Sashe 81
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yakeji. Fulani Salamatu ta tafe Hannu ta ce "ko kasan asalinta idan k'arya nai saika fad'a" sai kuma ta k'ara masa Wani kallo ta ce "waya sani ma ko shigeya ce Bata da uba akai cikin ta aka jefar Dan kada asirin uwar ya tonu kai Kuma ka d'auko ta ka kawo ta gidan nan? kai shegiyar ce ma tunda nidai har yau Banga Wani nata da ya neme taba" ta fad'a tana kallan Huyaam wacce ke kallanta Bata ko kiftawa Jin abinda take fad'a. Afeef ya d'aga hannu zai Mari Fulani Salamatu jikinsa na karkarwa adai dai lokacin da Mai martaba Wanda tun d'azu ya shigo falon Amma babu Wanda yay noticing yay gyaran murya.gabad'aya suka juya suna kallan sa har Fulani Salamatu wacce zufa ta yanko mata lokaci D'aya ganin Mai martaba nan ta sunkuyar da kanta k'asa gabanta na fad'uwa tana salati tana sallallami..ihun Huda kawai sukaji tana K'iran sunan HUYAAM lokaci D'aya tai kanta.Ai a sukwane Afeef ya juya Ganin fad'uwa zatai yay sauri ya tarota zuwa jikinsa tun kafin taje k'asan, Ammie ma tai kanta tana fashewa da Kuka tare da K'iran sunanta....... A masarautar zazzau kuwa yanzu haka k'arfe biyu da mintuna ne na Dare.Shakunmdum na tsaye a tsakiyar d'akinta waya ce kare a kunnanta bayan ta gama shirin ta tsaf na b'adda kamar da tai Dan zuwa b'angaren gimbiya Aysha dan aiwatar da aikinta.idan ba k'ura mata ido kaiba baza ka Gane mace ce ita ko kuma namiji ba saboda yadda tai shigar Dan babu Wanda zai iya Gane ta.waya ce kare a kunnanta da sukeyi ita da barzuk.tana zagaye inda take tsayen kafin ta dakata ta ce "na Gane uban gida yanzun nan zan tafi" daga can b'angaren Barzuk ya ce "Babu kuskure acikin aikin Fulani idan kuma Kika sake kika kuskure D'aya daga cikin abinda muka fad'a miki asirinki zai iya to nuwa Kuma Babu ruwanmu" shakundum ta ce cikin Tabbaci "bama zan kuskure ba uban gida" barzuk ya ce "Sa'a taki Fulanin zazzau" shakundum ta ce "godiya nake uban gida" daga haka ya kashe wayar itama sauke ta_ta ta d'auki abinda zatai aikin dasu ta nufi k'ofar fita daga d'akin.Bud'e k'ofar tai a hankali ta fito tana tafiya a hankali harta nufi stairs cikin sand'a tabi ta k'aramar K'ofar ta fice daga falon gabad'aya Babu Wanda ya ganta.Harta gama ficewa gabad'aya.da bin bango take tafiyar Dan kada Wani ya ganta tai b'angaren gimbiya Aysha da sauri...zube ta tadda duka dogarayen b'angaren gimbiya Aysha kwance suna bacci bayan ta isa da kuma tai Sa'a babu Wanda ya ganta..Wani numfashin salama ta sauke a hankali ganin ta isa part d'in.cikin sand'a ta bi ta Baya ta k'aramar k'ofar falon b'angaren, k'ofar ta tab'a taji a Bud'e take Hannu tasa ta Bud'e a hankali yadda k'ofar bazatai K'ara ba ta shiga ahankali cikin sand'a take tafiyar harta shigo tsakiyar main falorn gidan.kalle kalle ta farayi ganin Babu kowa sai k'arar AC data fan yasa ta nufi stairs d'in da zai SADA ta da b'angaren gimbiya Aysha ta haura da sauri cikin sand'a tana waige waige harta gama haurawa gabad'aya.a corridor ta tsaya tana Sauke numfashi kafin ta nufi inda d'akin gimbiya Aysha yake .tana Isa ta Tsaya a bakin k'ofar ta kasa shiga tana waige waige.tafi mintuna biyar a bakin k'ofar ta kasa shiga kafin ta iya tab'a k'ofar ta sa hannu ta Bud'e a Hankali datai Sa'a ma k'ofar ba'a rufe take ba saboda Wani lokacin Hajiya inna tana shigowa duba gimbiya Aysha lokaci lokaci acikin dare, shiyasa yauma Anty Amina Bata rufe k'ofar ba.Ahankali shakundum ta shiga Bud'e k'ofar ta yadda bazatai K'ara ba harta gama bud'ewa gabad'aya. Nan ta fara lek'awa cikin d'akin.babu haske a d'akin sai dumb light blue Wanda baida haske sosai nan ta hango iya gimbiya Aysha ce kwance saman gadon sai Anam a D'aya gadon Anty Amina Kuma Bata nan. k'arar ruwa da shakundum taji a toilet yasa ta Gane Anty Amina ce aciki cikin sauri ta shiga d'akin gadan gadan kan gadon gimbiya Aysha ta nufa Babu Bat'a lokaci ta fito da wani Abu ta watsa mata a fuskarta da duka jikinta gabad'aya .take gimbiya Aysha ta Bud'e ido jin Wani Irin zafi ya ratsa ta, tana kallan shakundum Bata ko kiftawa, kafin ta farga daga zafin daya ratsa ta tuni shakundum ta haye saman gadon ta d'agota ta zuwa jikinta nan ta fito da layar da tazo da ita zata cusa mata a cikin Bakinta. adai dai lokacin da Anty Amina ta Bud'e k'ofar toilet d'in ta fito.taku D'aya tai taji wani Irin nishi da K'aka Kari Had'i da kamar kokawa na tashi a Cikin d'akin nan da nan gaban ta ya yanke ya Fad'i ta d'aga kanta ta fara dube_dube a d'akin nan ta hango mutum ne a saman gadon gimbiya Aysha tana k'ok'arin cusawa gimbiya Aysha Abu a Baki,ai da Wani Irin speed ta nufi gadon tasa K'ara cikin kid'imewa tana cewa waye? shakundum da tayi nisa a San cimma burinta har Batama son lokacin da aka Bud'e k'ofar toilet d'in ba sai K'ara taji, cikin rud'ewa ta sauko daga saman gadon fuskarta a rufe da Wani Bak'in Abu da bama ka iya ganin komai sai k'waryar idonta.ganin Anty Amina ta nufo gunta zata kamata yasa ta nufi k'ofar fita a Wani mugun speed.da gudu Anty Amina tabi bayanta ganin tana k'ok'arin fita ta shak'o wuyan ta baya. Sha kundum ta rik'e hannun Anty Amina Dake wuyanta na ganin Anty Amina na k'ok'arin yage mata abinda ta rufe fuskarta dashi.nan dai suka fita daga d'akin Anty Amina na ihun a tai Maka musu, shakundum Kuma nata k'ok'arin k'wace kanta Dan kada Azo a kamata.Anty Amina kuwa tak'i sakinta saima Kara shak'eta da take tamau. nan Shakundum ta shiga kokawa da Anty Amina ita ko ta rik'eta gam tak'i sakinta tana cewa azo a taimaka mata ga Wani ya shigo musu d'aki .adai lokacin da Hajiya inna ta hauro stairs d'in tana tambayar meya faruwa cikin tashin hankali Jin hayaniyar tak'i k'arewa, kawai taga yadda mutum yay shigar b'adda kama baka gane shin macene ko namiji. ai shakundum ma ganin Hajiya inna ta zo ta kuma tasan tsaf zasu had'u su kamata have asirin ta ya tonu, tuni tai k'ok'arin d'aga hannunta ta bugawa Anty Amina guiwar hannun a gefen cikin ta Babu shiri Anty Amina ta saketa da sauri jin wata azaba ta saukar mata nan ta fad'i a k'asa.shakundum tai hanyar stairs d'in da gudu zata sauka Hajiya inna ta ruk'ota Aiko nan shakundum ta juyo ta hankad'a Hajiya inna nan itama ta fad'i ta baje a k'asa har tana buguwa da k'arfen stair d'in. ganin duk ta gama dasu Babu mai iya tashi ya biyota yasa ita Kuma ta fara saukowa stairs d'in cikin sauri, ganin guduwa fa zatai yasa Hajiya inna ta mik'e da k'yar tabi bayanta tana ihun a taimaka musu ga wani yashigo musu Wani yashigo musu b'angare a kama shi.mik'ewa Anty Amina ta Mik'e tabi bayan Hajiya inna suka sauko stairs d'in. Nan suka tadda har shakundum ta kusan fita daga falon gabad'aya. adai dai da Wani dogari ya farka agigice Jin ihun su Hajiya Inna nan shima ya yashigo falon sukai kicib'us da shakundum Dake k'ok'arin fita daga falon.Hajiya Inna ta ce cikin ihu "ka kama shi gashi nan zai fita" ganin wadda yaga Hajiya ita na nunawa tana ihun cewa ya kama shi yasa ya fisgota da k'arfi Hajiya inna ta ce "yauwa lurwanu Maza rik'e mana ta da k'arfi karta k'wace...... *End book one* K'arshen littafi na D'aya.bazance komai akan rayuwar gidajen sarautar nan guda biyu ba. Amma ke daga Jin tafiyar labarin Kin san yanzu aka fara ta. Amma bari na Dan Baku tsokaci kad'an daga ciki. *Tofa masu karatu Mai ke Shirin faruwa ne?shin wacece Huyaam acikin masarautar kano? shin da Gaske ne Huyaam ba 'yar gidan bace ma'ana ba Ammie da Mai martaba ne suka haifeta ba kamar yadda fulani Salamatu tazo tai baran bararma ta fad'a ko ya ya abun yake *Mai Cece makomarsm Huyaam a gidan idan Hakan ta kasance* *shin Wani Hali Ammie zata shiga* *Wani mataki Mai martaba zai d'auka akan Fulani Salamatu* *Shin yaya soyayyar HUYAAM da AZIZ CHIROMA da Kuma ABDALLAH SHATTIMA harma da LAMID'O duk da dai shi har yanzu ta bayan fage yake Bai fito ya bayyana mata kansa ba kamar u add Sauran sukayi BA? Shin acikinsu waye zai iyi samun soyayyar Huyaam harma ya samu nasarar auren ta?* *Shin burin Hajiya Lubabatu zai cika na ganin Salima ta auri Afeef ko Kuma bazai cika ba*? *Shin burin Fulani Salamatu zai cika na ganin ta aurawa Aziza Wanda take cewa zata had'a ta dashi ko bazai yuba*? *Mai zai faru idan akaje Egypt*? *Shin asirin shakundum na tunowa ko bazai tonu ba*? *Shin gimbiya Aysha da sultan zasu samu lafiya ko Kuma baza su samu ba* Duka amsoshin wannan tambayar suna cikin littafin HUYAAM book 2. 'yan uwa karku bari ayi wannan tafiyar Babu. Kamar yadda na fad'a muku Littafin HUYAAM na kud'i ne a man hajar WhatsApp regular group akan naira 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in 2270127432 Naja'atu umar zenith bank Evidence of payment 07066508376 *Yan Niger _zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA 07066508376 Alhamdulillah! Anan na kawo k'arshen Free pages na littafin HUYAAM book one.Book 2 Kuma na kud'i ne. akan naira dariyar 700 kacal. Amma akwai discounts ga Wanda suka fara biya zasu Bada naira dariyar kacal daga yanzu zuwa ranar da zuwa ranar da zamu cigaba da paid book idan ya wuce Kuma Zaku biya normal price wato 700. Ga masu bukatar magana da Marrbuyar Kuma zakuyi tun tubarta Mai tsaye ta wannan number 07066508376. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ __* *__(MRS SARAKIES )__* *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 4 _____________ Tun bayan dasu HUYAAM suka kai Anty khadija airport suka dawo gida har yau kimanin sati d'aya kenan Afeef baiyiwa Huyaam maganar komai ba Daya dangin wai ya ganta da Aziz ko Kuma yay mata tambayar Mai yasa ya gansu tare