Sashe 60
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
muryarsa.da k'yar Huyaam ta iya ansa masa gaisuwar a saman lab'b'anta tana Wani had'e Rai kamar Yana gabanta.tana Jin saukar numfashinsa a hankali kafin ya ce "wai Dan Allah Mai yasa baza'a bani Aran time bane na Fad'i Sak'on da nazo dashi ne? Huyaam tai shiru ta k'yaleshi.ganin tak'i magana yasa yace "Huyaam"ya fad'a da zazzak'ar muryarsa kamar shine ya rad'a mata Sunan saboda yadda ya iya furtawa.Huyaam ta ce "Wai Dan Allah waye kai ayina ka sanni da har kake K'iran suna na haka ne?" ta fad'a cikin sanyin muryarta Amma ita aganinta fad'a takeyi. lumshe idonsa yayi Yana bud'ewa lokaci D'aya yay murmushi ya ce "ai Baki tsayama kinji sak'on nawa ba". Huyaam ta ce "ok Ina jinka ka Fad'i Sak'on da zaka fad'a Ina da abinda nakeyi" yay murmushi Yana shafa sajensa ya ce "ok nasan Baki sanni ba Nima Kuma bansan kiba banma tab'a Ganin kiba sai a shekaranjiya da muka had'u a Wani park Ina patan zaki iya tunawa? Huyaam tai shiru tana sauraransa Amma kuma Batai magana ba tana tunanin maganganun sa. Ya ce "ko har kin manta ne? Ta ce cikin k'osawa"ni ban sani ba gaskiya Dan bansan Wanda muka had'u a park ba ni tunda mukaje har muka dawo babu da Wanda muka had'u" yay murmushi ya ce "okay naji Amma zaki iya tuna Wanda ya tareku time d'in da Kuka fito daga cikin wurin" sai a time d'in Huyaam ta tuna Amma Kuma sai ta girgiza masa kai kamar Yana kallanta ta ce "I don't recognize it" yay murmushi ya ce "nasan kin Gane kawai dai so kike ki bani Wahala Huyaam". Haka ya sake fad'ar Sunan ta.Huyaam ta ce cikin k'osawa "ka gama na kashe wayata? Yay saurin cewa Noo! banma Fad'i dalilin K'iran nawa ba ai" ta ce "ok am hear you"haka ta fad'a.ya ce "can I introduce my self before or you no need" Huyaam tai fari da ido ta ce "no need" ta fad'a atak'aice. Ya ce "ok let straight to the point a gaskiya tunda idanuwana suka sauka akanki naji gabad'aya natsuwa ta bar jikina zuciyata ta aminta Dake ma'ana Ina sonki HUYAAM" ya fad'a da Wani Irin sautin da Saida shi kansa zuciyar sa buga da sauri. Jitai gabanta yay Wani Irin Fad'uwa k'irjinta sai buguwa yake da mugun k'arfi yawun bakinta ya k'afe k'af ita ko ta shiga uku wannan mutumin zai jaza mata bala'i. Katse mata tunanin da take yay ta hanyar cewa "kinyi Shiru bakiyi magana ba" Huyaam ta ce cikin rawar murya "kaga kayi hak'uri agida ba'a barinmu mu kula samari dan Allah karka jamin fad'a ko Kuma duka kayi hak'uri karka sake k'irani kayi blocking number na Dan Allah" daga haka tai saurin kashe wayar ta Mik'e jiki na rawa ta haura sama da sauri tana fashewa da Wani Irin kuka. Suka bita da kallo Siyama ta juyo kalli Huda itama ta kalleta kafin ta ce " tashi mubita Babu Musu Huda ta Mik'e suka nufi d'akinsu.... kallan Huyaam da tunda suka Shigo d'akin dazu kawai Huda take ganin yadda take kuka bil hakk'i da gaskiya kamar wace aka fad'awa Wani mugun Abu.sauke numfashi Huda tai kai Zaune kusa da Huyaam tai k'asa da murya ta ce "wai Dan Allah kukan me kike haka ne Huyaam yanzu idan mummy ta jiyo ai sai ki tada mata da hankali" Huyaam ta d'ago ta kalleta da rinan nun idanuwanta Wanda kad'a suka rine lokaci D'aya Saboda kukan da Tasha ta ce cikin rawar murya "Huda wallahi tsoro nakeji bana son Yaya yasani ko kin manta Irin worning d'in da yay mana ni wallahi sai naji dama banje gunnan ba ke rik'e wayar ma gabad'aya yanzu nake Dana sani wallahi" ta k'arasa fad'a tana rik'o hannun Huda" Huda ta kalleta a nutse ta ce "yanzu ke meye damuwarki?" Huyaam ta ce Huda tun washe garin da nazo garin nan akwai wata number kullum sai tamin text message na kalamaun soyayya har cewa akayi wai na sauka Abuja lafiya wai yayi kewa ta tunda na bar kano Shima ya bar garin kano saina dawo zai dawo Dan Allah waye wannan Huda? Bama iya number bane akwai watama wacce itama ake min sms da kalaman soyayya Dan Allah Ina ake so nasa kaina dama haka rik'e wayar yake wallahi saina ajiye ba zan iya ba" ta fad'a tana fashewa da kunjin kuka" Huda da duk magan ganun Huyaam suka d'aure mata kai ta ce "ban Gane abinda kike nufi ba?" Mik'a mata wayar ta Huyaam tai tana kallanta ta ce "ki Karanta wannan zaki fahimci Mai nake nufi" karb'ar wayar Huda tai ta fara karanta sak'onnin D'aya bayan D'aya Saida ta gama Karantawa du sannan ta kalli HUYAAM Dake kallanta ta ce "na Karanta Amma suwaye wad'annan d'in? Huyaam ta Bud'e hannu alamar Bata sani ba ta ce "Taya zan sani tunda babu Wanda ya fad'amin waye shi acikinsu wallahi Huda so suke kawai su jaza min bala'i kawai Inba haka ba meye zasu Dunga yimin messages babban abinda ya K'ara bani mamaki bai wuci ayina suka samu contact d'ina ba nifa a iya sani na daga ke sai su ikleema sai 'yan gidan mu ne kawai kuke da contact d'ina" to ayina suka samu? ta fad'a tana kallan Huda. itama Hudan dai kallanta Kawai take.siyama da fitowar daga wanka kenan ta tsaya tana kallan su ta ce "to ayina suka samu contact d'in naki? Huyaam ta kalleta ta ce "oho" Huda ta sauke numfashi ta ce "Allah ya kyauta Amma Huyaam karki musu Rashin mutunci kamar yadda mummy ta fad'a kibi kowa a hankali har Allah yasa kisan waye sannan ku Rabu lafiya" Huyaam ta kalleta ta ce "naji Amma nidai bazan K'ara d'aga K'iran ko shi Wanda ya k'irani d'azu ba"Huda ta ce "shikenan" daga haka ta Mik'e ta koma saman gadon da take kwance Siyama ta k'araso tsakiyar d'akin tana Kallan HUYAAM ta ce "na fito kije kiyi wankan" mik'ewa Huyaam tai ta sauko daga saman gadon ta shiga toilet d'in bayan ta d'aura towel...... HUYAAM LAMID'O AZIZ CHIROMA AFEEF ABDALLAH Littafin HUYAAM na kud'i ne regular group akan naira 500 before mu gama free pages muka gamawa Kuma zai koma 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in 2270127432 Naja'atu umar zenith bank Evidence of payment 07066508376 *Yan Niger _zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA 07066508376 *TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!* *Ina kuke manyan mata masu capacity ? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."* *To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* *1,Atamfofi* *2, lesses* *3, Abaya* *4, kayan kwalliya ko Wani iri ne* 5,*D'an kunnaye(jiwelleries)* *6,takalma* *7,hand bag* *8, mayafai* *9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*. *domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka +234 811 190 1302 /09020337676* *Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta* *Sai mun Jiku 07066508376_______ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__* *___(MRS SARAKIES )__* My channel link https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 3 ____________ Tun daga wannan ranar kullum sai wannan mutumin da Huyaam har yau bata San sunan saba bare Kuma shi kansa ya dameta da k'ira Babu dare babu Rana, Koda ko baza ta d'auka ba baya tab'a gajiya bare ya hak'ura daga k'arshe Kuma idan yaga bazata tab'a yin picking d'in ba sai yay mata zazzafar sms na kalaman soyayya masu raza zuciyar masoya.Amma ita Huyaam ko a kwalar rigar ta saima take Ganin haka a matsayin takurata kawai yakeyi Dan Daya turo ko Bata kula ba indai ta Gani baya K'ara ko minti D'aya a wayarta take gogewa.gefe guda kuma Suma wad'an nan numbers d'in da Bata san ko suwaye ba kullum sai sun mata text message na kalaman soyayya Suma babu dare babu Rana ta rasa suwaye suke mata wannan text message d'in har mutane biyu Dan har garama shi Wanda yake k'iran nata ta sani Amma su wad'an nan biyun masu mata sms d'in Bata San ko suwaye ba bare sunan su kuma sunk'i bayyana Kansu har Yanzu agareta duk da Bata buk'atar Hakan Amma at least tasan ko suwaye yadda zata d'auki mataki akai ai yafi akan dai abarta acikin duhu tayi tunanin duniya ta rasa Gano su bare tasan suwaye... yanzu haka kwance take saman gadon da tun suka zo yake amatsayin nata bayan da tai sallahn Azhar ta koma saman gadon ta kwanta ta kasa tashi su Huda sun fita can main falor tun d'azu sunyi_sunyi ta fito ta ce musu suje tana zuwa,tunani ne fal ranta ta rasa ya zatai ta yage shi wannan Wanda yake yawan k'iran nata a waya ita har ga Allah har yau bata ji zata so Shi ko makamcin haka ba,ke ita soyayyar ma har yau bata ji zata iya ba tunda har yayansu yasa Musu