Sashe 36
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
haka ya d'auke hand out d'insa ya cigaba da karatun. anty Amina ta fita daga d'akin cikin farin cikin halin da tarar da sultan aciki tana yiwa Allah godiya da Kuma tasbihin ganin sauk'i ya fara samuwa a wajen sultan...... ___________ 3:45pm A Wani tsauni Dake can Wani k'auye Wanda yake lungu acikin wani k'auye Dake cikin garin ZARI'A.tsauni ne Wanda girmansa da Nisan gun zaiyi kilo meter 8, Dan kafin ma aje inda akesan zuwan ma wata uwar tafiyar ce. Cikin Wani tsohon Gini Wanda akai wata bukka ta Kara Irin Mai k'arfin nan a tsakiyar wurin ce Mai girman Gaske, na hango Wani Bak'in mutum kakkura Wanda duk jikinsa Zane ne gashi Babu wata sitirara kirki a jikinsa Dan jikin sama babu riga daga shi sai D'an kamfai.ke da inganshi dama zaki Gane ba bahaushe bane yare ne saboda yadda kaman ninsa suke, Amma idan kikaji Hausa a bakinsa kamar jakin kano.sanye yake da kaya irin na bokaye ya d'aura Wani Bak'in k'yalle a k'ugunsa sai Wani Abu Mai kama da fata daya d'aura a saman k'ugun nasa sai wasu layu Daya d'aura a duka dantsan hannunsa, gabansa kuma wasu k'warayene Wanda ke d'auke da kayan sidda barunsa aciki ,wasunsu ruwane aciki wasu Kuma wasu Irin ganyayyakine da garin magun gunan Iri daban daban na k'asa she daban daban. Gaban sa kad'an wata matace zaune tana kallansa Yana wasu Irin sum batu Amma sai naga idonta yana kansa da dukan alamu tasaba da zuwa wurin Dan naga ko tsoro Babu a tare da ita.sai da ya gama Sumbatunsa sannan ya kalleta da jaja jayen idanuwansa yace cikin wata iriyar murya wacce babu dad'in sauraro. "Wannan Karan mafa sai dai ke kiyi aikin da kanki ,Dan bazai yu Wani yay miki ba dole sai dai kije da kanki kisa mata maganin kamar yadda kika Saka mata a nafarko ,Wanda ta daina magana sannan kuma ta daina moruwa kwata kwata, to yanzunma idan kinaso aikin ya K'ara shigarta saidai kije da kanki Amma bazai yu mu tura aljanin muba aje a sake K'ona su a Banza kamar yadda akai waccen lokacin sukazo suka Sha jinya kamar bazasu tashi ba". Ya fad'a Yana zarewa gimbiya Hajara ido. Sha kudum ta gyara zamanta kamar zatai kuka Gaban ta na fad'uwa dum dum kamar zai tsage biyu tace. "Yanzu boka barzuk Babu yadda za'a Yi atura wani hatsabibi a cikin aljannun yaje yayi? wallahi wancan Karan ma daka sani nai da kaina nafi wata biyu kafin nasamu nai narasa akanta". Ta fad'a kamar zatai kuka.boka barzuk ya sheke da wata iriyar dariya har saidai wannan bukkar da suke ciki ta ansa dama ilahirin zagayen wajen gabad'aya, boka barzuk Yana kashe leb'e yace. "Yanzun ma zaki iya ai yadda kikai waccen aikin haka Zakiyi wannan ma". Shakundum tai shiru tana kallansa Gabanta har lokacin Bai daina fad'uwa ba, Dan Bata manta da waccan Karan bama Dan ba k'aramin wahala Tasha ba kafin tai nasarsa a kan gimbiya Aysha ba, Dan Saura kad'an ma a kamata Allah dai ya taimaketa..boka barzuk yace. "Ai yanzu aljannu baza su iya tun karar gimbiya Aysha ba, saboda addu'o'in da ake mata ana shafe mata duka jikinta dasu sannan ai mata rubutu Tasha Banda Karatun Al'qur'ani da Azkar da ake kunna mata kullum ta kwana Dashi tana sauraro.kinga ko ai babu Wani aljani duk mun hatsabibancinsa da zai iya zuwa yace zai tun kareta ta ko Kuma kusantarta,wancan lokacin ma Dan ke kikai aikin da kanki shiyasa komai ya faru.sannan ga can gidan iyayennta Suma Basu zauna ba kullum cikin addu'a suke mata da saukar Al'qur'ani sannan ga itama surukarku yadda Bata bacci Babu dare babu Rana tana tsaye Gaban ubangiji tana Kai masa kukanta Kuma duk akan matar d'anta da Kuma jikanta mafi soyuwa agunta". Ya k'arasa fad'a Yana Wani Irin murmushi.shakundum da duk ta jik'e da gumi Jin abinda boka barzuk ya fad'a tace cikin sanyin jiki. "Shikenan naji Zanyi da kaina boka". Boka barzuk Yay Wata iriyar dariya yace. "Yauwa 'yar gari ai dama nasan zaki iya" Sai Kuma yace. "yanzu me kike buk'ata ai miki Kuma ?... Ya fad'a Yana kallanta. shakundumTace. "so nake a kashe min ita kowa ma ya huta". Ta fad'a cikin b'acin Rai.boka barzuk yace. "kisa Kuma ? To bazai yuba domin tun ba yau kike so akashe taba Kuma Nasha fad'a miki gimbiya Aysha tana da tsawan Rai sosai Anan gaba shiyasa ma tun farko da Kika zo da wannan batun na ce Miki bazai yuba". Ya fad'a Yana kallan shakundum. Shakundum ta sauke numfashi tace. "to tunda kisan bazai yuba inaso ahauka tata tabi duniya ta yadda babu Wanda zai K'ara ganin ta bare Kuma aji labarin ta,dan so nake a Nisan tata da masarautar zazzau gabad'aya da shi kansa Mai martaba ko zai daina abinda yake min ya dawo da hankalinsa kaina kaga idan ta tafi daga can ta had'u da ajalin nata Idan ma ni ban kashe tanba ." Ta fad'a har cikin zuciyarta wacce Babu ko d'igon imani acikin ta.boka barzuk yace. "an gama".daga haka Kuma ya fara wasu Irin abubuwan sihiri ya d'auki tsawan mintuna Talatin yanayi sai kuma ya d'ogo ya kalli shakundum yace."Baganta ba Duhu kawai nake Gani". Shakundum ta zaro ido waje tana kallan boka barzuk tace. "Duhu Kuma barzuk.boka barzuk yace. "Tabbas duhu nake Gani dama fa na Sha faday Miki tana tare da Kariyar addu'o'in ubangiji shiyasa bazan iya ganin taba amma akwai mafita zan Baki duk abubuwan da zaki bi wajen hauka tatan akwai mata kai dayawa Wanda duk sai Kin bisu kafin aje ga wannan matakin shima idan akai ba wai take zata haukace ba ko Kuma tabar masarautar ba, dole sai Kin dawo nan kin karb'i Wani maganin da layu Shima Kuma sai tayi watanni kamar biyu tana hauka anan cikin masarautar sannan zamu mata kurciya tabar masarautar zazzau na har abada". Ya fad'a Yana Wani shek'ewa da wata iriyar dariya. Sai alokacin shakundum ta sauke ajiyar zuciyar salama duk da za'a d'au lokaci kafin komai ya kammala Amma Kuma hakanma sai taji taji Dad'i sosai jin za'a haukata gimbiya Aysha. Ta Kalli boka barzuk tace. Amma barzuk Babu yadda za'ayi ayi aikin a kusa". Boka barzuk yay mata wata tsawa yace. "Bafa ke kad'ai zaki aikin ba muma nan akwai abinda zamu tai Maka miki dashi sannan shi kansa aikin yana da matuk'ar Wahala dole sai anbi komai a sannu tukunna zamu kai inda muke San kai war". Gimbiya Hajara tace.."ayi hak'uri boka Mai zamani tuba nake".boka barzuk Yay k'wafa yace.. "sai Kuma me kike buk'ata?...". Ta k'ara gyara zamanta tace. "Sai Kuma sultan" boka yay shiru Yana sauraran ta tace. "Inaso ne a K'ara sa masa wani ciwon akan nada Dan so nake kullum ace Yana kwance Yana hauka shima baya moruwa ko kad'an kamar yadda uwarsa take sannan a K'ara nesanta sarki dashi yadda ko tausayin sa karya K'ara ji, bare Kuma ya dinga d'aukar sa a matsayin wata Rana zai masa amfani Dan naga fa yanzu har wai school yake zuwa ni Kuma abinda bana so kenan naganshi Yana rayuwa lafiya lafiya" .Ta fad'a tana kallansa. Boka barzuk yace . "Hakan bazai yuba Dan soyayyar sarki da sultan ginan Niyace ta har abada saidai A K'ara masa Wani ciwon, Kuma Shima sai lokacin da muka samu dama Dan Yanzu yana cikin tsarin addu'a na fad'a miki dukansu addu'a ake musu babu dare babu Rana". Shakundum ta had'e Rai azuciyarta tace. "wai maiyasa ake musu addu'a ne ba'a tab'a Bata dama tai nasara akansu lokaci D'aya dole sai an d'auki lokaci kafin asirin ya kamasu to kodai sun fara ganowa cewa asirin ake musu ba ciwon Allah da Annabi bane ba, Amma Kuma babu komai tunda zai Yuwu ba wai bazai yuba ai da sauk'i,Kuma dole sai tabi duk yadda zatai Dan adaina musu wannan addu'ar.maganar da boka barzuk yay ne yadawo da ita daga duniyar tunanin Data tafi.yace. "sai Kuma me?.." tace. "sai Kuma Anam". Tun kafin ta k'arasa fad'a boka barzuk ya daka mata uwar tsawa yace. "Kul karki sake fad'ar haka Zainab Anam tafi k'arfin mu yarinyar da tun tana ciki take tsare cikin addu'o'i da Kariyar ubangiji ko kin manta attabun da muka shayi akanta Wanda har Hakan ya kusan zama silar rayuwarmu". Shakundum tace jiki na rawa Dan har lokacin batai recovering daga tsawar da boka barzuk yay mata ba tace Baki na rawa . "Ban manta ba". Boka barzuk yace. " Tom sai a kiyaye nan gaba". Shakundum tace. "Na d'auka".ya K'ara cewa ".Sai Kuma me?..." Tace. "Shikenan", nan ya had'o mata duk magun da ganyayyakin da zatai amfani dasu cikin wasu takaddu sai layu kusan guda biyar ya zube a gabanta Yana kallanta yace. "gasunan, wannan maganin k'ulli shida ne ko wanne akwai number ajiki daga number 1 har 6 Kuma duk ta number zamu bi muyi aikin tun daga number ta farko harta k'arshe Ina fatan kinji?.. shakundum ta gyad'a masa kai yace. "Yauwa to kije dasu zamuyi waya idan har kin shirya".cikin farin ciki shakundum ta d'auka tasa acikin jakarta sannan ta ciro kud'i naira million goma ta ajiye agabansa sannan tai Mai sallama ta fita daga cikin bukkar ta baya .. Bak'aramar tafiya tai ba kafin ta fito daga kan wannan tsauni kafin ta k'arasa inda amintaccen dogarin gidan Wanda yake mata aiki wato haladu,inda yay parking motar,Yana ganin ta yay sauri ya fito daga cikin motar ya Bud'e mata bayan motar yana mata kirari har ya rufe sannan ya zaga driver seat da sauri ya shiga ya ta-da motar suka bar wajen da gudu sai palace....... HUYAAM LAMID'O AZIZ CHIROMA AFEEF *Muje zuwa mutanan MRS SARAKIES .ke daga Jin salon labarin kinsan zai k'ayatar ya Kuma fad'akar.akwai chakwakiya sosai anan gaba Dan labarin ma yanzu muka fara shi*. *ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in 2270127432 Naja'atu umar Zenith bank Evidence of payment (shaidar biya )via