Sashe 82
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shi.ko kad'an ko da wasa Bai mata Hakan ba, tun tana b'oyewa idan ta ganshi tana 'yar wasan b'uya dashi na karsu had'u har ta dawo da daina ta saki jikinta ta cigaba da sabgoginta ganin shi ko kallo ma Bata ishe shi ba, tun tana tunanin wata rana zai iya Mata maganar har ta dawo ta daina Damuwa da hakan ta cigaba da harkokin ta a gidan harma watarana su zauna tare dashi a main falon gidan ya gama zamansa ya tashi batareda da ya nuna mata alamar wai Yana rik'e da ita ba.Hakan yasa itama ta manta da zancen..A b'angarenta da Aziz chiroma kuwa tun tana basar dashi idan ya K'irata a waya har ta dawo tana picking call d'insa.yay ta janta da hira Wani lokacin ta tanka masa Wani lokacin kuwa tai Banza dashi ta k'yaleshi har ya gaji Dan kansa ya k'yaleta. daga baya Kuma abinda ta Gane idan tak'i tankasan Huda yake k'ira ya fadawa ya rok'e ta akan tazo ta rok'ar masa Huyaam ta dinga kula shi.to ita Kuma Huda idan taji haka saita ce masa karya Damu zata shawo masa kan Huyaam, haka zata to tai ta rok'ar Huyaam dayi mata rik'o da magiya da nasihu kala kala akan ta dinga kula Aziz ko yaya yane tana sakar masa fuska. tun Huyaam Bata sauran ta yau da gobe har ta dawo take sauraran Huda, ta yadda take D'an Kulashi sama sama harma ta dinga D'an bashi ansa a hirar da sukeyi. tun Huyaam Bata saki jikinta dashi ba harta dawo ta fara saki suke hira abinsu.to tun daga wannan Wani al'amari ya fara d'arsuwa azuciyar Huyaam game da AZIZ bawai taji tana sonshi bane sannan Kuma bawai Bata son shi ba, Haka dai take Jinsa a zuciyar ta a Wani sashe na Daban inda da Bata bashi wannan matsayin ba.ga wata iriyar shak'uwa da suka fara Yi ita dashi har mamakin kanta take Wani lokacin... tsakaninta da Abdallah shattima ma kuwa Shima dai kamar yadda take Jin Aziz haka Shima take Jinsa.sai dai har a zaciyarta bawai sonsu take ba kawai dai ta d'auke su ne matsayin masu Bata kuluwa da Kuma da d'ad'an maganganu da suke Yi a gareta.... Yanzu haka Zaune take a d'aki saman gadon ta wajen k'arfe 12 da Rabi ne na Rana. gama wayar su kenan da Aziz tana tunanin last words d'in daya fad'a mata tana murmushi.kamar wacce ta tonu da wani Abu Kuma sai tai saurin firgita ta sauko daga saman gadon da sauri tunawa da tai Ammie ta ce mata ta had'a kayanta a box Wanda zata buk'ata idan sunje Egypt Dan gobe ne idan Allah ya kaimu zasu tafi Egypt d'in,jirgin nasu na k'arfe biyu da Rabi ne na rana. da Huda ce ta ce ita zata had'a mata kayan tun d'azu data shigo d'akin ta fad'a mata,Amma gashi shine har yanzu bata zoba. Ganin time na tafiya har Yanzu wajen k'arfe shabiyu da Rabi Bata zoba yasa tai deciding gara Kawai tayi d'in kada Ammie ta K'ara zuwa tai mata magana akan had'a kayan.sauke numfashi tai nan ta K'arasa wajen box d'inta Dake a d'akin ta d'auko D'aya daga ciki ta k'arasa gaban press ta Bud'e ta fara fito da kayan da tasan zata buk'ata har suje su dawo.duk da Bata Son yaushe zasu dawo d'in ba Amma tasan baza su wuce 4 to 5 Days acan su dawo Nigeria ba.. tana cikin had'a kayan aka turo k'ofar d'akin, juyowa tai tana kallan k'ofar.Huda ce ta shigo nan ta d'auke kanta ta maida kan Abinda takeyi. Huda ta k'arasa shigowa cikin d'akin ta zauna nan Bakin gadon tana kallan yadda Huyaam ke had'a kayan nata ta ce "Mai yasa kike had'a kayan Bayan nace ni zan had'a miki?" Huyaam ta d'ago ta kalleta bayan tai zipping box d'in ta langwab'ar da kai ta ce "naga ne Baki zoba d'auka ta ma Ko kin Manta ne ni Kuma banaso Ammie ta k'ara zuwa tai min magana shiyasa kikaga nayi" Huda ta kalleta ta ce " shikenan kin kyauta ai" ta fad'a tana juyar da kanta gefe.HUYAAM tai murmushi ganin alamar Huda fushi tai ta k'araso kusa da ita ta rungumeta ta gefe ta ce "am sorry sis kiyi hak'uri kinji?" Huda ta fara tu reta daga jikin ta ta ce "ni dai ki Rabu Dani" Huyaam ta ce "okay tunda Baki hak'ura ba bari naje na fito da duka kayan in yaso sai ki sake had'a min" ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa. Rik'o hannunta Huda tai da Sauri ta ce "karki fito dasu na hak'ura" komawa Huyaam tai ta Zauna ta ce "thank you so much sis Kinga fa tun daga Yanzu harna fara kewarki" ta fad'a tana Wani Marai raice fuska.Huda ta kalleta ta ce "same to you wallahi Amma ai naji Ammie ta ce baza ku Dad'e ba idan kuka je ko? Huyaam tai fari da ido ta ce "eh Bai fi 4 to 5 days kamar yadda muka Saba" Huda ta sauke numfashi ta ce "Allah ya Kaiku lafiya" Huyaam ta ansa mata da Ameen.bud'e k'ofar d'akin akayi gabad'ayansu suka juya suna kallan k'ofar ya Zarah ce ta lek'o ta tsaya daga nan Bakin k'ofar tana kallansu kafin ta ce "ku Kuma zaman daki Kuka koma Yi Yanzu kenan?" Tafad'a tana kallansu.murmushi Huyaam tai tana sosa Kai ta ce "laa! ya Zarah Mai kika gani? Ya Zarah ta hararesu ta ce "ai nagane kwanan bakwa zaman falo koda yaushe zaman d'aki,ke tunda kuka dawo daga Abuja na kula Kun daina zaman falo yanzu" Huda ta ce "a'a ya zahra ba Haka bane ba yanzun dai Huyaam nake Taya had'a kayanta" ya Zarah ta tab'e Baki ta ce "aishikenan intai tsami maji nidai yanzu ku taso nasa ka ku Wani aiki please" Huda ta ce "Wani aiki? Ya Zarah ta ce "Dan Allah kuje ku gyara min d'akina na samu emergency call ne daga school yanzu zan tafi Dan Allah kuyi Maza kuje kumin yanzu kafin na dawo" ansa mata sukai da Ladabi sukai mata fatan dawowa Lafiya. ansa musu tai itama sannan ta juya ta bar Bak'in k'ofar.Huyaam na kallan Huda bayan ya Zarah ta tafi ta dafe k'irji da tsoro a fuskarta ta ce cikin sanyin murya"na shiga uku Huda karfa ya Zarah ta Gane ana K'irana a waya fa?" ta fad'a tana zare ido.huda ta girgiza mata kai ta ce" bana tunanin ta Gane gaskiya Dan Kinsan ya Zarah Bata shiru indai daga Abu tofa sai tayi Magana" Huyaam ta sauke idonta k'asa ta ce "Anya kuwa Huda nifa wallahi har yanzu Ina tsoron ranar da yaya ko Kuma Ammei wani acikinsu ya sani wallahi kasheni za'ayi" Huda ta rik'o hannunta ta ce "Dan Allah kidaina zancen kisan nan Babu Dad'i bare ma Babu Wanda zai sani idan ma sun sanin Babu abinda zai faru in Sha Allah! tunda ai kowa Yasan Ya Aziz d'in" Huyaam tai shiru batai magana ba tana tunanin maganar huda. Huda ta Mik'e tsaye ta ce "Dan Allah ki taso muje muyi aikin kafin lokacin sallah yayi" numfashi Huyaam ta sauke ta d'auki wayarta suka fita daga d'akin gabad'aya jikinta Duk a Sanyaye..... Da yamma wajen k'arfe biyar da Rabi,Anty Amina ce tsaye a jikin pres d'in kayan gimbiya Aysha tana zab'ar mata kayanta da zata sa da Wanda zata buk'ata Idan sukaje can Egypt d'in.knocking k'ofar akai bayan wasu seconds aka turo k'ofar aka shigo lokaci D'aya.Anam ce ta shigo d'akin sanye da uniform d'in islamiya a jikin ta da dukan alamu daga can ta dawo.ta k'araso shigowa har cikin d'akin bakinta d'auke da sallama , Anty Amina ta ansa mata tana cigaba da aikinta.Anam ta ajiye Jakar Hannunta Wacce take ta islamiya nan Saman kujerar dake d'akin.ta nufo Anty Amina ganin tana had'a kayan Maminta a box ta ce "Anty Ina Mami zata? Anty Amina tana cigaba da abinda take ta ce "Egypt" Anam tai murmushi ta ce "harda ni za'a? Anty Amina ta ce "a'a Banda ke" Anam tai shiru lokaci D'aya Jin ba da ita za'a tafi ba" juyowa Anty Amina tai tana kallan ta Sai Kuma ta sakar mata murmushi ta ce "Da wasa nake miki daughter Dake mana za'a Hajiya inna ta ce wa za'a barwa ke idan muka tafi muka barki ai k'afar ta k'afar ki" ta fad'a tana murmushi.ai sai Anam ta washe Baki ta ce "yeh! I love inna" nan ta ta fara murna Jin da ita za'a" Anty Amina ta ce "to jeki cire uniform d'in tukunna" juyawa Anam tai ta wuce wajen press d'in kayanta ta Bud'e ta d'auki wata doguwar riga marar nauyi sannan bar wajen ta nufi Wani D'an corridor Dake nan cikin d'akin ta fara cire uniform d'in ta sauya zuwa na gida sannan ta fito ta daga ciki ta k'araso cikin d'akin ta haye Saman gadon inda gimbiya Aysha take ta zauna nan kusa da ita tanai Mata magana kamar wacce zata ansa mata. ita dai gimbiya Aysha binta kawai take da ido.mik'ewa Anty Amina tai bayan ta gama had'a kayan ta ajiye box d'in a gefe inda nata trolling kayan yake tana kallan Anam ta ce "ki zauna tare da ita bari naje na gano Idan sultan ya had'a kayan nasa" gyad'a mata kai Anam tai ta ce "to Anty" daga haka Anty Amina ta fita daga d'akin bayan ta k'ullo musu k'ofar..Anam ta Maida hankali tana cigaba da yiwa Mamin ta zancen da take mata duk da tasan ba ansa mata zatai ba Amma Kuma ita tana Jin Dad'i aduk lokacin da take yiwa Maman nata zance..... ____________ Aziza ce ta shigo b'angarensu da gudu tana dafe da Kuncinta tana kuka kamar ranta zai fita, tana ihun mommy na makance. Fulani Salamatu da take d'akinsu su Ramla ta taje kwantar da walida ta fito da sauri jin ihun Aziz wacce kamar ranta zai fita.take k'irjinta ya buga da k'arfi Jin abinda aziza ke cewa na wai ta makance.tuni ta nufeta da sauri ganin ta zube a tsakiyar falon har lokacin ihun kuka take. D'agota Fulani Salamatu tai cikin tashin hankali tana tambayar Aziza da lafiya? Aziz ta kasa magana sai ma Wani Irin kuka da take tana k'ok'arin shid'ewa.ai tuni hankalin Fulani Salamatu ya K'ara tashi ta