Sashe 6
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ki Bud'e drower ki d'auko min maganinta yanzu sannan ki taho min da wayata akan mirror".ta fad'a tana tana rik'o HUYAAM.babu Bat'a lokaci Huda ta fita daga d'akin cikin sauri tai d'akin Ammie. babu dad'ewa ta dawo Hannunta rik'e da wata gora wacce ke d'auke da Wani magani aciki.ta Mik'awa Ammie gorar maganin da wayar. Ammie ta karb'a ta ajiye wayar nan gefenta ta Bud'e gorar ta tsiyaya a hannunta sannan ta shafa a fuskar HUYAAM wacce ta jik'e da gumi,ta K'ara d'iban Wani ta shafa mata a fuskarta .take HUYAAM taja wani dogon numfashi tana sakin jikinta a jikin Ammie.ganin haka yasa Ammie ta sauke ajiyar zuciya tana kallan Huyaam. ta juya bayanta Jin sautin Kukan muneefa ta kalli haidar tace. "Wayece ku shigo da ita?maza kamata ku fita da ita"Babu musu haidar ya kama hannun muneefa yana kallan Huyaam yace . "Allah ya K'ara lafiya".ya Zarah ta ansa da Ameen. daga haka ya fita daga d'akin rik'e da muneefa muneeb ma yabi bayansu.bayan Wani lokaci HUYAAM ta fara Bud'e idanuwanta ahankali a hankali ahaka har ta gama Bud'esu gabad'aya.ta tsaida su akan Ammie kafin ta juya Tana kallan sauran saikuma ta fara k'ok'arin mik'ewa zaune Ammie ta rik'eta tana cewa. "Me zakiyi haka ?.. HUYAAM tana yamutsa fuska tace. "Ammie meya faru?.."Ammie tai mata murmushi tace. "Kankine ke ciwo shine na Baki magani"ta fad'a tana kallan yadda HUYAAM take rarraba ido. Sai Kuma tace. "Kan ya daina ciwon yanzu ?..."ta fad'a tana k'ok'arin parking gashin HUYAAM. HUYAAM ta gyad'a mata kai sai kuma tace "Ammie Ina Abba?..."Ammie tace . "Yana masallaci Bai shigo ba "Huda ta kalli HUYAAM tace. "Sannu HUYAAM". HUYAAM ta gyad'a mata kai ya Zarah ma tai mata sannu ta ansa mata sai Kuma ta fara zame jikinta Daga na Ammie tace . "bacci nakeji". Ta fad'a tana juya bayanta.Ammie tace . "A'a tashi Muje kici Abinci". Huyaam tace Batare da ta juyo ba. "A'a sai anjima".daga haka ta K'ara gyara kwanciyar ta. Ammie batace komai ba ta d'auki wayarta ta kunna Karatun Al'qur'ani ta mik'e ta ajiye nan saman mirror Dake d'akin ta barwa Huyaam tana kallan su ya Zarah tace . "To muje mu barta ta huta anjima Huda sauki had'o mata abinci Dan kada ta kwana da yunwa"Huda tace. "To Ammie".daga haka suka fita daga d'akin Ammie ta jawo k'ofar ta rufe. Wajen k'arfe 9 na dare Mai martaba ya shigo part d'in Ammie Yana zaune a falonsa Dake nan part d'in bayan duk yaran sunzo sun gaida shi sannan suka fito daga falon. Muneefa tana mak'ale da mai marataba Da take bashi labarin HUYAAM Babu lafiya.Ammie ce ta shigo falon bakinta d'auke da sallama Hannunta rik'e da D'an k'aramin plate Wanda ta d'orowa Mai martaba black tea akai ta k'araso har falon cikin ta risina ta ajiye nan gaban Mai martaba.tana kallan muneefa tace. "Wato Baki tafi kin kwanta ba ko?..."Mai martaba yace cikin nutsuwarsa. "Fulani! wai jikin Huyaam ne ya K'ara tashi?..."ya fad'a Yana kallan Ammie. Ammie ta d'ago ta kalleshi sai Kuma ta Kalli muneefa wacce ke k'ifta ido tace. "Wato ke uwar surutu kece kika fad'a masa koh?..."muneefa ta sunkuyar da kanta k'asa. Ammie ta sauke numfashi tana Maida dubanta kan Mai martaba tace cikin Damuwa. "Shine rankai Dad'e Amma na Bata sauran maganin Daya rage Wanda da muka kaita Egypt muka karb'o Ina shafa mata nan da nan ta dawo hayyacinta". Tunda ta fara magana Mai martaba yake kallanta yay Jimm alamar tunani kafin ya sauke numfashi yace. "Allah ya Bata lafiya"Ammie tace . "Ameen ya Rabbi". Mai martaba yace . "Yaushe ne zaku koma?..." Ammie tace." nan da wata uku ne in Sha Allah. Mai martaba ya Jin Jina kai . Amma baice komai ba.Ammie ta kalli muneefa wacce ta fara gyangyad'i ta d'auke ta ta fita da ita daga d'akin Dan zuwa ta kwantar da ita .tana kwantar da ita ta shiga wanka ta fito ta kimtsa cikin kayan bacci bayan ta gama ta feshe jikinta da turaruka masu bala'in kamshi da tsada ta d'auki dogon hijab d'inta tabi tanan corridor Dake gefen d'akinta tai part d'in Mai martaba Dan yau kwanan tane. 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM (The love story) *Paid book *Free pages* *NA* *___NAJA'ATU UMAR FAROOQ ___* *___(MRS SARAKIES ___* *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 5 __________ Washe gari haka HUYAAM ta tashi kamar Bata tab'a wata jinya ba.baccin tama tasha babu Wanda ya tasheta sun bari ne ta tashi da kanta .Sai wajen k'arfe 11:30am ta tashi ,sannu a hankali ta sauko daga saman gadon daga ita sai rigar bacci ajikinta ta mik'e tsaya tana Mik'a kafin ta tafi ta d'auko towel ta d'aura ajikinta bayan ta cire rigar baccin tai hanyar toilet Dan yin Wanka . Babu dad'ewa ta fito d'aure da towel ajikinta kanta sai d'igar ruwa yake ta k'arasa wajen hanga Dake d'akin ta d'auko Wani k'aramin towel ta fara tsane gashinta kanta dashi, bayan ta gama ta d'auki hand dryer ta busar da gashinta bayan ta gama ta Maida ta ajiye a inda yake sannan ta koma gaban mirron ta d'auko lotion d'inta masu dadin kamshi da tsada ta fara shafawa saman lallausar fatarta. bayan ta gama ta k'arasa gaban wardrobe d'inta ta d'auko wata cotton d'in doguwar riga marar nauyi wacce Bata kama taba Sosai sannan ta D'ora hula akai kalar rigar sannan ta fito daga d'akin zuwa main falorn gidan. Iya Huda da muneefa ta tarar a falon zaune suna kallo ta k'araso cikin falon bakinta d'auke da sallama. Huda ta juya tana kallonta kafin ta ansa mata sannan ta Maida kanta kan tv tana cigaba da kallonta .muneefa kuma ta tafi da gudu ta rumgume Huyaam tace. "oyoyo ya Huyaam tun d'azu nake lek'aki Baki tashi ba sai Yanzu".ta fad'a Tana murmushi . Huyaam ta ja mata kumatu tana murmushi tace. "Gani yanzu na fito ai, Ina Ammie take?..."ta fad'a tana duba falon kamar zataga Ammien . muneefa tace. "tana D'aki tanana shirya ya muneeb zazu tafi masallaci". HUYAAM ta Jin jina kai ta rik'o hannun muneefa suka k'arasa shigowa falon tare. Huda ta juyo tana kallon HUYAAM tace. "Ya jikin?...." HUYAAM tai murmushi tace. "Alhamdulillah shine wato ko ki tasheni koh?..."ta fad'a tana Wani tura Baki gaba.Huda ta harareta kafin ta d'auke kai tana cewa. "Hmm borin kunya kawai kikeyi ,ked'in ce zakiso na katse miki baccinki idan kinayi keda kamar kasa haka kike indai kina bacci ai ko tashin ki nai bazaki tashi ba..." HUYAAM ta harareta kafin tace. "Me kike nufi wato nice ma kasa ko?.... Kafin Huda ta Bata ansa Ammie ta K'araso cikin falon tana kallan Huyaam tace . "Daughtern Ammie ya jiki?..."Huyaam na murmushi tace. "Naji sauk'i Ammie?..."Ammie tace . "To Allah ya K'ara lafiya hope kinyi breakfast dai?..." Huyaam tai murmushi ta Mik'e ta nufi hanyar dining tace. "yanzu Zanyi Ammie". Ammie ta girgiza kai tace "Allah ya shirya min ke Huyaam ace mutum Ya zauna har 12 baici abinci ba sai kin jawa kanki ulcer". Huyaam tace. "Yi hak'uri Ammie yanzu Zanyi".har lokacin murmushi ne a saman fuskarta. "Ammie ta girgiza kai tana zama kan D'aya daga cikin kujerun falon Muneeb ne ya sauko k'asa har zuwa falon cikin shirin tafiya masallacin juma'a yasha farar shadda tareda babbar riga ya tsaya kusa da Ammie Yana juya hular hannunsa yace. "Ammie ya haidar fa ya fito koya tafi masallacin ya barni?...."ya fad'a Yana kallan hanyar part d'in su ya haidar.kafin Ammie ta bashi ansa ya haidar ya sauko nan downstairs cikin shigar manyan kaya shima sai baza k'amashi yakeyi.Huyaam tai saurin cewa. "ya haidar kayi kyau ta fad'a tana murmushi. haidar ya kalleta yace . "Thank You sis". sai Kuma ya maida kallansa kan Ammei yace. "Ammie zamu tafi masallaci". Ammie tace. "Allah ya kiyaye". ya ansa da Ameen.sai Kuma ya Kalli muneeb yace . "Zo mu tafi time na tafiya". Ya fad'a Yana yin hanyar k'ofar fita daga falon.muneeb yabi bayansa bayan yayiwa Ammie sallama, Ammie ta Rakasu da fatan dawowa lafiya. Wajen k'arfe biyu da Rabi na Ranar aka sauko daga masallacin juma'a Dake nan cikin palace d'in dayake anan Mai martaba yake sallahn juma'arsa shima. yasa bakiga yadda masallacin ya cika da mak'il da mutane ba.sannan yawancin wad'anda ke zuwa yin sallahn ma yawancin su wad'an da ke kusa da gidan sarkin ne shiyasa duk nan masallacin palace d'in suke zuwa yin sallahn juma'arsu da . Can na hango yaran cikin palace d'in da samarin gidan irinsu ya haidar suna ta k'ok'arin shiga cikin palace d'in . Bayan sun shiga kuma kowa sai ya kama Hanyar part d'insu suna ta k'ok'arin shiga b'angarensu. kafin na hangi ya haidar Dake tafiya Yana duba wayarsa muneeb Kuma yana gefensa suna tafiya tare har suka k'araso b'angaren su.bayan sunyi knocking suka shiga cikin falon bakinsu d'auke da sallama. Huyaam ce kad'ai falon tana parking labulayen windows d'in falon Zatai parking d'insa jiki k'arfen da ake hanging labulayen.ta juya tana ansa musu ya haidar ya zauna kan D'aya ya cikin kujerun falon Yana cigaba da pressing wayarsa muneeb ya tunkaro Huyaam Dake kokawa da babbar rigarsa wadda ya kasa cirewa yace. "Ya HUYAAM cire min na kasa" Huyaam tace . "Tom". Ta fad'a tana matsawa kusa dashi Nan ta cire masa rigar sannan ta bashi ya karb'a ya haye sama wajen Ammie da sauri. Ganin ya haidar zaune a falon Yana latsa wayarsa yasa Huyaam ta k'araso cikin falon da murmushi a saman fuskarta ta zauna kusa da ya Haidar tace. "ya Haidar sannu da Zuwa "Sai Kuma tai shiru ta fara wasa da yatsun hannunta . Ya haidar Yana jinta bai dago ba.ganin yayi shiru Bai ansa ba yasa Huyaam ta k'ara k'asa da murya ta marai raice tace . "Ya haidar magana fa nake maka".ta fad'a tana kallansa .sai a sannan ya d'ago da kansa Yana kallanta kafin yace. "Menene?.... atak'aice. Huyaam tace . "Uhmm!! dama aran wayarka zaka bamu muje mu K'arasa game d'in ranar nan da bamu gama ba nida Huda".ta fad'a tana Wani langwab'ar da kai tana kuma kallansa . Shi dariya ma ta bashi, waishi zataiwa wayo.sai Kuma yace . "Bayanzu ba amfani nake da wayata". Huyaam tace. "To Dan Allah ya Haidar sai yaushe zaka bamu?..."ya kalleta a