Sashe 17
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fa sai ya sani to gani nai gara kawai a fad'a masan shi zaifi sauk'i, Kuma kawai Ammie sai a b'oye masa saboda kar ai mata fad'a ko yaya?kina fa kallo yadda Aziza take cutar Huyaam agidan nan ba Dole Abba ya sani ba danya d'auki mataki".Ammie ta d'auke kanta tace . "Nidai karki K'ara yimin Irin wannan". Sai Kuma ta Kalli ya haidar tace. "Kaje ka fito da motar mu tafi".Babu musu ya haidar ya fita daga falon. Ammie ta kalli Huda wacce sai zubar da hawaye take tana mak'ale da Huyaam itama tace. "Huda jeki d'auko mata hijab d'inta a daki yanzu". babu musu Huda ta tafi....har bakin part d'in ya Haidar ya kawo motar ya Zarah da baba magajiya suka kama Huyaam suka shigarta bayan motar inda Ammie ta shiga ya Haidar ya rufe musu murfin motar sannan ya zaga driver seat yaja motar suka tafi asibitin........ Mai martaba Yana dawowa daga masallaci direct b'angaren fulani Salamatu ya nufa.yana Isa b'angaren falon ya shiga bakinsa d'auke da sallama . Ramlat Dake Zaune falon suna kallo suka ansawa Mai martaba sallamar sa sannan kuma suka shiga gaida shi lokaci D'aya.Aziza Dake kusa da fulani Salamatu tana Bata labarin yadda taiwa Huyaam d'azu a wurin parting ta, tai shiru ganin Mai martaba ya shigo Dan basu tab'a tunanin zai shigo a wannan lokacin ba .bakinta na rawa itama ta ansa masa sallamar sa tana gaida shi. Mai martaba ya k'araso har tsakiyar falon sai a lokacin Fulani Salamatu ta mik'e tana kallan Mai martaba tace cikin girmamawa. "Barka da shigowa rankai Dad'e"ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa alamar girmamawa. Da hannu Mai martaba ya ansa mata fuska d'aure ya kalli Aziza data sunkuyar da kanta gabanta na fad'uwa Dan ta tabba kenan yanzu Mai martaba yasan abinda ta aikata. Mai martaba ya kalli Aziza yace cikin b'acin Rai. "Aziza meya had'a ki da HUYAAM da kika Huda mata k'afa da takalminki?.."Mai martaba ya fad'a Yana lura da yanayin Aziza. Aziza ta k'ara sunkuyar da kanta k'asa batai magana ba.mai martaba yace. "Badake nake ba?..". Da k'yar Aziza tace. "Abba Bada sani na bane bafa".Mai martaba ya mata Wani kallo yace. "Baki sani ba kamar Yaya? wad'an akai abin a gaban nasu sune zasu miki K'arya ko yaya? Nan ma Aziza shiru tai batai magana ba .Mai martaba yace. "To Kinga wannan shirun da Kikayi ya tabbatar min da cewa k'arya kike kenan kina sane kika takatan".ya cigaba yace. "Aziza na riga da nasan halin kowa acikinku sau nawa kina yiwa HUYAAM Irin wannan d'in ko kun d'auka ban sani bane ba? To na sani Wani abun kau da kai kawai nake Dalili kuwa shine saboda uwarta Batasan Hayaniya ko kad'an shiyasa ko nace Zanyi magana take hanawa da tunanin zaki gyara watarana. Amma duk na lura keda uwarki duk Baku San haka ba, sannan Baku San kawai cin da take muku ba har yanzu ko? Ko nace Bakwa Gani tunda gashi Baki fasa ba Shine yau ma kika K'ara ji mata Wani ciwon ko?. Aziza tai shiru tana k'ok'arin fashewa da Kuka Amma ta kasa yin hakan. Mai ya ya cigaba yace. "To bari Kiji zan Miki worning na k'arshe Aziza.kinyi na farko kinyi na k'arshe Kuma kinsan halina duk ranar da kika sake jiwa Huyaam Wani ciwo ko kikai mata kallan Banza ma agidan nan ke ba ita ba ko waye kika sake naji labari to aranar sai Kinga true color d'ina kinji ko bakiji ba?..."ya fad'a cikin b'acin Rai. Aziza na sheshshek'ar kuka da Bata tab'a ganin b'acin Ran Mai martaba ba kamar na yau ba tace. "Naji Abba". fulani Salamatu da ranta ya gama B'aci jin abinda Mai martaba ya fad'a Amma sai Bata nuna ba ta Kalli Mai martaba takwantar da murya tace. "A gafarceni Rankai Dad'e da abinda zan fad'a Allah ya taimakeka. Amma da ba haka ya kamata kace ba, kamata yay ka had'a su duka su biyun kai musu fad'a,idan ma Hakan bazai yuba to gara kawai kace kar Wanda ya K'ara yiwa Wani magana acikinsu nake Ganin Hakan zaifi".ta fad'a tana d'auke kanta daga kallan Mai martaba ganin tunda ta fara magana taga yadda yake mata Wani Irin kallo. Mai martaba ya Jin Jina kai Kafin yace. "da dukan alamu dai Fulani bakisan Irin raunin da Aziza taiwa Huyaam ba koh, Shiyasa zaki fad'i haka ?To bari Kiji na fad'a miki idan Baki sani ba Aziza ta kusan nakasta Huyaam tai a k'afarta tunda gashi har suka tafi asibiti jini Bai daina zuba a k'afar taba Allah ne ya tak'aita da ba wannan labarin ake ba yanzu.kuma da ace ta nakasta tatan me zaki cewa uwarta Fulani?". ya fad'a cikin b'acin Rai.fulani salamatu tai shiru kanta a k'asa Mai martaba ya cigaba yace."sannan Abinda na fahimta Dake wato fulani kome Aziza tai na laifi to ke awurinki ba laifi bane ke bama iya Aziza duka yaranki basa laifi idan ma sunyi sai kinyi yadda kikai ba'a ga laifinsu ba.to bari Kiji ni bazan d'auki wannan ba Aziza dai 'ya tace Kuma na Isa da ita bama ita kad'ai ba har ke Saboda haka idan Ina mata fad'a karki K'ara samun Baki kinji na fad'a miki,sannan Abu na gaba shine ni bazan yadda a rabamin kan 'ya'yana ba Kuma duk Wanda ya Sab'a umarnina bazai ji Dad'i ba nasan kema kinsan da wannan sai dai ki bawa Wani labari Ina fatan kinji?". ya fad'a Yana kallan Fulani Salamatu...da k'yar fulani Salamatu ta gyad'a masa kai tana Wani cin magani.mai Martaba ya cigaba Yace . "Sai Abu na gaba yanzu basa nan sun tafi asibiti Ina umar tarku da idan sun dawo zuwa gobe da safe inaso daga ke har Aziza kuje har b'angarensu ku duba HUYAAM sannan ku bawa uwarta hak'uri kinji na fad'a muku, kuma wallahi idan Baku jeba wallahi sainayi mumman Sab'a muku". Yana fad'ar haka ya nufi kofa ya fita daga falon gabad'aya. Yana fita Fulani Salamatu tace. "Tab' d'ijan lallai ma wato an tab'o 'ya'yan mowa ko? To wallahi babu inda zani".kawai Babu tambayar Mai ya had'asu saboda kaje an zugo ka shine zaka zo nan mu ka sauke mana ta wallahi wannan Karan sai dai ayi duk wacce za'ayi Amma babu inda zani".ta fad'a tana huci Ramla ta kalli Fulani Salamatu tace cikin sanyin murya. "Mummy Abba fa gaskiya ya fad'a Yaya Aziza ce Bata da gaskiya fa". Fulani Salamatu tace cikin b'acin Rai. "Dalla rufe min Baki marar zuciya kawai,keda bakya k'aunar naki bare kiyi kishinsu sai bare a gaban ki akayi da har zaki Yi Shardai zirr?..." Ramla tace . "Wallahi mummy agabana akayi" . Fulani Salamatu tace. "Dalla rufe min Baki idan na K'ara jin bakin ki a wurin nan saina fasa wallahi Sha Sha kawai marar hankali wacce Batasan masu k'aunar taba". Ramla taja bakinta tai shiru tana sauraran mummyn nasu. fulani Salamatu taja tsaki ta k'arasa wajen Aziza Dake kuka tace. "Tashi Muje kibar kukan nan ya isa haka aziza, ni wallahi kin mun dai dai dama kin karya k'afar tata sai muga ya za'ayi" Aziza Bata ce komai ba ta mik'e ta bar falon gabad'aya ta haura sama da sauri tana goge hawayen fuskarta. Fulani Salamatu tabi bayan ta.Ramla da walida suka bisu da kallo ganin yadda momyn nasu take ta fad'a kamar zata Ari Baki....... 07066508376_______ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *PAID BOOK *FREE PAGES* *NA* *__(MRS SARAKIES )__* *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 1 ____________ *Ingiland *5:40 pm* Alokacin da su Ammie suka tafi asibiti wajen k'arfe 7:40pm na dare anan ingiland Kuma k'arfe biyar da mintuna Arba'in ne . dawowarsa daga wajen aiki kenan Yana tsaye a tsakiyar d'akinsa bayan ya rage kayan jikinsa k'ugunsa d'aure da towel zai shiga wanka.har ya k'araso Bakin toilet d'in zai shiga kawai sai yaji yana son jin muryar Ammie a wannan lokacin Dan rabonsu da waya da ita tun a daren jiya yaso d'azu yana office ya K'irata to sai aiki ya Hanashi Hakan.ya dawo har Inda ya ajiye wayoyinnasa Dake gaban mirror d'akin ya d'auki wacce yake amfani da ita for important person more especially iyayensa sai siblings d'insa iya contact d'insu ne kawai aciki.bayan ya d'auka ya shiga call logs yay darling number Ammie sai da Yay mata 2 Miss call batai picking ba abun sai ya D'an bashi mamaki kad'an, Dan Bai fiye K'iran Ammie Batai picking ba ,Koda yaushe idan ya K'irata miss call D'aya biyu tai picking idan har Bata kusa kenan Hakan yasa ya K'ara dealing number nata a kar o na uku. A wannan lokacin kuwa da Afeef ke K'iran Ammie wayar tana d'aki Dan tashin hankalin ma da take ciki Bai sa Ammie ta tuna da wayar taba bare ta d'auka ta tafi asibitin da ita ba. Gabad'aya su kuma su Huda suna falon k'asa azaune tun tafiyar su Ammie Babu Wanda ya shiga ko da d'akine dukansu suna zaune a falon sai ya Zarah da tashiga d'aki yanzu bada dad'ewa ba .baba magiya ma tana zaune a falon tare da su, muneefa na kwance ajikinta ta mik'e da sauri daga jikin baba magajiya. Baba magajiya ta Kalleta tace.. "A'a muneefa Ina saki Kuma?..."muneefa ta ya Mutsa fuska tace. "Fitsari nake ji".daga haka ta haura sama da sauri zuwa d'akin Ammie ko kula baba magajiya Dake cewa Kizo ki shiga toilet d'in falon batai ba hankalinta yayi d'akin Ammie tana shiga tai cikin toilet d'in da sauri babu dad'ewa ta fito tana fitowa ta Tarar da wayar Ammie na ringing Hakan ta yasa ta k'arasa inda take Jin ringing d'in ta d'auko ta fita daga d'akin wayar na rik'e a hannunta da sauri ta koma falon ta K'arasa wajen Huda tace. "Ya Huda ga wayar Ammie ana ta k'ira".ta fad'a tana Mik'a mata wayar..Huda ta karb'a tana kallan Mai K'iran ganin yayansu sune yasa tai picking cikin girmamawa tace. "Assalamualaikum.barka da dare Yaya Ina wuni".ta fad'a cikin sanyin murya.take gaban Afeef ya Fad'i Jin Huda ce ta d'auki wayar Sannan kuma yaji muryarta Wani Iri amma sai Bai nuna Hakan ba yace cikin deep voice d'insa. "Lafiya Ina Ammie da kika d'aukar mata waya". ya fad'a cikin kamewa Huda tace cikin sanyin murya. "Batanan sun tafi asibiti ne shiyasa". ta