← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 85

Sashe 49

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Bismillahirrahmanirrahim* ____________ Da k'yar shakundum ta iya d'aga k'afarta daga nan Bakin toilet d'in ta fara Takawa zuwa cikin d'akin nata a hankali fargaba da tsoron waye yake mata knocking a wannan tsohon daren kawai ke mata kai kawo a cikin zuciyarta .dai ta Dai daita kanta ta fara k'ok'arin Yi saboda yadda jikinta yake Wani Irin rawa kamar mazari jiki a Sanyaye da k'yar ta iya Bud'e Baki tace. "Waye?..." A tsorace. Safara ce Dake Bakin k'ofar tai saurin cewa k'asa k'asa . "Nice ranki Dad'e". Ta fad'a kamar wata munafuka .Take shakundum ta Sauke wata wawuyar ajiyar zuciyar salama Jin muryar safara Dan duk d'aukarta ko Mai martaba ne Dan tasan Babu Mai zuwa mata b'angaren a wannan dare in ba Shiba, Amma Kuma ko shi d'inma Bai tab'a zuwa mata b'angare a Irin wannan lokacin ba,kawai dai abunka da Marar gaskiya shiyasa ta firgita Lokaci D'aya.d'aga murya tai tace. "Meya faru zaki zomin b'angarena a Irin wannan lokacin?..." Ta fad'a a fusace.safara tace cikin ladabi. "Ranki Dad'e sak'on da kika ce na kawo Miki k'arfe D'aya na dare saboda kada kowa ya ganni shine na kawo mikin".ta fad'a tana jiran ansar shakundum.Ajiyar zuciya shakundum ta sauke Dan shaf ta manta da maganar da sukai da safara d'azu wajen k'arfe goma na dare akan zata kawo mata Sak'o.Batace komai ba illa Bud'e k'ofar da tai tana kalle kallen Dan kada Wani ya gansu kafin ta mik'awa safara hannunta akan ta Bata . cikin girmamawa safara ta fito da Hannunta Dake cikin k'aton hijab d'in data Saka ta fito da abun data kawo matan ta mik'a mata Wani Abu Wanda ni kaina bansan menene ba ke d'aure acikin Leda an nannad'e shi da kusan linki biyar na Leda wanda yasha Nad'i bana wasa ba.karb'a shakundum tai tai k'asa da murya tana kallan safara tace. "Kin tabbata Babu Wanda yaga fito warki?. Tafad'a da sigar gargad'i.Jin Jina mata kai safara tai kafin tace cikin k'asa da murya. "Eh! Babu kowa ranki Dad'e". Sha kundum ta Jin jina kai kafin tace. "Shikenan jeki".daga haka tai saurin kulle k'ofar ta koma ciki.barin bakin k'ofar safara tai tana kalle kalle itama ta bar b'angaren gabad'aya ta koma nasu...Koda wasa shakundum batai gigin Bud'e wannan abu da safara ta kawo mata ba, iyaka kawai tsayawa tai a tsakiyar d'akin ta zuba masa ido tana kallansa Bata ko kiftawa tana sakin murmushi lokacin D'aya ga Wani Irin farin ciki na shigarta tana ganin kamar tana gab da Samun nasarsa ta ne. jujjuya shi ta fara yi a hannunta kafin ta K'ara sakin Wani shu'umin murmushin tana Ganin burinta na gab da cika .Sauke numfashi tai tareda takawa a hankali ta k'arasa inda duk take aje kayan k'ulle k'ullenta irin wannan tai masa mazauni Mai kyau Wanda Babu Wanda ya isa ya Gano inda yake inba ita data ajiye ba.barin wurin tai ta Koma saman gadonta ta kwanta tana lumshe ido.koda ta kwanta d'in ba bawai baccin tai ba duniyar tunani kawai ta fad'a tana tsare tsaren yadda zata samu mafitar samun gudanar da aikinta yadda zai tafi successful batareda an samu wata matsala ba haka ta dinga sak'awa da kwancewa Wanda da k'yar bacci b'arawo ya iya saceta a wannan dare Dan zamu iya cewa ma sai kusan asuba ta samu baccin yay awan gaba da ita........ Washe gari wajen k'arfe goma da Rabi na safe.Anty Amina ce Zauna a d'akin gimbiya Aysha tana Bata tea. Bayan gimbiya Aysha ta gama sha ta fara goge mata bakinta da duk inda ta Bat'a da tissue sannan ta d'auko maganinta ta Bata Tasha.knocking k'ofar d'akin akayi Hakan yasa Anty Amina ta juya tana kallon k'ofar kafin tace. "waye?.." Muryar baba uwani taji tace itace Hakan yasa Anty Amina ta Bata iznin shigowa.turo k'ofar baba uwani tai tashigo d'akin hannunta rik'e da Wani kullin magani a farar leda ta k'arasa inda anty Amina take tana kallanta tai murmushi ganin yadda anty Amina ta zubawa hannun nata Ido.tun kafin Anty Amina tai magana baba uwani tace. "Ranki Dad'e Mai babban d'aki ce tace idan za'a yiwa fulani wanka mudinga d'iba kad'an kad'an muna zuba wannan maganin a cikin ruwan wankan". Ta fad'a tana kallan yanayin Anty Amina. "Anty Amina ta sauke numfashi kafin ta Kalli baba uwani tace. "to shi wannan d'in maganin meye?. Baba uwani tai murmushi tace. "Ranki Dad'e tace maganin karya sihine". Anty Amina ta tab'e Baki tace. "Nifa banasan Irin wannan magun gunan na gargajiya da inna take cewa ayiwa Yaya gimbiya amfani dashi Dan wallahi ba so nake ba,Dan Wani ma bakasan ayina aka samo Shiba,Mai kyau ne marar kyau ne sai Allah Amma inna ta dage tace wai dole sai anyi amfani dashi". Ta fad'a cikin damuwa.baba uwani murmushi kawai tai kafin tace. "To Ranki Dad'e kar ayi amfanin dashi kenan?..." Anty Amina tai saurin cewa a'a ai dole idan Ba'ayi bama idan tazo kinsan saita tace mun Raina mata k'ok'arinta da takeyi". Baba uwani tai murmushi tace. "gaskiya kan to bari na shiga na Had'a ruwan wankan". Anty Amina ta ansa mata da to...Babu Dede'wa baba uwani ta had'a ruwan wankan ta fito daga cikin toilet d'in tana kallan anty Amina tace. "Ranki Dad'e an had'a". Anty Amina tace. "to shikenan k'araso mu kamatan". Ta fad'a tana mik'ewa baba uwani ta k'araso suka kama gimbiya Aysha da dabara da komai kamar yadda suka Saba suka shigarta toilet d'in...Bayan Wani lokaci suka fito da gimbiya Aysha suka zaunar ta nan Saman wata kujerarta Dake nan d'akin Wacce idan ta gaji da kwanciyar suke dawo da ita Kai ta huta.baba uwani tana kallan anty Amina tace. "Ranki Dad'e Adama mata kunun yanzu ko sai anjima". Anty Amina tace. "A'a ki bari zuwa anjima da Rana ko Kuma da yamma sai adama matan tunda Kinga yanzu ta gama cin abincin". Baba uwani tace. "To to Shikenan babu damuwa bari naje na k'arasa aikin da nakeyi"..anty Amina ta kalleta tace. "Allah ya saka Miki da Alkhairi baba muna godiya sosai da d'awai niyar da kike tayani Yi da Yayata Allah ya bar zumunci". Ta fad'a cikin Jin dad'in yadda baba uwani Bata Wani damuwa ko nunawa afuska alamar gajiyawar d'awainiyar da take da gimbiya Aysha.baba uwani da har ta juya ta juyo tana kallon anty Amina tai saurin cewa. "Haba haba ranki Dad'e yanzu duk abinda naiwa Fulani Aysha kina ganin na Fad'i ne? Ai ko kad'an ban biyata kan abubuwan datai min ba,idan ban tsaya kan duk Wani Abu da ya sameta na farin ciki ko na Bak'in ciki ba Mai Zanyi ni uwani?ashema na zama butulu indai ban tsaya tsayin daka na kula da ita halin da take ciki ba , saboda haka Dan Allah ranki Dad'e karki K'ara min godiya akan wannan D'an abinda nake Yi , wallahi Ranki Dad'e Ina Jin gimbiya Aysha ne araina kamar 'yar data fito daga cikina.damuwar ta damuwa tace ,Haka samun lafiyar ta Nima shine farin cikina a kullum muna addu'a da Allah ya tashi kafad'unta Allah ya Bata lafiya". Tafad'a cikin rauni.anty Amina ta sauke numfashi tace. "Shikenan baba mungode Allah ya bar zumunci". Baba uwani tace. "Ameen thumma Ameen bari naje" daga haka ta nufi k'ofar fita daga d'akin..Anty Amina Kuma ta d'auki lotion ta fara Shafawa gimbiya Aysha kafin ta gama ta shiryata cikin wata doguwar rigar tsaddan material d'inkin doguwar riga wanda dai bazai takura taba. bayan ta gama tai parking d'in doguwar kitson kalbar datai mata two days ago da rinbbom tana Kallon gimbiya Aysha tai k'asa da murya tace. "Na barki kan kujerar ko Kuma na kaiki saman gadon?..." Tafad'a tana kallanta Dan jiran ansarta. Gyad'a mata kai gimbiya Aysha tai kamar da wasa.take Anty Amina ta saki murmushi tace cikin Wani irin shaukin farin ciki Daya shigeta lokaci D'aya ganin yadda yau dai gimbiya Aysha ta gyad'a kai da kanta da da ko d'aga kan nata batayi Amma yau itace tai nudding kanta ai da Wani Irin farin tace. "Yaya gimbiya yanzu kece kika gyad'a mini Kai haka?.."ta fad'a har sannan murmushi ne a saman fuskarta.Lumshe idonta gimbiya Aysha tai,anty Amina ta d'aga hannunta sama tace. cikin Wani irin farin ciki. "Alhamdulillah ya Allah! Allah mun gode Maka da wannan ni'ima da kafara mana ,ya Allah ka bawa wannan baiwa taka lafiya Mai d'orewa ta har abada gabad'aya da ita duk Wasu masu fama da jinya" sai Kuma ta Sauke hannunta k'asa nan ta fara gyara mata zamanta akan kujerar. Bud'e k'ofar d'akin akayi Hajiya inna ce ta shigo.Anty Amina ta juya tana kallon k'ofar Jin anbud'e taga Hajiya inna ce take ta saki murmushi tana kallanta .Hajiya inna ta ta rufo k'ofar tana kallan anty Amina tace. Haya niyar me nake ji Ina falo lafiya dai ko?.." Anty Amina na murmushi tace. "Wallahi inna yanzu Ina tambayar yay gimbiya akan na barta nan Saman kujera ko Kuma na kaita kan gado kawai naga ta gyad'a mini kanta abinda ban tab'a Gani ba ko tunani tunda ta fara jinyar nan.." Ta fad'a tana no kasa b'oye farin cikinta. Mamaki ya bayyana sa man fuskar Hajiya inna itama Batasan lokacin data k'arasa shigowa cikin d'akin ba tana kallon Anty Amina tace. "Ke da Gaske Dan Allah Amina ko dai wasa kikeyi?.Anty Amina na murmushi tace. "Wallahi Hajiya". Hajiya Inna itama ta d'aga hannayenta sama tace cikin farin ciki. " Allah mun gode Maka,ya Allah yadda ka nuna mana wannan Rana ya Allah ka nuna mana ranar da Aysha zata samu Lafiya gabad'aya". Anty Amina na murmushi ta ansa mata da "Ameen ya Allah inna". Hajiya Inna ta shafa addu'ar ta Kalli gimbiya Aysha Dake Kallansu itama tace. "Aysha Allah ya cigaba da Baki lafiya Kinji?.." this time around lumshe idonta tai sai Kuma ta gyad'a musu kan ahankali". Inna tace. " Wallahi kuwa Nima na gani Allah mun gode maka". Sai Kuma ta kalli Anty Amina tace. "Ina fatan Babu Wanda kika fad'awa wannan maganar dai ko? Anty Amina da har lokacin murmushi ne with surprised a fuskarta ta gyad'a ma inna kai tace. "Babu Wanda na fad'awa inna". Hajiya inna tai k'asa da murya tace. ",to banaso kowa yaji wannan maganar dagani saike Amina Dan ko Mai martaba bazan fad'awa ba gudun sub'utar Baki wannan abun yazama sirrin da har
Chapter 49 · 0% Book details