kike tunani ba" ta fad'a tana kallanta.Huyaam dai kallanta take Bata ko kiftawa tana nazarin zancen ta. Haka ma falon yayi d'iff kamar Wanda ruwa ya cinye...Jin muryar Afeef sukai Wanda tunda fulani Salamatu ta fara gayawa Huyaam ko wacece ita ya sauko stairs d'in Dan hayaniyar ta ce ma ya fito dashi daga b'angarensu Dan Yana zaune a falonsa yana Aiki a laptop kawai ya juyo magan ganun Fulani Salamatu a tsakiyar kansa, Hakan yasan ba lafiya ba,Babu shiri ya fito yaga mai ke faruwa.wata uwar tsawa ya dakawa Fulani Salamatu Yana nuna ta da yatsansa ya ce "ya isheki haka" da wata iriyar murya Lokaci D'aya idonsa ya kad'a yay jajir jijjiyoyin kansa duk suka fito rad'o rad'o yana cigaba da tafiya har ya k'arasa shigowa falon yana nuna mata kofa yace "gate out before I loss my control malama" Fulani Salamatu tana masa Wani kallo ta ce "bazan fita ba,duk abinda na fad'a k'arya nai koba Kaine ka tsintota ba? ka tsintota ka kawo ta nan gidan ko na ba haka akai ba? Ta fad'a tana masa Wani Irin kallo.Afeef dai kallanta yakeyi kirjinsa na bugawa sama da k'asa Yana Jin kamar ya shak'eta saboda irin abinda