Sashe 70
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
jira" kashe wayar tai tana kallan su ta ce "ya ce gashi can muje" daga haka tai gaba Suka bi bayan ta suka nufi inda Aziz d'in ya ce musu Yana wurin...Huda ce ta shiga front seat d'in bayan sun k'arasa, Dan Huyaam k'in shiga tai_tai maza ta shige bayan Motar wurin su siyama Dan kad'a ma Siyaman ta ce mata ta Shiga. ta-da motar Aziz yay bayan sun shiga suka fice daga cikin palace d'in. Akan idon Afeef da shigowarsa gidan kenan Yana Jin gine jikin motar sa Yana answering call duk da darene Amma Kuma ya ganesu tunda ga hasken wutar lantarkin nan ko ta Ina Daya haske ko Ina na gidan Babu Wanda baza ka iya Gani ba a wannan daren saboda yadda haske ya bayyana a ko Wani angle dake gidan. kallan su kawai yake Dan tun da ya shigo gidan ya hangesu Babu wacce Bai Gane ba Acikinsu ,Yana kallan lokacin da suka nufi wajen motar Aziz har suka shiga,kallan motar kawai yake har suka fice daga cikin palace d'in gabad'aya ya sauke numfashi ya rufe motar ya nufi b'angarensu..... _____________ A wajen palace d'in aziz ya tsaya da motarsa Yana jiran motocin dake gaban sa su wuce shima yabi bayansu.Huyaam dai Dake zaune bayan motar tana kallan yadda sauran motocin Amaren ke tafiya a hankali Kallan Huda Aziz yayi ya ce "wa zaku raka ne acikin su?" ikleema Dake Zaune a bayan motar tai saurin cewa ya zulaihat zamu fara rakawa saboda ita tafi nisa idan muka dawo sai mu biya gidan ya Bahijja" gyad'a kai Aziz yayi ya ja motar ganin motar da za'a kai ya zulaihat d'in tayi gaba tareda sauran motacin Dake gabansu haka nan dai ya bi bayansu.Saida motocin d'aukar ya zulaihat kaf suka fara wucewa sannan masu rakiyar Bahijja suka bi bayansu....Sun shiga har cikin gidan ya zulaihat Wanda ya gaji da tsaruwa da had'uwa basu Dad'e ba suka fito Dan Basu manta da gargad'in Ammie ba,daga nan Kuma gidan ya Bahijja suka nufa,itama gidan ta ya had'u sosai nan ma dai basu dad'eba suka fito daga cikin gidan gabad'aya suka shiga mota Suka koma gida...basu suka dawo gidan nan ba sai wajen k'arfe 10 da mintuna na dare lokacin har 'yan rakiyar Amaren wasu sun daddadawo.Aziz Yana yin parking duk suka fito kowa ya gaji Dan haka sukai sallama da junansu kowa ya wuce b'angaren su.binsu HUYAAM Aziz yayi da kallo yana son yayiwa Huyaam magana amma tak'i bashi fuskar Hakan tun a Hanya yake tai Mata message akan idan sun dawo gida ta daure ta tsaya ta Saura reshi Amma tak'i,Dan ko reply batai masa ba Kuma Yana da Tabbacin ta Gani kawai k'yaleshi tai.ganin su ikleema duk sun kusan shiga b'angaren su yasa yay saurin b'alle murfin motar ya fito yabi bayan su HUYAAM Yana K'iran sunan ta ganin suna gab da shiga b'angaren su. juyowa Siyama tai Ganin ana K'iran sunan HUYAAM haka ma Huda ita ko Huyaam tsaf ta Gane muryar sa yasa tai Banza ta k'yaleshi saima ta K'ara saurin tafiyar ta_ta. ganin Aziz ne yasa Huda ta ce "HUYAAM ki tsaya mana ya Aziz ne fa me K'iran ki?" Huyaam tai banza ta k'yalesu saima ta K'ara saurin tafiyar ta .siyama ma ta ce "Dan Allah Huyaam ki tsaya Kinga Babu Dad'i fa" juyowa Huyaam tai a fusace ta ce"wai Baku San Yaya Yana nan bane da zakuce na tsaya?idan ya fito ya sameni dashi fa Mai zance masa?be side ni bazan iya tsayawa ma dashi ba saboda Banda ra'ayin Hakan.Siyama ta ce "ai Kuma Yaya ma bazai tab'a kawowa Wani Abu ba tunda yasan ya Aziz ne ba Wani ba" Huyaam ta girgiza kai ta ce "dan Allah ku rabu Dani Huda wallahi bazan iya ba" Huda ta dafa ta ganin Aziz na Isowa gab da su ta ce "na rik'oki sis ki saurare shi Babu kyau walak'anta mutum, sannan mutum Irin ya Aziz ma ai Bai kamata ace Yana miki magana Kin rabu dashi ba, ki tuna Alkhairinsa garemu, please badan niba Dan Allah Huyaam ki tsaya ki Saura reshi kona 2 minutes ne Dan Allah" daga haka taja hannun siyama suka Shiga b'angaren nasu, Huyaam ta bisu da kallo sai Kuma ta juyo ta sunkuyar da kanta k'asa ganin Aziz d'in ya k'araso.... Aziz yay sallama Yana gyara tsayuwar sa lokaci D'aya Yana kallanta ita dai bata yadda ta d'ago da_ kanta ba, yay k'asa da murya ya ce "barka da wannan lokaci sweet" ya fad'a da Wani Irin shaukin Santa ganin yadda ta k'ara masa kyau ba kad'an ba" Banza tai dashi ta K'ara tsuke fuska ta Aziz yay murmushi ya cigaba ya ce "please sweet kimin magana ko zanji Dad'i mana?" ya fad'a Yana Wani kashe murya.kamar Huyaam baza ta ce komai ba sai Kuma can ta ce Batare da ta kalleshi ba "Dan Allah ka Fad'i abinda zaka fad'a na tafi kar yaya yazo ya same ni" ta fad'a cikin tsoro. Aziz ya K'ara sakin Wani murmushin Yana shafa sajensa ya ce "in Sha Allah bazai ma ganki ba Kuma idan ya gankima nasan Babu Abinda zai miki tunda ai yasan nine" Huyaam ta K'ara Kau da kanta gefe ta ce "nidai kaga na tafi" ta fad'a tana k'ok'arin juyawa zata bar Wajen Aziz yay saurin cewa" Noo! Please ,haba sweet dan Allah karki tafi" ya fad'a da Wani Irin sauti, Huyaam Bata saurareshi ba ta juya gabad'aya da nufin Shiga b'angaren su sukai ido hud'u da Afeef dayake D'an nesa dasu .Wani Irin rass gaban ta ya Bada sauti take zufa ya keto mata Wani Irin tsoro da firgici suka shige ta lokaci D'aya. Shiko Aziz baima Kula da Afeef saboda Baya ya bashi Kuma idonsa ya makance a akon San Huyaam ta saurare shi ya ce"okay thank you for your time and good night sweet love".ya fad'a da d'an k'arfi Yana juyawa yabar wajen ganin tak'i sauraransa.sauke idonta k'asa Huyaam tai tana kasa kallan Afeef saboda irin kallon da yake mata .shidai Afeef kallanta Kawai yake sama da k'asa Dan Fitowar sa daga b'angaren nasu Kenan zaije ya d'auko a Abu a mota tun daga nesa yake kallansun yana mamakin Mai ya tsaida Huyaam da Wani Kuma ganin Aziz ne yasa mamakinsa linkuwa har yaga ya juya ya bar wajen bai daina kallansa ba, Yana mamakin Maiya tsaida su su biyun.da k'yar Huyaam ta iya d'aga k'afarta tai saurin shigawa b'angaren nasu da sauri tana dafe k'irjinta Dake bugawa da k'arfi har tana had'awa da gudu a haka har ta shige cikin falon nasu batare da ta tsaya ba tana toshe bakinta da Kuka keson kufce mata ai da gudu ta haura stairs bayan ta shiga Falon ta shige d'akinta ta rufo k'ofar har tana murza key sannan ta jingina da k'ofar ta saki Kukan da take ta rik'ewa tana cewa ta shiga uku shikenan yayansu zai kasheta su Huda sun ja za mata bala'i dama Saida tace yayansu zai gansu Amma suka ce ba haka ba gashi Yanzu ya gansu ai, da k'yar da Jan k'afa ta k'arasa cikin d'akin ta fad'a Saman gadon tana cigaba da Kukan ta kamar Wanda aka Mata wani abun,tana cikin kukan taji ana knocking k'ofar,ai da Wani Irin expression ta d'ago da kanta tana kallan k'ofar tana yarfe Hannu k'irjinta na bugawa da k'arfi tana cewa ta shiga uku ta lalace gashi yanzu Afeef ya biyota har d'akinta zai kashe ta tana ji Aka K'ara knocking d'in for the second time Amma ta kasa tashi bare ta iya Bud'e wa.sai ma Wani marayan ihun kuka data saki tana yarfe hannuwanta..... Saura 2 page mu gama Free pages saboda haka ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in Littafin HUYAAM na kud'i ne regular group akan naira 500 before mu gama free pages muka gamawa Kuma zai koma 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in 2270127432 Naja'atu umar zenith bank Evidence of payment 07066508376 *Yan Niger _zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA 07066508376 HUYAAM LAMID'O AZIZ CHIROMA AFEEF ABDALLAH SHATTIMA *TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!* *Assalamualaikum warahmatullah.* *Ina kuke manyan mata masu capacity ? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."* *To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* *1,Atamfofi* *2, lesses* *3, Abaya* *4, kayan kwalliya ko Wani iri ne* 5,*D'an kunnaye(jiwelleries)* *6,takalma* *7,hand bag* *8, mayafai* *9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*. *domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka +234 811 190 1302 /09020337676* *Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta* *Sai mun Jiku