← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 85

Sashe 27

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dawo".ta fad'a tana murmushi. Ammie ta rik'e ta tace. "Sannunku da zuwa".dukkansu suka had'a Baki wajen gaida Ammie.nan ma Ammie ansa musu tai tana murmushi . Huyaam na cire hijab d'in jikinta anan falon tace . "Ammie yayan ya dawo ne?.ta fad'a tana kallan Ammie..Ammie ta girgiza kai tana kallonta tace. "D'azu aka tafi d'auko shi,Amma nasan yanzu haka ma suna hanyar dawowa in Sha Allah".Huyaam ta sauke numfashi . muneefa tana kallan Huda tace. "Ya Huda addu'a ta ta karb'u Yaya Bai rigamu dawowa ba".ta fad'a tana murmushi.huda ta gyad'a mata tace. "Eh fa. tom Allah ya kawo su lafiya". Ammie da Huyaam suka ansa da Ameen. Ammie na kallansu tace. "to Maza kuje ku shirya kafin su iso". Huyaam da Huda suka ansawa Ammie kowa ya shige d'akinsa ita dama ya Zarah tun tuni ta bar wajen tun bayan data gaida Ammie..Ammie Kuma ta kama hannun muneefa suka shige d'akinta Dan ta shirya ta itama ...... Horn d'in motar farko ce datai a bakin gate d'in yasa D'aya daga cikin fadawan Dake zaune a bakin gate d'in yay saurin mik'ewa Daga inda suke zaune,ya taso da sauri ya k'arasa har gaban gate d'in ya danna Wani D'an Abu take Gate d'in ya Wangale motocin suka fara danno kai cikin gidan D'aya bayan D'aya.gabad'aya dogarayen Dake Bakin gate d'in saida suka mik'e ganin shigowar yarima Afeef cikin masarautar. motacin na k'arasowa dai dai inda suke tsaye take suka zube a k'asa kawunansu na kasa da babbar murya suka Shiga jero masa Barka da zuwa had'i da kirari. bayan motocin sun gama wucewa Kuma suka mik'e gabad'aya wasu sukabi bayan motocin da sauri kowa Yana k'ok'arin yaga shiya Bud'ewa yarima Afeef motar da yake ciki duk da Basu San a wacce yake ciki ba Sauran kuma suka tsaya suna Tsaron gate d'in.gabad'aya suka zube a k'asa bayan sun k'arasa inda motocin sukai parking suka jeru gaban motar kaf ma'aikatan gidan sarki saida suka fito dan yiwa yarima Afeef barka da zuwa.motar Dake tsakiyar duka motoci hud'un na hango Wani dogari wanda dashi akaje d'auko Afeef a air port ya fito da Sauri Yana gyara zaman babbar rigar jikinsa Irin ta dogarai yasa hannu ya bud'ewa Afeef bayan motar da yake ciki ya ja baya da Sauri Yana kirari da cewa. "Eh!! fitowarka Lafiya takawarka yariman kano magaji magajin masarautar kano idan Allah yaso ya yarda. gaisheka saraki madara Mai kama da nono d'a Mai kamar uba.ire Iren wannan kirarin suka dinga jero masa.yana jinsu Bai iya yace musu komai ba.illa K'afarsa D'aya daya fara zirowa sannan ya ziro da d'ayar ma kafin ya gama saukowa daga cikin motar gabad'aya .kamar had'in Baki haka dogarayen nan da suka zube tun k'arasorsu wajen suka shiga yiwa Afeef barka da zuwa kansu a k'asa Cikin girmamawa.matsawa daga jikin motar Afeef yay yana ansa musu lokaci D'aya Yana k'arewa gidan nasu kallo kamar Wanda ya sauya masa .ya haidar ne ya yazo wajen fuskarsa da murmushi Shima dawowar sa gidan kenan ya k'arasa har wajen yayan nasa ya bashi hannu tareda Yi masa side huge Afeef ya sake shi Yana ansa masa sannu da zuwan da yake masa kafin ya bar wajen ya haidar ya bishi suka jera zuwa b'angaren Ammie gabad'aya. tuni dogarayen suka Bud'e boots d'in suka kai kayan nasa bangaren Ammie. Tun shigowar motacin da muryoyin fadawa da suke ta jerowa Afeef kirari Had'i da barka da zuwa su Huyaam suka San yayan nasu ne ya iso,ko Wacce tayi wanka ta shirya cikin shiga Mai kyau Huyaam da Huda kaya iri D'aya suka sa, doguwar rigar atamfa ce D'inkin beat work Mai bala'in kyau ga stone sai Wani walwali sukeyi.Huda ce ta shigo d'akin HUYAAM tana kallanta tace cikin farin ciki. "Yanzu yaya suka iso ki taso muje falon k'asa muga shigowarsa".ta fad'a tana kallan Huyaam..Huyaam Dake gaban mirror tana kokarin Parking gabanta da ribbons tace ."jeki Gani nan Dan sai nayi sallah ma zanzo lokacin ya huta Dan yafi ganina da kyau".ta fad'a tana kallan Huda ta cikin mirror d'in . Huda ta tab'e Baki tace. "To saikin fito bari nidai naje Dan naji kamar muryarsu ya Zarah ma a falon k'asa". Tana fad'ar haka juya tabar d'akin.huyaam ta juya ta k'arasa parking gashin. A falon k'asa kuwa gabad'aya su Ammie da ya Zarah suna tsaye suna zaman jiran shigowar Afeef Huyaam ce kawai Bata nan.ya haidar ne ya fara shigowa falon sai Afeef Dake biye dashi a Baya Hannunsa cikin na muneeb suka shigo bakinsu d'auke da sallama.har suka k'arasa shigowa falon. da gudu muneefa taje ta rumgume shi tana murmushi cikin murna tace . "Well come back Yaya".ta fad'a tana k'ank'ame shi .hannu yasa ya d'agota yana sakin fuskarsa yace. "Thank you so much muneefa" gabad'ayansu suna tsaye suna kallansa fuskarsu da murmushi kafin kowa ya shiga yi masa Barka da zuwa kallansu yayi D'aya bayan D'aya Yana ansa musu.Ammie na murmushi tace. "Sannu da zuwa Afeef".ya k'arasa gaban Ammie da murmushi a fuskarsa ya cire face mask d'in fuskarsa ya zare hular kansa sannan ya D'an duk'ar da kansa kad'an agaban Ammie.hakan da yay Ammie ta Gane Mai yake nufi,Ta K'ara fad'ad'a murmushinta . kafin ya furta . "Lafiya lau Alhamdulillah Ammie nasameku lafiya". Ammie na murmushi tana kai hannunta ta shafa kansa tace. "lafiya lau Alhamdulillah! sannu da zuwa ka k'arasa ciki ka huta". ya dago da kansa yana kallanta yace cikin deep voice d'insa. "Alwala Zanyi naji ana K'iran sallahn magrib ne". Ammie ta Jin jina kai tace. "Eh hakane ka k'arasa cikin to saika fito". ya Jin jina mata kai Daga haka Afeef ya haura sama zuwa b'angarensa . Bayan tafiyarsa Ammie ta sauke numfashi tana kallansu Huda tace. "A'a! ina huyaam ya bangan taba?..." Ta fad'a tana waige waige a falon ko zata ga inda ta mak'ale.Huda tace. "tana d'aki Bata gama bane". Ammie tace. "Ok shikenan to ku wuce kuma kuje kuyi alwalan sai kuyi sallahn".Babu musu duk suka juya suka haura sama Dan zuwa suyi sallahn ya haidar kuma da muneeb suka fita daga falon suka tafi masallacin palace d'in..... ____________ Tunda Afeef ya Fita sallahn magrib Bai dawo ba Har Sai da akai har sai da akai sallahn isha'i sannan suka dawo b'angaren nasu shida ya haidar sai muneeb .da sallama suka shigo babu kowa a falon sai k'arar AC data fan da suke tashi.bayan sun k'arasa shigowa falon ganin Babu kowa suma su Ammien Basu Sau ko ba yasa ya Afeef ya Haura sama zuwa d'akinsa Dan ya watsa ruwa,shi Kuma ya haidar ya samu waje anan falon ya zauna kan D'aya daga cikin kujerun falon. muneeb kuma ya wuce ya haura sama zuwa d'akin Ammie...Da shigar Afeef falonsa Wani daddad'an k'amshi ne ya Doki hancinsa ya lumshe ido at the same time Yana bud'ewa Dan d'azu Daya shigo da yake ko zama Bai yiba yasa Bai k'arewa falon d'akin kallo ba.karasawa k'ofar bedroom d'insa yayi ya Murd'a k'ofar a Hankali ya tura ya shiga ciki .nan ma Wani daddad'an k'amshin ne ya sake ziyartar hancinsa tsayawa yayi ya Shiga k'arewa d'akin kallo yayi neat kamar Wanda ba tafiya yay ya Barshi a haka ba, sai dai wannan an gyara shi an can za zanin gadon da kayan Dake kan mirror Wanda duk yawancinsu ma kayan shafa shafa ne kamar su lotion sai turaruka na maza kala kala d'akin dai yayi masa sosai yadda yake buk'atar ganin sa Dan sai kace dakin wata amarya yasan Kuma wannan ba aikin kowa bane saina Ammie.sauke numfashi yayi ya k'arasawa gaban makekem gadonsa ya fara rage kayan jikinsa Yana gamawa ya shige toilet d'in nanma dai Wani k'amshin ya tadda a toilet d'in, shima kansa banda k'amshi Babu abinda ke tashi acikinsa babu Bat'a lokaci ya cire towel d'in jikinsa sannan ya had'a ruwan wanka ya shiga bath tube d'in.... A falo kuwa su Huyaam suna yin sallahn isha'i kowa ya fito Suka zazzau na a nan falon saman kujeru ,Huyaam da Huda na zaune waje D'aya suna hira k'asa k'asa ya Zarah kuwa wayarta ta d'auka ta kunna data,Ammie ce k'arshen fitowa bayan ta zauna kan kujera tana kallan ya haidar tace . "Ina Afeef d'in yake?.." ya haidar ya d'ago da kansa daga kan wayar sa Yana kallan Ammie yace. "Bai fitoba Yana d'akinsa".Ammie ta Jin jina kai tana kallansu Huyaam tace. "Ku taso ayi dinner kafin ya fito ko?..Babu musu suka mik'e suka k'arasa dining d'in....fitowarsa daga wanka kenan duk jikinsa Yana d'igar ruwa ya k'arasa tsakiyar d'akin ya yatsa hannunsa rik'e da k'aramin towel ya fara goge ruwan jikinsa dashi tun daga kansa har gadon Bayansa bayan ya gama ya k'arasa gaban mirror ya fara shafa lotion d'insa bayan ya gama ya K'arasa wardrobe ya d'auki k'ana nun kaya zai sa yasa ya ya d'au tarare ya feshe duka jikinsa dasu sannan yasa hannunsa ya d'auki comp ya fara gyara gashin kansa bayan ya gama ya k'arasa kan gadon ya d'auki wayoyinsa sannan ya fito daga d'akin bayan ya kullo k'ofar.tun kafin ya gama saukowa downstairs k'amshin turaransa ya fara isar musu da zuwansa,take duk suka zubawa stairs d'in ido har ya k'arasa sauko gabad'aya Yana rik'e da wayoyinsa ahannunsa.yana d'ago da kansa idanuwansa akan Huyaam suka fara sauka wacce itama ta zuba masa nata Idon tana kallansa,kafin ta D'an Bud'e ido kad'an alamar Mamakin ganinsa da tai tana kallansa tare D'an murmushi sai Kuma ta rufe Bakinta har lokacin murmushi take Wanda ya kasance na murnar one and only yayan nasu tasowa tai daga dining d'in ta k'araso cikin falon har inda taga yaja ya tsaya ya rungume hannunsa Yana kallanta ganin ta nufoshi d'aukar sa yanzun ma rungume shi zatai ya hanata. Aikuwa dai sai yaga rungume shin zatai take yay mata Wani kallo jiki a Sanyaye Huyaam taja ta Tsaya a inda take ganin Irin kallon da yake Mata ta sunkuyar da kanta k'asa kafin ta d'ago tai masa murmushi kan kyakkyawar fuskarta da k'yar ta iya cewa. "Well come back Yaya".ta fad'a tana langwab'ar da kanta tana kallonsa. janye idonsa yayi Daga nata Yana wuceta yace. "Thank you". HUYAAM ta juya tana kallonsa ganin yadda ya ansa mata ta sai Kuma tura Baki gaba tana k'unk'uni tabi bayan sa sudai su Huda kallansu kawai
Chapter 27 · 0% Book details