Sashe 44
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tana kallon Anam data dawo daga islamiya k'arfe b'iyar da Rabi na yamma.har ta k'araso shigowa falon ta risina ta gaida Hajiya inna.hajiya inna ta ansa mata tana cewa". Andawo Zainabu?..." Anam ta gyad'a mata kai . Hajiya inna tace. "Sannu da dawowa Zainabu Allah ya Bada ilimi Mai amfani".Anam ta Ansa mata tana mik'ewa Hajiya inna tace. "Maza ta kwara jeki sauya kaya kizo ki k'arb'i abunda Dana akeyi miki". Anam ta gyad'a mata tace. "To" sannan ta wuce zuwa d'akin gimbiya Aysha Dake nan upstairs d'in....baba uwani ce ta fito daga kitchen d'in downstairs ta k'araso falon ta tsugunna har k'asa kusa da Hajiya inna tace. "Mai babban d'aki an gama dafa maganin". Hajiya inna ta juyo tana kallon uwani tai k'asa da murya tace. "Ba haka ya kamata kice ba uwani yanzu idan wannan yaron Yaji me kika fad'a min fa?kinsan fa Yana nan d'akin k'asa Yana karatu kar yaji Mai kike cewa anjima idan na Kai masa yace bazai shaba".baba uwani ta sunkuyar da kanta k'asa tace. "Tuba nake Mai babban d'aki ban sani ba." Hajiya inna tace."to yanzu abinda za'ayi ki samu wankakken mazubi Mai Fad'i ki juye bayan kin tace ki barshi yasha iska anjima zan Miki magana saiki kawomin". Baba uwani tace. "To ranki Dad'e a tashi lafiya". daga haka ta koma kitchen d'in bayan kamar mintuna 10 ganin Anam Bata saukoba gashi sai K'iran sallahn magrib akeyi yasa Hajiya inna mik'ewa ta shiga wani sapare d'aki Dake nan downstairs d'in Dan nan ta D'an tattaro kayan ta tadawo tun lokacin da sultan ya fara k'ok'arin guduwa idan ciwonsa ya tashi tace gara ta dawo b'angaren nasu ta zauna kar aje wata Rana ya gudu ba'a sani ba su shiga uku.ita anty Amina abun ya mata yawa ga jinyar uwa Kuma gata d'a ai dole a tausaya mata.toilet d'in d'akin ta shiga bayan ta shiga d'akin Dan d'auro alwala.... Turo k'ofar d'akin akayi bayan anyi sallama. Hajiya inna Dake kan darduma tana lazumi ta juyo Jin anshigo mata d'akin. Anam ce ta Gani ta shigo ta k'araso cikin d'akin ta haye saman gadon tana kallan Hajiya inna tace. "Na zo ki bani abinda kikace zaki banin?..." Hajiya inna ta kalleta tace. "Ayya wuceki tunda Baki dawo da wuri ba sai yanzu". Anam ta tura Baki gaba tace. "Ai na dawo bansameki ba shine nace bari nima naje nai sallahn saina dawo". Hajiya inna ta tab'e Baki tace. "Kedai kika sani Mik'o min wancan k'waryar abun Yana ciki". Anam ta juya tana kallon inda Hajiya inna ke nuna mata ta k'arasa ta d'auko k'waryar ta Mik'a mata sannan ta koma ta zauna.Hajiya inna ta Bud'e k'waryar nan Anam taga miye aciki Ashe zuma ce.hajiya inna ta d'auki Wani spoon ta d'ibi Zuman ta Mik'awa Anam.Anam ta gyara zamanta tace. Ki Mik'o min mana". Hajiya inna tace. "Ta ya ya zan Mik'o mikin ina zaune". Anam ta taso ta karb'a tace. "Kuma iya D'an wannan zaki bani inna". Inna ta mik'a hannu tace" idan baza kishaba ki bani kayata". Anam ta harareta sannan ta mik'e ta koma saman gadon ta fara Shan Zuman... K'arfe takwas da mintuna inna tashigo d'akin gimbiya Aysha ta samu anty Amina tana goge mata Bakinta da tissue bayan ta gama Bata abincin data kawo mata.anty Amina ta juya tana ansa sallamarta. Hajiya inna ta k'araso d'akin hannunta rik'e da Wani jug ga extra cup a hannunta tana kallan gimbiya Aysha tace. "Sannu Aysha Allah ya K'ara Miki lafiya". gimbiya Aysha ta lumshe idonta alamar ansa mata". Hajiya inna na kallan anty Amina tace."Amina maganin Da aka kawo min ne nasa uwani ta dafa musu gashi wannan natane a jug ki fara bata tun daga Yanzu na kwana ukune duk bayan da ta ci abinci shi zakina Bata tana Sha "Anty Amina ta karb'a tace ."to shikenan inna in Sha Allah za'a na batan Allah ya Saka da Alkhairi". Inna tace. "Ameen bari naje na kaiwa sultan danshi sai dai na ajiye nasa agunnawa Ina bashi Dan Kinsan halinsa" Anty Amina tace."hakane kan inna". Inna tace. "Bari naje". Daga haka tai hanyar k'ofar fita daga d'akin anty Amina tai ta mata godiya.... Hajiya inna ce tsaye bakin k'ofar dak'in sultan tana knocking ta kusa minti Biyu tsaye .kafin ya taso ya bude k'ofar Yayi tsaye Yana kallanta yak'i ya Bata hanyar ta shiga Yana kallonta sama da k'asa."Hajiya inna ta zuba masa ido sai itama ta tsuke tata fuskar ta had'e Rai tace. "Muje ciki mana ka tsaya min aka kak'i bani hanya kana kallona". juyawa sultan yayi ya koma Cikin d'akin ya zauna nan gefen gadon Yana kallan Hajiya inna data zauna kan kujera da cup a hannunta.ta Mik'a masa tace. "Ungo wannan shanye yanzu ka bani cup d'in maganin sammu ne". Sultan ya Kalli cup d'in yaga Wani Bak'in ruwa kamar tea kamar ba Shiba sai Kuma ya kalli Hajiya inna ya girgiza kai yace. "Bazan Sha ba ni wai na ce Miki bani da lafiya ne da kullum zaki na kawomin jik'e jik'e kina cewa Nasha".ya fad'a Yana had'e Rai. Hajiya inna tai k'asa da murya tace. "Haba sultan Kasan dai bazan tab'a baka Abinda zai cutar dakai ba ko?nace Maka maganin sammu ne na Wani abun ba Ka daure kasha magani ne komai sai anayi ana daurewa". Ta fad'a tana kallansa. Sultan yace. "Nifa Inna bazan Shaba Lafiyata k'alau kullum sai kuyi ta D'ora min jinya". Hajiya inna ta marai raice tace cikin lallashi."naji lafiyar ka k'alau sultan Amma Kuma so nake ka K'ara samun wata lafiyar akan wacce kake da itan". sultan ya girgiza mata kai alamar shifa bazai shaba.hajiya Inna ta dinga lallashinsa daga k'arshe tace. "yanzu sultan zan baka Abinda zai cutar da kai ne naga kai Jini nane jika nane fa Kai wanda nake k'auna Kuma Dan bansan me nake ba sai na cutar da kai?bama fa iya kai kad'ai na bawa ba na kaiwa har babarka ma itama Kuma Tasha In Sha Allah muna sakaran samun sauk'inta" Saida sultan yaji haka tukunna ya Karb'i cup d'in daga Hannun hajiya inna ya kai bakinsa Yana Sha Yana yamutsa fuska. itadai Hajiya inna kallansa kawai take tana Jin Dad'i tareda godewa Allah data samu yaSha d'in harya gama Shanyewa ya Mik'o mata cup d'in ta karb'a tana murmushi tace. "Yauwa Mai gida Kuma Mai babban suna haka nake so Allah ya K'ara Muku lafiya Baki D'aya.Amma fa maganin na kwana ukune Mai gida duk da lafiyarka k'alau Amma inaso Dan Allah idan na K'ara kawo Maka Wani kada kacemin baza kasha ba". sultan ya gyad'a mata kai Yana yamutsa fuska saboda testing d'in maganin da babu Dad'i Hajiya inna tacce. "To kaci abinci dai ko?.nan ma sultan gyad'a mata kai yayi.tace. "to ayi azkar kafin ka kwanta Saida safe". Daga haka ta Mik'e sultan ya bita da kallo har ta fita sannan ya tashi ya kullo k'ofar ya dawo ya haye saman gadon ya kwanta Yana d'aukar handouts d'insa Yana karantawa...... HUYAAM LAMID'O AZIZ CHIROMA AFEEF *mutanan MRS SARAKIES Kuna Ina ne? ana ta payments na book d'in Huyaam ku an barku a Baya to Maza ku garzayo yanzu kar wannan garab'asar ta wuce ku*. *ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in 2270127432 Naja'atu umar Zenith bank Evidence of payment (shaidar biya )via 07066508376 Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku mutanan arziki. 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ __* *__(MRS SARAKIES )__* PAGE 2 *TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!* *Assalamualaikum mutanan arziki barkanmu da wannan lokaci* *Ina kuke manyan mata masu capacity ? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."* *To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* *1,Atamfofi* *2, lesses* *3, Abaya* *4, kayan kwalliya ko Wani iri ne* 5,*D'an kunnaye(jiwelleries)* *6,takalma* *7,hand bag* *8, mayafai* *9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*. *domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka +234 811 190 1302 /09020337676* *Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta* *Sai mun Jiku