← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 85

Sashe 61

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

doka har ga Allah Bata son karya masa wannan dokar Daya gindaya musu harta iya kula wani a bayan idonsa.tana wannan tunanin ne wayarta tai K'ara Alamar shigowar message yasa ta juya tana kallon secreen d'in wayar,D'aya daga cikin 2 numbers d'in Dake mata message ne Yay sak'on.kallan screen wayar kawai take tana karanta contents d'in Bata ko kiftawa "good afternoon my sweet, hope kin tashi Lafiya. Anya ko bazan biyoki Abujan nan ba ko na samu Wani relief kan abinda nakeji akan Rashinki kuwa? Dan Allah ki tausayawa marayan Allah wallahi zuciya ta ta kasa jira har sai kin dawo Batare da na samu nayi tozali da kyakkyawar fuskar kiba " iya a binda ya rubuta kenan.gaban tane ya yanke ya Fad'i Jin abinda ya fad'a tana zare ido tana duba d'akin kamar Wanda take tsaron Wani yaga abinda aka rubuta matan na wai ya biyo ta Abuja? Kallan wayar ta sake Yi Jin Wani sak'on ya sake shigowa "zan iya k'iranki yanzu?" iya abinda aka rubuta kenan.k'ara zare ido tai k'irjinta na bugawa da sauri da sauri ita kan ta shiga uku Waye wannan waye yake Neman ja mata bala'i haka tana zaman zamanta share hawayen da bata ji saukar suba sai danshin su kawai taji tai, Karan farko data ji zatai replying message d'in taji ko waye shi d'in.k'ara damk'e wayar tai a hannunta ta shiga Yi masa reply kamar haka "waye kai please?" kamar jira ake tai reply d'in nan da nan saiga reply ya shigo ko minti D'aya Ba'ayi ba "can I call you to introduce my self know?" iya abinda aka rubuta kenan. kallan sak'on ta dinga Yi bata ko kiftawa ta shiga Yi masa reply kamar haka "yes Yo can" alokacin Daya ga message d'in kasa gaskatawa yay Saida ya murza idonsa da kyau yaga dai da gaske ne wai yau Huyaam ce ke masa reply abinda Bai tab'a tunani ko tsammani ba, cikin sauri ya Maida akalar message d'insa zuwa k'ira yana Jin ta shiga zuciyar sa ta dinga bugawa da sauri da sauri har yaji ta katse ba'ai picking ba take Kuma jikinsa ya fara rawa ya K'ara dealing hopping tai picking azuciyarsa ya ce "gara na sanar miki da ko ni waye Dan bazan tab'a iya hak'ura har ku dawo batare da na bayyanar da kaina a gareki ba ko zanji abinda nakeji akanki ya ragu my sweet" Haka ya fad'a Yana Wani lumshe ido.ita ko Huyaam alokacin Daya k'ira kasa yin picking tai Saita tsinci kanta tana Mai fargaba da tsoron d'aga K'iran nasa take ta runtse idonta hawaye na zubowa zuciyar ta na bugawa da sauri da sauri ta runtse ido har K'iran ya katse tana ji aka sake k'ira sai da ta kusan katsewa sannan tai picking takai kunne tai shiru batai magana.shima kansa shirun yayi ya rasa Kuma Mai zai ce mata ya tsaya yana sauraran bugun zuciyarta Wanda ke bugawa da sauri da sauri ganin yak'i magana yasa Huyaam tai k'arfin halin cewa cikin rawar murya "Dan Allah waye kai? waye kai daka ke so ka sa ruyuwata acikin masifa da Bala'i kake so ka katsemin farin ciki da walwata Mai nai Maka Dan Allah?" ta fad'a tana rufe fuskarta da tafukan Hannunta Dan har ga Allah tun ranar su Suka fara tura mata da message d'in nan gabad'aya take a tsorace da damuwa tana fargabar ace yayansu ya sani ko Kuma Wanda yasa ya dinga sa Musu ido ace ya sani harya fad'a masa .Shiru yayi kamar Yana sauraran yadda take rera masa kuka a hankali Yana Jin K'aunar ta na k'aruwa a duka sassan jikinsa dama ruhinsa gabad'aya, gyaran murya yayi ya ce Cikin muryar da ko a mafarki idan Huyaam taji ta sai ta Gane ta "okay let me introduce my self first" take Huyaam ta runtse idonta da k'arfi tana tsoron gaskata abinda zuciyar ta keson tuna tar da ita kaddai ace shine innalillahi wainna ilaihi raji'un kai Ina tasan ma bashi bane ba" maganar da yayi ne ya dawo da lta daga duniyar tunanin Data tafi " Dan Allah Huyaam duk abinda zakiji Daga gareni Dan Allah karki kice ba haka ba, Dan Allah idan kika fahimci ko waye Dan Allah karki kashe min wayata please & please Dan Allah ki tsaya ki Saurareni" Haka ya fad'a kamar zaiyi Kuka.tunda ya fara magana Bugun zuciyarta ya K'ara tsananta bugawa da sauri tana k'ok'arin rasa nutsuwarta gabad'aya shine fa shine fa. "Huyaam!" ya K'ara K'iran sunanta a karo na Biyu ya cigaba ya ce "suna na Abdul'Aziz shehu chiroman bicci Ina fatan kin Gane ni Kuma Zaki tsaya kisaura reni? Take Huyaam ta zaro ido waje Jin ko waye ya AZIZ CHIROMA fa? ya AZIZ dai na gidansu cikin rawar murya ta ce "ya chiroma dama Kaine kake ta yimin barazana da zuciya ta da wasa da hankali kasani a cikin damuwa kana tada min da hankali na Mai nai Maka Dan Allah Dana can canci haka daga gareka"? Haka ta fad'a tana toshe bakinta duka biyun"lumshe ido Aziz yayi yana sauraran yadda take rera kuka "yay karfin halin K'iran sunan ta da "Huyaam!" K'ara toshe bakinta tai jin Kuka na k'ok'arin kufce mata tun kafin Wani acikin su Huda ya jita.jin tana rera kuka yasa Aziz yay k'asa da murya ya ce "please Huyaam Dan Allah ki saurareni Kiji Abinda zan fad'a miki wallahi na kasa b'oye abinda na Dad'e tun tuni Ina fama da shi ne azucita,yanzu ne danaga bazan iya ba na kasa jurewa na zab'i Dana sanar Dake tun wuri" tsayawa yayi yana Sauke numfashin ya cigaba ya ce "tun lokacin da nake Zaune a palace ta kano na kamu da sanki Amma na kasa furtawa Miki nake ganin yanzu ne dai dai lokacin Daya dace na fad'a miki tun kafin Wani ya riga ni. Dan Allah Huyaam karki ce Bakya Sona wallahi zan iya shiga Wani Hali" ya fad'a da wata iriyar murya kamar Wanda shima zai saki Kukan. Runtse idonta ta K'ara Yi tana Jin saukar kalamansa kamar saukar ruwan dalma a kunnuwanta.jin tayi shiru yasa ya ce "say something please" ya fad'a da murya me ban tausayi.Huyaam Dake jinsa Amma Kuma ta kasa magana yasa ta Dake kai k'arfin hali ta ce "ya Aziz Yanzu Dan Allah Mai nai Maka da Zaka ce kana Sona duk 'yan matan garin kano karasa wacce zakace kana so Saini? yanzu ni nawa neke da har Zaka tsareni da kalmar soyayya ko ka manta a yanzu ne na gama secondary school zan shiga jami'a Dan Allah ka rabu Dani karka Kara k'irana kaje ka nemi dai dai dakai" ta fad'a cikin rawar murya.Aziz chiroma Da Lokaci D'aya ya dawo sense d'insa Jin abinda Huyaam ta fad'a ta fara girgiza kai ya ce cikin Tashin hankali "please Huyaam karki ce haka Dan Allah ki daure ki ansa soyayya ta wallahi Ina sonki zan iya rasa Raina idan na rasa ki" ya fad'a cikin karyewar murya. ta ke Huyaam ta k'walo ido waje Jin abinda ya fad'a duk da firgicin da take ciki ta ce "wai Dan Allah so kake Yaya ya kasheni ne? yafa hanamu kula samari Dan Allah ka k'yaleni karka sake k'irana na rok'eka Dan Allah" ta fad'a tana sheshshek'ar kuka.Aziz ya girgiza kai ya ce "indai Afeef ne zan fad'a masa cewa Ina sonki na tabbatar bazai hanaki kula niba"da sauri Huyaam ta girgiza masa kai ta ce "A'a karka k'irashi wallahi kasheni zaiyi idan yaji Dan Allah" ya ce "to naji, Amma Dan Allah zan rok'i wata Alfarma agunki, Dan Allah idan na k'iraki ki d'inga d'agawa Koda Baza kiyi magana" cikin k'osawa Huyaam ta ce "eh naji Dan Allah ka rabu Dani" tana Jin buguwar Zuciyasa . Cikin Mamakin abunda ta fad'a ya ce "da gaske kike my sweet" Bata ansa masa ba cikin sauri ta ce "please leave a lone" daga haka ta kashe wayar tana sauke numfashi kafin ta jefar nan saman gadon ta kifa kanta cikin filo tana sheshshek'ar kuka Saida tai Mai isarta sannan ta hak'ura ta koma sauke numfashi a jejere anan bacci ya d'auketa.....the Same da magrib Huyaam tana kwance saman gado har bacci ya fara d'aukar ta saboda Kukan da tai tayi d'azu da Rana yasa ciwon kai ya saukar mata Mai zafi da k'yar dai ta samu ya sauka bayan tasha magani. wayar ta Dake gefen ta ce tai ringing alamar shigowar k'ira,jawo wayar tai tana duba Mai K'iran take ranta ya B'aci taja tsaki tana K'un K'uni, wannan Mai K'iran ba Aziz bane ba wannan Wanda ya ce d'in sun Had'u a park ne Ranar shine ya K'iratan.kallan Huda tai Ganin tana kallanta yasa ta kauda kanta kamar bazatai picking ba sai Kuma tai ta kai kunne tai shiru batai magana ba "Assalamualaikum warahmatullah. barka da dare ko harma kin fara bacci ne na tasheki?" shiru tai batai magana ba yasan dama bayin zatai ba ya ce tun ya Saba ya cigaba ya ce "wai har yau Baki shirya sanin waye ni da suna na ba?" Ya fad'a Yana sauraran Mai zata ce .nan ma dai Shur6un ne ya biyo Baya kamar bazatai magana sai Kuma can ta sauke numfashi ta ce cikin k'osawa "Dan Allah waye kai mai Kuma kake buk'ata daga gareni da kuka takura min?" Ta fad'a Tana Hararar wayar.murmushi yayi har tana Jin sautinsa daga can ya ce "sanin wane ne ni abun bamai Wahala bane sarauniya ta, sannan sanin Mai nake buk'ata daga wajenki Kuma ai na fad'a miki tun tuni sai dai ko kina so na K'ara Mai Mai ta Miki ne sai nayi" ya cigaba ya ce "suna Abdullah shattima nida iyayena muna Zaune a garin Abuja kuma Ina Son HUYAAM so Mai tsananin Gaske, Kuma idan har ta bani dama zan iya zuwa har Inda take na gabatar mata da kaina a gidansu sannan ki ganni Tunda Dama kince Baki sanni ba"ya fad'a cikin sassanyar muryarsa. Huyaam ta murgud'a Baki kamar Yana kallanta ta ce "bana buk'ata" yay Wani killer smile ya ce "Mai yasa"? Ta ce "saboda mu agida ba'a barinmu kula samari tunda bamu isa ba" ya ce "okay naji Amma zaki bani dama nazo na samu Abba zan jira har lokacin da zakin fara
Chapter 61 · 0% Book details