Sashe 75
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cewa na wai ta makance.tuni ta nufeta da sauri ganin ta zube a tsakiyar falon har lokacin ihun kuka take. D'agota Fulani Salamatu tai cikin tashin hankali tana tambayar Aziza da lafiya? Aziz ta kasa magana sai ma Wani Irin kuka da take tana k'ok'arin shid'ewa.ai tuni hankalin Fulani Salamatu ya K'ara tashi ta ce cikin rawar murya "Aziza ki fad'a min Mai ya faru Maiya sameki? Da k'yar Aziza ta iya cewa "mummy yaya ne" ta fad'a tana kasa k'arasa zancen saboda Kukan Daya kufce mata.fulani Salamatu da duk hankalinta ya gama tashi lokaci D'aya tsabar rud'ewa tama kasa Gane wanne yayan Aziza take nufi ta ce "waye Kuma wani Yaya?" Aziza ta ce "ya Afeef mana" Fulani Salamatu ta ce "to Mai Yay miki? Aziza ta ce "marina yayi sannan yay ta ball dani" fulani Salamatu ta ce "Mai kikai masa yay miki wannan zalincin haka? Aziza ta ce tana sheshshek'ar kuka "Akan Huyaam ne wai Dan mum had'u a hanya nafito daga b'angaren su ikleema zan wuce ta gaban b'angaren su ita kuma sun fito ita da Huda ko Ina zasu ban sani ba kawai ta harare ni Nima na rama sannan na wanka mata Mari Ashe yayan Yana bayansu kawai ya fusgoni ya wanka min Mari har Sau uku sannan ya dinga Ball dani" ta k'arasa fad'a tana fashewa da gunjin kuka" fulani Salamatu dai kallanta kawai take tun lokacin da take Bata labarin har ta kai k'arshe. lokaci D'aya fuskar Fulani Salamatu ta sauya zuwa B'acin Rai Jin Afeef ne wai yaywa 'yarta haka ya kumbura mata duka fuska Kuma wai akan HUYAAM.bata ce komai ba saboda Tama kasa furta ko da kalma D'aya ce ,nan ta juya ta nufi sama zuwa d'akinta, Babu dad'ewa ta dawo da mayafi a ahannunta. Aziza ta mik'e ganin mommynsu ta d'auko mayafinta da k'yar ta ce "mummy Ina zaki? Fulani Salamatu ta juyo ta ce "zuwa Zanyi wallahi yau komai zai faru Saidai ya faru na gaji da cin zalin da yake Miki Aziza akan wata can zai Yi miki wannan marin ya kumbura miki fuska Bai tsaya nan ba shine harda yay ball Dake saboda ya riga da ya Raina min hankali sannan Babu Mai d'aukar mataki akai daga uwarsa har shi kansa Mai martaba saboda zalinci sannan ace ni Kuma bazan Yi magana ba ko Kuma na d'auki mataki ba, wallahi zuwa Zanyi nayi Abinda ran kowa zai Baci a gidan nan harshi kansa mai martaban sai dai yau ya sakene" tana fad'ar haka ta juya ta nufi k'ofa. Aziza batai gigin binta ba saboda karta je ta k'ara jawa manya Afeef ya K'ara mata Wani Marin.... Gabad'aya su Ammie suna zazzaune a falon Mai Huyaam sun kallo kawai sukaga an Bud'e k'ofar falon da k'arfi anshigo har k'ofar tanayin k'ara.mik'ewa sukai gabad'ayansu da sauri ganin yadda aka han kad'o k'ofar aka shigo da mamakin waye?Amma Banda Ammie wacce ke zaune tana kallon Mai shigowar, ganin Fulani Salamatu ce ta shigo tana huci kamar wata zakanya yasa Ammie mik'ewa tsaye itama cikin nutsuwa tana kallon fulani Salamatu Wacce ke mata mugun kallo tare da sauran yaran. Amma Sai Ammie ta basar tana murmushi ta ce "sannu da zuwa fulani" Wata muguwar hararar Fulani Salamatu tai mata kafin ta ce cikin hargowa "Kinga ga alamun zama ne ya kawo ni Maryam? Nace Kinga alamun zamane ya kawomini Maryam? zuwa nai gunki ba gun mahaukacin d'anki da idan haukarsa ta Motsa yake dakar min 'ya ba. Amma kafin nan bari na fara ta Kansa Ina yake? Nace Ina yake shi marar mutuncin? Ta fad'a tana dube dube a falon kamar Wanda zata ganshi.ganin baya nan yasa ta ce da sigar warning"nazo ne na tuna masa matsayin wannan a golar yarinyar nan agidan nan da yake fifita ta akan Aziza idan har shi ya manta to ni bari yau na tuna masa" ta fad'a tana nuna Huyaam.a tare Ammie dasu ya Zarah da Huda suka kalli HUYAAM wacce fulani Salamatu ke nuna ta da yatsa.itako Huyaam Kallan fulani Salamatu kawai take tana nazarin zancen ta.Ammie ta juyo tana kallon Fulani Salamatu gabanta na Wani Irin fad'uwa lokaci D'a ya Jin zancen da fulani Salamatu tazo musu dashi yau a b'angaren nata.da k'yar Ammie ta iya had'a kalamanta ta ce "Fulani Mai kike fad'a Haka ne, waye matsayin su ba D'aya da Aziza ba Agidan nan? Fulani Salamatu mata tai Wani murmushi Jin abinda tazo dashi ya fara karyar wa da Ammie zuciya ta ce "wacece Kwa idan ba Agolar gidan nan ba ko akwai wata Agolar ne bayan ita wacce aka fifita ta akan 'yar gidan har ana Neman akashe 'yar masu gida akan ta" sai Kuma ta Wani tafe hannu ta ce "Au mantawa nai,Ashe fa har yanzu Baku fad'a mata ko ita wace ce a gidan nan ba ko? Da aje a kashemin 'ya akan agola gara ni nazo na fara sanar mata da matsayinta Agidan nan" ta fad'a tana kallan Huyaam.Ammie da ranta ya fara B'aci lokaci D'aya Irin Wanda bai tab'a B'aci ba ta ce cikin tsawar da batama San taiwa Fulani Salamatu ba "Fulani Mai ya faru haka ne da zaki zo kinayin wad'an nan magan ganun marasa tushe a gidan nan Dan Allah? Ta fad'a tana kallanta.Fulani Salamatu zata K'ara magana kuma Ammie tasan ba alkhairi ne zai fito daga bakin ta ba yasa ta ce "Dan Allah kiyi shiru muje b'angaren ki muyi maganar" Fulani Salamatu tai Wani murmushi ta ce "Babu inda zani agaban kowa Za'a yi wannan maganar.wato bakya son yarinya tasan matashin tasan ko wacece ita a gidan nan bane kome?To idan Baku fad'a mata yanzu ba yaushe kuka shirya fad'a matan, ko sai anzo Neman Auren ta tukunna? Ta fad'a tana kallan Ammie ido cikin ido ganin ta kasa magana.Su dai su yay zarah kalllan Fulani Salamatu kawai suke gabansu na fad'uwa suna k'ok'arin fahimcitar inda zancenta ya dosa ganin Ammien su tayi shiru tak'i magana hakama Huyaam da duk take cikin compused d'in zancen Fulani Salamatu.ganin duka yaran sun rud'e sannan itama kanta Huyaam d'in Bata fahimci zancen taba yasa fulani Salamatu ta Kalli HUYAAM ta ce "Kinga yarinya bari na fad'a miki Abinda ake ta b'oye b'oyen fad'a miki shekara da shekaru,ke ba 'yar gidan nan bace ba agola ce.Fulani Maryam da Mai martaba ba su suka haife kiba kamar yadda kike tunani ba" ta fad'a tana kallanta.Huyaam dai kallanta take Bata ko kiftawa tana nazarin zancen ta. Haka ma falon yayi d'iff kamar Wanda ruwa ya cinye...Jin muryar Afeef sukai Wanda tunda fulani Salamatu ta fara gayawa Huyaam ko wacece ita ya sauko stairs d'in Dan hayaniyar ta ce ma ya fito dashi daga b'angarensu Dan Yana zaune a falonsa yana Aiki a laptop kawai ya juyo magan ganun Fulani Salamatu a tsakiyar kansa, Hakan yasan ba lafiya ba,Babu shiri ya fito yaga mai ke faruwa.wata uwar tsawa ya dakawa Fulani Salamatu Yana nuna ta da yatsansa ya ce "ya isheki haka" da wata iriyar murya Lokaci D'aya idonsa ya kad'a yay jajir jijjiyoyin kansa duk suka fito rad'o rad'o yana cigaba da tafiya har ya k'arasa shigowa falon yana nuna mata kofa yace "gate out before I loss my control malama" Fulani Salamatu tana masa Wani kallo ta ce "bazan fita ba,duk abinda na fad'a k'arya nai koba Kaine ka tsintota ba? ka tsintota ka kawo ta nan gidan ko na ba haka akai ba? Ta fad'a tana masa Wani Irin kallo.Afeef dai kallanta yakeyi kirjinsa na bugawa sama da k'asa Yana Jin kamar ya shak'eta saboda irin abinda yakeji. Fulani Salamatu ta tafe Hannu ta ce "ko kasan asalinta idan k'arya nai saika fad'a" sai kuma ta k'ara masa Wani kallo ta ce "waya sani ma ko shigeya ce Bata da uba akai cikin ta aka jefar Dan kada asirin uwar ya tonu kai Kuma ka d'auko ta ka kawo ta gidan nan? kai shegiyar ce ma tunda nidai har yau Banga Wani nata da ya neme taba" ta fad'a tana kallan Huyaam wacce ke kallanta Bata ko kiftawa Jin abinda take fad'a. Afeef ya d'aga hannu zai Mari Fulani Salamatu jikinsa na karkarwa adai dai lokacin da Mai martaba Wanda tun d'azu ya shigo falon Amma babu Wanda yay noticing yay gyaran murya.gabad'aya suka juya suna kallan sa har Fulani Salamatu wacce zufa ta yanko mata lokaci D'aya ganin Mai martaba nan ta sunkuyar da kanta k'asa gabanta na fad'uwa tana salati tana sallallami..ihun Huda kawai sukaji tana K'iran sunan HUYAAM lokaci D'aya tai kanta.Ai a sukwane Afeef ya juya Ganin fad'uwa zatai yay sauri ya tarota zuwa jikinsa tun kafin taje k'asan, Ammie ma tai kanta tana fashewa da Kuka tare da K'iran sunanta....... A masarautar zazzau kuwa yanzu haka k'arfe biyu da mintuna ne na Dare.Shakunmdum na tsaye a tsakiyar d'akinta waya ce kare a kunnanta bayan ta gama shirin ta tsaf na b'adda kamar da tai Dan zuwa b'angaren gimbiya Aysha dan aiwatar da aikinta.idan ba k'ura mata ido kaiba baza ka Gane mace ce ita ko kuma namiji ba saboda yadda tai shigar Dan babu Wanda zai iya Gane ta.waya ce kare a kunnanta da sukeyi ita da barzuk.tana zagaye inda take tsayen kafin ta dakata ta ce "na Gane uban gida yanzun nan zan tafi" daga can b'angaren Barzuk ya ce "Babu kuskure acikin aikin Fulani idan kuma Kika sake kika kuskure D'aya daga cikin abinda muka fad'a miki asirinki zai iya to nuwa Kuma Babu ruwanmu" shakundum ta ce cikin Tabbaci "bama zan kuskure ba uban gida" barzuk ya ce "Sa'a taki Fulanin zazzau" shakundum ta ce "godiya nake uban gida" daga haka ya kashe wayar itama sauke ta_ta ta d'auki abinda zatai aikin dasu ta nufi k'ofar fita daga d'akin.Bud'e k'ofar tai a hankali ta fito tana tafiya a hankali harta nufi stairs cikin sand'a tabi ta k'aramar K'ofar ta fice daga falon gabad'aya Babu Wanda ya ganta.Harta gama ficewa gabad'aya.da bin bango take tafiyar Dan kada Wani ya ganta tai b'angaren gimbiya Aysha da sauri...zube ta tadda duka dogarayen b'angaren gimbiya Aysha kwance suna bacci bayan ta isa da kuma tai Sa'a babu Wanda ya ganta..Wani numfashin salama ta sauke a hankali ganin ta isa part d'in.cikin sand'a ta bi ta Baya ta k'aramar