← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 85

Sashe 71

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

0706650376_________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__* *__(MRS SARAKIES )__* My channel link https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y *Bismillahirrahmanirrahim* *Saura 1 page mu gama free pages ku hanzarta ku biya kud'in Karatunku* PAGE 4 _____________ Muryar Siyama da Huyaam taji tana cewa ita ce ta Bud'e mata k'ofar yasa Huyaam Sauke wata wawuyar ajiyar zuciyar salama Jin ba Afeef d'in bane kamar yadda take tunani ba,A hakan ma ba wai ta dawo dai dai bane daga fad'uwar gaban da takeji kawai dai ta d'anji nutsuwa ne Jin siyama ce.da k'yar da k'yar ta iya Tashi ta sauko daga saman gadon ta nufi k'ofar walking slowly tana tafiya har ta Isa Bak'in k'ofar inda tasa Hannu ta Bud'e k'ofar, tsuke fuska tai Ganin siyama yasa ta tsaya tana kallan Siyama wacce itama kallon nata takeyi.siyama ta ce "Mai ya faru kike Kuka ne? tafad'a tana kallan fuskar HUYAAM wacce tai JAA Lokaci D'aya Saboda Kukan da Tasha.harara Huyaam ta maka mata batai magana ba,nan siyama ta sakar mata murmushi ganin yadda take Hararar ta da Gaske kafin ta ce "toni Ban hanya na wuce ciki" ta fad'a tana gimtse dariyarta ta .k'ara tsuke fuska HUYAAM tai Ganin lallai ma siyama ta Raina Mata hankali wato dariya ma take mata koh? Su jaza mata bala'i Amma Kuma su b'uge ta yi mata dariya.kwafa tai ta matsa gefe tana bawa siyama hanya har ta shigo d'akin kafin itama tabi bayanta ganin ta shiga ciki. Zama tai kusa da siyama wacce ta zauna bakin gadon har lokacin murmushi ne a saman fuskarta tana kallon Huyaam ta ce "hope everything is going well sisto?" sai Kuma ta gyara zamanta tana kallan Huyaam wacce ta fara hawaye lokaci D'aya,dafa kafad'arta tai ta ce cikin damuwa "Mai ya faru Kuma kike hawaye?" Sauke hannun siyama Huyaam tai daga saman kafad'arta ta ce cikin rawar murya da b'acin Rai "siyama Kun cuceni Saida nace muku Yaya zai iya zuwa ya samemu tunda Yana gidan Amma kuka ce lallai bazai ganmu ba idan ma ya ganmu Babu abinda zai min to gashi yanzu kunja ya ganmu wallahi Kuma nasan kashe ni zaiyi na shiga uku" Ta fad'a tana fashewa da gunjin Kuka. Jikin siyama ne yay sanyi lokaci D'aya Jin wai Afeef ya gansu, sai kuma taji Bata ji Dad'i aranta ba Dan kuwa tabbas su suka jaza mata Amma saita dake ta ce cikin k'asa da murya "ya ganku fa kika ce Huyaam? Gyad'a mata kai Huyaam tai tana goge hawayen fuskarta. Siyama ta ce "Kuma Mai yace miki? Huyaam ta kalleta sai Kuma ta ce " Wallahi Wani kallo yamin Kuma indai Yay mana Irin wannan kallon munsan Mai yake nufi Allah ne kad'ai yasan Irin hukuncin da zai mun, Dan wallahi sai na Sakan kance zakiga ya nemeni.ni yanzu babban damuwata siyama bansan Wani Irin hukunci zai min ba, wallahi gabad'aya yanzu a tsorace nake da abinda Yaya zai min" ta fad'a hawaye nabin kuncinta.rasa abin cewa Siyama tai sai Kuma can ta sauke numfashi ta ce cikin lallashi "ki kwantar da hankalinki Huyaam in Sha Allah Babu abinda zai miki tunda ai yanzu biki ake bazai tunanin Wani abun bane ba,idan ma ya k'iraki zai tambayeki kice masa mantatuwa kikai amotar shine ya biyo ki ya kawo Miki" Huyaam tai mata wani kallo ta ce "tab' Baki San waye Yaya da brain bane wallahi tsaf zai Gane,ni tsorona ma Allah yasa Bai Ji abinda ya Aziz d'in ya fad'a min lokacin dana juya zan shigo b'angaren mu ba" siyama ta Bud'e ido Cikin mamaki ta ce "Mai yace Miki? Huyaam ta harareta ta d'auke kanta ta ce "bansani ba duk ba kune kuka jamin ba sannan yanzun kizo kina tambayar Mai yace min to bazan fad'a ba" ta fad'a tana tura Baki gaba. dariya siyama tai har tana rik'e ciki kafin ta tsagaita ta ce "ohh! yau Kuma mu ake b'oyewa abinda ya Aziz d'in ya fad'a kenan?" Huyaam ta ce "eh d'in Dan Allah tashi ki bani waje ni bacci Zanyi" siyama ta sa dariya ta ce "kefa yarinyar nan mu kike rainawa hankali Amma kin fara kamuwa da son ya Aziz kawai kece dai Baki sani ba har yanzu, Amma nasan soon zaki San hakan" Huyaam ta harareta ta ce "Allah ya sawak'e wallahi kije ki wanke bakinki dan baida tsarki yanzu" dariya siyama tai ta mik'e ta ce "Abdallah shattima fa nasan shima dai am masa wuri acan k'asan zuciya ko?" Ta fad'a tana gimtse dariyarta.Huyaam ta wawuro filo ta bugawa siyama tana cewa wallahi zatai mata rashin mutunci. Siyama ta kauce da sauri tana dariya ta ce "to na daina Dan Allah kiyi hak'uri bari na shiga wanka Dan yau a d'akinki zan kwanta" banza Huyaam tai mata ta hau saman gadon ta juya mata baya .nan siyama ta k'arasa inda towels d'in Huyaam suke ta d'auko D'aya Dake jikin hanga acikin press sannan ta shiga Wani lungu ta cire kayan jikinta ta d'aura towel d'in sannan ta fito ta nufi toilet har lokacin murmushi take tana satar kallan Huyaam.ita dai HUYAAM tai banza ta k'yaleta ta nuna Bata ma San tanayi ba saima latsa wayarta da take, ganin siyama ta shige toilet d'in yasa itama ta mik'e ta nufi press d'in ta d'auki Wani towel d'in daban sannan ta fita daga d'akin Dan zuwa tai wanka a d'akin Dake nan kusa da nata...... Washe gari har k'arfe Sha biyu na Rana Huyaam Bata yadda ta sauko downstairs ba tana tsoron kada ta fito su had'u da Afeef. tana zaune a d'akin ta kasa fita ko nan da can Dan ko break fast ma Bata sauka tayi ba sai Huda ce ta kawo mata har d'akin.da Ammie ta tambayi Huda cewa lafiya yau bata ga Huyaam ta sauko ba? Nan Huda ta ce mata lafiyarta lau kawai dai ta ce yau Bazata sauko downstairs d'in bane ba. Ammei bata takura tace wai saita sauko ba ta k'yaleta tunda taji ance lafiyarta lau....yanzu haka k'arfe D'aya Saura ne na Rana,tana zaune Saman gadon ta tana chatting bayan ta gama waya da Abdallah shattima Wanda Shima Dak'yar tai picking call d'in nasa bayan yayi mata text message na rok'o da magiya akan ta daure tai picking call d'in nasa shiyasa tai Amma da baza tai ba.tana nan zaunen lokaci lokaci take kallan Bakin k'ofar duk a tsorace take Dan Gani take ko da yaushe Afeef zai iya shigowa d'akin nata ya sameta shiyasa duk tak'i sakin jikinta,tunda har yanzu Bata Ji ya Aiko yace taje ba ko Kuma shi yazo ya sameta ba... K'iran Aziz ne ya sake shigowa wayarta a karo na Babu adadi nan ta duba wayar ganin shine yasa taja tsaki da k'arfi tai rejecting call d'in tana k'unk'uni k'asa k'asa Dan tun safe yake Nacin K'iranta Amma tak'i picking,azuciyarta ta ce bayan duk kai ka jawomin zaman d'akin yau sannan kai tunanin idan ka k'ira Zanyi picking ai baka Isa ba" tsaki ta K'ara ja Jin ya sake k'ira ta kashe wayar ma gabad'aya ta jefar nan saman gadon tana huci.babu dad'ewa Huda tai knocking k'ofar ta turo lokaci d'aya ta shigo d'akin.d'aga kai Huyaam tai tana kallan Bakin k'ofar Ganin Huda ce yasa ta kauda da kanta gefe tana ansa mata sallamarta ta ciki_ciki.Huda ta k'araso ta zauna a gefen gadon rik'e da wayarta a hannunta tana kallan Huyaam tai murmushi ta ce "sai kace wata amaryar kulle kinzo kin d'aurawa kanki zaman d'aki shi Wanda Kike Yi domin shi d'inma k'ila ya manta kawai kece dai kika bi kika sa kanki a damuwa" ta fad'a tana kallan Huyaam, Kallanta Huyaam kawai take Bata ko kiftawa Jin abinda Huda ta fad'a kafin tai mata wani kallo ta ce "eh ai dole kice haka tunda ba kece a condition d'in da nake ba,duk ba ku kuka jamin zaman d'akin ba ,ai komai nai kune kuka ja,ko kin manta waye Yaya? ke kanki kinsan baya mantuwa baya hukunci lokacin da kai Laifi sai ka manta sannan shi zai Maka nasa hukuncin saboda haka ko Mai nai Babu ruwanki" ta fad'a tana k'ok'arin juyawa huda baya hawaye na taruwa idonta.sauke numfashi Huda tai sai kuma tai k'asa da murya ta ce "to kiyi hak'uri Dan Allah nasan duk mu muka ja Miki d'in,Amma Dan Allah kiyi hak'uri ki yafe mana? Banza Huyaam tai da ita ta k'yaleta saima gyara kwanciyar ta da tai.Huda ta mik'e ta koma ta side d'in da Huyaam take passing ta zauna ta kamo hannunta ta ce cikin k'asa da murya "kinji sisto Dan Allah kiyi hak'uri" Huyaam ta kalleta sai Kuma ta Sauke Idonta k'asa ta gyad'a mata kai alamar taji" Huda tai murmushi ta ce "thank you so much sis in Sha Allah Babu abinda Yaya ma zai miki" ita dai HUYAAM Bata tanka taba Dan Wani Irin d'aci take Ji aranta a duk lokacin da ta tuno da Irin kallon da Afeef yay mata a daren jiya da Kuma tunanin hukuncin da zai mata Sai taji duniyar tai Mata zafi.Huda ta ce " yauwa ya Aziz ya k'irani ya ce tun safe yake K'iranki Amma kink'i kiyi picking call d'insa daga k'arshe ma kika kashe wayar Mai yasa sis?" ta fad'a tana jiran ansar Huyaam. Kamar Huyaam baza tai magana ba Jin wata tambayar rainin hankali da Huda tai mata kamar Batasan Mai ya faru ba, ita a tuna ninta duk irin abinda Yaja mata a daren jiya gashi har yau bata fita daga cikin Saba zatai picking call d'in sane. Huda ta ce "bakiyi magana ba? Huyaam ta mik'e Zaune tana kallan Huda ta ce a fusace "nai picking call d'in sa fa kika ce Huda? Duk abinda Yaja min a daren jiya kina Tunanin Zanyi picking call d'insa ne?" Ta fad'a tana hucin b'acin Rai.Huda tai k'asa da murya ta ce "ba haka nake nufi ba,Amma Kuma Huyaam Hakan bazai sa kik'i picking call d'in Saba" Huyaam ta ce "oh! ke a ganin ki Bai kai ba ko? Sai Kuma tai wani murmushi mai ciwo ta ce "to ni a gani na ya kai har yayi yawa ma" Huda tai k'asa da murya ganin Huyaam ta hau ta ce "naji ya kai Amma Bai kamata ki kashe wayar
Chapter 71 · 0% Book details