← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 85

Sashe 65

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__* *__(MRS SARAKIES )__* My channel link https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 3 ___________ Washe gari da safe wajen k'arfe shad'aya da Rabi na safe, Huyaam na zaune a main falon gidansu kusa da ya Haidar da yake Aiki a laptop d'in shi sai surutu take masa tana bashi labarin Irin wuraran da suke just for enjoying a Abuja Dan har wannan park d'in da suka je babu abinda ta manta Bata fad'a masa ba,ya Zarah dai tana zaune a gefe tana kallan yadda HUYAAM Bata tab'a gajiya da Bada labarin nan Dan Suma jiya da daddare Saida ta Basu labarin hadda Ammie kafin su kwanta bacci ta ishesu da surutu,to Shine Yanzun ma take sake bawa ya Haidar labarin.d'agowa da kansa ya haidar yayi daga kan laptop d'in nashi Yana kallan Huyaam Cikin k'osawa da surutun da take masa ta k'yale shima da pressure na aikin Dake kansa ma ya isheshi ya ce "to naji yanzu dai Dan Allah ki barni haka na k'arasa aikin da nakeyi kinji?" Ya fad'a Yana kallanta .tura Baki tai gaba tana wasa da yatsun hannunta ta ce "to Yaya zaka kaimu ko sau D'aya ne ance a kano ma akwai?" Rungume hannunsa Yay a k'irjinsa Yana kallanta kafin ya ce "ai dama nasan abinda zaki fad'a daga k'arshe Kenan na kaiku Toni banida da wannan time d'in" marai Rai ce masa tai tai k'asa da murya ta ce "Dan Allah Yaya?" Hararar ta yayi ya ce "tashi ki bani waje kafin nai ball Dake anan" mik'ewa tsaye tai tana tura Baki gaba tare dasa kukan k'arya ta haye sama da sauri har tana had'awa da gudu, ya haidar ya bita da kallo yay k'wafa kafin ya d'auke kansa ya Maida kan laptop d'in gabanshi.ya Zarah tai Murmushi ta ce "aikuwa yanzu zaka ga Ammie ta zo gunka tunda ka tab'a mata ita" Wani Irin kallo ya wullawa ya Zarah kafin ya d'auke kansa baice komai ba ya mik'e hannunsa rik'e da system d'in na shi ya wuce b'angaren su Dan ya k'arasa aikin nasa acan.ya Zarah ta bishi da kallo....in the next day .shirye shiryen bikin su ya zulaihat kawai akeyi Dan yau bikin baifi Saura sati D'aya da kwana hud'u ba, shiri ake na musamman more especially daga b'angaren Hajiya Lubabatu Dan ita wannan bikin ta d'auke shi da matuk'ar muhimmanci saboda zata aura da first daughter d'in tane, gayya kan Babu Irin gayyartar da batai ba k'awayenta matan masu kud'i da masu kud'in kansu duk ta gayya cesu. Hajiya Aysha itakan baiwar Allah shirin ta take a hankali cikin nutsuwa Bada wata Baragada ba, kuma komai zatai saitayi shawara da Ammie saboda tace Ammie ai itace uwar zulaihat ba ita ba,itako Hajiya Lubabatu tare suke k'ulla komai ita da Fulani Salamatu duk da ba ko Wani Abu take Sako ta aciki ba Amma Kuma saboda ita makira ce tasan ta kan duniya ta iya zaman ta da kowa saita ta dinga nuna ma Fulani Salamatu komai idan zatai saita nemi shawarar ta..Yanzu haka k'arfe hud'u da Rabi ne na yamman Ranar Laraba, ya Zarah ce ta sauko downstairs d'in cikin shirin fita da dukan alamu dai fita zatayi, tana kallan Huyaam da Huda da suke zaune a falon suna kallan screen d'in wayar Dake hannun Huyaam da dukan alamu d'aya ne yake nunawa D'aya Abu acikin wayar.maganar da ya Zarah tai musu ne yasa suka d'ago da kansu a tare suna kallanta ta ce "acikin ku waya gyara mun d'akina d'azu da safe?" Huyaam ta ce "nice" ya Zarah ta ce "Ina kika samun ATM d'ina Dana ajeye akan mirror? Huyaam ta ce "nasa miki cikin hand bag D'inki?" Ya Zarah tace "jeki d'auko min" mik'ewa Huyaam tai tana bawa Huda wayar Hannunta sannan ta wuce stairs d'in Babu dad'ewa ta dawo rik'e da ATM d'in ta Mik'awa ya Zarah,karb'a ya Zarah tai ta nufi hanyar k'ofar fita daga falon Ganin fita zatai yasa Huyaam ta d'aga murya ta ce "ya Zarah Ina zaki?" batare da ya Zarah ta juyo ba ta ce "inda kika aikeni" daga haka ta fita daga falon gabad'aya,kallan Huda Huyaam tai ta rik'e hab'a ta ce "ko Ina zata oho?" Huda ta Bud'e hannuwanta alamar itama Bata sani ba.sauke numfashi Huyaam tai nan suka Maida hankali kan abinda suke kallo a cikin wayar sunyi nisa da abinda suke. Ammie ce ta Sauko downstairs d'in ta k'araso har tsakiyar falon tana kallansu ta k'ira sunansu .d'agowa da kansu sukai a tare suna ansa mata . Ammie ta ce "kuje ku shirya za'a Kaiku wurin tailor za'a d'auki measurements D'inku" Huyaam ta ce "Ammie na miye?" Ammie ta ce . "Na bikin su zulaihat mana ba'a kawo ankon da wuri bane sai yanzu" Huyaam ta ce "waye zai kaimu Kuma? Ammie ta kalleta Jin tambayar da tai mata kafin ta ce "wannan ne Kuma bansani ba Dan Yanzu Hajiya Aysha ta K'irani take fad'a min ni Kuma ban tambayeta wannan ba" mik'ewa sukai suka haura sama zuwa d'akinsu.babu dad'ewa suka dawo falon cikin shirin fita doguwar rigar abaya suka Saka ash color sunyi rolling mayafin iri D'aya suka sa ita da Huda sunyi kyau ba kad'an ba, sallama sukai wa Ammie sannan suka bar falon gabad'aya... Suna gab da shiga b'angaren su safna sai ga safna ma ta fito nan suka juya suka nufi parking lot ahanya suka had'u da ikleema ta fito daga b'angaren su had'uwa sukai suka k'arasa compound d'in suka tsaya daga gefe kusa da wata mota wacce aka fito da lta da dukan alamu acikin motar za'a kaisun.suna nan tsaye suka hango Aziza ta fito daga b'angaren su taci kwalliya ba kad'an ba sai Wata Irin tafiya takeyi kamar bazata taka k'asa ba, kallo D'aya Huyaam tai mata ta d'auke kanta tana kallan gefe kafin ta Maida kallanta kan safnah Wacce suke ta zance ita dasu Huda ta ce "waye zai kaimu wai? safna zatai magana suka hango lamid'o ya fito daga b'angaren su hannunsa rik'e da key d'in motar ya nufo compound d'in Yana tafiya cikin nutsuwa, kallan Huyaam kawai yake tunda ya hangota daga nesa Daya fito daga b'angaren nasu,itama Kuma Kallansa take daga nesan da take hangoshi tana mamakin yaushe ya dawo gidan? Bata farga ba harya ya k'araso wajen motar tasa inda suke tsaye.gabad'ayansu suka had'a Baki wajen gaishe shi ansa musu Yayi da Kulawa Yana k'ok'arin Bud'e driver seat zai shiga ya ce "enter" babu musu suka ansa masa gabad'ayansu. su Hud'un ne suka shiga back seat sai safna Data shiga front seat.ta_da motar yayi bayan sun shiga yay reverse ya nufi babban gate d'in palace d'in.tun kafin su k'araso aka wangale musu gate d'in suka fita daga cikin palace d'in gabad'aya fadawan Dake Bakin gate d'in sukai tai musu fatan dawowa Lafiya...tunda suka d'au titi ikleema da Huda suke da zance k'asa Amma Banda Aziza Wacce ta kama kanta agefe tana latsa wayarta,dan tunda suka shiga motar uffan Bata cewa kowa a cikin su Hudan ba Suma Kuma Babu Wanda yay mata magana Dama daga can left door d'in k'ofar motar ta shiga sai ikleema a kusa da ita sai Huda sannan Huyaam.lokaci Lokaci lamid'o Dake gaban motar ya ke d'agowa ya Kalli direction d'in HUYAAM ta mudubin motar Batare da ya bari su Huda sun lura da Hakan ba, itakan Huyaam Batama San yana yiba ta juyar da kanta tana kallan gefen titin ta window motar. juyawar da zatai idonta ya sauka akan na lamid'o Dake kallan ta ta cikin mudubin motar,nan taga lamid'o ya zuba mata Ido Yana mata Wani Irin kallo,ai tuni ta sunkuyar da kanta k'asa tana Jin Wani Irin Fad'uwar gaba ta takure jikinta waje D'aya Bata yadda ta k'ara dago da kanta ba.shiko lamid'o Wani Irin Abu yaji Wanda ya K'ara motsoma masa da wutar soyayyar Huyaam acikin ransa Yana Jin Wani Irin feeling a game da ita Nan ya K'ara d'aga kansa ya Kalli mirror yaga ko zata Kalleshi Amma sai yaga tak'i d'ago da kan nata ma bare su had'a Ido.sauke numfashi yayi a hankali Yana cigaba da tuk'insa cikin nutsuwa lokaci lokaci Kuma ya d'ago yaga Huyaam ko zata Kalleshi Amma saiya ga Tak'i d'agowa a haka har suka isa plaza d'in da aka kai musu D'inkunan nasu Amma har lokacin Huyaam Bata k'ara yadda ta k'ara dago da kanta bare ta k'ara had'a ido dashi ba.... Yana zaune a cikin motar Yana jiransu su fito daga cikin shagon.tun Daga nesa yake kallanta baya ko kiftawa har suka k'araso gab da motar Bai d'auke idonsa akan taba, ita ko kallo D'aya tai masa ta d'auke kanta tana sunkuyar da kanta k'asa tana Jin Wani Iri. azuciyarta ta ce "ita kan ta Shiga uku da wannan Abu ace mutum yayi ta kallan ka, shi yanzu ya lamid'o Mai zaisa ya dinga mata Irin wannan Kallan haka" shiga motar itama tai da Sauri ganin duk sun shiga sun Barta.ta_da motar lamid'o yayi suka bar wajen gabad'aya..AWani k'aton store ya tsaya inda ake saida kayan sanyi irinsu ice cream da yogurt da sauransu, Bayan yayi parking ya juya Yana kallan su Yace "am coming" ansa masa sukai ya b'alle murfin motar ya fita yana tafiya a hankali har ya shige cikin store d'in.suna zaune acikin motar ya dawo Hannunsa rik'e da ledoji manya ya shiga ya Mik'awa safna Dake gaba Leda D'aya sauran Hud'un Kuma ya Mik'awa su Huyaam da suke bayan motar .Huda ce ta karb'a ta ce "thank you so much ya lamid'o" Suma sauran duk godiya sukai masa har Huyaam datai masa godiyar k'asa k'asa,ta-da motar yayi suka bar wajen sai palace.... ____________ Suna isa gida adai dai alokacin da ake K'iran sallahn magrib.fitowa sukai gabad'ayansu daga cikin motar sukaiwa lamid'o godiya, ansa musu yay Yana lucking motarsa gabad'aya kafin ya bar wajen ya nufi masallacin cikin palace d'in.suma sukai sallama da junansu nan ko Wacce ta nufi b'angaren su..bayan sallahn isha'i wajen k'arfe 9 Saura na dare suna zaune a falon gabad'ayansu .Ammie ta juya Ganin taga kowa zaune a falon Amma Banda Huyaam wacce suka barta a dining tun d'azu bayan sun gama yin dinner ta ce "wai Huyaam Mai kike a dining d'in nan
Chapter 65 · 0% Book details