← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 85

Sashe 62

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kulasamarin nayi ALKawarin zan iya jiranki" cikin tsoro da fargaba Huyaam ta ce "a'a nidai Babu ruwana sai anjima" ta fad'a tana k'ok'arin kashe wayar yay saurin cewa"Dan Allah to ki barni na dinga k'iranki Ina Jin Jin daddad'ar Muryar ki Koda Baza ki barni Nazo gida ba?" Girgiza masa kai tai tana kashe wayar lokaci D'aya ta juya ta kwanta tai rufda ciki tana sheshshek'ar kuka...siyama Dake zaune kan gado kusa da Huda tana sauraran duk conversation d'insu ta d'aga kanta ta Kalli HUYAAM ta ce "ke wallahi wannan mutumin daga Jin muryarsa ma ko Baki ganshi ba kinsan kyakkawane wai Dan Allah waye shi? Huda ta ce "ina Wanda ya taremu ranar a park har yake cewa Huyaam ta bashi Aran lokacinta? Siyama tai Jimm alamar tunani sai Kuma can tace "tabbas na gane shi" Huda tace "to shine fa" ai tuni siyama ta mik'e Zaune da sauri tana kallan Huyaam ta ce "wallahi Huyaam Wannan mutumin ya Had'u kinsan Allah karkiyi wasa da damarki ki saurareshi Koda Baza ki bari yazo gidan bane ba ko iya waya kuke yima ai ta isa,ko Huda?" ta fad'a tana kallan Huda.Huda ta gyad'a mata kai tana murmushi Amma batai magana.can Kuma Siyama ta ce "to abin mamakin ayina ya samu contact D'inki nan ma banza tai ta k'yaleta. Huda tace "Nima Abinda nake tunani kenan Amma haryan na kasa samun ansa ta" Siyama ta ce "ita Huyaam d'in ta tambaya shi ne?" Huda ta ce "inama ma ta saurara shi da har zata sani? Siyama ta ce "uhmm to bari Idan ta huce na tambayeta".Ita dai Huyaam tana Jin su batai magana ba Dan Bata jin ko uwar had'uwa yayi zata tab'a kula shi ba, ita su barta ma da abinda yake damunta.tana wannan tunanin har bacci ya d'auketa tana jinsu suna ta hirar had'uwar da yayi sama sama... __________ Da daddare misalin k'arfe biyu Saura na dare a cikin masarautar zazzau, lokacin idanuwa sun rufe ma'ana kowa yayi bacci,shiru babu motsin ko wanne Maha luk'i a Cikin wannan dare,Dan ko Kukan tsuntsu bakyaji sai daddad'ar iska Dake Kad'awa tana kad'a bishiyun Dake shuke a cikin palace d'in.a Kuma wannan lokacin a Wani sashe Dake nan cikin masarautar cikin Wani d'aki mai bala'in duhu Wanda bakya tab'a ganin komai aciki ko da hannun Kane.daga tsakiyar d'akin na hango wasu mutane su biyu mace da namiji suna tsaye da dukan alamu magana sukeyi. muryar ta namijin da naji ta doki dodon kunnuwana Yana cewa macen Dake kusa dashi a tsaye "bazai yuba Razik'a,bazai yuba,Dan ko Bazan tab'a kashe sultan a yanzu ba har sai lokacin dana tsara yayi,ai ni ba sultan ne yamin Laifi ba da zan kashe shi? ni ubansa ne yamin Kuma Kinsan fansa nake d'auka akan sultan ba akan ubansa ba,saboda haka sultan Babu abinda yamin kawai dai so nake na k'unta tawa ubansa akan sarautar sarki da aka bashi Mai makon ni shiyasa nake so ciwon zuciya ya kashe shi lokaci D'aya zuciyar sa tai bundaga ya Fad'i ya mutu ta hanyar jinyar ciwon haukan da muka sawa sultan yakeyi shiyasa kikaga nake bin Komai a hankali bana gaggawa kema Kuma nake goya Miki baya kike duk abinda kika ga dama" ya fad'a Yana zare ido. Sauke numfashi wacce aka k'ira da Razik'a tai ta ce "Amma maina Bai kamata nazo Maka da buk'ata ta kace ba haka ba" maina yay Wata iriyar dariya ya ce "Razik'a Kenan kin manta waye ni? Ki Fad'i wata buk'atar nai Miki Amma ba wannan ba" harararsa tai acikin duhun d'akin tana Jin Kamar ta shak'e shi ya mutu haka take ji ta ce "so nake na cika aikina akan gimbiya Ayush" maina ya kalleta ya ce "eh Nima nazo da Wani abun Amma Mai kike buk'ata akan nata?" gyara tsayuwarta tai ta ce "so nake nayi aikin da boka na yabani nayi amma na rasa ta wacce hanya zanbi maina?" Maina yay jimmm alamar alamar tunina sai kuma can ya ce "ayina zaki aiwatar da aikin naki?" Razik'a ta ce "acikin d'akin tane maina Amma nasara ta Ina zan fara gabad'aya wannan k'anwar tata ta Yi bak'e bak'e a d'akin na rasa ta Ina zan shiga har na aiwatar da aikin ga itama jara babbiyar tsohuwar nan Hajiya inna taje ta tare a part d'in ta kasa ta tsare na rasa ta Ina ma zan fara" ta fad'a cikin damuwa.Jin jina kai maina yayi ya ce "wannan Mai sauk'i ne" Razik'a ta ce "Taya ya ya zama Mai sauk'i?" Maina ya ce "kamar yadda mukai a wancan Karan a wannan ma haka zamuyi "ni zanji da komai ke Kuma ke zaki je ki aiwatar da aikin" ta ce "na fahimta ya ce "shikenan ke dai kisa lokaci kawai Ina jiranki" sauke numfashin salama Razik'a tai Jin abinda maina ya fad'a take murmushi ya bayyana a Saman fuskarta ta ce "godiya nake sarkin masarautar zazzau na gobe"wata iriyar dariyar farin ciki maina yayi kafin ya ce "an gaisheki sarauniyar masarutar zazzzu ta gobe" sai Kuma ya ce "Nima akwai abinda nazo dashi Wanda duk zaki had'a kiyi Aikin tare" kallansa Razik'a tai kafin tace"menene maina?" Mik'a mata Wata jarka yayi Yana kallanta, karb'a Razik'a tai tana jiran K'arin bayaninsa ya ce "duk ranar da zakiyi wannan aikin naki ki zuba mata ajikinta kafin ki fara naki aikin" Razik'a ta kalleshi cikin rashin fahimcita tace "shikuma na miye?" Ya kauda da kansa gefe yace "ke idan zakiyi naki aikin Ina tambayar ki na miye?" Girgiza masa kai tayi.ya ce "to Nima wannan nawa aikin ne na Daban" ita dai Razik'a kallansa kawai take . Ya ce "mu bar gunnan lokaci fa Yana tafiya kar wasu su fito su ganmu" Jin jina e kai Razik'a tai kafin ta ce "hakane Maina bari na tafi idan na shirya yin aikin zan maka magana" ya ce "saikin shirya d'in Ina sauraranki" daga haka yabi bayan Razik'a ganin ta nufi hanyar k'ofar suka fita daga d'akin gabad'aya bayan sun kullo k'ofar a Hankali,suna fita daga d'akin kowa ya nufi b'angarensa ta boyayyiyar hanyar da suke biyo wa a duk lokacin da zasu had'u d'in..... HUYAAM LAMID'O AZIZ CHIROMA AFEEF ABDALLAH SHATTIMA Littafin HUYAAM na kud'i ne regular group akan naira 500 before mu gama free pages muka gamawa Kuma zai koma 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in 2270127432 Naja'atu umar zenith bank Evidence of payment 07066508376 *Yan Niger _zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA 07066508376 *TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!* *Ina kuke manyan mata masu capacity ? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."* *To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* *1,Atamfofi* *2, lesses* *3, Abaya* *4, kayan kwalliya ko Wani iri ne* 5,*D'an kunnaye(jiwelleries)* *6,takalma* *7,hand bag* *8, mayafai* *9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*. *domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka +234 811 190 1302 /09020337676* *Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta* *Sai mun Jiku 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *___NAJA'ATU UMAR FAROOQ__* *__(MRS SARAKIES )__* *Bismillahirrahmanirrahim* My channel link https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y PAGE 3 ___________ Tun daga wannan ranar Aziz chiroma da Abdallah shattima suka Saka Huyaam agaba da yawan k'iran waya Babu dare babu Rana kullum ne idan garin Allah ya waye sai sun K'irata Koda Baza tai picking ba basa tab'a hak'ura, gefe guda kuma wannan d'aya number data rage da har yau Batasan kowa ye ba Kuma dayak'i bayyana mata kansa shima sai yayi mata sms da barka da safiya da Kuma good night.yanzu shi kad'ai ne kawai Daya rage da Bata San ko waye shiba,and thank God ma da yak'i bayyana Mata kan nasa a gareta ita Hakan ma shine dai dai Dan Bata son a k'ara Bata Wani mamakin Wanda yafi na Aziz chiroma Kuma, Wanda har yau ta kasa daina Mamakinsa wai shine ya furta mata Kalmar so, yake sonta.bai tsaya iya nan ba gefe guda kuma ke mata kalaman soyayya ko kunya bayaji. Abu D'aya ne a yanzu yake damunta na yadda zata dak'ile Yi mata message d'in da akeyi Dan harta gaji da goge Wanda yake mata kullum. Ga suma kansu su Aziz da Abdallah shattima Banda Anty khadija ta ce Babu kyau walak'anta Wanda ya ke sonka ta dinga Sauraransu har su Gane Batason nasu su hak'ura su k'yaleta su Rabu lafiya da wallahi ba abunda sai Hana ta blocking dinsu tun tuni.,Ita gabad'aya zuwanta Abuja ma ba hutune ya kawota ba Damuwa ce kawai aka Sakata aciki. yo inba haka ba Mai zaisa kace baka Son mutum Amma ya nace Maka dole saika so shi.gashi har yau satin su biyu da Kwana biyu a Abuja har suna shirye shiryen komawa kano... yanzu haka da misalin k'arfe hud'u da Rabi na yamma zauna take agefen gado
Chapter 62 · 0% Book details