← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 85

Sashe 15

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

damar tashi ko? kodan ba laifinki bane ba ,mu mun Isa muyi Irin wannan baccin ai sai ke ".ta fad'a tana d'auke kanta daga kallan Huyaam.Huda da batai magana ba ta juyo tace. "Wallahi fa ya zarah ni ban isa ma nayi Irin wannan baccinba". ta fad'a tana kallan Huyaam Ya zarah tace. "Ai wallahi itama ta kusa dainawa Yaya Yana dawowa ne".ta fad'a tana kallan Huyaam wacce ta take kallanta da mamakin abinda ta fad'a. Huda ta Mik'e zaune daga kishin gid'en da take jikin kujera jin abinda ya Zarah ta fad'a da Mamaki tace. "Da Gaske ya Zarah Yaushe zai dawo?...."ta fad'a tana kallan ya Zarah. Ya zarah tace uhmmm. "Ki tambayi Ammie ita tasan yaushe zai dawo". ai Jin haka yasa Huyaam ta dawo falon da sauri babu shiri k'arasa ta tsaya gaban Ammie tace. "Ammie yaushe yayan zai dawo?..." Ta fad'a tana kallan Ammie. Ammie ta d'ago ta kalleta tace. "Nan da two weeks ne in Sha Allah aikinji ko? To Dan Allah jeki ci abincin" ta fad'a tana kallan Huyaam. HUYAAM ta saki murmushi ta d'aga hannayenta duka biyun sama irin dai yadda yara sukeyi idan Wani abun farin ciki ya samesu tace. "Yeeh Yaya zai dawo,Aiko Yana dawowa Muma za'a siya mana waya irinta ya Zarah dama haka Abba yace idan Yaya dawo za'a siya mana waya".ta fad'a tana Wani Irin juyi anan tsakiyar falon.ba Ammie ba hatta ya Zarah da huda Kai harma dasu muneefa kallon Huyaam kawai sukeyi da mamakn abinda tai. Ammie ta rik'e baki tace. "Oh!!! Ni Maryam nagodewa Allah Daya bani 'ya Mai hankali". Ta fad'a tana kallan Huyaam sai a lokacin HUYAAM ta lura a abinda tai Dan wallahi ita murna ce ta sata tai hakan .ta sunkuyar da kai k'asa cikin Jin kunyar abinda tai tace. "wallahi Ammie mantawa nai ba ni kad'ai bace murna ce ta sani haka".ta fad'a tana nufar dining d'in.ya Zarah tace. "Allah ya shiryeku keda Huda itama badan a Zaune take ba had'uwa zasuyi suyi juyin tare Ammie Dan naga Tunda suka fara zana WAEC kansu yake rawa nasu zasu zama graduate sai kace akansu aka fara candy".ta fad'a tana hararar su. Huda tai murmushi tace. "Wallahi ya Zarah banda ni iya itace ke Yi"ta fad'a tana kallan Huyaam. Ya zarah tace . "Hmm kudai cigaba karku nutsu har Yaya ya dawo Baku nutsu ba Kunsan ai baya d'aukar shirmenku ko?.."HUYAAM tai murmushi tace. "In Sha Allah kafin nan ma nikan na nutsu tunda nayi graduation d'in ai zan dawo kamar da"ta fad'a tana kallan Huda. Huda ta harareta tace. "Ai ke Huyaam ko zaki daina komai Banga alamar zaki daina bacci ba". kafin Huyaam ta Bata ansa sukaji Muryar Ammie tace. "ya isa haka kuyi shiru ku barta taje taci abincin mana time na tafiya".Babu Wanda ya K'ara magana acikinsu .Huyaam ta zauna kan kujerar dining d'in ta Bud'e warmers d'in ta zuba abincin da Yay mata ta fara ci gefe D'aya Kuma tana tunanin dawowar yayan nasu Dan tabbas tasan baya son hayaniya indai Yana gidan nan to Baki isa kunyi wani motsi ba sai Dai idan baya nan ta sauke numfashi ta kauda tunaninta gefe tana cigaba da cin abincinta........ Da yamma ya haidar ya shigo falon bakinsa d'auke da sallama Babu kowa afalon hakan ya k'araso shigowa ciki zaiyi hanyar b'angaren da d'akinsu suke HUYAAM ta fito daga kitchen d'in downstairs da ruwan roba a hannunta tana ganinsa tai saurin cewa. "Ya haidar!!". Bai ansa ba ya juyo Yana kallanta. HUYAAM ta k'araso har wajen sa ta tsaya a gabansa tana kallan sa kafin ta tura Baki gaba tace. "Ya haidar Jiya Ina ka tafi bayan kasan cewa zamuyi graduation shine baka dawo da wuri ba".ta fad'a tana Kallansa. Ya haidar ya sauke numfashi yace. "Bana nan Abba ne ya aikeni shiyasa". Huyaam tai murmushi tace. "to munyi graduation,ya Haidar na zama candidate".ta fad'a with confidence. Ya haidar ya kalleta sama da k'asa kamar zai maketa dan haushin Abinda ta fad'a Amma saiya danne yace cikin k'asa da murya. "To congratulations to you, yanzu Kuma sai a k'yalemu da zancen zama candidate d'in nan Wanda baya k'arewa tunda yanzu kin zama ko?..."ya fad'a Yana kallan ta .Huyaam ta gyad'a masa tace. "Sai Kuma university ba". Yace. "Uhmm"kafin yay gaba.huyaam tai saurin cewa. "ya haidar baka ga gifts d'in da aka Bamu ba fa?..."Batare da ya juyo ba yana cigaba da tafiya yace . "zan Gani anjima". Huyaam tace. "Na kawo Maka d'akinka?..."yace. "Karki dameni fa nace miki sai anjima"Daga haka ya haye stairs d'in da zai kaishi b'angarensu da sauri.Huyaam ta juya ta haura sama itama tana Murmushi ita kad'ai Aranta, Dan idan ta tuno da wai yau tayi Candy sai taji Wani sabon Dad'i ya lullub'e ta .... 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *PAID BOOK *FREE PAGES* *NA* *__(MRS SARAKIES )__* *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 1 ___________ Haka su HUYAAM suka cigaba da Shan hutunsu na waiting results kafin kuma su shiga university.ita kan HUYAAM Bata da aiki a wannan lokacin sai na bacci, Dan Wani sabon babin bacci ta Bud'e agidan nan, Kuma Babu Mai mata magana idan Huda tai magana sai Ammie tace abarta ta huta tunda yanzu lokacin hutun sune,Suma ba'a hanasu su Huta ba ,bare su sa mata ido idan Batai huta Yanzu ba yaushe zata Zata huta suna shiga jami'a Kuma shikenan baccin ya k'are, baka Ammie take fad'a ga duk Wanda yay magana akan baccin da Huyaam takeyi.jin haka yasa Basu K'ara magana ba suka k'yaleta take Shan baccinta San ranta har Sai lokacin da ta gaji da baccin ta tashi Dan kanta...... *Bayan sati D'aya* *After One week* Ranar Friday da yamma wajen k'arfe 4:30pm na yamman Ranar Huda na tsaye gaban mirror d'akinsu tana d'aurin Dan kwali,Huyaam kuma har ta gama shiryawa tana zaune gefen gado tana kallan Huda Dake shiryawa lokaci D'aya ta d'auke kanta daga kallan Huda ta Maida gefe tana kallan bango.huda tana yafa mayafinta saman kayan jikinta tace. "Huyaam Baki cemin nayi kyau ba". ta fad'a tana murmushi idanta na kallan mirror..dan fita zasuyi zasuje b'angaren fulani Salamatu Dan yau dai Aziza zatai parting ta na graduation kamar yadda fulani Salamatu ta fad'a Kuma har nan b'angaren aziza tazo ta fad'awa su Huyaam akan tana gayyatar su zo.to jin Huyaam tai shiru batai magana ba yasa Huda ta kalleta ta cikin mirror taga hankalin Huyaam ma bama ya kanta Yana Wani wajen daban Hakan yasa ta juya tana kallonta kafin ta k'arasa kusa da ita tace. "Sis". HUYAAM ta juyo tana kallon Huda Wacce ke sanye cikin shigar less d'inkin doguwar riga fitted gown Ash color da ratsin golding mayafin shima kalar kayan tasha uban d'auri tayi kyau sosai ba kad'an ba shigar su iri D'aya sukai da Huyaam. Huyaam ta kalleta Amma Batai magana ba.Huda tace. "Ke tunanin me kike tun d'azu Ina tai Miki magana kinyi Shiru?..."ta fad'a tana kallan Huyaam bayan ta zauna a gefenta Huyaam. Huyaam ta ya Mutsa fuska tace . "Wallahi sis ji nake kamar banda lafiya".ta fad'a tana dafe kanta. Jikin Huda yay sanyi ganin Huyaam ta dafe kanta tana tsoron ace ciwon tane zai tashi.sai kuma tai saurin cewa. "A'a sis in Sha Allah ma Babu abinda zai sameki ".ta fad'a cikin tausayawa.huyaam ta d'ago ta kalleta tace . "Sis kawai Kije ni bazan jeba". Ta fad'a tana k'ok'arin yaye mayafin jikinta.huda tai saurin rik'e mayafin HUYAAM ta marai raice tace. "Please sis Dan Allah karki ce baza kije ba kinga Hakan Babu Dad'i fa,kawai ki daure muje in Sha Allah babu abinda zai sameki,Abinda yasa ma kike Jin jikin naki haka Babu Dad'i baccin da kikayi ne yasa kike jin Wani Iri amma muna fita in Sha Allah zakiji kin ware, karki ce kin fasa zuwa Dan Allah Dan nima idan baza kije ba nima Babu inda zani". Huda Ta fad'a itama tana k'ok'arin cire mayafin jikin nata . Huyaam tai murmushi ta rik'e mayafin Dan tasan indai baza taba to itama Huda ba zuwan zatai ba Hakan yasa tace. "Shikenan zani muje". Ta fad'a tana murmushi. Huda ta sauke ajiyar zuciya tai murmushi tace. "Ko kefa ki kwantar da hankalinki in Sha Allah Babu abinda zai sameki itadai Huyaam murmushi kawai take.huda ta mik'e ta tafi inda suke ajiye takalmansu da hand bag d'insu ta d'auko musu iri D'aya sannan ta dawo ta ajiye ma Huyaam nata a gabanta tana kallan ta tace. "Kisa mu tafi ko bashi kike so ba?.."ta fad'a tana kallanta .Huyaam ta Bud'e ido tace. "A'a yayi mana tunda kema irinsa kika sa".Huda ta kamo hannun Huyaam bayan sun d'auki hands bag d'insu sannan suka fita daga d'akin. Saida sukaje har d'akin Ammie sukai mata sallama sannan suka fito daga b'angaren gabad'aya . Abakin gate d'in bangaren su suka had'u dasu ikleema da suka biyo musu.safna ta saki murmushi tana kallan su tace . "Ikleema ai gasu ma sun fito ba sai mun shiga ba"Huda tace. "to kuzo mu koma ciki mana". Ikleema tace. "A'a tunda kuka fito mu tafi kawai idan muka dawo ma shigo ko safnah?..."ta fad'a tana kallan safnah. Safnah tai murmushi tace. "Eh" sai kuma ta Kalli HUYAAM tace . "Irin haka wannan kyau lallai kunsha kyau ba kad'an ba".Huda tace. "zaki fara ko safnah?...dalla wuce mu tafi Keda bakya gajiya".safna tai murmushi tace . "Ai gaskiya na fad'a ko ikleema?..." ta fad'a tana kallan ikleema. Huda tace. "sai kiyi tayi nidai Kunga tafiya ta". tai gaba suka bi bayanta suna Murmushi. _____________ A b'angaren fulani Salamatu kuwa Aziza ce zaune kan kujera gaban mirror ga me make up d'in da fulani Salamatu ta k'ira for home service tazo tana yiwa Aziza kwalliya ga k'awayen Aziza nan suna zaune a d'akin suna jiranta Mai make up d'in ta Kalli Aziza bayan ta gama mata d'auri tace. "Wow Masha Allah gimbiya kinyi kyau sosai" ta fad'a tana murmushi.Aziza da take cikin shigar Wani D'an k'areren yadi Wanda idan kikaji kud'insu saikinyi mamaki saboda tsadar sa sai Wani fidda hasken stone yake ta ko Ina different colors tai murmushi tace. "Thanks", Mai make up d'in ta fara mata pictures da videos a wayar Hannunta bayan ta gama ta nunawa Aziza adai dai lokacin da hadimar
Chapter 15 · 0% Book details