← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 85

Sashe 1

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry WordDocument 0Table Data Normal Default Paragraph Font Table Normal No List Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD Start 12 November,2025 HUYAAM Date: Started on 18/11/2025. day Monday (The heartless love story) *NA* *___NAJA'ATU UMAR FAROOQ___* *___(MRS SARAKIES )___ daga marubuciyar littafin 1,*AURENAH* 2, *JAMI'AR TSARO* And now HUYAAM *Bismillahirrahmanirrahim* Page 1 _________ *7 April,2008* "Sannu ranki Dad'e! sannu Allah ya saukeki lafiya Mai martaba Yana zuwa tunda yanzu gimbiya Bilkisu tai masa waya"naji muryar wata yar dattijuwa tana yiwa wacce ke d'urkushe bakin gadon Dake d'akinta magana data dafashi tana wasu Irin nishi da numfarfashi tana runtse idonta tana addu'ar duk da tazo bakinta alamar tana cin wahala ba kad'an ba .adai lokacin da aka Bud'e k'ofar d'akin,Wani hamshak'in mutum na gani yashigo cikin nutsuwa bakinsa d'auke da sallama cikin shiga Irin ta sarauta idansa babu inda ya sauke sai akanta,gimbiya Bilkisu na biye dashi a Baya ta tsaya daga bakin k'ofar tana sunkuyar da kanta k'asa amma fa da kin ganta itama ba'a cikin nutsuwarta take ba saboda tashin hankali.jakadiya ta zube a k'asa ta sunkuyar da kanta cikin girmamawa tace." Barka da zuwa rankai Dad'e Allah ya K'ara Maka lafiya da Nisan kwana" ta fad'a cikin girmamawa,ya ansa mata da ka kafin ya nufi gaban gadon cikin sauri Yana kallanta cikin tausayawa idan kika kalleshi azahiri baza ki tab'a cewa Yana cikin damuwa ba saboda kamewar da yayi Dan kwata kwata azahiri Bai nuna Hakan ba.Amma Kuma cikin zuciyar sa cike take da tsantsar tausayin matar tasa,Yana k'arasawa gaban ta ya duk'a ya rungumota zuwa jikinsa Yana mata sannu cikin damuwa,dama tuni jakadiyar ta fita daga d'akin tana ganin sarkin ya shigo,cikin dauriya ta Jin jina masa kai alamar ansawa tana cije leb'e, Dan tun shekaran jiya take Nak'uda Kuma idan aka kaita asibiti suce ai har lokacin a 2Cm take ita kuma zaman asibitin ne Bataso shiyasa take cewa adawo gida. to yanzu k'arfe biyun dare ne Nak'udar ta k'ara tasar mata ganin haka yasa gimbiya Bilkisu tai k'iran Mai martaba.dan akaita asibitin. ya lumshe ido Bai juya ba yay k'iran gimbiya Bilkisu Dake tsaye bakin k'ofar har lokacin ta sunkuyar da kanta k'asa,tana jin K'iran nasa ta k'araso tana cewa" Gani rankai Dad'e". ta fad'a cikin girmamawa. inda ya D'an d'ago ya kalleta yace cikin nutsuwarsa da kamewarsa a Koda yaushe."ku kamata yanzu ku fito da ita ga mota nan a bakin part d'in nata kushiga driver zai kaiku zuwa asibitin kafin na k'araso"ya fad'a Yana mik'ewa daga kusa da ita Dan bawa gimbiya Bilkisu Daman kamata,ya juya ya fita daga d'akin cikin nutsuwa Dan zuwa part d'insa ya shirya ya biyo su zuwa asibitin Yana fita jakadiya ta shigo tana kallan gimbiya Bilkisu kafin tai magana gimbiya bilkisu ta rigata da cewa" kamata uwani mu fita da ita zuwa mota",.uwani ta.amsa cikin girmamawa inda suka saka mata hijab d'inta Babu Bat'a lokaci suka fita da ita daga d'akin gabad'aya ta k'ofar baya inda suka shigarta ambulance d'in da aka zo da ita Dan d'aukar ta , duk suka zauna suna tare da ita abayan motar suka tafi zuwa asibitin Dake nan cikin palace d'in Dan girmansa ya wuce yadda zan misalta muku shi,sai dai Wanda ya gani kawai.tun wajen k'arfe ukun dare da sukazo take na k'uda har yanzu da ake K'iran sallahn magrib Bata haihuba,sai k'arfe shida Saura Allah ya sauketa lafiya ta haifo 'yarta mace kyakkyawa kamar ita,bayan an gyara babyn itama aka gyara mejegon suka Mik'o mata 'yarta da murmushi a fuskar doc tace. "Congratulations ranki Dad'e Allah ya raya baby bisa Sunnah kema Allah ya Baki lafiya", tafad'a tana murmushi.itama murmushin ta Maida mata kafin tace. "Thank you" a saman lab'b'anta Dan Har lokacin da murmushi a fuskarta.doc ta fita daga d'akin Dan sanarwa da su gimbiya Bilkisu Dan tun da suka kawota suke waje Basu shigoba.bayan fitar doc, ta Maida dubanta kan jaririyar tata Dan tunda ta D'ora idonta akan ta taji gabad'aya 'yar ta shiga ranta da yawa,tana Jin wata iriyar matsinanciyar k'aunarta ta shiga ranta lokaci D'aya,ta tsura mata ido Bata ko kiftawa kamar Wani ne zai k'wace mata ita,sai Kuma taji Wani Irin fad'uwar gaba D'aya saukar mata lokaci D'aya da Batasan ko ta mecece ba.kafin tai addu'a ta kauda tunanin ta adai dai lokacin da aka Bud'e k'ofar ta d'aga kai ta kalli k'ofar ido hudu sukai da Mai martaba har ya shigo d'akin bakinsa d'auke da sallama ta ansa masa ya zauna kan kujerar dake bakin gadon, inda ya har lokacin idonsa Yana kanta.ta sunkuyar da kanta k'asa cikin girmamawa tace . "Barka da safiya rankai Dad'e",Dan batai tunanin ganin saba a wannan lokacin.ya D'an k'ura mata ido kad'an kafin ya saukesu kan cute babyn Dake hannunta,sai alokacin yace. "Mun tashi lafiya gimbiya Aysha?".,tai murmushi tace. "Alhamdulillah ". Ya Mik'a hannu ya karb'i babyn bayan ta Mik'o masa ita Yana kallan babyn Bai San lokacin da murmushi ya sub'ace masa ba,ya sumbaceta a goshinta Dan shima lokaci D'aya yaji babyn ta shiga ransa da yawa,ya d'ago da kansa ya kalleta kafin yace"sannu gimbiya Aysha! Kinyi k'ok'ari Allah yay miki albarka ya raya mana abinda kika haifa". Ya fad'a Yana kallanta Yana K'ara Jin Santa na k'aruwa Koda yaushe acikin zuciyarsa.tai murmushi tace. "Ameen thumma Ameen rankai Dad'e"yay murmushi ya mik'e tsaye tunowar da yay su gimbiya Bilkisu suna waje suna jiransa Daya fito su shiga,ya k'arasa har kusa da ita ya Mik'a mata babyn kafin ya duk'a ya sumbaceta a kan leb'enta yace . "I love you" a hankali,tai murmushi tace "we love you too" Ya Mik'a mata babyn kafin yace . "naji doc tace yanzu za'a sallameku?so bari na koma fada Ina da Bak'in da gansu saina shigo anjima in Sha Allah "ya fad'a Yana kallan ta .ta Jin jina masa kai kafin tace. "Allah ya kaimu, Allah ya K'ara Maka lafiya da Nisan kwana ubangiji ya kareka aduk inda kake rankai Dad'e "ta fad'a tana kallansa. Yace"Ameen thumma Ameen gimbiya".ya fad'a Yana Mai Jin Dad'in addu'ar da tai masa.daga haka ya fita daga d'akin.bayan fitarsa gimbiya Bilkisu ta shigo ita da hadimar gimbiya Aysha wacce suka kawota asibitin tare Mai suna uwani. "sunnu Yaya gimbiya!, me aka samu?kinyi k'ok'ari sosai Allah ya raya"cewar gimbiya Bilkisu ta fad'a tana murmushi tare da sa hannu ta karb'i babyn hannun gimbiya Aysha.itama uwani ta risina taiwa gimbiya Aysha barka da saukarta lafiya tareda da jero mata kirari kamar me.Gimbiya Aysha tai murmushi ta gyad'awa uwani Kai Dan Wani irin bacci bacci takeji Yana fusgarta, gimbiya Bilkisu ta kalli gimbiya Aysha fuskarta da murmushi har sannan tace. "Yaya gimbiya yarinyar nan Allah ya zuba mata kyau Masha Allah! wallahi har naji ta shiga Raina da yawa",ta k'arasa fad'a tana murmushi. Gimbiya Aysha tai murmushi itama Amma Batace komai ba, uwani ma ta karb'i babyn tana Gani ,tana ta Saka mata albarka da jera mata kirari kamar tana jinta,doc ta shigo da takardar sallama inda ta risina ta mik'a musu cikin girmamawa gimbiya Bilkisu ta karb'a tana rik'e da babyn har lokacin,uwani Kuma ta taimakawa gimbiya Aysha ta sauko daga saman gadon tare da tai makon doc suka shigarta mota ta musamman da sarki yasa aka d'auko ta Dan d'aukar su.dama already driver ya Bud'e musu motar suna zuwa shigar da gimbiya Aysha sukayi bayan gimbiya Bilkisu ta shiga sai uwani a gefenta .doc ta risina tai musu fatan sauka lafiya kafin ta koma ciki.dama already driver ya zube har k'asa ya gaida su kafin ya zaga driver seat ya shiga inda motar sai palace.. Suna isa wasu daga cikin dogaran Dake tsaron part d'in gimbiya Aysha sukai saurin d'aukar da kansu k'asa alamar girmamawa driver ya fito da sauri ya Bud'e musu motar har suka fito ya zube har k'asa Yana K'ara yiwa gimbiya Aysha barka tareda fatan lafiya ta ansa da Ameen cikin sanyin murya.suna Isowa k'ofar part d'in gabad'aya dogarayan suka zube har k'asa suna kwasar gaisuwa tareda Yi mata sannu ta gyad'a musu kai har suka K'arasa ciki,bayan sun shiga d'aki ta kwanta saman gadon tana lumshe ido alamar bacci Yana gab da d'aukar ta. Gimbiya Bilkisu ta kalle ta tace. "Yaya gimbiya bacci zakiyi?".ta fad'a tana kallanta, batareda ta Bud'e idoba ta gyad'a mata kai cikin sanyin murya tace. "Kije ki duba sultan kiga koya tashi?".ta fad'a tana gyara kwanciyar ta.sauke numfashi gimbiya Bilkisu tai tana gyad'a mata kai ta kwantar da babyn kusa da ita,ta kalli uwani tace. "Uwani a D'ora mata ruwan wanka zanje na duba sultan! idan na dawo Kuma ni zan zauna da ita"ta fad'a tana kallan uwani. Uwani ta sunkuyar da kai tace cikin girmamawa. "angama ranki Dad'e". daga haka ta fita zuwa k'aton kitchen d'in Dake part d'in ,ita Kuma ta tsurawa yarinyar ido tana kallanta Dan ji take kamar ta had'iye ta kafin ta mik'e Dan zuwa duba sultan kamar yadda gimbiya Aysha ta fad'a. Kafin Azhar gabad'aya masarautan nan ta San haihuwar da akayiwa Mai martaba,cewar gimbiya Aysha ta haihu, yawanci duk Wanda ke cikin palace d'in nan sunzo yiwa gimbiya Aysha barka tunda suka ji labari, Amma Banda shakundum d'in Mai martaba wato hajara . kuma Sarai ta ji ba Bata jiba sai can wajen yamma ta nufi part d'in gimbiya Aysha tare da rikiyar hadimanta danyi mata barka cikin izzarta da nuna mulki Irin nata da ganin tafi kowa. Tana shiga folon ta dinga k'are masa kallo Wani irin takaici da Bak'in ciki tareda hassada na mamaye mata duka Zuciyar ta tana cigaba da tafiya har suka k'arasa bakin k'ofar ta shiga har d'akin bayan D'aya daga cikin hadimanta sunyi knocking anbud'e mata k'ofar.hadimanta da suka mata rakiya suka tsaya daga bakin k'ofar Dan jiranta. Ta samu gimbiya Bilkisu da uwani Wanda suka gaisheta lokaci D'aya a d'akin ta ansa musu tana aro murmushin da Bai kai zuciyarta ba.ta zauna kan kujerar Dake gaban gadon cikin izzarta da mulki tana kallan gimbiya Aysha wacce ke murmushi tana mata barka da zuwa,cikin tsantsar tsanar da taiwa gimbiya Aysha tace Dak'yar Dan ji take kamar ta Shake'ta har saita daina numfashi tace. "Sannu gimbiya Aysha! Ashe ansamu k'aruwa?".ta fad'a tana kallan ta.gimbiya Aysha tai murmushi tace. "Wallahi fa". Ta Jin jina kai kafin Tace Dak'yar kamar wacce aka tilasta .
Chapter 1 · 0% Book details