Sashe 69
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__* *__(MRS SARAKIES )__* My channel link https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 4 ___________ Washe gari da safe Kuma da shirye shiryen d'aurin AUREN aka Tashi,tun daga k'arfe 11am na safe Bak'i suka fara sauka a cikin palace d'in,manyan Bak'i wad'an ba ba'a kusa suke ba daga nesa zasu taso zuzo Irin su sarakuna da da governor ni da Manyan 'yan kasuwanni wad'an da suke abokan Mai martaba tun kafin k'arfe Sha biyu suka iso, suna can an sauke su a masauki Mai kyau cikin palace a fadar mai martaba.suna can suna hutawa Kafin lokacin d'aurin AUREN yayi,Dan k'arfe 2:00pm dai dai bayan anyi sallahn juma'a za'a d'aura auren. Ga DSS da police na governor's d'in da suka zo Wanda Suke a matsayin guard d'insu sai shawagi suke a harabar masarutar Kano Dan bawa ubayen gidan nasu TSARO na musamman ke kyace Wani abun ne ya faru marar kyau...Acikin gida kuwa nan ma dam yake da mutane 'yan uwa da abokan arzik'i both b'angagarorin Dake gidan har na Ammie da fulani Salamatu duk akwai mutane aciki saboda gabad'aya familyn su Mai martaba duk sun zo bikin,matan da suka zo Kuma a part d'in matan gidan suka sauka Maza Kuma acan b'angaren Bak'i Dake cikin palace d'in anan Suma aka sauke su.. Amare Kuma suna can b'angaren Antyn su ikleema wata k'anwar su Mai martaba mai suna Hajiya Amma ita ta ce su tattaro kayansu su dawo b'angaren Antyn su ikleema su sameta ita zata shirya su, Babu musu kuwa suka dawo tun a ranar da tazo ta...yanzu haka k'arfe sha biyu da Rabi ne na Rana,Hajiya Amma ce ta turo k'ofar bedroom d'in da Amaren ke ciki bayan tayi sallama.d'aga kai ya zulaihat tai dake zaune kan stool tana shafa lotion tana kallon Ammah.hajiya Ammah ta rufe k'ofar bayan ta shigo tana kallan ya zulaihat ta ce "wai zulaihat tun d'azu da nace kuyi wankan bakuyi ba sai yanzu ko ya_ya?" ya zalaihat ta sunkuyar da kanta k'asa ta ce cikin sanyin murya "Ammah d'azun ummi ce ta k'irani shiyasa ni banyi ba sai yanzu" Hajiya Ammah ta ce "Ina ita Bahijjan take?" Zulaihat ta kalli k'ofar toilet d'in ta ce "tana ciki wanka takeyi" Hajiya Amma ta sauke numfashi ta ce "to ke kiyi Maza ki fito ga Mai kwalliyar nan tana falon Antynku tana k'iranku kunga dai Yanzu saura one hour and some mintutes a d'aura auren, To gara ke ki fito a fara miki kwalliyar lokaci na tafiya" gyad'a mata kai ya zulaihat tai" daga haka Hajiya Ammah ta fita daga d'akin ta koma falon Antynsu ikleema Inda Mai kwalliyar take jiransu.... b'angaren Ammie Shima dai cike yake da Bak'in har cousin sisters d'inta Dake AURE anan kano da yaransu Suma duk sunzo wasu duk sunyi wanka sun shirya suna zaune a falo wasu Kuma suna cikin d'akunan suna wanka tunda yanzu k'arfe D'aya da mintuna.hadiman gidan kuwa sai kai da komowa suke acikin falon kowa Yana aikinsa. su Huyaam Kuma ana can d'aki anai musu make up.... Afeef ne ya saukowa daga stairs zuwa downstairs cikin shigar manyan kaya, yasha milk color d'in shadda da hula zanna bukar wacce ta dace da kayan jikinsa,sai takalmin Daya sa black kalar agogon hannunsa kayan sun masa kyau ba kad'an,Dan ya fito sak a babban mutum sai Wani tashin k'amshi yakeyi fuskar sa tayi Wani Irin fresh kamar Wani sabon ango sai dai fuskar dai babu yabo babu fallasa kamar ko yaushe Amma dai ya kame kansa kamar Wanda baya so akawo masa raini.tunda ya sauko mutanan Dake zaune falon suke kallansa shiko kallo D'aya yay musu Ya d'auke kansa harya k'arasa saukowa falon.da har zai nufi k'ofar falon ya fita Batare da yayiwa kowa magana ba sai Kuma ya fasa ganin akwai manya acikinsu gaishe su yayi cikin deep voice d'insa kamar Wanda baya son maganar.suko suka ansa masa da fara'a har suna tambayar sa kwana biyu shi ba'a Ganin sa wata da take a matsayin kanwar Ammie ce ta fad'a,D'an sakin fuskar tasa yayi Yana sosa kansa Amma baiyi magana ba har ya cigaba da tafiya zai fita daga falon Ammie ta sauko downstairs d'in tana kallan sa juyo wa yayi Jin muryar Ammie ya gaisheta ya ce "zan tafi masallacin Ammie" Ammie ta ce "Allah ya kiyaye" ansa mata yayi Yana fita daga falon gabad'aya.... K'arfe biyu da Rabi dai dai aka shaida d'aurin AUREN su ya zulaihat,Wanda ya samu halartar manyan mutane Wanda duk yawancinsu mutanan Mai martaba ne saboda shi duk suka zo ciki kuwa harda governor kano Dan mai martaba yayi gayya Babu laifi shima.bayan angama anyi reception wasu Bak'in duk suka fara tafiya. alokacin ne Kuma angwaye da Dan dazon abokan su suka shigo cikin palace d'in yin gaisuwar iyaye kowa ya nufi b'angarensa surukansa shida rakiyar abokansa....wata k'anwar hajiya Aysha ce ta ce mutanen Dake falon kowa ya kimtsa ga angon zulaihat nan ya shigo da abokan sa, kimtsawa kowa ya farayi har suka shigo bayan an Basu Iznin shiga sukai gaisuwa bayan sun gama akace za'a Rakasu b'angaren matan sarki su Gaida da su,nan suka fito suka nufi b'angaren Ammie kafin na Fulani Salamatu tunda Ammie ita ce a farko... Ammie na zaune a main falor tareda su Anty khadija da sauran Bak'in Dake b'angaren angwaye suka shigo cikin ladabi suka duk'a har k'asa suka shiga gaishe da Ammie da Sauran mutanan wajen cikin girmamawa. Nan kowa ya ansa musu da kulawa.basu jima ba sukai wa Ammie sallama suka fita sukai b'angaren Fulani Salamatu.... K'arfe 8 dai dai akace za'ayi rakiyar Amare.dan ko wacce a yau za'a kaita gidan ta,tare da key d'in motocin da Mai martaba ya bawa ko Wacce acikin su d'ai d'ai Kuma acikinta Za'a kaita .ita dama ya Bahijja anan kano zasu zauna ya zulaihat ce dai zasuyi two weeks Anan Kano kafin nan da two weeks tabi mijinta zuwa turai inda nan ne yake business d'in sa, Amma Kuma jere da komai duk anan gidan mijin Dake nan kano anan aka Mata jeran.Tun k'arfe bakwai da mintuna Arba'in motocin d'aukar Amaren suka iso kad'an ne suka iya shigowa cikin palace d'in sauran da akazo d'aukar Amaren dasu duk an barsu a nan bakin gate d'in palace d'in ne saboda yawan motacin Dake harabar gidan wanda duk aka fito dasu saboda hidimar bikin ne yasa ba'a Maida suba ma'ajiyar suba, duk suna Parke a nan compound d'in gidan shiyasa harabar palace d'in ta cika ba damar ashigo da wasu motocin duka.... K'arfe takwas da mintuna aka shigo da ya zulaihat b'angaren Ammie Dan itama tai mata Fad'a tareda da Dan dazon wad'an da zasuyi Mata rakiya zuwa gidan ta.kuka kawai ya zulaihat take tana sauraran Ammie Dake mata fad'a cikin sigar lallashi,har Ammie ta gama mata.ya zulaihat ta mik'e da k'yar ta rumgume Ammei tana kuka kamar me.Ammie na murmushi tana shafa bayanta kafin ta d'ago ta ta ce "Allah ya Baku zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba zulaihat".da k'yar dai ta saki Ammie nan aka kamata aka fitar da ita daga falon akai compound da ita zuwa wajen motar ta... Ammie na kallan su Huyaam da suke k'ok'arin bin bayan masu rakiyar ta ce "Ina zaku?" A tare suka juyo suna kallanta Suka ce rakiyar Amaren zamuyi" Ammie ta ce "A'a ku hak'ura ku dawo karkuje" Huyaam ta Bat'a Rai ta ce "harda su safnah fa zamu Ammie" Ammie ta ce "A'a nifa bana son ku fita da daddaren nan ku dawo kuyi zaman Ku a gida" wata k'awar Ammie Dake zaune a kusa da ita ta ce "ranki Dad'e da a k'yalesu Mana suje tunda naga ai ba iya su kad'ai zasu ba Ina harda sauran yaran gidan" Ammie ta ce "waye zai kaikun Dan gara Nasan Wanda zai kaisun"ta fad'a tana kallan matar.matar ta ce "eh wannan kan gaskiya ne"Huyaam tai saurin cewa "ya Aziz ne ya ce zai kaimu" ta fad'a tana Jin Kamar ta fad'i wani Abun zunubin,Dan in ba acikin shida lamid'o ta ce Wani ne zai kaisun ba tasan ba lallai Ammie ta yarda ba, Kuma tun d'azu ma Aziz d'in yay ta damunta da rok'onta akan idan har zasu kai Amarya Dan Allah zai kaisu,abinda yasa yanzun ma ta cewa Ammie shi zai kai su dan Ammien ta barsu ne yasa ta fad'i hakan.Ammie ta ce "tunda Aziz ne zai kaiku da sauk'i Amma Karku Dad'e Kuna zuwa kuce Aziz d'in ya dawo daku" ansamu mata Sukai suna fita daga falon gabad'aya.... Kallan HUYAAM siyama tai bayan sun fita daga b'angaren Ammie ta ce da sigar tsokana " ah lallai ne Huyaam wato mutumin da ake cewa ba'a so yau shi aka ce zai kaimu Kai Amarya? Ah lallai ya Aziz ya iya sace zuciya" ta fad'a Tana kallan Huyaam wacce ta kalleta a firgice lokaci D'aya nan siyama ta fashe da dariya" Huyaam ta harareta ta ce "waye ya iya sace zuciyar? Aini Banga Wanda ya isa ya sacemin zuciya ba kema kinsani Kuma shaida ce, tunda nace banasan sa to bana son nashin har abada Yanzum ma dan kada Ammie ta hanamu zuwa ne shiyasa kikaga nace mata shi zai kai mun Amma badan haka ba kema kinsan ko mutuwa ake ana dawowa bazan tab'a yadda na shiga motar Saba,Kuma Yanzun ma na fasa zuwa tunda har kika ce haka kuje ku nemi Wanda zai kaikun" ta fad'a tana makawa siyama harara tareda juyawa kamar zata koma b'angaren nasu.siyama tasa dariya tai saurin rik'o HUYAAM tana cewa sorry wallahi da wasa nake miki Dan Allah kiyi hak'uri" banza Huyaam tai mata tana k'ok'arin k'wacewa daga rik'on da siyama tai mata" Saida Huda tasa baki tana Bata hak'urin sannan Huyaam ta hak'ura da k'yar suna nan tsaye saiga su ikleema sun iso wurin itada safna adai lokacin da wayar Huyaam tai ringing dubawa tai tana juyar da kanta gefe,sai taji Wani Iri ganin Aziz d'in ne ke k'ira kamar bazata tai picking sai kuma dai ta dai dai ta kanta ta saki ranta ganin yadda duk suka Zubo mata ido suna kallan ta, Dan kada ma su zargi Wani Abun a tsakaninta da Aziz d'in yasa ta ce "Hello! eh gamu nan mun fito kai muke