← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 85

Sashe 63

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana saka igiyar ta kalminta, Dan Anty khadija ta ce su shirya zasu fita unguwa su Huda har sun shirya sun fita can main falor ita kawai suke jira.bud'e k'ofar d'akin akayi bayan anyi sallama d'agowa tai daga duk'en da take bayan ta gama Saka igiyar ta kalmin ta Mik'e tana kallan Siyama data shigo d'akin tun kafin tai magana Huyaam ta ce "Gani nan na gama" daga haka ta d'auki hand bag d'inta da wayarta tabi bayan siyama Data fita daga d'akin ta kullo k'ofar gabad'aya ta sauka downstairs.acan ta Tarar da Anty khadija tana tsaye tare dasu Huda iya Hassan da Hussain ne kawai banda su za'a, sai imaan wacce da ita za'a tafi da dukan alamu ita kawai suke jira.sauke numfashi Anty khadija tai tana kallansu ta ce "ku wuce mu tafi ko? Driver na jiranmu" k'ofar falon suka nufa Anty khadija tabi bayansu har zuwa compound inda driver ke jiransu.siyama ce agaban motar sai Anty khadija da imaan sai Huda da Huyaam ne a bayan motar, ahaka driver Yaja Motar suka bar gidan gabad'aya ya nufi inda aka bashi instruction d'in zuwa.... Awani k'aton mall Dake garin Abuja driver yay parking suka fito gabad'ayansu suka tsaya suna jiran Anty khadija Dake magana da driver.kallansu tai bayan ta k'araso gunnasu ta ce "muje" gaba sukai tana binsu a Baya Saida suka shiga ciki sannan ta ce su fara zuwa wajen gown kowa ya zab'i irin wacce yake so da takalma da hand bag da dai duk abinda suka Gani indai suna so su d'auka, godiya sukai mata nan suka wuce b'angaren dogayen riguna ita Kuma ta kama hannun imaan suka wuce b'angaren jewelleris...sunyi siyayya ba kad'an ba Dan su da farko kad'an suka d'auka kayan Saida Anty khadija ta k'ara musu komai da kanta ganin 'yar siyayyar da Sukayi Bai taka Kara ya karya ba.bayan ta gama tai musu magana nan suka bar wajen suka nufi wajen cashier.kayane ta Siya musu ba kad'an ba masu bala'in kyau da tsada. fitowa sukai daga cikin Mall d'in gabad'aya bayan Anty khadija ta biya kud'in, D'aya d'aga cikin workers d'in Mall na biye dasu da kayan siyayyar da Sukayi har zuwa wajen motar su driver ya Bud'e masa boot d'in motar ya zube kayan gabad'aya aciki sannan ya koma cikin mall d'in bayan Anty khadija ta sallameshi.. fitowar sa Daga cikin motar sa kenan bayan ya kulle Motar, tafiya ya farayi a hankali zuwa interance d'in Mall d'in, tsayawa yayi cikin fad'uwar gaba Yana kallan Wacce har yau fuskarta ta kasa goguwa a kwanyar kansa ko a mafarki idan ya ganta saiya Gane ta Saboda Irin yadda ya haddace kamanninta Kamar karatun sallahr sa. tunda suka fito daga cikin Mall d'in nan yake kallansu daga nan inda yake tsayen baya ko kiftawa har suka k'araso wajen motar ta su, zuwansa kenan shima cikin mall d'in zaiyi siyayya kallanta Kawai yake Wanda ita batama San Yana Yi ba suna tsaye kusa da motar suna k'ok'arin shiga ciki Dan gabad'aya hankalinta da nutsuwarta Yana tare da 'yan uwanta, har su Huda dasu ma Basu lura dashi ba. shiko yayi nisa a shagalar da yayi da kallanta har suka shiga cikin motar driver Yaja suka bar wajen.sai alokacin ya dawo sense d'insa cikin Sauri ya juya zuwa inda yayi parking motarsa ya shiga yabi bayansu da sauri...... Tafiya sukai Mai D'an tsayi kafin yaga sun isa unguwar tasu har zuwa k'ofar gate d'in gidan, inda yake Kyau tata zaton nanne gidan nasu.gidan ne dai Wanda kwanaki ya biyosu ranar da suka had'u a park shine dai suka zo driver ke k'ok'arin shigar da motar ciki. sauke numfashi yay Yana Zaune a cikin motar sa inda yayi parking a can bakin titin shigowa layin nasu daga can gefe yadda baza su tab'a ganin Saba ko Kuma Wani ya farga da cewar binsu yake ba.Saida yaga sun shiga har cikin gidan security sun rufe gate d'in sannan yay zooming up ya bar wajen ya wuce Wani masallaci Dake nan cikin unguwar ganin ana k'ok'arin shiga sallahn magrib.... Wajen k'arfe 9 Saura na dare suna zaune a d'akinsu Tun bayan da sukai dinner suka hauro sama Suka mak'ale a d'akin shine basu koma downstairs d'in ba.hira kawai suke suna dariya gabad'ayansu harda rik'e ciki HUYAAM ta ce tana dariya "Dan Allah ya isa haka siyama karkisa cikina ya k'ulle aini kece kike ban dariyar ma bawai Shi Wanda kike bamu labarin ba, dan yadda kike acting kad'ai zai sa mutum ya sume saboda dariya" siyama zatai magana wayar Huyaam tai ringing alamar shigowar k'ira.juyawa tai tana kallan Mai K'iran take ta daina dariyar da take Yi ganin number Aziz ne,nan ta had'e Rai siyama Dake kallanta ta ce "waye" Huyaam ta ya Mutsa fuska kamar zatai kuka ta ce "wa kika sani?" Huda ta ce "ya Aziz ne ko Abdallahn? Juya musu secreen d'in wayar tai tana nuna musu.kallan screen d'in siyama tai kafin ta rik'e hab'a ta ce "iKon Allah wai Yaya Aziz da soyayya da Huyaam! nifa har Yanzu ganin abun nake kamar a mafarki wallahi,badan kin fad'a mana ba da bazan tab'a yadda ba?" Huyaam ta harareta ta ce "ni karki K'ara Dan gan tani dashi yanzu ma Dan mommy ta ce ne na daina wulakanta su Amma badan haka ba wallahi da ko mutuwa zasuyi bazan tab'a sauraran suba" ta fad'a tana hararar siyama. Huda ta ce "to kiyi maza kiyi picking karta K'ara katsewa bakiyi ba" nan ma wata uwar hararar ta k'ara makawa Huda kafin tai picking call d'in tana k'unk'uni bayan ta katse an K'ara K'ira a K'aru na biyu.shiru tai tana sauraransa har ya gama zancensa uffan Bata ce masa ba sai ma Wani hararar wayar da take yi.ganin tak'i yin magana yasa Aziz ya ce mata bari ya k'yaleta ko bacci take ji? Cikin k'aguwa ta ce masa "eh" a d'ad'are .murmushi yayi bayan yadda yaji ta ansa masa a cunkushe ya lumshe ido ya Bud'e lokaci D'aya yana Jin wutar sonta na ruruwa a azuciyarsa nan ya sakar mata wani Irin kiss Mai ratsa duka sassan jiki da barg'o a wayar, saurin janyewa tai daga kunnen ta tana jefar da wayar nan Saman gadon jikin razana tana dafe k'irji tareda zare ido Lokaci D'aya Dan abin yazo mata a bazata.mai Huda da siyama zasuyi In ba dariya ba Huyaam ta ce kamar zatai kuka "wato dariya ma kuke mun ko? Siyama ta ce tana rik'e dariyar ta "a'a mu mun Isa ni abunda kikai ne Yaban Dariya" Huda tana tsagaita dariyarta ta ce "wallahi Nima dama haka ya Aziz ya iya kiss? Huyaam ta ce har lokacin gaban ta Bai daina fad'uwa ba "iskanci dai ba kiss ba, sai ma na K'ara d'aga K'iran nasa bare ma harya samu damar K'ara yimin Haka.wai kinsan shima wannan Abdallahn d'azu bayan magrib ya K'irani bayan nayi picking wai ya shigo layin mu Yana ma k'ofar gidan mu wai zai iya zuwa har gida ya ganni?" Ta fad'a tana kallan su Huda.siyama tai saurin mik'ewa zaune tana cewa."k'ofar gida Kuma?to dama yasan gidan ne ko ya_ya?" Huyaam ta ya Mutsa fuska ta ce"wai d'azu da muka je shopping ya ganmu mun fito daga cikin Mall shine ya biyo bayan mu to anan yaga gidan,Kuma Kinsan ba tun yau yasan gidan ba wai tun time d'in da muka je park d'in nan? to wai ranar ma ya biyo bayan mu anan yaga gidan". Huda ta ce "iKon Allah ke Kuma Mai kika ce masa? Huyaam ta Wani kalleta ta ce "me kuwa zance masa haka nace wallahi ko ya bar k'ofar gidan ko Kuma na fito nai Masa ihu nace b'arawo ne a kamashi" ta fad'a har tana tura Baki gaba.siyama tai dariya Mai isarta kafin ta tsagaita ta ce "wallahi Huyaam Allah ya shirye ki ni ban tab'a Ganin mace Irin kiba ace ana sonki amma kidinga jawa mutane Ra'ayi wallahi ni har sun fara bani tausayi daga ya Aziz d'in har shi Abdallahn duk da shi bansan Shiba Amma wallahi tausayi yake bani yadda yake damuwa akanki da baya ma tab'a yin zuciya duk kuwa da Irin Rashin mutuncin da kike masa" Huyaam ta sauka daga saman gadon tana yiwa siyama Wani Irin kallo ta ce "koba tausayi ba? ke idan sun miki basai na had'a Kuba" siyama ta harareta ta ce "Allah ya sawak'e aike suke so bani ba" Huyaam tai Wani dariya har tana tafe hannu ta ce "Indai kina sonsu ni Kuma zan had'a ku Kinga shi Kenan na Rabu da k'aya sai kuje can mu k'arata keda su" daga haka ta nufi hanyar toilet d'in tana dariya ganin yadda siyama ta rarumo filon Dake kusa da ita zata jefa mata .tuni HUYAAM ta goce tana dariya ta ce "ai gaskiya na fad'a ko ba haka na Huda?" siyama ta K'ara daukar Wani filon ta jefa mata tana cewa Allah ya sawak'e...... ___________ *Bayan kwana biyu* Yau satin su Huyaam uku a Abuja ayau Kuma suke shirye shiryen komawa gida kano. gabad'aya jikin siyama yayi sanyi Dan har Wani zazzab'i zazzab'i ne ya ke Neman rufeta saboda zatai kewa ba kad'an ba, Dan zuwan su Huyaam ba k'aramin Dad'i taji ba, ji take kamar karsu koma Inama su zauna tare su cigaba da zama a Abuja,Amma tasan Hakan ba bazai yuba dole sai sun koma d'in.. Zaune take a gefen gadon tayi tagumi tana kallan yadda suke had'a kayan su a cikin trolling su suna k'ok'arin zipping d'insu.huyaam ce da itama jikinta duk yayi sanyin ta K'araso kusa da siyama ganin yadda ta zuba uban tagumi kamar wacce akayiwa mutuwa.ta zaune a nan gefenta ta dafa tana kallan tace cikin sanyin murya "Haba siyama meye hakan? ba zakuzo bikinsu su Yaya zulaihat ba in the next 2 weeks ba,Dan Allah kidaina damuwa ai zamu had'u Kuma idan kuka zo ba Zaku Dad'e ba kafin ku koma? Dan Allah ki sauke wannan tagumin da kikayi" ta fad'a tana cire Hannun siyama Dake Kuncinta tana mata murmushin k'arfin hali Dan ita ji take kamar ta saki Kukan.sauke numfashi siyama tai ta kamo hannun Huyaam tana kallanta sai Kuma ta ce cikin rawar murya"wallahi ji nake kamar karku tafi Dan Allah ku zauna" ta fad'a tana matse k'wallar
Chapter 63 · 0% Book details