Sashe 56
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
su ace Babu Wanda zai taimakawa wad'an nan bayin Allahn da suka rik'e sultan lallai sai yanzu na yarda da ake cewa naka naka ne Amma dad'in zama sai bare Wallahi sai yanzu na yarda" ta fad'a tana Sauke numfashin b'acin Rai.Anty Amina tai k'asa da murya ta ce "kiyi hak'uri inna" Hajiya inna ta goge idonta da k'walla ta kusan zubowa ta Kalli dogarayen da suke rik'e da sultan tace su tai Maka su shigo dashi ciki "Mai martaba yay gyaran murya ya ce cikin nutsuwa Yana b'oye rauni da Damuwar da yake ciki aduk lokacin Daya wayi gari yaga sultan a irin wannan halin yaro saurayi Wanda ak'allah zaiyi 25 to 26 haka a shekaru Amma shine ke wannan ciwon haukan har yanzu Abu sama da shekaru 28 "ku rik'e shi kawai " cewar Mai martaba Yana bawa dogarayen umarnin K'ara rik'e sultan. matsawa sarki yayi kusa da sultan yasa hannu ya dafa shi Yana karanto masa addu'o'i tsawan Wani lakaci take sultan Yaja Wani dogon numfashi lokaci D'aya jikinsa ya saki ajikin dogarayen Dake rik'e dashi Mai martaba ya Basu umarnin su shiga dashi ciki Babu musu suka ansa masa tareda ta rik'o sultan suka shiga dashi ciki.a kan gadon sa suka Kwantar dashi suka duk'a har k'asa sukaiwa Mai martaba sallama cikin girmamawa sannan suka juya suka fito daga d'akin gabad'aya.Mai martaba ya k'araso d'akin cikin nutsuwa hakama Hajiya inna sai anty Amina zama yayi a gefen gadon Yana kallan sultan Dake kwance Abuwa masu yuwan da nauyin gaske suna dan k'are a ransa Hajiya inna ta Tsaya tana kallan sultan ta fashe da Kuka ta ce "kullum Abu sai K'ara girma yake Allah na tuba ni Abu Kwana biyun nan har Ina murna cewa sauk'i ya fara zuwa musu Ashe abun lafawa yayi" ta fad'a tana share hawayen idonta.mai Martaba ya d'ago ya kalleta yay k'asa da murya ya ce "Hajiya kiyi hak'uri kuje ku kwanta ni zan zauna dashi har safiya in Sha Allah" Hajiya inna ta ce "a'a kadai barni kai kaje ka huta ni zan zauna dashi" Mai martaba ya Sauke numfashi ya ce "Hajiya ki daiyi hak'uri ki barni dashi d'in Kuna bukatar hutu keda Amina Dan Allah kuje ku kwanta" Anty Amina ta sunkuyar da kanta k'asa alamar girmamawa ta ce " in Sha Allah rankai Dad'e ta Kalli Hajiya inna ta ce "Hajiya muje tun da Mai martaba ya ce zai zauna" kamar Hajiya inna zatai musu sai Kuma kawai ta hak'ura ta Kalli sultan Dake kwance har lokacin Bai farka ba tace cikin sanyin murya "Allah ya Baku lafiya Allah ya kawo k'arshen wannan wahalar"daga haka ta juya tabi bayan Anty Amina ganin tana Neman fashewa da Kuka suka fita daga d'akin gabad'aya.sauke ajiyar zuciya Mai martaba yayi ya zubawa sultan Ido kawai Yana kallansa baya ko kiftawa Abubuwa na masa kai kawo a ransa...... HUYAAM LAMID'O AZIZ CHIROMA AFEEF Littafin HUYAAM na kud'i ne regular group akan naira 500 beforehand mu gama free pages muka gamawa Kuma zai koma 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in 2270127432 Naja'atu umar zenith bank Evidence of payment 07066508376 *Yan Niger _zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA 07066508376 *TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!* *Assalamualaikum* *Ina kuke manyan mata masu capacity ? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."* *To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* *1,Atamfofi* *2, lesses* *3, Abaya* *4, kayan kwalliya ko Wani iri ne* 5,*D'an kunnaye(jiwelleries)* *6,takalma* *7,hand bag* *8, mayafai* *9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*. *domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka +234 811 190 1302 /09020337676* *Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta* *Sai mun Jiku 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__* *__(MRS SARAKIES )__* My channel link https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y PAGE3 ___________ Kwance tashi Babu wuya a wurin Allah gashi yanzu har su Huyaam sunyi kwanaki biyar a Abuja, rayuwarsu suke cikin walwala da Jin Dad'i agidan Anty khadija duk abinda suka ga dama shi sukeyi, Amma ba Wanda ya Sab'a dokar addini ba ko kuma al'ada kawai duk dai Wani abinda ya Dan ganci Jin Dad'in rayuwa Wanda zai sasu nishad'i to shi sukeyi Dan babu laifi Anty khadija tana San Yara sosai musamman akace 'ya'yan 'yan uwan tane nanfa zakiga nuna soyayya kamar 'yay'an data haifa a cikinta. Yanzu haka k'arfe biyar Saura na yamman ranar saturday shiri kawai suke zasu fita unguwa ne za'a kaisu su ga gari sannan a zaga dasu suga ko Ina a garin Abuja da kewayenta.huyaam na gaban mirror tana shafa lip balm leb'enta bayan ta gama ta juyo tana kallon Huda Dake gyarawa siyama kwallin Daya D'an zazzago ta k'asan idonta.siyama ta kalli HUYAAM bayan angama mata tace. "Wow Masha Allah! kinga yadda kikai kyau kuwa? HUYAAM tai murmushi tace. "Thank you so much sis kema kinyi kyau ai" siyama ta D'an Bat'a Rai tace. "Ya za'ayi nai kyau bayan duk kun kama kunsa kaya iri D'aya ni Kuma nasa nawa daban gaskiya bazan yadda ba saidai Wani ya cire ya sauya Wani kayan in yaso duk mu fita with differents dresses" ta fad'a tana Wani tura Baki gaba.Huyaam tai murmushi ta ce "to ke in Banda abunki wayake Raba hanta da jini". Siyama ta ce "Allah sarkie ni wato Dan Kunga ni kad'ai ce bani da 'yar uwa shine za'a min gori ko? Huda ta rik'o hannunta tana Murmushi ta ce "da wasa take Miki fa, mu mun Isa muce haka kema kinsan mu 'yan uku ne ba 'yan biyu ba" sai Alokacin siyama ta saki murmushi taiwa Huyaam gwalo. Huyaam ta ce "zamu had'u ne yarinya" Ramma ce tai knocking k'ofar tare da sallama suka Bata Iznin shiga.turo k'ofar tai tashigo tana kallansu ta ce "Anty tace ko fito driver na jiranku a waje" ansa mata sukai da to.sannan ta juya ta fita daga d'akin bayan ta rufo musu k'ofar. Huyaam ta d'auki hand bag d'inta da wayarta a hannunta ta ce tana kallansu"ku fito mu tafi Dan Allah" Daga haka tai hanyar k'ofar fita bin bayanta sukai bayan suma sun d'auki wayoyinsu da handa bag suka fito daga d'akin gabad'aya bayan sun kullo k'ofar...a Falon downstairs Suka Tadda Anty khadija Zaune saman kujera sai imaan akusa da ita Hassan da Hussain Kuma suna can back yard d'in compound suna ball . Anty khadija na kallansu ta ce "Kun fito kenan?" Suka ansa mata ta ce "to Maza ku wuce ku tafi tun d'azu driver ke jiranku ko duk kwalliyar aka tsaya Yi ne" ta fad'a tana kallan su .sunkuyar da kai sukai k'asa suna Murmushi Amma basuyi magana ba.Anty khadija tai murmushi ta ce "to ko dai siriki za'a min a garin Abujan ne ban sani ba" ta fad'a da sigar tsokana.ai tuni suka rufe fuskokinsu da tafukan Hannayensu suna Murmushi suka hau cewa "a'a mummy" Anty khadija tai dariya ta ce "aishikenan Allah ya tsare" ansa mata sukai tareda Yi mata sallama. tana kallansu ta ce "karku kai Dare fa" sukace in Sha Allah" d'aga haka suka nufi hanyar fita daga falon gabad'aya imaan tasa rigima akan zata bisu mummy ta hanata ta rarrasheta tukunna ta hak'ura....tunda suka fito daga cikin unguwar nan gabad'aya acikin mota suna tafiya Batare da sun fad'awa driver Ina zai fara kaisu ba,hirar su kawai suke a Bayan motar.jin shiru Basu Fad'i inda zasu ba gashi driver sai tafiya yake Bai San Ina suka nufa ba yasa drivern ya ce Yana kallan gabansa "ranku ya Dad'e Ina zamu fara zuwa? Siyama ta Kallesu ta ce "Ina ya kamata mu fara zuwa? Huyaam ta ce "ai kece 'yar gari ke kikasan wurare" Huda ta ce "tun da an bamu zab'i nidai muje ShopRite ko Kuma Wani park haka " Huyaam ta ce "Nidai indai akwai wurin zuwa mutum yayi wasa ko ya hau kan Doki ko Kuma mota to akai mu can" siyama tai murmushi ta ce"ai duk irin wuraran da kuke so a Garin Abuja akwai just choose the one and go" Huda ta kalli HUYAAM ta ce "to wanne ya kamata muje" Huyaam tai fari da ido ta ce "nidai inda na fad'a shi nake son zuwa" Huda ta ce "to muje" siyama ta kalli driver ta fad'a masa inda zasun .yasan wurin Hakan yasa Babu musu ya ansa musu suka kama Hanyar wajen...wurin shak'atawane babba Wanda aka gina shi na musamman for Irin 'yay'an anjeboters d'in nan like them.wuri ne Mai d'auke da differents places of plays and enjoyment. Tun da driver Yay parking Suka sauko daga cikin motar ya juya zai kai motar inda kowa yake parking idan yazo Huyaam ke kallan wajen Wani irin farin ciki ne Kawai ya kamata bisa ga tozalin da tai da abuwan enjoyments d'in da take so awurin, take taji