← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 85

Sashe 2

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah ya raya"ta fad'a tana aro murmushin yak'e. Gimbiya Aysha tace . "Ameen"kafin gimbiya Bilkisu ta ajiye mata babyn kan cinyar shakundum Hajara.ta Kalli babyn take taji zuciyarta ta tsinke ganin kyan yarinyar Bata bari ta fallasa sirrin zuciyar taba tai yak'e tace. "Masha Allah"daga haka Bata k'ara cewa komai ba.haka d'akin ya d'auki Shuru na wani lokaci nan da nan uwani ta cika mata gabanta da kayan marmari,itadai shakundum ta zubawa babyn ido kamar tana kallan ta Amma Kuma a bad'ini ba ita take kallo ba tunani kawai take kala kala can sai ta Mik'e tana mik'awa gimbiya Bilkisu babyn tace. "Bari naje Allah ya raya".daga haka tai hanyar k'ofar fita.suka bita da fatan sauka lafiya,da daddare Mai martaba har yazo K'ara duba gimbiya Aysha da jaririyar ta,ya jima a d'akin kafin ya tafi. Bayan kwana hud'u Cikin wata masarauta Dake cikin garin Zazzau misalin k'arfe biyu na daren ranar na hango Wata k'asaitacciyar mace tsaye cikin Wani rantsatstsan d'aki Wanda ya gaji da had'uwa Irin na matan manya, manyan ma Irin su sarakai Wanda sukeji da mulki da Kuma izza bugu da k'ari Kuma ga sarauta, duk da duhun d'akin Hakan bai hanani ganin fuskar matar ba, wacce take babu walwala kwata kwata,dakinganta kinsan tana cikin damuwa da tashin hankali ba kad'an ba,sai safa da marwa takeyi dan ta kasa zama .A k'asan carfet din d'akin Kuma wasu hadimanta na gani su su biyu mace da namiji,D'ayan dogari ne d'ayar kuma jakadiyar tace ta hannun Daman ta,. Dogarin ya d'aga hannunsa sama Dake dunkule kad'an alamar girmamawa yace cikin zufar data keto masa Ganin alamar ran uwar d'akin nasu ya gama B'aci. "Allah ya tai makeki wallahi! Yauma kwata kwata bamu samu damar shiga inda take ba saboda kinsan kullum part d'inta cikin TSARO yake kum...."da kata" haka ta fad'a cikin fushi kafin ta cigaba tace. "sakaran bawa kawai tai k'wafa kafin ta juya ta nuna safara wacce ke zare ido kanta a k'asa tace."Haddake safara! Kina matsayin mace Amma ki kasa shiga har cikin d'akin nata kiyi abinda na saki,ai babu Wanda zai gane ki tunda kema jakadiya ce a masarautar nan, jakadiyar ma data d'auki tsawan shekaru acikin gidan nan kina mun aiki ace Kuma kin kasa sanin sirrin gidan nan haryanzu,dare nefa? kiyi b'adda kama mana Wazai Gane ki ai kowa ya ganki a part d'inta d'auka za'ayi kamar jakadiyar tace uwani , Amma ki kasa aikata D'an wannan aikin"ta fad'a tana huci. Safara ta K'ara sunkuyar da kanta k'asa tace cikin rawar jiki data murya . "wallahi Ranki Dad'e nayi duk iya bakin k'ok'arin naga nabi duk wata hanyar da zan shiga Amma abun yaci tura ga Kuma kinsan tare suke kwana da gimbiya Bilkisu, Kinsan ai ba....."dakata!! bak'ar muna fuka", ta fad'a a fusace" ta cigaba "banasan Jin komai daga k'azamin bakin ku,to bari kuji na fad'a muku na Baku nan da kwana uku wato Ranar suna indai bakuyi abinda nace ba wallahi saina sa an kashe min ku dan bazaiyu kusan sirrinaba sannan ku cigaba da zama Dani ba,Kuma idan kuka bari aka kama ku wallahi shima hukuncin kisa zan muku kunji ko Baku jiba"ta fad'a cikin kashedi. Tare suka K'ara duk'ar da kansu k'asa cikin girmamawa kafin suce. "Allah ya huci Zuciyarki ranki Dad'e! akasi aka samu Amma in Sha Allah aranar ma zamuyi kiyi hak'uri"suka fad'a kamar zasu kwanta .taja tsaki kafin tace. "Ku tashi ku bani wuri ". Cikin rawar jiki suka Mik'e har lokacin hak'uri suke Bata suka bar d'akin.ta bisu da harara kafin itama ta fito daga cikin d'akin naga ta biyo Wani dogon corridor Wanda zai kaita har d'akin ta,tana shiga d'akin ta zauna bakin gadonta ta fashe da Wani Irin kuka tana shafa cikinta kafin tace afili. "Na shiga uku,Ni sai yaushe,sai yaushe zan samu D'an Kaina,Ina zaune a auro wata tazo ta haihu, haihuwar ma har biyu Amma ni haryanzu shiru ko b'atan wata ban taba yiba ,tana share hawayenta tace"to wallahi tunda bansamu dama awancan ba wannan Karan dole saina samu wannan damar,ta k'arasa share hawayenta ta mik'e ta shiga toilet d'in cikin d'akin. ___________ *Ranar suna 4th April 2008* A Ranar palace ta cika mak'il da don dazon mutane daban daban,Daga ita Kanta masarautar zazzau d'in har 'yan uwa da abokan arzik'i anzo sunan baby girl wacce aka rad'awa suna Zainab sunan goggo mahaifiyar Mai martaba,zo kiga yadda masarautar zazzau ta d'auki al'umma zuwa wannan sunan harda matan manya da sarakuna, wasu daga cikin 'yan gidan kuwa wasu suna cikin farin ciki wasu Kuma ta ciki na cikine kawai baza su fito su nuna bane irinsu shakundum Hajara Dan da k'yar tazo part din d'azu ta zauna akai shagalin Sunan shima Dan kada azargi wani abunne,bata Dad'e ba ta koma part d'inta.gimbiya Aysha tayi kyau harta gaji itada jaririyar ta Zainab harda su gimbiya Bilkisu Dan sai shiga suke suna fita a wannan Rana fuskokinsu kuwa d'auke suke da murmushi.sai d'aukar babyn ake ana Gani kowa nasa mata albarka anci ansha an godewa Allah. wajen k'arfe 10 na dare lokacin wasu daga cikin wad'an da sukazo sunan har sun watse sai kad'an daga sauran mutanan gidan.gimbiya Bilkisu ta karb'i babyn daga hannun wata 'yar uwarsu wacce tazo sunan itama tana cewa anzo d'aukar ta zata tafi, gimbiya Aysha tai K'iran gimbiya Bilkisu akan tazo ta kaiwa wasu goggoninsu da sukazo sunan babyn su Gani da yake dare ne,sannan Kuma a Wani d'aki na musamman aka sauke su , gimbiya Bilkisu ta karb'i babyn ta bar falon ta biyo ta Wani korido kenan taji Mararta ta k'ulle tana Jin fitsari kamar zai zubo ga Kuma tazo gab da toilet adai dai lokacin da matar ta shanyo kwana daga wata hanyar da zata sadata zuwa main falorn part d'in inda gimbiya Bilkisu ta fito Kawai Sukai kicib'us da ita.gimbiya Bilkisu Bata kawo komai aranta taba tace. "Yauwa Dan Allah rik'emin babyn Nan nashiga toilet ki tsaya anan yanzu zan fito" ta fad'a tana Mik'a mata babyn.dan batama Kalli fuskar matar sosai ba ta dai ganta da nik'af. Matar ta karb'a tana sauke wata iriyar ajiyar zuciyar salama da Kuma murna ganin hak'arta ta cimma ruwa.tana ganin gimbiya Bilkisu ta shiga toilet d'in ta juya gabanta da bayan ta taga Babu kowa take ta Saka babyn cikin hijab yadda babu Wanda zai gane tana d'auke da Abu a jikinta,tabi ta wata k'ofa ta bar part d'in gabad'aya tana fita tai Wani lungu hanyar k'aramar k'ofa Wanda babu mutane a wurin ta b'uya a wajen ta tsaya tana haki da waige waige K'irjinta sai bugawa yakeyi ta lalumo wayarta ta danna wata number Saida tai Miss call biyu sannan akai picking akai Shuru ba'a Yi magana ba. Cikin fad'uwar gaba da rawar murya tace . "Ranki Dad'e, Allah ya taimakeki na d'auko abinda kika sakani yanzu, bari na k'ira haladu mu had'u a inda kikace d'in sai muje mu aiwatar da abinda kika fad'a".ta k'are maganar tana haki tana Kuma waige waige Dan kada Wani ya ganta.daga D'aya bangaren akace cikin jindad'in labarin da taji cike da Isa da izzah. " lallai Kun cika ALK'awari,inji dai babu Wanda ya ganki koya ganeki?..." Cikin k'asa da murya tace. "Ranki Dad'e Babu Wanda ya ganni".ta fad'a tana waige waige. Ta sauke numfashi tace. "To maza Maza ki bar masarautar nan yanzu kafin a farga da Rashin yarinyar,Kuma idan har kuka aiwatar da abinda nasakaku ba'a kama Kuba to akwai kyauta ta musamman Dana tanadar muku" daga haka ta kashe wayar tana sakin Wani Irin murmushi. ____________ Acan part d'in gimbiya Aysha kuwa, gimbiya Bilkisu data fito daga toilet bataga matar data bawa baby Zainab ba gashi Kuma Bata gantaba bare ta tambayi inda take ba,sai kawai tai tunanin k'ila ko ta shiga da ita cikine tunda taga can zata Dan haka ta sauke numfashi ta juya ta koma cikin falon ta cigaba da hada_hadanta. Bayan 'yan suna wasu duk sun watse Can saiga gimbiya Aysha ta fito daga d'akinta cikin shiga ta Alfarma ta fito a gimbiyarta sak tana kallan gimbiya Bilkisu ta D'an Bud'e ido tace. "A'a!! ke Kuma Ina kikaje? Kefa nake NEMA fa tun d'azu su goggo sunce Baki kai musu babyn sun Gani ba?"ta fad'a tana kallan gimbiya Bilkisu. Dumm!!! gaban gimbiya Bilkisu ya ansa kafin ta taso tace Cikin sanyin murya . "Yaya gimbiya!wai kina nufin babyn Bata gunki?".ta fad'a cikin fad'uwar gaba. "Take ita itama gaban gimbiya Aysha ya ansa Amma saita maze tace. "A'a ai tana gunki da nace ki kaiwa su goggo ita". Gimbiya Bilkisu ta fara duba falon kafin tace " mun had'u da wata mata danaga zata shigo nan falon ga nikuma fitsari ya matseni alokacin,danaga Ina gab da toilet d'in d'akin Dake corridorn yasa na Bata babyn nace ta rik'emin ita kafin na fito,dana fito Kuma bangan taba d'auka Tama ko ta k'arasa shigowa ta kawo Miki ita".ta fad'a cikin fad'uwar gaba Dan bataga matar a falon ba yanzu. Itama gimbiya Aysha juyawar tai tana kallan mutanan Dake falon kafin tace. "wacece kika bawa babyn ?".ta fad'a tana k'arewa sauran wad'anda suka rage afalon kallo Wanda duk yawancinsu ma 'yan cikin palace d'in ne da basu k'arasa tafiya ba suna hira. Gimbiya Bilkisu tana zare ido tace . "wata me nik'af ce Banga fuskarta ba",ta fad'a cikin rawar murya.gimbiya Aysha tace . "Me nik'af kuma?... gaskiya Banga wata Mai nikaf ta shigo falon nan ba"ta fad'a tana k'arewa mutanan falon kallo kamar zataga Mai nik'af d'in. Sai Kuma ta shiga tambayar su da cewa sunga wata Mai nik'af ta shigo falon lokacin da bata nan?kowa yace a'a Dan sun dad'e afalon suma kuma tabbas basuga wata Mai nik'af Koda wasa ta shigo falon ba,take duk suka rikice suka fara Neman matar data d'auki babyn,ko kuma ta bawa wasu Amma shiru kakeji tun suna nema cikin falon har aka bazama zuwa cikin palace d'in Neman babyn part by part ko Kuma Wanda yaga matar Amma shiru kakeji wasu sunce tabbas kamar sun ganta Amma kuma Basu kula da inda tai ba,take suka K'ara shiga cikin Tashin hankali cikin k'an k'anin lokaci palace d'in nan tasan halin da ake ciki na jaririya ta Bat'a hankalin wasu duk ya tashi ya za'ayi ace acikin palace za'a zace jaririyar da satin
Chapter 2 · 0% Book details