← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 85

Sashe 4

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wani Irin kallo. Gimbiya Aysha ta sunkuyar da kanta k'asa tana gyad'a masa kai hawaye na zirarowa a saman fuskarta tuni Mai martaba ya kau da kansa Yana barin d'akin gimbiya Aysha ta d'ago ta bishi da kallo . ___________ Alokacin da su safara suka jefar da baby Zainab Basu dawo gidan ba Dan wanna umarnin shakundum ne saboda tace Dan kada a zargesu karsu sake su shigo masarautar a wannan lokacin har sai anshiga masallaci Dan yin sallahn ASuba, alokacin ne idon mutane baya kan kowa saboda a wannan lokacin da kowa yana masallaci ne Dan yin ibadah,Aiko haka akayi Dan awannan lokacin suka samu damar dawowa masarautar kuma da sukai Sa'a babu Wanda ya gansu Daga nan suka cigaba da aikinsu. Awannan dare haka shakundum tai bacci Irin Wanda ta Dad'e batai irin Saba ,Dan Yanzu kan ta k'udiri aniyar idan har Sau Dubu gimbiya Aysha zata haihu to itama sau dubu saita salwantar mata da abinda ta haifa Dan bazata fasa ba .Ai Allah nema yasa wannan cikin zaizo duniya Amma tun ranar da ta San gimbiya Aysha tana da ciki tai ta D'ana mata tarkon mugunta tana tsallakewa Allah ne kad'ai yasa zata haihun sai gashi yanzu bayan ta haihun asannan burin nata ya cika.yanzu sultan ne kawai ya rage Shine matsalarta ta rasa yadda akai har haryau sultan yak'i mutuwa duk da abubuwan da tasa akai tai masa Amma sultan yak'i mutuwa Kuma tabi duk wata hanya da sata sa a b'atar dashi abinci yaci tura, to shiyasa Yanzu tunda hak'arta ta kasa cinma ruwa akan sultan yasa tasa masa ciwo kullum acikin ciwo sultan yake baida ishashshiyar lafiya baya zuwa ko Ina acikin gidan sarautan nan ada ko school baya zuwa sai dai ai masa lesson Amma taga yanzu ya fara zuwa school d'in dole kuma ta k'ara dak'ile wannann hanyar sultan kusan 10years yake a Shekaru Amma Yanzu idan kika ganshi kamar D'an shekara 5 saboda yadda ya koma baya shiga cikin mutane kullum Yana part d'insu, part d'in nasuma sai dai d'akin uwarsa ko kuma Wanda ake kula dashi.yanzu haka tana zaune bakin gado tashinta daga bacci kenan ta zauna take wannan tunanin farin ciki ne fall zaciyarta tai Wani murmushi kafin Tace a fili . "wallahi Aysha ni sarauniya Hajara Kuma shakundum indai Ina numfashi a duniya baki isa kin haihu da Mai martaba agidan nan ba matuk'ar ni ban haihuba". tana fad'ar haka ta Mik'e Dan shiga toilet danyin wanka bayan ta fito a gurguje ta shirya tunda taji labarin cewa an sallamo gimbiya Aysha tun d'azu daga asibitin Hakan yasa zataje tai mata jaje Dan kada a zargeta..haka ta fito hadimanta sukai mata rakiya har part d'in gimbiya Aysha Wanda alokacin suma 'yan cikin masa rautar suna ta zuwa dan Yi mata jaje. __________ Goggo hauwa ta dubi gimbiya Aysha wacce ke kwance saman gadon d'akin nata zazzab'i ya gama rufeta ruf tace cikin kwantar da murya. "Dan Allah gimbiya Aysha kiyi hak'uri idan Mai sunan Mai babban d'aki (sunan Daada kenan mahaifiyar Mai martaba Ina fatan kun Gane shi akasawa jaririyar)rabo ce Za'a ganta Dan Allah kiyi hakuri kinji"ta fad'a cikin sigar rarrashi.dan tunda suka dawo daga asibitin nan gimbiya Aysha take kwance Bata tashi ba . gimbiya Aysha batai magana ba Dan ita kad'ai tasan halin da take ciki ayanzu. Gimbiya Bilkisu ce dake zaune kan kujera dake d'akin ta haday Kanta da gwiwa damuwa fal ranta idonta ya kumbura yay suntum saboda Kukan da Tasha tace cikin rawar murya wacce k'iris ya rage ta saki Kukan da take rik'ewa. "Dan Allah Yaya gimbiya kiyi hak'uri nasan nice silar faruwar komai Dan Allah ki yafemin wallahi idan na tuno da cewa nice silar faruwar komai sai naji kamar zan Mutu saboda Damuwa,Dan Allah Yaya gimbiya ki yafemin".ta fad'a tana Wani Irin kuka Mai ratsa zuciya. Jin Muryar k'anwar tata yasa Gimbiya Aysha ta Bud'e idanta kad'an da suka kumbura saboda Kuka tana kallan gimbiya Bilkisu tace cikin dashashshiyar Murya. "Ko kad'an Bakimun Komai ba Bilkisu dama can Allah ya tsara koba ta silar kiba sai an rasa babyn mu ki daina fad'ar Irin wannan nidai banga laifin kiba "ta fad'a cikin rawar murya. Gimbiya Bilkisu ta Kalli gimbiya Aysha tace. "Nagode da kika fahimceni Yaya gimbiya in Sha Allah za'a ga babyn duk Wanda ya d'auketa ma Allah bazai tab'a Basu damar cutar mana da ita ba"ta fad'a tana share hawayen ta.goggoninsu duk suka ansa da in Sha Allah.itadai gimbiya Aysha kukun zuci kawai take .aranar haka akai ta zuwa yiwa gimbiya Aysha jaje wasu basa samun damar ganinta saboda halin da take ciki.hajiyarsu data ji wannan Abu haka tai ta K'iran gimbiya Aysha tana Bata Baki ita ko Daada mahaifiyar Mai martaba tana can india ganin likita shiyasa Bata san halin da ake ciki ba ,kuma Mai martaba da kansa ya hana a fad'a mata saboda karsu ta-da mata da hankali Dan batanan akai haihuwar tana can, aikuwa tunda taji labarin haihuwar da Kuma takwarar da akai mata take ta murna da muradun dawowa taga takwararta. Wasa wasa har baby Zainab tai sati D'aya da Bat'a ba'a ganta ba Babu labarinta babu dalilinta nan dai gimbiya Aysha ta sare da samun 'yarta Dan tasan tunda har aka kai wannan lokacin ba'a gantaba tofa samunta sai dai tsananin rabo .Ahaka dai ta fawwalawa Allah lamuranta tana addu'a babu dare babu Rana akan idan 'yarta tana raye Allah yasa ta tafad'a Hannu nagari idan kuma Bata raye Allah yay Mata Rahma Dan ita yanzu tama daina kukan filin sai dai na zuci ta Mik'awa Allah duka Al'amuranta.A Ranar da baby Zainab ta cika sati biyu da Bat'a a Kuma ranar su goggo hauwa suka tafi bayan sunyiwa gimbiya Aysha nasiha sosai tunda dama sun D'an K'ara zamane dan kwantar wa da gimbiya Aysha hankali Ba Dan komai ba, itadai ta nuna musu ta karb'i k'addara ahaka har akai wata D'aya ba'a ga baby Zainab ba zuwa lokacin Kuma gimbiya Aysha harta gama fiddarai daga samun baby Zainab wacce ko nickname ba'a sa mata ba Mai martaba da hajiyar su kullum cikin kwantar mata da hankali da nasiha suka mata kuma har lokacin Daada Bata dawo k'asar ba bare ta sani .ahaka dai har gimbiya Aysha ta fitar da Rai Daga samun baby Zainab Amma fa ciwon nan Yana nan Acikin zuciyarta Bai warke ba Bata kuma tunanin akwai ranar da zai warke tunda har ta rasa 'yarta a haka ta cigaba da safgoginta Amma fa abun Yana nan a ranta . A wannan lokacin kuwa shakundum Wani Irin farin ciki take ciki tareda walwala ganin yadda gimbiya Aysha ke cikin k'unci wannan shine babban burinta a rayuwa kullum taga gimbiya Aysha cikin k'unci gefe D'aya Kuma tana nan tana shirin yadda zata K'ara Sako sultan agaba dasa masa ciwuwuka iri iri ahaka har ya mutu shima shikenan idan tai haka burin ta ya gama cika sannan Bata da wata sauran far gaba.wannan kenan. *Tofa masu karatu meke shirin furuwa ne haka ? Wannan Karan Kuma ga inda Alk'alamin MRS SARAKIES ya kawo mu ,shin Ina baby Zainab take Shin tana raye ko Bata raye?idan tana raye tana Ina?su waye suka d'auketa?kudai ku kasance Dani Dan jin yadda labarin zai kasance dan war ware muku shi bit by bit Dan wannan tafiyar ta banbanta da sauran* Present 4 April,2025 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM (The love story) *NA* *____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____* *___(MRS SARAKIES ___* *Bismillahirrahmanirrahim* Page4 __________ *Present* 4 April,2025
Chapter 4 · 0% Book details