← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 85

Sashe 18

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fad'a muryar ta na rawa. Afeef yaji gabansa ya Wani K'ara fad'uwa Jin wai Ammie na asibiti to waye babu lafiya ko itace,Sai kuma yace . "Asibiti kuma? Meya faru?..." Cikin rawar murya Huda tace. "Huyaam ce Bata lafiya".gabansa yay dumm kad'an kaddai ace ko ciwon nata ne ya tashi, afili Kuma yace . "Mai yasa mete?..." Huda tace. "Aziza ce ta take mata k'afa da takalminta shine k'afar ta fashe take zubar da jini shine aka tafi kaita asibiti". Huda ta fad'a tana sheshshek'ar kuka..shiru Afeef yayi kamar Wani Mai tunani har na tsawan 30 seconds har huda tayi tunanin koya Kashe wayarne ta duba sai taga Kuma Yana reading Bai kashe ba Hakan yasa tai shiru itama tana sauransa Saida ya maula Dan kansa sannan yace. "How". nan Huda ta kwashe komai ta fad'a masa". Afeef yay shiru kamar bazai ce komai ba sai Kuma yace. "It's okay,idan Ammie sun dawo let me know". Huda tace. "to in Sha Allah".Daga haka ya kashe wayar huda tabi wayar da kallo wasu sabbin hawaye na zubo mata ,baba magajiya ta Kalleta tace cikin sanyin jikin daya shigeta itama tunda aka fita da Huyaam daga gidan. "kiyi hak'uri Huda in Sha Allah zata samu lafiya Kinji ?...."Huda Bata ce komai ba tana rik'e da wayar a hannunta tana kuma goge hawayen fuskarta. Afeef Yana sauke wayar ya kusan 4 minutes Bai iya tashi daga inda yake Zaune ba yana Mamakin Hali irin na Aziza kafin ya furzar da huci Mai zafi ya mik'e ya shiga toilet d'in Dan yin Wankan da zaiyi..... *Hospital* Ya haidar Yana yin parking a gaban A&E na hospital d'in direct ciki aka shiga da HUYAAM Saboda bleeding d'in da k'afarta keyi har lokacin.Ammie dai tana tsaye jikin motar bayan an shigar da Huyaam tana kallon bakin A& E d'in, dap d'in asibitin ne ya k'araso har wajen motar Yana kallan Ammie ya gaidata cikin girmamawa.Ammie ta ansa masa jikinta a Sanyaye .ya risinar da kansa k'asa yace . "Am ranki Dad'e Mai zai Hana ku shiga office d'ina ku zauna kafin a fito da ita".ya fad'a Yana kallan Ammie. Ammie ta kalleshi tace. "Nan ma yayi doc zamu jira har ku gama aikinku sai mu tafi".doc ishaq yace cikin girmamawa. "Ranki Dad'e ba musu nake Dake ba Amma ai ba girmanku bane tsayuwa anan Nima bazan so haka ba,gimbiya Kuma tana lafiya Ba Wani babban issue bane kawai wanke wurin zamuyi muyi dressing d'in wajen shikenan".ya fad'a da Ladabi.Ammie tai shiru batai magana ba ya haidar ya kalleta yay k'asa da murya yace. "Kiyi hak'uri Ammie muje ciki Babu komai in Sha Allah". Ammie ta sauke ajiyar zuciya tace . "Shikenan muje"doc yay gaba Dan Yi musu jagora ya haidar da Ammie suka bi bayansa. Wajen 0ne hour Ammie na zaune kan sofan Dake k'aton parlon office d'in doc ishaq tai tagumi gabad'aya hankalinta baya tare da ita Yana can wajen HUYAAM tana tunanin halin da take ciki Gani take kamar komai ma zai iya faruwa da ita Dan tun d'azu da doc ishaq ya kawosu office d'in ya koma emergencyn Bai dawo ba har yanzu daga ita sai ya haidar Dake tsaye Bak'in k'ofar falon office d'in Yana tsaye shima gabad'aya ransa Babu Dad'i. Doc ishaq ne ya shigo cikin office d'in bakinsa d'auke da sallama.. Ammie da ya haidar suka ansa masa suka bishi da kallo har ya k'araso gaban table d'insa ya zauna kan kujerar Yana zare hand gloves d'in hannunsa. Ammie tace. "Doc Ina take".ta fad'a cikin damuwa. Doc ishaq yay murmushi ya risinar da kansa alamar girmamawa yace. "Lafiyanta lau ranki Dad'e na barta ne ana k'arasa mata dressing d'in but yanzu za'a shigo da ita in Sha Allah.ko rufe Baki doc ishaq baiyi ba aka turo k'ofar falon office d'in wata nurse ce ta shigo tana rik'e da wouldchair Wanda ake D'ora marasa lafiya akai wanda HUYAAM ke zaune aciki idonta sun kumbura sunyi suntum saboda Kukan da Tasha Dan alokacin da ake wanke mata ciwon bakiga Irin kukan da Tasha ba kamar Wanda ake k'ok'arin rabata da ranta.da sauri Ammie ta juya tana kallon Huyaam, idonta ya sauka akan k'afar Huyaam Dake nan nad'e da bandage gabad'aya an rufe k'afar da bandage d'in cikin damuwa Ammie ta taso Babu shiri ta k'araso wajen da HUYAAM take ganin haka yasa nurse d'in ta tsaya daga tura HUYAAM da take ta koma gefe.Ammie tasa hannu ta d'ago da fuskar HUYAAM tana kallanta tace cikin tausayawa. "Sannu daughter".Huyaam ta kalleta da kumburun idanuwanta kafin ta gyad'a mata kai .ya haidar ya k'araso Yana kallon k'afar shima sai kuma ya kalli HUYAAM yace. "Sannu HUYAAM". Batare da ta kalleshi ba ta gyad'a masa kai Ammie ta juya tana kallon doc tace. "Shikenan ko doc zamu iya tafiya?..." Doc ishaq yace. "Eh ranki Dad'e angama komai yanzu sai magun gunan da nai mata prescription suma gasu an had'o su,indai tana Shan magun gunan in Sha Allah nan da 3 to 5 days ciwon zai warke bandage d'in zai bushe ya d'aye da kansa gabad'aya bama sai an sake wankewa ba in Sha Allah". Ammie ta sauke numfashi tace. "Allah yasa".ya Haidar ya k'arasa ya karbi ledar magun gunan sannan ya k'araso wajen su HUYAAM doc ya taso shima Yana kallan nurse d'in yace. "Sister ki turata kuje har wajen motar su ki shigar ta ciki". nurse d'in ta risinar da kai ta ansa masa cikin girmamawa.sannan ta kama hannun wouldchair d'in ta juya suka fita daga office d'in doc ya kalli Ammie yace. "Allah ya K'ara lafiya ranki Dad'e". Ammie ta ansa da Ameen. ya Haidar ya Mik'a masa hannu sukai musabaha sannan yabi bayansu Ammie yana ansawa doc ishaq da Allah ya kiyaye d'in da yake musu. _____________ K'arfe 9 da Rabi dai dai na daren ya haidar yay parking a gaban b'angaren su Dan har gaban part d'insu ya kawo mator Yay parking a kofar dama already ya k'ira ya Zarah akan tazo su shigar da Huyaam ciki..horn ya Haidar yay Babu dad'ewa ya Zarah ta fito ita da baba magiya harma dasu Huda.ya haidar ya fito ya zaga ya Bud'e wa Ammie back seat Ammie ta fito tana kallon ya Zarah bayan k'araso gunsu tace. "Zarah zo tanan ki goyata".baba magajiya tai Saurin cewa. "A'a ranki Dad'e ki bari na goyata meye anfanina".ta fad'a tana K'arasowa wurin. Ammie tace . "A'a magajiya barshi kawai Zarah ma zata iya". Baba magajiya tai murmushi tace. "Ranki Dad'e Dan dai karkice ina musu dake Amma da kin barni na goyotan ai zan iya ita da ba nauyi ne da ita ba".. ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa. Ammie ta sauke numfashi tace. "Shikenan Zarah Tayata sai ta goyatan".Babu musu ya zarah ta ansa mata baba magajiya ta k'araso side d'in da HUYAAM take ta tsugunna ya Zarah ta taimakawa HUYAAM ta hau bayan baba magajiya Dan bazata iya taka k'afar ba..A haka Baba magajiya ta shiga da HUYAAM har cikin falon, Ammie na biye dasu ita dasu Huda bayan sun shiga falon Ammie ta Kalli baba magajiya tace. "magajiya ki kaita d'akina".Babu musu baba magajiya ta ansawa Ammie cikin girmamawa ta kai Huyaam har d'akin Ammie ta ajiye ta saman gadon baba magiya ta fita bayan ta k'ara yiwa HUYAAM ya jiki... gabad'aya su ya Zarah sun shigo d'akin idonsu gabad'aya Yana kan k'afar Huyaam Dake nannad'e da bandage. Huda ta kalleta tace . "Sannu HUYAAM".ta fad'a jikinta a Sanyaye.HUYAAM ta gyad'a mata kai Amma batai magana ba Dan ita tasan rad'ad'in da take ji. ya Zarah tai mata ya Jiki itama ,nan ma da ka ta ansa musu gabad'aya Saida kowa yaywa HUYAAM ya jiki harsu muneefa.... Ammie ta zauna bakin gadon tana kallan Huyaam data kwanta ta rufe Idonta hawaye na zubo mata . Ammie ta jawota zuwa jikinta tace .. "Sannu HUYAAM zafi yake Miki ne?..."HUYAAM ta rufe fuskarta a k'irjin Ammei ta fashe da Kuka tace. "zafi take mun Ammie".ta fad'a tana kan k'ame Ammie... Ammie tai rapping hannunta a bayan Huyaam tana lallashinta tace. "Zai daina In Sha Allah da kinsha magani ne shikenan zai daina zaki samu sauk'i in Sha Allah.yanzu ki fara cin abincin tukunna sai Kisha maganin". Ammie ta fad'a cikin lallashi. HUYAAM ta girgiza mata kai tace cikin dashashshiyar Muryar Wacce kuka ya gama cinyeta. "Na k'oshi Ammie". Ammie ta girgiza kai tace. "A'a HUYAAM rabonki da abinci fa tun d'azu da Rana Shima bana kirki kika cigaba saboda haka baza ki zauna ki kwana da yunwa ba". HUYAAM ta girgiza kai tana cewa ita ta k'oshi Ammie Bata saurareta ba ta kalli Huda tace. "Huda jike kitchen ki Had'o mata tea da abinci". babu musu Huda ta ansa mata ta fita daga d'akin.babu dad'ewa Huda ta dawo d'akin rik'e da mug na tea sai turiri yake Yi ta Mik'awa Ammie kafin ta koma da d'auko plate d'in data zubawa HUYAAM Abincin ta ajiye nan kan table d'in Dake d'akin. Ammie ta Kalli HUYAAM tace . "tashi Kisha tea d'in saiki ci abincin". HUYAAM ta marai raice tace. "Nidai Ammie iya tea d'in kawai zansha na k'oshi da abincin".ta fad'a kamar zatai kuka .Ammie tace. "Naji to tashi Kisha".da k'yar ta mik'e Ammie ta shiga Bata a baki baifi kurb'a hudu tai ba tace ta k'oshi.ya haidar ne ya shigo d'akin rik'e da ledar maganin Yana kallan Ammie yace. "Ammie gashi"ya fad'a yana Mik'a mata ledar maganin.. Ammie ta karb'a ta Bud'e bayan duba yadda HUYAAM d'in zata Sha .ya haidar kalli HUYAAM yace. "Allah ya sawak'e Ammie saida safe". Ammie tace . "Sannu da k'ok'ari Allah ya tashe mu lafiya".ya ansa da ameen Yana fita daga d'akin gabad'aya.. Ammie ta b'alli maganin ta d'auki gorar ruwa ta Mik'awa HUYAAM..nan HUYAAM ta d'auke kanta tace. "Ammie banaso bazan shafa". Dan Huyaam Bata San magani ko kad'an saidai idan Ba'a cikin hayyacinta bane zata Sha . Ammie tace cikin lallashi. "Ki daure Kisha kinje HUYAAM D'ina".da k'yar Huyaam ta yadda ta karb'i maganin nan Tasha...bayan Tasha Ammie ta taimaka mata ta kwanta ya Zarah ta sauke numfashi tace. "Allah ya sawak'e HUYAAM".Bata jira cewar taba ta Kalli Ammie tace. "Ammie saida safe Allah ya K'ara lafiya..ta fad'a tana k'ok'arin juyawa zata fita daga d'akin.Ammie ta
Chapter 18 · 0% Book details