Sashe 41
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Bismillahirrahmanirrahim* ___________ *Bayan kwana biyu* K'arfe shida Saura na ranar Sunday. Dawowar su daga islamiya kenan bayan an sauke su a mota kowa ya shiga b'angaren su . gabad'ayansu suka shigo falon bakinsu d'auke da sallama.Babu kowa a falon sai hadiman Ammie da suke ta kai kawo a falon suna gyara ko ina ganin komai yayi tsaf tsafa Kamar yadda sukeyi koda yaushe.sannu da zuwa suka shiga yiwa su Huyaam bayan sun ansa musu sallamar tasu.ansa musu sukai da Kulawa suna musu sannu da aiki.kafin su shige Cikin falon gabad'aya ga dama sai K'iran sallahn magrib akeyi aduka masallatan Dake nan kewayen masarutar tasu harma da masallacin cikin palace d'in.haurawa sama sukayi kowa ya shiga d'akinsa Dan zuwa su rage kayan jikinsu.huyaam ce ta tura k'ofar d'akinta tashiga Sai Wani wak'e Wak'en larabci takeyi kamar ba ita bace tai Rashin lafiya shekaran jiya ba,gashi har ta warke kamar Bata tab'a wata jinya ba, kodan dama ita Irin wannan jinyar haka take na d'an lokaci ne idan kayi kana tashi Kuma Zaka jika kamar baka tab'a yin wata jinya ba .kullo k'ofar tai bayan ta shiga ta k'arasa cikin d'akin.rage uniform d'in jikinta ta farayi kafin ta k'arasa wodrobe ta d'auki wata sassauk'ar doguwar rigar roba marar nauyi tasa. Mararta ta dafe jin yadda fitsari ya cika mata ita tai hanyar toilet d'in da sauri tashiga ta rufo k'ofar Dan dama tun a school ta fara Jin fitsarin Amma Batai ba ta bari saita dawo gida sai tayi.babu dad'ewa ta fito jikin ta da Danshin ruwa alamar har alwala ma ta d'auro,ta k'arasa inda darduma take ta d'auko D'aya ta Shimfid'a anan tsakiyar d'akin kafin ta Bud'e wardrobe d'inta ta d'auko go geggen hijab d'inta tasa sannan ta dawo kan dar dukan ta ta-da sallah.bayan ta idar tai azkar d'inta tana gamawa ta mik'e ta linke dar duman ta Maida inda take sannan ta k'arasa inda Al'qur'aninta yake ta d'auko D'aya ta fito daga d'akin nata ta jawo k'ofar ta rufe sannan ta sauka downstairs har lokacin Bata cire hijab d'in jikinta ba. Tana K'arasawa falon ta tarar har su Huda sun fara tulawar haddarsu ta islamiya zama tai itama tai joining d'insu nan ta fara nata haddar itama.. K'iran sallahn isha'i da akeyine daga masallacin palace d'in yasa duk suka dakata da karatunda da sukeyi bayan sun kai aya sukai addu'o'i sosai.ganin za'a shiga sallahn yasa duk suka mik'e suka bi jam'i Dan babu Abinda basaji na Karatun sallan da ake daga cikin masallacin... Ammie ce ta saukowa downstairs d'in ta tsaya anan bakin stairs d'in tana kallan baba magajiya dake jera warmers a dining d'in,kafin ta maida dubanta kan su Huyaam ta zuba musu ido tana kallansu, suna Zauna saman kujerun falon suna kallo Dan tun bayan da suka idar da sallahn isha'in Huda ta linke k'atuwar daddumar da suke karatun akanta ta Maida inda take sannan ta dawo suka zauna nan falon suna kallo. baba magajiya ce ta k'araso inda Ammie ke tsaye ta tsugunna har k'asa tana kallanta tace. "Ranki Dad'e an gama had'a teburin". Ta fad'a Cikin girmamawa. Ammie na kallonta tace. "To magajiya sannu da k'ok'ari yanzu zaku koma bangaren nakune?". Ta fad'a tana kallan ta.Baba magajiya na tsugunne kanta a k'asa tace. "Eh ranki Dad'e ko akwai abinda kike buk'ata ne?. Ammie tace. "A'a Babu komai kawai tambayar ki nai dama". Sai Kuma tace. "yauwa! Magajiya idan kika shiga kitchen d'in akwai wata kula acan wajen fridge kan kanta ki d'auka ki tafi da ita". Baba magajiya tace. "To ranki Dad'e na nagode sosai Allah ya K'ara girma da sutura Allah yasa afi haka". Ammie tace. " Ameen tashi kije". Daga haka Ammie ta k'araso cikin falon.cikin girmamawa baba magajiya ta ansawa Ammie sannan ta mik'e ta wuce kitchen Dan d'aukar Sak'on da Ammie tace ta d'auka. Ammie na kallan su ya Zarah tace. "To ku taso muje kuyi dinner".Babu musu suka mik'e D'aya bayan D'aya suka k'arasa dining d'in. Sunyi nisa da cin abincin ya Haidar ya shigo tareda Afeef Dan daga masallaci suke bakinsu d'auke da sallama.gabad'ayansu suka ansa musu suna kallansu.ya Haidar ne kawai ya k'araso dining d'in ya zauna yay joining d'insu har Yana tsokanar Huyaam itadai sai tura Baki take tana cewa ita ba haka bane ba . shiko Afeef kallo D'aya yay musu ya wuce stairs d'in b'angaren su tun kafin ma su samu zarafin masa magana.bai dawo ba kuma har suka gama cin abincinsan . Sun dawo falon suna zazzaune harda Ammie dake zaune a falon itama,ta kalli wayarta ganin k'ira ne ya shigo Kuma Afeef ne ke K'iran nata Hannu tasa ta d'auki wayar ta kai kunne, ajiye wayar tai bayan taji abinda ya fad'a mata tana kallan Huyaam tace. "HUYAAM". HUYAAM ta juyo tana kallon Ammie tace. "Na'am Ammie". Ammie tace. "Jeki had'owa yayanku abinci ki kai masa falonsa". Tana fad'ar haka tai shiru.huyaam ta ansawa Ammie kafin ta Mik'e ta k'arasa dining d'in dama tasan Mai yake so Dan shi ba ma'abocin cin abu Mai nauyi bane ba da daddare ba.k'aramin tea flask d'in Dake kan dining d'in ta d'auka wanda ke d'auke da ruwan zafi aciki sai cup D'an tasan coffee zai had'a kuma Yana da komai da zai had'a coffee d'in acikin d'akin nasa. sai wata k'aramar warmer data d'auka da plate da spoon duk ta D'ora akan Wani madai daicin tray sannan ta bari dining d'in ta haye sama zuwa b'angaren Mazan gidan . knocking tai a Bak'in k'ofar falon nasa bayan ta Isa .Afeef dake zaune a falon d'akinsa nan kan sofa Yana operating system d'inshi.Dan communicating suke da Mr Patrick Akan dai yadda suke tafiyar da aikin companyn nasu ne, duk da baya nan Amma Kuma Yana sanin duk wani abinda ke faruwa a can companyn.sannan Yana sanin duk Wani income da out come da suka samu,Dan dama haka suke tunda ya dawo gidan kullum sai sunyi communicating da Mr Patrick.Afeef ya d'ago da kansa Jin ana knocking k'ofar falon yasan bazai wuce Ammie ce ta Aiko akawo masa abinda yace akawo masa d'inba, iznin shigowa ya Bada.turo k'ofar Huyaam tai bakinta d'auke da sallama ta shigo da tray d'in hannunta ta k'araso ta ajiye nan Saman table d'in Dake gaban sofan da Afeef yake Zaune .ta d'ago tana kallan afeef Wanda ke sanye da black shirt sai dogon Wando Kuma har lokacin Bai d'ago da kansa daga abinda yake ba tunda ya kalleta saud'aya.tana murmushi tace. "Yaya gashi na kawo".. Wani kallo yay mata alamar tana ganin Yana waya Amma take masa magana.hakan da Huyaam taga yayi mata yasa ta Gane Mai yake nufi tai shiru tana kallansa,tsura masa ido tai Ganin yadda yake turanci cikin k'warewa ke bakyace ya iya hausa ba haka ta dinga kallan sa batare da ta sani ba. bata farga ba kawai taga har ya rufe laptop d'in bayan sun gama abunda suke tattaunawa .Yana kallanta Yace cikin tsuke fuska. "Kina da hankali kuwa Ina waya zakina mun magana akaina?..." Ya fad'a Yana mata wani Irin kallo.huyaam tai shiru tana tura Baki gaba Amma Batai magana ba.kallanta kawai yake Yana mamakinta sai Kuma yay tsaki k'asa k'asa ya Kali agogon bangon Dake manne a falon ganin 8: 30pm har tayi,Sauke numfashi yayi ya dawo da kallansa kan Huyaam Dake tsaye tana wasa da zoben hannunta, kallon zoben hannun nata yayi Shima Wanda ya K'arawa hannun nata kyau kafin ya d'auke kansa Yana kallan gefe yace.kije ki k'iramin su Aziza dasu safna ke dukanku 5 candidates d'in nan ki had'u kujirani a falon k'asa yanzu idan na gama zan fito na sameku"..Yana fad'ar haka ya Wani had'e Rai ya jawo table d'in gabansa.huyaam ta ansa masa cikin girmamawa sannan ta fita daga falon ya bita da Kallo Ganin yadda ta taja masa k'ofar..... Ammie na kallon Huyaam tace. " A wannan daren zaice ki fita ki k'ira masa su ikleema akan ya bari Saida safe".sai Kuma ta tuna Ashe fa yace mata gobe Yana da tafiya kuma da wuri zai tafi Hakan yasa tana kallon ya haidar Daya sauko downstairs d'in da dukan alamu fita zaiyi tana kallansa harya k'araso tsakiyar falon tace. "Haidar Ina zaka Yanzu?.yace zan D'an fitane Amma bazan Dad'e ba zan dawo akwai Wani Abu ne?..." Ammie tace. "Eh Akwai,Dan Allah aikenka Zanyi ko Kuma idan ka samu Wani cikin masu aikin gidan ka aika Wani". Haidar yace. ",Ina ne?". Tace. "Yayan kune ya aiki Huyaam ta k'ira masa su Aziza to kuma kaga dare yayi bazai Yu ace sun fita yanzu ba, Kuma ko nima banson aikinsu da daddare shine nace ko zaka k'irasun?..." Haidar yace. wai duka har su safna ko Kuma iya Aziza?..."Ammie tace. "Dukkansu". Yace. "Ok". Daga haka ya fita daga falon..bayan kamar 15 minutes akai knocking k'ofar safnah da ikleema ne suka shiga bakinsu d'auke da sallama har suka k'arasa shigowa cikin falon suka zauna nan saman carpet d'in suna gaida Ammie.Ammie ta ansa musu da kulawa sannan suka gaida ya Zarah itama ta ansa musu. Zaman su a falon da kusan 10 minutes sannan Afeef ya sauko downstairs d'in Kuma har lokacin Aziza Bata zoba kowa yayi mamaki da k'in zuwan nata Amma Kuma Babu Wanda yay magana.Afeef ya k'araso shigowa falon hannunsa rik'e da wata k'atuwar bag sai Wani k'amshi yakeyi na tsadaddan tutarensa. samun guei yay ya zauna nan Saman kujera Yana ajiye bag d'in hannunsa agefensa.Daman already su Huyaam suma sun sauko k'asan carpet d'in sunyi joinin d'insu ikleema.ya shiga k'are Musu kallo ganin su hud'u ne babu Aziza amma baiyi magana ba yay shiru.kansu a k'asa suka shiga gaida shi, Batare da ya Kallesu ba ya ansa musu.huci ya furzar Mai zafi daga bakinsa zaiyi magana kenan Aziza tai sallama ta shigo tana Wani sinne kai k'asa tare da tura Baki gaba. idon da suka had'a da Afeef da Yay mata Wani mugun kallo ne yasa ta sauke idonta k'asa k'irjinta na bugawa da k'arfi dan tasan halinsa ba kad'an ba saidai Ta bawa Wani labari.tun kafin ta k'araso cikin falon Afeef yace. "Kneel down here" ya fad'a da kakkausar murya.ai sai bugun zuciyar Aziza ya K'ara gudu cikin rawar jiki tai abinda yace d'in kafin ta marai raice kamar zatai kuka tace. "Yaya wall... Tun kafin ta k'arasa Afeef