← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 85

Sashe 79

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta shak'o wuyan ta baya. Sha kundum ta rik'e hannun Anty Amina Dake wuyanta na ganin Anty Amina na k'ok'arin yage mata abinda ta rufe fuskarta dashi.nan dai suka fita daga d'akin Anty Amina na ihun a tai Maka musu, shakundum Kuma nata k'ok'arin k'wace kanta Dan kada Azo a kamata.Anty Amina kuwa tak'i sakinta saima Kara shak'eta da take tamau. nan Shakundum ta shiga kokawa da Anty Amina ita ko ta rik'eta gam tak'i sakinta tana cewa azo a taimaka mata ga Wani ya shigo musu d'aki .adai lokacin da Hajiya inna ta hauro stairs d'in tana tambayar meya faruwa cikin tashin hankali Jin hayaniyar tak'i k'arewa, kawai taga yadda mutum yay shigar b'adda kama baka gane shin macene ko namiji. ai shakundum ma ganin Hajiya inna ta zo ta kuma tasan tsaf zasu had'u su kamata have asirin ta ya tonu, tuni tai k'ok'arin d'aga hannunta ta bugawa Anty Amina guiwar hannun a gefen cikin ta Babu shiri Anty Amina ta saketa da sauri jin wata azaba ta saukar mata nan ta fad'i a k'asa.shakundum tai hanyar stairs d'in da gudu zata sauka Hajiya inna ta ruk'ota Aiko nan shakundum ta juyo ta hankad'a Hajiya inna nan itama ta fad'i ta baje a k'asa har tana buguwa da k'arfen stair d'in. ganin duk ta gama dasu Babu mai iya tashi ya biyota yasa ita Kuma ta fara saukowa stairs d'in cikin sauri, ganin guduwa fa zatai yasa Hajiya inna ta mik'e da k'yar tabi bayanta tana ihun a taimaka musu ga wani yashigo musu Wani yashigo musu b'angare a kama shi.mik'ewa Anty Amina ta Mik'e tabi bayan Hajiya inna suka sauko stairs d'in. Nan suka tadda har shakundum ta kusan fita daga falon gabad'aya. adai dai da Wani dogari ya farka agigice Jin ihun su Hajiya Inna nan shima ya yashigo falon sukai kicib'us da shakundum Dake k'ok'arin fita daga falon.Hajiya Inna ta ce cikin ihu "ka kama shi gashi nan zai fita" ganin wadda yaga Hajiya ita na nunawa tana ihun cewa ya kama shi yasa ya fisgota da k'arfi Hajiya inna ta ce "yauwa lurwanu Maza rik'e mana ta da k'arfi karta k'wace...... *End book one* K'arshen littafi na D'aya.bazance komai akan rayuwar gidajen sarautar nan guda biyu ba. Amma ke daga Jin tafiyar labarin Kin san yanzu aka fara ta. Amma bari na Dan Baku tsokaci kad'an daga ciki. *Tofa masu karatu Mai ke Shirin faruwa ne?shin wacece Huyaam acikin masarautar kano? shin da Gaske ne Huyaam ba 'yar gidan bace ma'ana ba Ammie da Mai martaba ne suka haifeta ba kamar yadda fulani Salamatu tazo tai baran bararma ta fad'a ko ya ya abun yake *Mai Cece makomarsm Huyaam a gida* HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ __* *__(MRS SARAKIES )__* *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 4 _____________ Tun bayan dasu HUYAAM suka kai Anty khadija airport suka dawo gida har yau kimanin sati d'aya kenan Afeef baiyiwa Huyaam maganar komai ba Daya dangin wai ya ganta da Aziz ko Kuma yay mata tambayar Mai yasa ya gansu tare shi.ko kad'an ko da wasa Bai mata Hakan ba, tun tana b'oyewa idan ta ganshi tana 'yar wasan b'uya dashi na karsu had'u har ta dawo da daina ta saki jikinta ta cigaba da sabgoginta ganin shi ko kallo ma Bata ishe shi ba, tun tana tunanin wata rana zai iya Mata maganar har ta dawo ta daina Damuwa da hakan ta cigaba da harkokin ta a gidan harma watarana su zauna tare dashi a main falon gidan ya gama zamansa ya tashi batareda da ya nuna mata alamar wai Yana rik'e da ita ba.Hakan yasa itama ta manta da zancen..A b'angarenta da Aziz chiroma kuwa tun tana basar dashi idan ya K'irata a waya har ta dawo tana picking call d'insa.yay ta janta da hira Wani lokacin ta tanka masa Wani lokacin kuwa tai Banza dashi ta k'yaleshi har ya gaji Dan kansa ya k'yaleta. daga baya Kuma abinda ta Gane idan tak'i tankasan Huda yake k'ira ya fadawa ya rok'e ta akan tazo ta rok'ar masa Huyaam ta dinga kula shi.to ita Kuma Huda idan taji haka saita ce masa karya Damu zata shawo masa kan Huyaam, haka zata to tai ta rok'ar Huyaam dayi mata rik'o da magiya da nasihu kala kala akan ta dinga kula Aziz ko yaya yane tana sakar masa fuska. tun Huyaam Bata sauran ta yau da gobe har ta dawo take sauraran Huda, ta yadda take D'an Kulashi sama sama harma ta dinga D'an bashi ansa a hirar da sukeyi. tun Huyaam Bata saki jikinta dashi ba harta dawo ta fara saki suke hira abinsu.to tun daga wannan Wani al'amari ya fara d'arsuwa azuciyar Huyaam game da AZIZ bawai taji tana sonshi bane sannan Kuma bawai Bata son shi ba, Haka dai take Jinsa a zuciyar ta a Wani sashe na Daban inda da Bata bashi wannan matsayin ba.ga wata iriyar shak'uwa da suka fara Yi ita dashi har mamakin kanta take Wani lokacin... tsakaninta da Abdallah shattima ma kuwa Shima dai kamar yadda take Jin Aziz haka Shima take Jinsa.sai dai har a zaciyarta bawai sonsu take ba kawai dai ta d'auke su ne matsayin masu Bata kuluwa da Kuma da d'ad'an maganganu da suke Yi a gareta.... Yanzu haka Zaune take a d'aki saman gadon ta wajen k'arfe 12 da Rabi ne na Rana. gama wayar su kenan da Aziz tana tunanin last words d'in daya fad'a mata tana murmushi.kamar wacce ta tonu da wani Abu Kuma sai tai saurin firgita ta sauko daga saman gadon da sauri tunawa da tai Ammie ta ce mata ta had'a kayanta a box Wanda zata buk'ata idan sunje Egypt Dan gobe ne idan Allah ya kaimu zasu tafi Egypt d'in,jirgin nasu na k'arfe biyu da Rabi ne na rana. da Huda ce ta ce ita zata had'a mata kayan tun d'azu data shigo d'akin ta fad'a mata,Amma gashi shine har yanzu bata zoba. Ganin time na tafiya har Yanzu wajen k'arfe shabiyu da Rabi Bata zoba yasa tai deciding gara Kawai tayi d'in kada Ammie ta K'ara zuwa tai mata magana akan had'a kayan.sauke numfashi tai nan ta K'arasa wajen box d'inta Dake a d'akin ta d'auko D'aya daga ciki ta k'arasa gaban press ta Bud'e ta fara fito da kayan da tasan zata buk'ata har suje su dawo.duk da Bata Son yaushe zasu dawo d'in ba Amma tasan baza su wuce 4 to 5 Days acan su dawo Nigeria ba.. tana cikin had'a kayan aka turo k'ofar d'akin, juyowa tai tana kallan k'ofar.Huda ce ta shigo nan ta d'auke kanta ta maida kan Abinda takeyi. Huda ta k'arasa shigowa cikin d'akin ta zauna nan Bakin gadon tana kallan yadda Huyaam ke had'a kayan nata ta ce "Mai yasa kike had'a kayan Bayan nace ni zan had'a miki?" Huyaam ta d'ago ta kalleta bayan tai zipping box d'in ta langwab'ar da kai ta ce "naga ne Baki zoba d'auka ta ma Ko kin Manta ne ni Kuma banaso Ammie ta k'ara zuwa tai min magana shiyasa kikaga nayi" Huda ta kalleta ta ce " shikenan kin kyauta ai" ta fad'a tana juyar da kanta gefe.HUYAAM tai murmushi ganin alamar Huda fushi tai ta k'araso kusa da ita ta rungumeta ta gefe ta ce "am sorry sis kiyi hak'uri kinji?" Huda ta fara tureta daga jikin ta ta ce "ni dai ki Rabu Dani" Huyaam ta ce "okay tunda Baki hak'ura ba bari naje na fito da duka kayan in yaso sai ki sake had'a min" ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa. Rik'o hannunta Huda tai da Sauri ta ce "karki fito dasu na hak'ura" komawa Huyaam tai ta Zauna ta ce "thank you so much sis Kinga fa tun daga Yanzu harna fara kewarki" ta fad'a tana Wani Marai raice fuska.Huda ta kalleta ta ce "same to you wallahi Amma ai naji Ammie ta ce baza ku Dad'e ba idan kuka je ko? Huyaam tai fari da ido ta ce "eh Bai fi 4 to 5 days kamar yadda muka Saba" Huda ta sauke numfashi ta ce "Allah ya Kaiku lafiya" Huyaam ta ansa mata da Ameen.bud'e k'ofar d'akin akayi gabad'ayansu suka juya suna kallan k'ofar ya Zarah ce ta lek'o ta tsaya daga nan Bakin k'ofar tana kallansu kafin ta ce "ku Kuma zaman daki Kuka koma Yi Yanzu kenan?" Tafad'a tana kallansu.murmushi Huyaam tai tana sosa Kai ta ce "laa! ya Zarah Mai kika gani? Ya Zarah ta hararesu ta ce "ai nagane kwanan bakwa zaman falo koda yaushe zaman d'aki,ke tunda kuka dawo daga Abuja na kula Kun daina zaman falo yanzu" Huda ta ce "a'a ya zahra ba Haka bane ba yanzun dai Huyaam nake Taya had'a kayanta" ya Zarah ta tab'e Baki ta ce "aishikenan intai tsami maji nidai yanzu ku taso nasa ka ku Wani aiki please" Huda ta ce "Wani aiki? Ya Zarah ta ce "Dan Allah kuje ku gyara min d'akina na samu emergency call ne daga school yanzu zan tafi Dan Allah kuyi Maza kuje kumin yanzu kafin na dawo" ansa mata sukai da Ladabi sukai mata fatan dawowa Lafiya. ansa musu tai itama sannan ta juya ta bar Bak'in k'ofar.Huyaam na kallan Huda bayan ya Zarah ta tafi ta dafe k'irji da tsoro a fuskarta ta ce cikin sanyin murya"na shiga uku Huda karfa ya Zarah ta Gane ana K'irana a waya fa?" ta fad'a tana zare ido.huda ta girgiza mata kai ta ce" bana tunanin ta Gane gaskiya Dan Kinsan ya Zarah Bata shiru indai daga Abu tofa sai tayi Magana" Huyaam ta sauke idonta k'asa ta ce "Anya kuwa Huda nifa wallahi har yanzu Ina tsoron ranar da yaya ko Kuma Ammei wani acikinsu ya sani wallahi kasheni za'ayi" Huda ta rik'o hannunta ta ce "Dan Allah kidaina zancen kisan nan Babu Dad'i bare ma Babu Wanda zai sani idan ma sun sanin Babu abinda zai faru in Sha Allah! tunda ai kowa Yasan Ya Aziz d'in" Huyaam tai shiru batai magana ba tana tunanin maganar huda. Huda ta Mik'e tsaye ta ce "Dan Allah ki taso muje muyi aikin kafin lokacin sallah yayi" numfashi Huyaam ta sauke ta d'auki wayarta suka fita daga d'akin gabad'aya jikinta Duk a Sanyaye..... Da yamma wajen k'arfe biyar da Rabi,Anty Amina ce tsaye a
Chapter 79 · 0% Book details