← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 85

Sashe 45

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Bismillahirrahmanirrahim* ____________ K'arfe 10am Saura na safen ranar Wednesday AFEEF ya fito daga Wani k'aton bedroom room dake cikin k'aton gidan Abban nasu dake garin Lagos Wanda ke kusa da companyn motocin da lamid'o ke jagorantar companyn.tafiya yake cikin nutsuwa zuwa cikin k'aton falon gidan.sanye yake cikin k'ananun kaya riga da Wando,rigar farace K'al Mai layi layin Bak'i sai Wandan Daya kasance Bak'i kayan sun masa kyau ba kad'an ba tamkar ki sace sa ki gudu.dan tunda yazo garin Lagos agidan ya sauka kuma kullum saiya fita yaje companyn Mai martaba sai dare yake dawowa gidan shida lamid'o,har yau Daya kasance Ranar wednesday da yay dai dai da kwanan sa biyu a gidan.tsakiyar falon ya ya tsaya bayan ya k'araso ya tsaya Yana k'arewa sauran bedroom d'in Dake cikin k'aton falon kallo,a d'akin Daya kasance na lamid'o ya tsaida idonuwansa akai Yana kallo kamar Wanda zaiga ma mallakin d'akin ya fito daga cikinsa, d'auke kansa yayi ya cigaba da takawa har ya k'arasa dining d'in tunowa dayay lamid'o ya fita tun Wajen k'arfe 9 na safen ya shigo har bedroom d'insa yay Masa sallama akan ya fita saboda urgent call Daya samu daga companyn. sauke numfashi yayi yaja kujera ya zauna Yana zube wayoyinsa nan Saman table d'in.kafin Yasa hannu ya Bud'e wasu tsadaddun wamers yana ganin abinda aka girka for breakfast.rufe Sauran warmers d'in yayi ya bar D'aya Wanda aka dafa masa abinda aka San shine favorite d'insa a breakfast ya d'ibi abinda Yay masan Dan dama tunda yazo gidan da workers d'in suka tambaye shi me yakeso adinga girka masa d'in ya fad'a musu abinda yake so to shine tun daga nan suka San abinda zasu girka masa fo breakfast and dinner Wani time d'in ma baya dinner saidai kawai yasha tea or coffee ya kwanta .bayan ya gama breakfast d'in ya Mik'e Yana gyara hannun rigarsa .d'aya daga cikin masu musu girkin gidan ne ya fito daga kitchen d'in sanye yake da rigar girkin cikin sauri ya k'araso wajen da Afeef ke tsaye ya risina yace. "Sir good morning". Ya fad'a cikin ladabi Afeef ya ansa masa ba tare da ya kalleshi ba.kukun yace."sir! you need anything?. Afeef ya d'ago da kansa ya kalleshi kafin ya d'auke idansa akansa yace. "Nothing". Izic ya duk'ar da kansa cikin girmamawa ya bar wajen ya koma kitchen d'in dama goge goge yakeyi.... Afeef kuma ya d'auki wayoyinsa ya fito daga falon gabad'aya zuwa compound ma'aikatan gidan sai faman gaida shi suke cikin ladabi Yana ansa musu.motarsa Daya zaba yake fita acikinta tunda yazo aka fito masa da ita,an wanke masa ita sai faman shining takeyi ya k'arasa ya shiga ya ta-da motar.tun kafin yayi horn gate man d'in ya wangale masa gate ya fita da motar gabad'aya direct companyn nasu ya wuce Wanda tsakanin sa da gidan da suke ciki baifi 5 kilo meters ba..... Daya isa companyn ya tarar Lamid'o Wanda dama already Ya iso Yana cikin office d'insa tare da wasu abokan bussness d'insu da suka zo siyan motor Dan duk idan garin Allah ya waye sai anzo an Siyan motoci a wannan companyn nasu Kuma ba D'aya ba biyu ba Sannan kar kice k'ana nun mutane ne suke Zuwa su Siya, a'a manyan mutane ne Wanda kud'i ya gama ratsawa ke aikowa asiya musu wasu ma da kansu suke zowa Dan aka ce zuwa da kai yafi Sak'o tunda babu Wanda Bai San companyn motocinsu a fad'in Nigeria ba Wanda ke garin lagos ba.Wanda saboda kyau da quality kayansu yasa ake San siyan motoci a wurinsu nasu... Saida mutanen suka ragu sosai sannan lamid'o ya taso ya K'araso inda Afeef ke Zaune a Wani D'an falo Dake cikin office d'in ta ciki Wanda falo biyu ne awurin.nan suka zauna da Afeef suka cigaba da aikin Daya kawo afeef d'in na sabbin tsare tsaren da za'a yiwa company da Kuma abubuwan da ake buk'ata yadda idan ya koma Ingiland za'a parking komai na wannan companyn yadda idan ZA'A Aiko sai a Aiko dasu completely Batare da sauran Wani Abu ba.sun kusan 5 hours suna Zaune suna tattaunawa sallahn Azhar ne kawai ya ta-da su suka d'auro alwala suka tafi masallacin Dake cikin companyn..... K'arfe 3 Saura na yamma su Huyaam har sun gama shirin tafiya islamiya suna tsaye a falon ko Wacce Tasha hijab har k'asa ga face mask a fuskarsu saboda yanayin garin hannunsu rik'e da bag d'in islamiyar tasu muneefa suke jira itace kawai Bata fito ba Babu dad'ewa kuma suka sauko downstairs d'in tare da Ammie data rakota suna saukowa Huyaam ta kama hannunta sukai wa Ammie sallama.Ammie tai musu fatan dawowa Lafiya sannan ta wuce kitchen d'in. ansa mata sukai suka fita daga falon gabad'aya.fitowar su Kenan daga b'angaren nasu ko k'arasawa wajen motar Dake jiran su Basu yi ba kawai Huyaam taji kanta ya Wani Irin Sara mata da k'arfi kamar Wanda aka doka mata guduma akan natan, lokaci D'aya Kuma taji kamar ansha k'e mata wuya da hijab d'in jikin nata tamau Wanda harta Kai ga ta fara kokawa da lumfashinta saboda azaba lokaci D'aya ta saki hannun muneefa at the same time Kuma taji kamar an jawo ta ta baya, tai taga taga zata Fad'i kiris ya rage taje k'asa ya Zarah Dake bayan tai saurin tareta tana kallan tace cikin Damuwa. "Me ya faru Huyaam?..."Amma Ina Huyaam Bata jinta saboda yadda aka shak'e mata wuyanta ga idonuwanta dukan sun fir fito waje sai Kowa take da numfashinta.take ya Zarah ta rikice ta fara K'iran sunan HUYAAM cikin kid'imewa .wannan abinda Huyaam take yasa muneefa tasa ihu ganin Huyaam tana rik'e da wuyanta gashi ta kasa magana lokaci D'aya zufa ya keto mata .Huda da har ta k'arasa wajen motar ta juyo ihun muneefa Haka nan ta dawo wajensu da sauri cikin tashin hankalin abinda ta Gani ta fara tambayar ya Zarah da Mai ya faru? Ya zarah bata samu damar ansawa Huda tambayar taba saboda itama kanta a rikicen take da lamarin Huyaam.Su ikleema da safna suka k'araso suma gunsu da sauri suna tambayar lafiya? ya Zarah ta Kalli Huda cikin tashin hankali tace. "kamata mu kaita gida". Cikin sauri Huda ta kamata suka su nufi b'angarensu, ikleema kasa binsu tai hakama safna suka tsaya suka bi su ya Zarah da kallo saboda Suma kansu sun tsorata da lamarin Huyaam d'in. Salima ce ta k'araso gurin ganin su ikleema tsaye sunyi carko carko tace. " Ku Kuma me kuke jira anan da Kuka Wani ja kuka tsaya Baku shiga motar ba?ku taho mu tafi time na tafiya". Ta fad'a tana k'ok'arin k'arasa wajen motar.jiki a Sanyaye Ikleema tace. "Ya salima su ya Zarah muke jira". Salima tace cikin har zuk'a. " Wai dama Basu fito ba gashi lokaci sai tafiya yakeyi?".safna tace. ".sun fito Huyaam ce Babu lafiya shine suka tafi su kaita gida". Salima ta tab'e Baki tace. "Allah ya sawak'e to mudai ku taho a kaimu in yaso a dawo a d'aukesun daga baya Dan lokaci Yana tafiya, kuma ma ba musan Wani lokacin zasu d'auka kafin su fito ba".. Aziza tai gaba ta shiga motar tana cewa gaskiya dai ya Salima gara dai mu akaimun.ikleema tace. "A'a ya Salima Baza mu tafi ba mudai jira sun tukunna"..salima ta harareta tace. "Sai dai ke ki jira sun Amma ba Salima ba". Ta kalli driver tace. Kaga muje mu ka kaimu Dan time na tafiya".dogarin Dake musu rakiya ya duk'ar da kansa k'asa yace cikin girmamawa. "Ranki Dad'e da ki d'anyi hak'uri mu jira sun dai koh? ko Kuma Wani yaje ya gano mana halin da take ciki, Amma kimin afuwa idan na Fad'i ba dai dai ba". Ya fad'a Yana risinar da kansa k'asa.Salima ta wulla masa Harara tace a fusace."da kai nake da zaka Sako mun wannan k'azamin bakin naka ina magana?.naga da Wanda zai tuk'amun nake". Mutumin ya d'ago Ya kallate da mamakin abinda ta fad'a masa Dan wallahi ya kusan haifarta idan Bai haife taba. " Sai Kuma ya sauke idonsa k'asa yace. "Kiyi hak'uri Ranki dade". Salima ta sake wulla masa Harara sannan taja tsaki.sai Kuma ta kalli driver dashima yay shiru ya kama kansa tace. "Kai kuma inai Maka magana bakai magana ba kai shiru kamar gunki ko kaima kai mun ne baza kai ba? Idan kaima baza ka kaimun ba sai ka fad'a min". Ta fad'a cike da gadara.Driver ya girgiza kai yace. "Ba haka bane ranki Dad'e Amma da kin bari dai munga zuwa anjima idan Basu fito ba sai mu kaikun Dan kada Muyi laifi".mamaki ya kama salima Jin yadda suke mata gaddama gabad'ayansu.Sai Kuma can tace cikin takaici". Wai har ni Ina fad'a Maka Abu kana fad'amin yadda za'ayi".ya duk'ar da kansa yace cikin ladabi. "Kiyi hak'uri Ranki Dad'e" Salima tai tsaki tace. "To ka wuce mu tafi idan ba so kake ranku ya B'aci ba". Babu musu driver ya zaga sai shiga driver seat saiga ya zalaihat nan ta k'araso wajen Dan itama hadda ita za'a tafi islamiyar. ya Bahijja ce dai dama tunda aka kawo lefanta tace Bazata Kar'a zuwa islamiya ba.ya zulaihat tana kallonsu D'aya bayan D'aya Ganin yadda suke tsaye har lokacin Basu tafi ba iya K'annen su k'ana nun ne kawai ke cikin motar sai Aziza tace."au Ashe ma Baku tafi ba? ni har nake cewa na makara nasan ma Kun tafi k'ila sai dai idan ankai ku a dawo a kaini". Ta fad'a tana kallan su.salima tai saurin cewa yanzu za'a kaimu wai kinsan Huyaam ce Bata da lafiya bayan har sunzo nan shine wai sai mun jira sun dawo saimu tafi ga lokaci sai k'urewa yakeyi shine ni Kuma nace kawai mu tafi a dawo a d'aukesu daga baya, shine fa wai wad'an nan 'yan rainin hankali bayin sukace wai lallai sai dai mun jirasu". Ta fad'a tana wani hararar dogarin da driver da suke tsaye har lokacin.mamaki ya kama ya zulaihat ganin Wad'an da Salima kewa Rashin kunya ita d'aukar tama Koda su safnah take ashe wai da Wad'an nan dattijan take haushi ya kama ya zulaihat ganin yadda suma suka d'ago suna kallon Salima yadda ta ci musu fuska. ya zulaihat ta rasa me zata ce mata kawai ta wanke salima da Wani gigitaccen Mari tana nunata da yatsa tace.
Chapter 45 · 0% Book details