← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 85

Sashe 39

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Bismillahirrahmanirrahim* ____________ Washe gari da safe har k'arfe shad'aya Saura Huyaam Bata tashi daga baccin safen da take nay Wanda ta koma bayan sallahn ASuba ba, dama tun jiya ta daddare ta kwanta da complain d'in kanta na mata ciwo.nan dai Ammie ta d'auko maganinta ta bata ta Sha,to anan ta samu har bacci ya d'auketa,to d'azu da ASuba ma dai Ammien ta k'ara lek'ata Taga jikin nata da sauk'i Dan har tashi tai tai sallahn ASuba ma. Shine Ammien fa tace kar kowa ya tashe ta a barta ta huta har sai ta tashi Dan kanta.to kuwa wannan maganar datai yasa babu Wanda yay gigin zuwa inda Huyaam d'in ma take har ita Kanta hudan.. Ammie ce ta sauko downstairs ta k'araso falon ta tsaya tana kallan Huda Dake Zaune afalon nan saman kujera tana karanta Wani book daya ke babu kowa Agidan sai iya Hudan tunda su su muneefa sun tafi school tun da safe ya Zarah ma dai itama ta tafi school d'in,Ammei na kallan Huda tace. "Huda Ina HUYAAM na lek'a d'akinta bangan taba?..". Huda ta juyo tana kallon Ammie sai Kuma tace. "Eh tana d'akina can ta koma d'azu". Ammie ta sauke numfashi tace. "To har yanzu Bata tashin bane?..." Ta fad'a tana kallanta .Huda tana kallon Ammien nasu tace. "Eh Ammie har yanzu Bata tashi ba d'azu na lek'a ta sai naji jikinta da zafi".gaban Ammie ya D'an Fad'i Jin abinda Huda ta fad'a sai kuma tace. "Shikenan Allah yasa dai lafiya?.Huda ta Mik'e tana kallan Ammie tace. "Ameen, Amma Ammei bari naje na lek'ata kota tashi ta yanzun?..."Daga haka Huda ta Mik'e daga zaunan da take tana ajiye book D'in hannunta nan saman kujerar data tashi ta haura sama zuwa d'akin nata da sauri.. tura k'ofar tai bayan ta isa Amma sai taji k'ofar a rufe K'ara turawa tai nan ma dai the same thing,Hakan yasa ta fara knocking k'ofar tana turawa lokaci D'aya Amma Kuma shiru Babu alamun za'a Bud'e sai Kuma ta fara K'iran sunan HUYAAM lokaci D'aya da cewa ta Bud'e k'ofar itace amma Shiru Babu alamun za'a Bud'e k'ofar nan dan tafi mintuna 10 tana knocking k'ofar Amma shiru Huyaam Bata Bud'e ba, gajiya Huda tai da knocking d'in ganin Huyaam bazata Bud'e ba Hakan yasa ta juya zata bar Wajen kenan taje ta sanar wa da Ammie cewar HUYAAM d'in Bata Bud'e k'ofar ba kawai taji Wani Irin K'ara da Huyaam tasa ata cikin d'akin Wanda yasa gabad'aya Saida part d'in ya amsa har Ammie Dake zaune falon downstairs tare da Afeef Wanda ya sauko yanzu Bada dad'ewa ba yana gaida Ammien, kawai Sai Kuma sukaji wannan ihun na Huyaam ga Kuma k'arar fad'uwar abubuwa acikin d'akin Mai kama da fashewar kwalabe kodai something like that.take gaban Huda ya Fad'i zata sauka k'asa kenan suka kusan cin karo da Ammie data hawo upstairs d'in cikin akid'ime hankali tashe Afeef na biye da ita har lokacin HUYAAM ihu take tana kuka Bata kuma fasa bige bigen ta takeyi ba. Ammie ta k'arasa bakin k'ofar ta fara bubbugawa da jijjigawa da k'arfi Tana K'iran sunan HUYAAM Amma shiru bata ansa ba. Afeef ya kalli Huda yace. "Wai meya sameta ne?...." Huda da kamar zatai kuka ta kalleshi tace. "Nima bansani ba Amma Inaga ko ciwon nata ne ya Tashi". Afeef yace. " Ya akai tasawa k'ofar key Kuma? Sannan Mai zaisa kema ki bar key ajikin k'ofar?....". Ya fad'a ransa a b'ace.Huda tai saurin cewa "A'a akan mirror na barshi k'ila d'auka tai Amma bari na d'auko nata sai agwada ko ta cire key d'in bayan ta kulle k'ofar". tana fad'ar haka ta bar wajen tai d'akin Huyaam da sauri" Afeef ya bita da Wani Irin kallo.ita kan Ammie Bai war Allah sai faman bubbuga k'ofar take tana K'iran sunan HUYAAM akan ta Bud'e k'ofar kamar zatai kuka Amma ko alamun Huyaam zata Bud'e k'ofar nan Babu Kuma har lokacin kuka take da ihu ahad'e , gabadaya hankalin Ammie ya gama tashi da halin da Huyaam take ciki ,ita kanta baba magajiya Saida ta lek'o daga kitchen amma Bata haura stairs d'in ba ganin mutanan gidan a wurin.ahaka har Huda ta kawo key d'in ta Mik'awa Afeef, kamar bazai karb'a dan Gani yake kamar Huyaam d'in tabar key d'in ajiki ne ,nan ya matsa kusa da k'ofar yana Kallan Ammie Dake ta K'iran sunan HUYAAM akan ta Bud'e k'ofar yay k'asa da murya cikin lallashi yace. "Ammie bari na Bud'e,ki kwantar da hankalinki bari na gwada ko k'ofar zata Bud'e". Ammie ta kalleshi tace cikin Damuwa. "Ka gafa Afeef sai ihu take tana fashe fashe kar naje ta jiwa kanta ciwo fa ?.." ta fad'a murya a karye . Afeef yace. "In Sha Allah babu abinda zai sameta bari nai trying idan ma baiyi ba sai a b'alla k'ofar kawai".ya fad'a cikin lallashi da k'yar Ammie ta D'an matsa baya Afeef yasa key d'in Amma Kuma sai dai Kash akwai key ata ciki ajikin k'ofar ,nan shima hankalin Afeef d'in ya K'ara tashi Ganin to ta inama za'a fara, bare a cetota daga jiwa kanta ciwon da takeyi Dan yasan Hakan ce zata faru .sauke numfashi yayi ya kalli Ammie yace. "Da key ajikin k'ofar Ammie dole sai dai a b'alleta". Ammie ta girgiza kai tana kallonsa tace. "Afeef waye zai b'alle k'ofar gaskiya bazan iya jire har sai an k'ira Wani Mai b'alle k'ofa ya zoba ni tsorona ma karta jiwa kanta ciwo Dan Allah Afeef ya za'ayi?..." Ta fad'a cikin damuwa.Afeef ya K'ara k'asa da murya yace shima cikin damuwar Dan fa da Gaske Huyaam buge buge kawai take acikin d'akin nan tana kurma ihu lokaci D'aya yace. "Ni zan b'alla k'ofar Ammie ki kwantar da hankalinki Babu abinda zai sameta"? Ammie ta girgiza kai tace. "To Kuma yanzu Afeef idan kaje ka b'alla k'ofar ta fad'a a kanta fa?...." Afeef yace. "In Sha Allah ma Hakan bazai faruba ku matsa baya". Ya Kalli Huda wacce sai kuka take yace. "Taja Ammie suyi baya". Babu musu Huda ta rik'o hannun Ammie da k'yar ta iya yadda Huda ta kamata suka matsa baya Nan Afeef shima yay baya kad'an ya daki k'ofar da K'afarsa Amma ko gizau batai ba ya kuma Dakar k'ofar nan ma dai babu alamun k'ofar zata Bud'e.ya kusan 5 minutes Yana k'ok'arin ganin ya b'alla k'ofar Kuma da dukan k'arfinsa yakeyi Amma k'ofar nan ko gizau batai ba kamar wata k'ofar rodi,wata dubara ce ta tazo masa na Mai zai Hana ya daki dai dai inda key d'in yake. nan ya fara dukan saitin wajen key d'in k'ofar ,da k'yar da k'yar k'ofar ta Bud'e akai Sa'a Bata balle bama gabad'aya Dan iya wajen key d'in ne kawai ya tashi daga aiki sai dai a sake Saka Wani .. cikin sauri ya shiga Ammie ma ta k'araso da sauri ganin ya b'alle k'ofar har suna rige rigen shiga ita da Huda. tsaye suka Samu Huyaam a birkice, Sanye da kayan bacci riga da Wando, kannan nata da babu D'an kwalli bare hula ribbon d'in ma yay nasa wajen gashin nan nata ya bar baje nan tsakiyar kanta hannunta rik'e da wata kwalbar turare wacce ta fashe Kuma har lokacin Bata daina kuka da ihun da take ba tana ta dukan bangon d'akin da kwalbar turaren hannunta da duka k'arfin ta, ga yadda ta wargaza d'akin kamar Babu wata halittar data tab'a rayuwar acikinsa saboda yadda taiwa d'akin kaca kaca Dan kuwa babu matsakar tsinke acikinsa ko Ina kwalabene da kayan kwalliya data b'aro su daga kan mirrorn,ga k'afar ta da hannunta sai d'igar jini sukeyi alamar dai ta yanki jikinta.Afeef dai kallanta Kawai yake cikin tausayawa can ya taka zai kanta ya rik'o ta ganin haka yasa Huyaam tai baya da sauri tana zare masa ido tana yin baya at the same time tana sakin Wani ihun da k'arfi , Afeef Bai kula ta ba ya bita ya rik'o ta Cikin dabara da sauri, ganin ya rik'o ta yasa ta rikice masa ta fara k'ok'arin k'wacewa daga rik'on da yay mata Tana ya gunsa tana Kuma K'ara sakin wani ihun da iya k'arfinta, Wanda Saida yasa Afeef ya rintso idonsa ya rik'o ta zuwa jikinsa Bata fasa kokawa dashi ba tana Neman k'wacewa hakan yasa Ammie ta k'araso ta rik'e ta itama Afeef ya sakar mata ita ganin Ammien ta rungumeta zuwa jikinta tana cewa. "HUYAAM menene? Stop it please sorry daughter ya Allah! Innalillahi wainna ilaihi rajiun". haka kawai Ammie take fad'a sannan ta jawota suka Zauna nan gefen gadon har lokacin huyaam tana jikinta rungume da ita .Afeef ya D'an matsa kusa dasu ya rik'o hannun Huyaam d'in Dake k'ok'arin fusge gashinta nan ya fara Yi mata addu'ar duk da tazo bakinsa Ammei na tayashi kafin ta kalli Huda Dake kallan Huyaam da tausayawa tana jero mata Sannu tace. "jeki d'auko mun maganinta a d'akina Yanzum nan". Babu musu Huda ta fita daga d'akin cikin sauri". Babu dad'ewa ta dawo Hannunta rik'e da goran maganin ta Mik'awa Ammie. nan Ammie ta karb'a ta Bud'e ta shafa mata a fuskarta sai da tai mata Sau uku har lokacin Afeef addu'a yake mata kafin can ta daina ihun ta fara sakin numfashi tareda ajiyar zuciya lokaci D'aya shi dai Afeef kallanta Kawai yake cikin tausayawa yadda fuskarta tai jaga jaga da hawaye,saida sukaga bacci ya d'auketa sannan Afeef ya daina mata addu'ar.Ammei ta kwantar da Huyaam nan saman gadon bayan sun gyara shi ta fara duba K'afar HUYAAM Dake d'igar jini da Hannunta take hankalinta ya K'ara tashi Ganin yadda kwalbar duk ta yanki Huyaam ta kalli Afeef tace cikin Damuwa. " Kaga fa Afeef ta yanke ko kwalbar ma ta shiga k'afar tata ne naga sai d'igar jini takeyi?..." Afeef da shima kallan k'afar Huyaam d'in yake da kuma hannun nata yace. "Bari a k'ira doc". Ammie na kallansa tace. " To Maza Dan Allah" Sai Kuma yace. "Wai dama har yanzu Bata daina wannan abun ba?.." Ammie tace cikin Damuwa "Eh! har yanzu Bata daina ba, Da ya lafa Amma naga Kwanan nan Yana yawan tashin mata".ta fad'a cikin Wani Irin sauti . Afeef ya Jin Jina kai yace. "Allah ya sawak'e". Ammie Tace. "Ameen jiki a Sanyaye so nake ma mu koma
Chapter 39 · 0% Book details