Sashe 55
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta ce "na k'oshi ne mummy" Anty khadija ta Kalli plate d'in gabanta sannan ta Kalli HUYAAM ta ce "D'an wannan Abincin da kika ci shine har kika k'oshi? Huyaam ta Sauke Idonta k'asa ta ce "Allah da Gaske nake mommy na k'oshi" Anty khadija ta Sauke numfashi ta ce "ai shikenan Kya K'ara anjima" ita dai HUYAAM murmushi tai ta bar dinning d'in ta koma falo ta zauna tana duba wayar ta .bayan kamar mintuna biyar suma duk suka baro dining d'in suka dawo nan falon suka zauna suna hira da Anty khadija Dake tambayarsu gida da Kuma school su kuma suna Bata ansa . D'aga kanta tai tana kallan time ganin k'arfe uku Saura na Rana yasa ta kalli siyama tace "lafiya kuwa yau har k'arfe uku saura su imaan Basu dawo ba? ko rufe Baki batai ba sai ga sallamar yaran sun shigo falon cikin nutsuwa su uku, Maza biyu sai mace D'aya macen ce ta taho da gudu direct Wajen mommyn nasu ta nufa sa'ar muneefa ce Amma kuma muneefa ta Bata watanni itace autar anty Khadija.Anty khadija ta d'ago imaan daga jikinta tana kallanta tace "Baki ga Bak'i bane zaki taho da gudu ki rumgume ni?" sai a sannan Imaan ta juya tana kallansun Huyaam Dan Sam shigowar ta Bata kula dasu ba hankalinta na kan mommynta.sakin Anty khadija tai ta nufi wajen su da Sauri tana cewa "Yaya HUYAAM da Yaya Huda Yaushe kuka zo? Ta fad'a tana murmushi.Huda tana D'an Murmushi ta ce "d'azu muka zo lokacin Kuna school" imaan ta ce "well come,amma kwana zakuyi ko?" Ta fad'a da sigar tambaya.Siyama ta ce "to uwar surutu kin dawo zaki fara ko? itadai Huyaam murmushi kawai takeyi tana kallan imaan kafin ta Mik'a mata hannu alamar tazo gareta.babu musu imaan ta k'arasa wajen Huyaam. 'yan biyun Anty khadija ne Hassan da Hussain Suka gaida su Huyaam cikin ladabi tareda Yi musu Sannu da zuwa cikin farin ciki.HUYAAM na murmushi ta ce "Hassan and Hussain" suka Kalli juna sannan sukai murmushi.. Ramma ce ta shigo falon tana kallan imaan ta ce "babyn mummy an dawo? Imaan ta gyad'a mata kai ta ce "anty Ramma zafi nakeji" Ramma na murmushi ta ce "Aishiyasa ma Ina Jin hayaniyarku na fito muje acire kayan" tana fad'ar haka ta k'araso ta kamo hannun imaan suka haura sama. Anty khadija na kallan su Huyaam ta ce "ya kamata Kuma kuje ku D'an kwanta ku huta ko zuwa anjima ne saiku fito kafin nan jikinku ya war ware ko ya ya ne" gyad'a mata kai sukayi suna ansa mata ta Kalli siyama ta ce "siyama kuje d'akinki ko Kuma Wanda aka gyara musun" Ansa mata Siya ma tai suka mik'e suka haura sama zuwa d'akin siyama...... Jirginsu su Afeef Bai tashi akan lokaci ba saida ya K'ara wajen 4O minutes sannan akai boarding classes gabad'aya. Yana zaune a VIP kamar yadda ya saba ya jingina da kansa Jikin kujerar jirgin.lamshe idonsa yayi slowly Yana Jin yadda jirgin ke tafiya a hankali har ya fara d'agawa sama cikin ikon Allah withing a minutes jirgin ya gama tashi a sararin samaniya zuwa k'asar ingiland a wannan lokacin Afeef bacci ne kawai ya daukeshi.... ___________ Da daddare su Huyaam suna kwance a d'akin siyama. Huyaam na saman gadon siyama ita kad'ai tana kwance sai Huda da siyama Dake kwance a D'aya gadon ko Wacce rik'e da wayarta suna latsawa gefe D'aya Kuma suna hira. HUYAAM na rik'e da wayarta tana sake dealing number Ammie bayan wayar da sukai tun bayan da suka iso suka Sanar mata Isowar su, to shine yanzun ma take K'ara dealing number nata.bugu biyu Ammie ta d'auka cikin shagwab'a Huyaam ta ce "good evening Ammie" daga can b'angaren Ammie tai murmushi ta ce "evening daughter ya Abuja" Huyaam ta gyara kwanciyar ta ta ce "lafiya lau Alhamdulillah Ammie Ina su muneefa da ya Zarah? Ammie Dake Zaune a d'akinta kan gado ta ce "duk lafiya lau suke Zarah tana d'akinta ni Kuma kin ganni na kawo muneefa da tai bacci d'aki" Huyaam ta ce "to Ammie ki gaida su"Ammie ta ce "zasuji in Sha Allah" Huyaam ta ce " Ammie Ina Ya haidar d'azu na k'irashi Bai picking ba?" Ammie ta ce "aikuwa d'azu ya dawo may be bai kula ba ko Kuma baya kusa da wayar ne" Huyaam ta ce "okay good night" Ammie na murmushi ta ce "good night and take care of yourself dear" Huyaam ta lumshe idonta ta Bud'e ta ce "in Sha Allah! daga haka sukai sallama" Bud'e k'ofar d'akin akayi Anty khadija ce ta lek'o tana kallan su ta ce "hope you are comfortable here daughters dan naga k'unk'i zaman d'akin da nasa aka gyara muku shiyasa nasa aka d'auko D'aya gadon aka kawo d'akin nan tunda naga duka ku ukun bakwa San rabuwa da juna" Huda Dake kwance a D'aya gadon ita da siyama ko Wacce tana latsa wayarta suka d'ago suna kallon Anty khadija sai Kuma sukai murmushi suka ce "eh mummy we are comfortable" Jin jina kai Anty khadija tai tana kallan su ta ce "babu abinda kuke buk'ata ne? Girgiza mata kai sukayi alamar babu komai ta ce "to ayi addu'a kafin akwanta Saida safe" ansa mata sukai daga haka ta juya ta rufo musu k'ofar gabad'aya.... Afeef ba su suka isa inglanda ba sai wajen k'arfe 11 na dare .agajiye ya K'arasa saukowa daga matattakalar jirgin ya fito daga area wurin gabad'aya bayan ya d'auko kayansa . John ne ya taho da sauri Yana welcoming ogan nasa cikin farin cikin dawowar sa ya karb'i kayan hannunsa,Afeef bai hanashi ba ya sakar masa Dan Allah ya Gani a gajiye yake sosai , bin bayan John kawai yake har suka k'araso wajen da yay parking yana kallan John Daya Bud'e masa back seat da sauri Yana K'ara welcoming d'insa,da ka kawai Afeef ya iya ansa Masa ya shige bayan Motar John ya rufe a hankali sannan ya Bud'e boot ya sa box d'in ya zaga driver seat ya shiga ta-da motar yayi suka fita daga cikin airport d'in gabad'aya.john ya d'ago ya Kalli Afeef bayan ya ajiye masa box d'in kayan nasa anan tsakiyar falon yay masa sallama sannan ya juya ya fita daga falon gabad'aya bayan ya kullo masa K'ofar .sauke numfashi kawai Afeef yayi Yana ya rik'e da k'ugunsa Yana k'arewa falon kallo ganin yadda yake agyare tsaf Kamar jiya jiya Yabar gidan alamar dai ana kula da komai na gidan yadda ya kamata ajiyar Zuciya ya sauke bayan ya d'au box d'in nasa ya nufi hanyar stairs Dan zuwa d'akin sa.wanka kawai Afeef ya iya yi bayan ya k'arasa d'akinsa ya haye saman gadon sa wanda shima an gyara shi tsaf Kamar yadda yake buk'atar ganin sa ya kwanta ko Ammie Bai samu ya K'ira ba ganin dare yayi yasa ya bari zuwa gobe da safe idan Allah ya kaimu ya K'iratan yadai turawa Mai martaba text message akan ya sauka daga haka ya ajiye wayar nan gefensa ya lumshe ido yana karanto addu'ar kwanciya bacci..... *2:30am* Agigice Hajiya inna ta fito daga cikin d'akinta cikin kid'imewa Jin ihun sultan Wanda shine ma ya Tasheta daga nan nauyan baccin da takeyi Dan yau ko sallan daren da take tashi tayi yau ta makara Bata tashi ba tana gyara zaman hijab d'in jikinta suka kusa cin karo da Anty Amina itama data sauko downstairs d'in agigice d'akin sultan kawai dukansu suka nufa saboda gigicewar da sukai sunma kasa tsayawa su kashe kunne Suji ta Ina ihun yake fitowa burinsu su gansu a d'akinsa,suna isa suka tsaya Turus ganin k'ofar falon a Bud'e basu tsaya nan ba suka k'arasa har cikin d'akin nan ma dai Turus d'in suka tsaya suna k'arewa d'akin kallo alamar dai baya ciki Hajiya inna na kallan anty Amina cikin d'imuwa arikece ta ce "Amina Ina sultan d'in yake Kinga fa baya cikin d'akin mun Shiga uku ni Abuwa" ta fad'a tana rarraba ido.anty Amina ta ce "Nima banganshiba hajiya muje ta k'ofar falon naga kamar ta nan nake Jiyo ihun ai tun kafin ta rufe Bakinta Hajiya inna ta bar d'akin ta fito gabad'aya tai Hanyar k'ofar babban falon rikice a nan k'ofar falon daga waje taga yadda fadawa K'arti har su Hud'u suna kowawa da sultan sun rik'e shi suna son dawo dashi ciki Amma yak'i fir ya tirje ihu kawai yake Yana fusge fusge sai kace Wani mahaukaci ga wasu daga cikin fadawan gidan da ma wasu daga cikin mazan palace d'in suma sun fito sun taru kamar Wani Taron biki suna kallo Amma Kuma sun kasa taimaka musu su rik'e shi kowa Yaja gefe ya tsaya yana kallon sultan .Anty Amina da inna suka k'araso wajen a firgice adai dai lokacin da Mai martaba ma ya iso Wajen daga shi sai jallabiya da Hirami Daya yafa anan saman kansa saboda K'iran waya Daya samu daga da Wani acikin mazan palace d'in ya fad'a masa.kallan Hajiya inna yayi data had'e Rai tana taiwa mazan palace da sauran fadawan da su suka fara silalewa D'aya Bayan D'aya suna barin wajen ganin Hajiya inna da Mai martaba sun iso Hajiya inna ta nuna su da yatsa cikin b'acin Rai ta ce "muna fukai kun tsaya kuna kallo Amma kaf cikin ku Babu Wanda yayi k'ok'arin yaga ya rik'e sultan kun kaishi ciki Saidai kuja ku tsaya kun Kasa tab'uka komai kun tsaya kuna kallo" sunkuyar da kai k'asa sukai suna Mai Jin kunya.a tsawa ce tace su wuce su Basu wuri muna fukan banza muna fukan wofi" haka tai ta fad'a .sum sum kuwa suka fara farin wajen D'aya bayan D'aya sarki ya bisu da kallo ganin harda waziri Ashe a wurin girgiza kai yayi Yana Mai Jin Wani Irin d'aci a ransa .tsaki inna ta jaa da k'arfin Gaske bayan itama taga wazirin tace da k'arfi "muna fukan banza muna fukan wofi ahaka zaku k'are in Sha Allah Kuma da iKon Allah sai jikana ya samu lafiya Idan Wani ne ma yay Masa wannan aikin sai dai ya koma kan nasa 'ya'yan" Anty Amina ta shiga bawa inna hak'uri ganin tana Neman sub'utar Baki a gaban bayin gidan.hajiya Inna ta ce a gusay "K'yaleni Amina kina ganin Ashe suna wajen Amma kaf cikin