← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 85

Sashe 31

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ma ta ansa musu da kulawa sai kuma salima taiwa ya Zarah magana da cewa . "Zarah Ina Ammie kuwa? Naga na shigo ban ganta ba". Ta fad'a tana Wani dube dube a falon kamar anan zata ga Ammien". Ya zarah ta kallate a zuciyarta tace ji wata gulma Kuma?Koda zuwa take duba Ammien oho ,a fili kuma tace. "Eh yanzu ta shiga ciki Amma nasan yanzu zata sauko".Salima ta Jin jina kai tace. "Okay! Dama nazo gaida Ammien ne sannan kuma na gaida ya Afeef nai Masa barka da dawowa kinsan tunda yazo bamu had'u ba kuma Inaso ne mu had'u nai masa godiyar tsaraban da ya iyo Mana Allah dai yasa yau dai Yana nan Dan kullum idan nazo bana samunsa".ta fad'a tana Wani murmushi.ya Zarah tace. "Okay! Ya dawo Yana b'angarensu".Salima tace. "Indai zai Sakko Aiko zan jira shi yau dai mu gaisa".ya Zarah kan batai magana ba illa Wani kallo datai ma Salima . Ammie ce ta sauko falon tana cewa. "Books d'in waye a k'asa tsakanin muneefa da muneeb?..." muneefa ta mik'e tana murmushi tace. "Nawane Ammei homework nakeyi idan na gama zan kwashe". Ammie tace. "Kin kyauta Kuma yin homework har Sai an watsar da littafai gobe Kuma idan Kun tashi tafiya school ki ishi mutane da cikiya ko? Muneefa tai shiru tana kallan Ammie.Ammie tace. "to kina gamawa Maza kije ki kwashe tun kafin na K'ara magana". muneefa tace. "To" tana komawa ta zauna.Ammie ta k'arasa shigowa cikin falon tun kafin ta zauna Salima ta zamo daga saman kujerar ta zugunna har k'asa ta gaida Ammie... Ammie ta ansa mata da kulawa tana cewa. "A'a! Salima kece da daren nan?...." Salima na murmushi tace. "Nice Ammie". Ammie ta Jin jina kai tace. "Masha Allah ya karatun Kuma?...." Salima tace . "Alhamdulillah". Ta fad'a tana komawa kan kujerar ta zauna tana Wani sinne kai k'asa... Ammie tace. "Masha Allah! Allah ya taimaka". Salima na murmushi ta Ansa da Ameen.k'amshin turaran da sukaji Yana kusan toso Mai d'adin Gaske ne yasa duk suka juya suna Neman inda k'amshin ke fitowa .Afeef ne yake saukowa downstairs d'in sanye yake cikin k'ananun kaya Wanda sukai masa bala'in kyau sai baza k'amshi yake ta ko Ina tunda ya fara saukowa downstairs d'in Salima ta zuba masa ido tana kallansa Bata ko kiftawa ya Allah haka ta Ambata a ranta Dan Wani Irin kibiyar sanshi ne ya Kara chakarta a wannan lokacin.shiko Afeef Bai ma kula da ita ba Ammie kawai ya gani a falon sai 'yan uwansa Amma baiyi tunanin ma akwai wata Salima a wurin ba.dining zai nufa Hakan yasa Salima tai saurin cewa . "Yaya sannu da zuwa Barka da dare". Ta fad'a tana Wani lank'washe murya tare da k'ura masa ido".ba su Huyaam ba hatta Ammie saida ta taji Wani banbara kwai Jin yadda Salima ta sauya murya Lokaci D'aya, Amma Basu yi magana ba, bama Wanda ya kawo komai a ransa illah d'auke kansu da sukai suka nuna bama susan Mai tayi ba.shima kansa Afeef d'in mamakine ya kama shi jin yadda aka lank'washe murya anai masa magana kamar bazai juyo ba sai kuma ya juya Yana kallan Mai maganar ganin Salima ce yasa ya d'auke kansa daga kallanta Yana ansa mata da "yauwa". Atak'aice. ganin zai juya ya cigaba da tafiyar sa yasa Salima tai saurin cewa. 'Munga Sak'o mun gode Allah ya K'ara Bud'i Yaya". ta fad'a cikin wani Irin salo.bai ansa ba iyaka kawai da ya cigaba da tafiyarsa harya k'arasa dining d'in yaja kujera ya zauna. Sharetan da Afeef yayi baisa Salima taji haushin Saba illa sansa ne ma da taji ya K'ara ruruwa a azuciyarta ta lumshe idonta ta Bud'e lokaci D'aya ta cigaba da kallonsa kamar ta samu TV juyawar da tai suka had'a ido da ya Zarah ne yasa ta d'an ji kunya kad'an sai Kuma ta mik'e cikin Jin kunya tace . "Bari na tafi Ammie sai anjima". Ammie ta juyo tana kallonta tace. "Tafiya Zakiyi Salima?..." Salima na murmushi tace. "Eh Ammie sai da safe". Ammie tace. "To shikenan Allah ya tashe mu lafiya ki gaida Hajiya Lubabatun". Salima na murmushi tace. " Zataji in Sha Allah". daga haka tai hanyar fita daga falon tana Satan kallan Afeef ta gefen Wanda yak'i kallanta dan tunda ya zauna falon Bai d'ago da kansa ba Yana cin abincinsa ne kawai gefe D'aya Kuma Yana kallan screen d'in wayar sa.. A hanya Salima ta Had'u da yayansu Aziz chiroma zai shigo b'angaren Ammie hannunsa rik'e da Manyan bags, da yake gidan da a kwai haske ta ko Ina kamar Rana Yasa Salima ta ganeshi,mamakine ya kamata ganin wannan uban kayan da yay b'angaren Ammie dasu bama bangaren suba .lab'ewa tai cikin wasu flowers d'in Dake compound Dan kada Aziz ya ganta ta zuba masa ido tana kallansa tana tunanin kodai ba nan d'in zashi ba Amma Kuma sai taga nan d'in dai yake nufa Hakan yasa ta cigaba da kallonsa harya shige b'angaren Ammie, fitowa tai daga cikin flowers d'in ta nufi b'angarensu da sauri Dan kaiwa mamansu rahoto tana waige waige harta k'arasa shiga b'angaren su...... HUYAAM LAMID'O AZIZ CHIROMA AFEEF *Muje zuwa mutanan MRS SARAKIES .ke daga Jin salon labarin kinsan zai k'ayatar ya Kuma fad'akar.akwai chakwakiya sosai anan gaba Dan labarin ma yanzu muka fara shi*. *ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in 2270127432 Naja'atu umar Zenith bank Evidence of payment (shaidar biya )via 07066508376 Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku mutanan arziki. 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__* *__(MRS SARAKIES )__* PAGE 2 *Tallah! Tallah!! Tallah!!!* *Ina kuke hajiyoyin gidan nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zomu har inda kuke *Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma akanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka *Atamfofi da lesses* *Abaya* *Shadda* *Hand bag* *Shoe* *Veil na manya Dana Yara* *Socks rin hands made d'in nan masu net*. *Hula ta 'yan Gayu* *Siyan D'aya ko sari* *Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki* *Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka* 08135305790 *Sai mun jiku *Bismillahirrahmanirrahim* ___________ Da sallama a bakin Aziz chiroma ya k'arasa shigowa falon bayan yayi knocking an bashi iznin shiga.da mamaki kowa ke kallonsa ganin yadda ya shigo da kaya rik'i rik'i a hannunsa ,har Afeef Wanda ke zaune Bai tashi daga dining d'in ba kallan sa yake shima.duk suka ansa masa sallamar tasa ,Aziz chiroma ya zauna nan kan kujera Yana ajiye kayan Dake hannunsa anan gabansa kansa a k'asa ya shiga gaida Ammie.. Ammie na murmushi tace. "Lafiya lau Alhamdulillah Aziz ya gida ya aiki?..." Ta fad'a tana kallan sa.Yana shafa kansa tare da D'an murmushi yace. "Lafiya lau Ammie". Ammie ta Jin jina kai tace. "Masha Allah! Allah ya taimaka".ya ansa da ameen har lokacin kansa Yana k'asa Bai d'ago ba.Su ya Zarah ne suka shiga gaida shi ya d'ago da kansa Yana ansa musu tareda kallansu lokaci D'aya.har lokacin Bai lura da Afeef Dake zaune a dining ba, Shiko Afeef Yana kallansa bayan ya gama cin abincin ne ya tsaya Yana replying messages d'in da aka turo masa Yanzu ta wayarsa sa ,Dan tun shigowarsa ya ganshi.Aziz chiroma na d'an kame kame ya D'an sauke numfashi kad'an yace. "Ammie dama na Kawowa su Huyaam graduation gift d'in su da nai musu ALK'awari zan kawo musu, to bansamu naje nai musu lokacin graduation d'in ba sai yau dana samu time na fita,gashi Babu yawa ma". Ya Fad'a yana Satan kallan Huyaam ta gefen ido wacce tunda ta kalleshi sau D'aya bayan ya shigo ta d'auke kanta Bata k'ara yarda ta had'a Ido dashi ba .... Ammie tana kallan sa tace. "Chiroma Mai yasa zaka wahalar da kanka wajen siya musu Wani gifts bayan Wanda duk suka samu". Aziz na D'an murmushi yace. "Ai Ammie Babu komai Duka sud'in sisters d'ina ne Kuma ba iya su kad'ai na siyawa ba gabad'ayansu duka na siyawa." Ammie tace. "Tom shikenan Allah ya Saka da Alkhairi ya K'ara Bud'i". Aziz ya ansa da Ameen a kunyace. Huda na murmushi tace. "Mungode ya chiroma Allah ya Saka da Alkhairi ya K'ara Bud'i". Ta fad'a cikin Jin Dad'i.Aziz ya kalleta yana murmushi yace. "No thanks sis".kamar Huyaam bazatai magana sai kuma ta D'an juyo kad'an ta kalleshi Karan farko data K'ara kallansa tace. "Thank you ". Ta fad'a a tak'aice.Aziz yay mata murmushi yace. "No thanks sister". Kamar ance ya juya ya hango Afeef Yana kallan screen d'in wayar sa Wanda ya Bada attention sosai akai ke kyace Bai San me akeyi a falon ba nan ko Babu abinda bayaji .Aziz Yana kallan Ammie yace. "Wancan yarima ne?..." Ammie ta kalli Afeef sai kuma ta kalli Aziz chiroma tace. "Eh shine kaje ku gaisa mana?..." ta fad'a tana kallan sa.Babu musu Aziz ya mik'e ya k'arasa dining d'in har wajen Afeef ya Mik'a masa hannu Yana cewa. "Barka da dare yariman kano". Ya fad'a da murmushi a fuskarsa.Sai a lokacin Afeef ya d'ago ya kalleshi sannan ya Mik'a masa nasa hannu sukai musabaha.Aziz yana D'an murmushi yace. "Ashe ka dawo k'asar Kuma? Sai dai tunda ka dawo Allah baisa mun had'u ba sai yanzu Allah yayi". Ya fad'a Yana murmushi.Afeef ya D'an Saki fuskarsa kad'an tareda motsa bakinsa yace. "Eh! Alhamdulillah!". Aziz yace. "Masha Allah sannu da dawowa". Afeef yace. "You are
Chapter 31 · 0% Book details