← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 85

Sashe 59

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bari mu fara gaisawa ba kafin ki tambayi waye d'in? Huyaam ta harari wayar kamar shine a gabanta ta ce "kaga Malam ya za'ai bansanka ba Kawai ka k'irani kana damuna? tukunna ma a Ina ka samu contact d'ina da har Zaka k'irani? Ta fad'a cikin b'acin Rai. Lumshe ido yayi Yana sauraran dadd'ar muryarta tare da damk'e filon da yake kai Yay Wani miskilin murmushi Yana gyara kwanciyar a saman gadon sa da yake kwance ya ce "ni na sanki kece dai Baki sanni ba?Kuma kema nasan da zaki ganni zaki Gane ni" ya fad'a Yana murmushi.Huyaam da duk ta k'agu waye ta ce cikin k'osawa "please let straight to the point I said who are you?ko ka fad'amin waye kai ko Kuma na kashe wayata" ganin fa da Gaske take kashe wayar zatai yasa yay saurin mik'ewa zaune ya ce "please Huyaam dont cut my call please " Huyaam ta ce "ok to waye? Ya ce "masoyin kyakkyawar budarwa ne Irinki" HUYAAM ta zaro ido waje Jin abinda ya fad'a ta Kalli siyama da Huda taga kallanta suke Hakan yasa tai saurin katse wayar ta jefar nan saman carpet tana dafe k'irji kamar Wanda ta d'auki wuta. siyama Data gama Jin duk Wani conversation d'insu tai murmushi ta ce "waye ne halan?. Huyaam da idonta har ya kad'a saboda gigicewar da tai ta ce cikin rawar murya "I don't know who's Kawai K'irana akai" Huda tai murmushi ta ce "kodai munyi D'an uwane bamu sani ba ake b'oye mana? Ta Fad'a tana k'unshe dariyar ta ganin yadda HUYAAM ta Wani kalleta a fusace. Siyama ta ce "Kai Dan Allah fa? Ta fad'a da mamaki tana kallan Huda wacce tai maganar.Huyaam ta ce "sai dai abinda yafi D'an uwa ba D'an uwa ba a'a D'an uba.ta cigaba ta ce "nashiga uku wannan mutumin so yake ya jamin masifa yanzu idan Yaya yaji fa kinsan fa ya ce kar mu sake mu kula kowa kuma wallahi ni bansan waye ba bansan ma ayina ya samu contact d'ina ba wallahi blocking d'insa Zanyi"ta fad'a tana k'ok'arin d'aukar wayar tata.me Huda da siyama zasuyi idan ba dariya ba .Anty khadija ce ta shigo falon tana kallansu D'aya bayan D'aya taga yadda suke dariya k'asa k'asa ga sai Wani kallon Huyaam suke alamar da ita suke nan ta juya ta tsaida donta akan HUYAAM ganin yadda take a firgice tana latsa wayarta cikin tashin hankali.Anty Khadija ta ce "Mai ya faru HUYAAM? Siyama ta ce tana kunshe dariyar ta har lokacin "mummy wai Wani ne ya K'irata yanzu shine duk ta firgice haka" ta fad'a tana kallan Huyaam.Anty khadija ta zauna a kan kujerar kusa da Huyaam tana kallonta tai k'asa da murya ta ce "daughter waye ya k'irakin? Huyaam ta d'ago da dara daran idanuwanta tana kallan Anty khadija kamar zatai kuka ta ce "I don't know mummy wallahi bansan Shiba Dan Allah ki yarda Dani Kinga su Kuma sai dariya suke min Dan Allah Anty kar Yaya yaji wallahi idan yaji saiya dawo Nigeria ya zaneni"ta fad'a tana matse k'wallar D'ata zubo mata. Anty khadija tai murmushi Jin abinda ta fad'a sai Kuma ta dafa ta ce "waye shi d'in? Huyaam ta ce "wallahi mummy Bansan Shiba ki yarda Dani kawai k'irana yayi Kuma d'azu mafa ya k'irani nai picking naji muryar namiji ne yasa Nai saurin kashewa mantawa ma nai banyi blocking d'insa a time d'in ba,yanzu Kuma muna Zaune kawai ya k'irani Dana ga shine ma da bazanyi picking ba Huda ce tasa nai picking shiyasa nai Amma Wallahi mummy banso nai picking d'inba".ta fad'a tana rufe fuskarta da tafukan Hannunta tana sheshshek'ar kuka.Anty khadija dai murmushi kawai take tana kallan Huyaam Ganin yadda duk ta tashi hankalinta ta rud'e lokaci D'aya.sai Kuma Taga ta d'auko wayar tata ta rik'e Anty khadija ta ce "Mai Zakiyi? Huyaam ta ce "blocking d'insa Zanyi mummy Dan kada ya sake K'irana". Anty khadija ta karb'i wayar tana girgiza mata kai ta ce "kar kiyi blocking d'insa" Huyaam ta zaro ido Jin abinda Anty khadija ta fad'a d'aukar tama itama d'in zatai mata fad'a ne Amma shine taji ta ce haka.Anty Khadija ta dafata tana kallanta cikin nutsuwa tai k'asa da murya ta ce "Huyaam ki tsaya saureni Kiji Abinda zan fad'a miki, kince Bakisan waye ya k'iraki ba ko? Saurin Gyad'a mata kai Huyaam tai.Anty khadija ta cigaba ta ce "Daya k'irakin Mai yace miki? Huyaam ta sunkuyar da kanta k'asa ta kasa magana.Anty khadija ta ce "ce wa yayi Yana sonki?" Ina k'asa take Huyaam ta Shige saboda kunya sai Kuma tai saurin ta girgizawa Anty khadija kai kafin ta ce cikin sanyin muryar "wai haka ya ce masoyine" Anty khadija tai murmushi ta ce "ai haka zaice da kin saurareshi". Huyaam ta kalleta da mamakin abinda ta fad'a. Aunty Khadija ta gyad'a mata kai ta ce "karkiyi blocking d'insa kinji daughter ki tsaya ki Saura reshi kiji da Mai yazo ba'a yiwa saurayi haka indai har mutum ya furta Maka kalmar soyayya to ko Bai Maka ba baka sanshi ba'a Yi masa haka kabi shi a hankali har ku rabu lafiya ina fatan Kin fahimta" Huyaam ta gyad'a mata kai sai Kuma ta ce "Anty Yaya fa ya hanamu kula samari dan lokacin Daya bamu waya haka yace Babu kula samari Kuma yasa a dinga sa mana Ido ko Baya nan yanzu idan ya Gani fa ko Kuma aka fad'a masa cewa Ina kula saurayi wallahi Anty saiya kusa karya ni besides ni banma Isa Kula samari ba tunda ko jami'a bamu shiga ba". Ta fad'a tana tura Baki gaba tareda da wasa da yatsun hannunta.anty Khadija ta kalleta Baki sake tana Jin Jina wawta da yarintar Huyaam sai Kuma ta ce "waye Wani Yaya? Kinga Huyaam karki sake ki biye Afeef Yana Ina ma yasan Mai yake faruwa to idan ya hanaku kula samari so yake Ku zauna a gaida kenan Babu AURE kome? Ke Kuma dayake Sha Sha Sha ce ke shine kika d'auki maganar tasa, Nima bance ku kula samari ba Amma indai mutum da Gaske yake Yana sonku da AURE mai zaisa baza a bashi dama ba Koba yanzu zakuyi auren ba ai Kun saurari mutum" su dai su siyama da Huda sunyi shiru suna kallan mummyn nasu" Anty khadija ta juya tana kallonsu ta ce "Kuma bari na had'a daku Kunga yanzu Jami'a zaku shiga idan har saurayi Yana sanku indai har da aure yake son naku Kuma kun kaga yayi dai dai da zab'inku to kuce yazo gidan ku ya samu iyayenku bance wai ku kula samari ahanya ko Kuma a school ba Banda wannan ku kawo su har gida a San dashi Ina fatan kunji? K'walo ido waje sukai dukansu suna kallan Anty khadija Jin abinda ta fad'a siyama ta ce "nidai mummy ban Isa AURE ba tunda ko university ban shiga ba". Anty khadija tai mata dak'uwa ta ce "ungo naki siyama an fad'a miki Yanzu girma da shekaru har Wani Wahala ce dasu ai yanzu zakiga har kunshiga Jami'a Kun gama wuyar ta dai ku Shiga d'in,yo ko Kafin ku gama school d'inne indai har kunsamu mazajen AURE Mai zai Hana ai muku auren in yaso kwa cigaba Agidan mijin naku Yanzu a wannan zamanin fa ba'a wasa da dama indai ka samu dama kawai Kai amfani da ita rufe fuskar sukayi alamar Kunya Anty khadija ta cigaba ta ce "Nidai abinda nake daku shine kar kuyiwa wad'an da suke sanku Rashin mutunci Kuma bance a tsaida Ku awaje ko titi ku tsaya ba duk wanda yake sonku kuce yazo har gida ya samu iyayenku ina fatan kunji dai" gyad'a Mata kai sukai dukansu alamar ansawa" ta juya ta Kalli HUYAAM tana kallanta da sigar tsokana ta ce "waya sani ma ko a fitar da kukai jiyane Allah ya ansa addu'a ta na samu siriki D'an Abuja Kunga shikenan 'yata zatazo kusa Dani tai AURE dama Ina kewa" dariya sukai gabad'ayansu Huyaam ta Mike ta haura sama da sauri har tana had'awa da gudu saboda kunya Huda kuwa dariya kawai suke anty khadija ta mik'e tana D'an murmushin itama ta Kalli agogon bangon Dake falon ganin k'arfe D'aya Saura na Rana yasa ta ce "bari naje nai sallah ta fad'a tana barin falon Imaan ta d'auki littafin tabi bayanta siyama da Huda ma suka mik'e suka haura sama zuwa d'akinsu....... ___________ The same day Da daddare wajen k'arfe 9 da Rabi gabad'ayansu su ukun suna zaune a falo suna kallo saidai iya TV ce kawai take aiki Dan hankinsu bama ya kanta Yana kan wayoyinsu Tunda sukai dinner suka zaune Basu tashi ba Anty khadija Kuma tana falon babansu siyama daya dawo daga turai tun jiya . wayar Huyaam ce tai K'ara Alamar shigowar k'ira, nan Huyaam ta juya tana kallon number Bata ko kiftawa ilai kuwa shine tsaki taja da k'arfi tana rejecting call d'in har Saida ta jawo hankalin su siyama kanta Huda ta ce "ke Kuma keda waye kike Wani Jan tsaki ke kad'ai? Huyaam ta Wani kalleta kamar bazatai magana ba sai Kuma ta ce "wannan number ne mana aka sake K'irana da ita" siyama tai murmushi adai dai lokacin da aka sake k'ira ta ce "D'aga Kiji Mai zaice mikin" Huyaam ta yamutsa fuska ta ce "nifa wallahi gabad'aya tsoro nakeji kar naje Yaya ya sani" ta fad'a kamar zatai kuka. Siyama ta ce "ai mummy ta ce "babu komai kuma wazai fad'a masa tunda babu Wanda ya sani sai iya mu" Huyaam ta girgiza kai ta ce "siyama dan ba'a gabanki Yaya ya fad'a bane shiyasa zaki ce haka ita ai Huda ta sani shiyasa batai magana ba" Huda ta sauke numfashi ta ce "hakane Amma ai kinji dai abinda mummy ta fad'a ko?babu kyau kaiwa Wanda yake sonka wulakanci nidai anawa tunanin Mai zai Hana ki saurari da Mai yazo? Huyaam ta harareta tace "sai dai abinda yafi Wanda yake sonka ku kinji ance sona yake? Huda ta ce "Allah ya Baki hak'uri" tsaki taja ta Kalli wayar ganin har lokacin ringing take Bai hak'ura ba kamar Mai d'aukar wuta haka ta kai hannu ta d'auki wayar takai kunne bayan tayi picking tai Shiru batai magana ba "Assalamualaikum warahmatullah". haka ya fad'a da zazzak'ar
Chapter 59 · 0% Book details