← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 85

Sashe 43

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Bismillahirrahmanirrahim* ___________ Washe gari tun bayan sallan ASuba da Afeef ya dawo masallaci bayan yaje har b'angaren Ammie ya gaidata daya dawo ya had'a kayansa cikin box d'in da zaiyi tafiyan Acikinsa,bayan ya gama zuba kayan cikin box d'in yay zipping d'insa sannan ya Mik'e tsaye ya fara rage kayan jikinsa bayan yasa rigar wanka ya shiga toilet Dan yin wanka.shiryawa ya farayi bayan ya fito daga toilet d'in ya shafa lotion d'insa masu k'amshin Dad'i sannan ya k'arasa har kan bed ya d'auki kayan daya ajiye zaisa yasa ya feshe duka jikinsa da turarukansa masu bala'in dad'in k'amshi,ya fito daga d'akin hannunsa rik'e da box d'in kayansa sai wayoyinsa a D'aya hannun nasa ya jawo k'ofar ya rufe ya k'arasa falon lokacin 8:45 har tayi Yana k'ok'arin fita Ammie ta shigo falon tana kallansa ya k'arasa kusa da ita Yana kallanta Ammie tace. "Badai har ka shirya ba?." Yana shafa kansa Yace "Eh na gama". Ammie tace. "To ga breakfast can kaje kayi an had'a Yana dining ko dai a kawo Maka nan d'in?." Ya langwab'ar da kai yace. "Ammie anya ko zan tsaya saboda time Yana k'ok'arin tafiya". Ya fad'a Yana kallan disigner watch d'in dake d'aure a tsintsiyar hannunsa.Ammie ta harareshi tace. "Ai da saura k'arfe nawa Yanzu ba kace jirgin k'arfe 10 bane ba?....".yace. "eh! but inaso ne naje wajen takawa kafin na tafi shima kinsan zan iya spending some minutes acan kafin na tafin". Ammie tace "duk da haka Afeef akwai sauran time kusan one hour fa". Ya Sauke numfashi ganin Ammien ta dage dole sai yayi breaking d'in yace. "Shikenan muje ko iya tea ne Nasha". Daga haka yabi bayan Ammie suka fita daga falon gabad'aya bayan ya kullo k'ofar falon nasa suka Sauka downstairs d'in.... Zama yayi kawai Yana kallan Ammie da mamakin yadda take loda masa abinda aka girka for breakfast kawai yake Kallo.gabansa ta kawo ta dire plate d'in tana kallansa tace. "Gashi nan kaci naga iya plate tunda kaga tafiya zakayi". Ta fad'a tana barin wajen kafin ya samu zarafin Yi mata complain.kallan abincin kawai Afeef yake Yana tunanin ta ina ma zai fara Dan shi ganin yawan breakfast d'in data had'a masa ma tsoro kawai yake bashi duk da itama kanta Ammien tasan ba iya cin ko Rabi zaiyi ba.sauke numfashi yayi ya d'auki spoon ya fara Shan tea d'in dake gaban sa shima baifi sipping hud'u yayi ba ya ajiye sannan ya d'auki fork spoon ya Dan caccakali Irish d'in with source stew d'in kafin yaji he is fully sannan ya ajiye fork d'in ya d'auki bottle water ya b'alle murfin ya kafa a bakinsa ya fara Sha cikin nutsuwa bayan ya gama Sha ya ajiye Sauran nan kan table d'in sannan ya d'auki tissue ya goge bakinsa da ita.mik'ewa yayi ya bar dining d'in ya k'araso nan tsakiyar falon inda box d'in nasa take ya duba wayarsa Jin shigowar text message Mai aikin b'angaren Nasu data ke aiki zata wuce ta duk'a har k'asa ta gaidashi ansa mata yayi with out looking at her. Huyaam ce ta sauko downstairs d'in Dan tun bayan ASuba da tai sallahn sukai karatun Al'qur'ani ta d'auko wayar ta tafi d'akin ya Zarah akan ta Bud'e mata komai duk da dama dai tasan kusan komai daya Dan ganci waya acikin wayar Ammie tunda suna d'auka Wani time d'in ita da Huda suyi latse latsensu aciki idan suka gaji Kuma su ajiye,da Allah Kuma ya taimakesu duka akwai sim card masu register acikin wayoyin nasu .tsaye tai a stairs d'in tana kallon Afeef da yake latsa wayarsa yayi kyau cikin kayan Daya sa ba kad'an ba, ga facing cap d'in Daya D'ora akansa ta hannunsa D'aya a cikin aljannun Wandansa d'ayan kuma Yana latsa wayarsa dashi kwata kwata baiji motsin kowa ba tunda replaying message yakeyi.tsintar kanta kawai tai da shiga cikin Camara wayar Tata tashiga Yi masa pictures Wanda sukai kyau ba kad'an ba duk da daga nesa tai Amma Kuma yayi kyau wasu tai zooming kafin ta d'auka wasu kuma ahakan daga nan nesan tai masa su . murmushin tai Ganin harta gama d'aukar tasa Bai sani ba saboda kwata kwata hankalinsa na kan wayarsa.dan tasan idan ya sani saiya kusan tattaka ta. k'arasa saukowa stairs d'in tai Jin motsi foot steps a bayanta Ammie ce take saukowa sai alokacin afeef ya d'ago d a kansa daga latsa wayar tasa da yakeyi ya Kalli Ammie Dake saukowa downstairs d'in Wadda direct hanyar kitchen d'in tai tana ce masa tana zuwa,ansa mata yayi da okay sannan ya Kalli HUYAAM data k'araso ta D'an tsaya kusa dashi tana murmushi tace. "Good morning Yaya".yana kallonta yace. "Morning". Ta D'an tura Baki kad'an tana langwab'ar da kai tace. "Yaya Ashe wai tafiya zakayi". Yace. "Ba gashi kin Gani ba". Tace. "Yaushe zaka dawo Kuma?." Batareda ya kallate ba yace. "I don't know". Atak'aice . Huyaam Tai murmushi tace. "Wallahi ka sani". Ya kalleta Fuskarsa a had'e yace. "Yaushe na fara wasa Dake HUYAAM da zan Fad'i Abu kice min wai nasani". Tai murmushi tana Toshe Bakinta da hannunta duka biyun tace. "Kayi hak'uri bazan sake ba". Ya d'auke kansa Amma Baice komai ba.Ammie tafito Daga kitchen dai dai lokacin da a kai knocking k'ofar wata Mai aikin Ammie ce Dake goge goge a falon ta ajiye dust d'in hannunta tafi Jin Muryar namijine ta Bud'e k'ofar D'aya daga cikin drivers d'in gidan ne Yana kallanta yace. "Kicewa yarima an fito da Motar?. juyowa tai ta Koma cikin falon ta tsugunna har k'asa kanta a k'asa tace. "Rankai Dad'e driver ne yace an fito da motar". Afeef yace. "Okay". Daga haka ta Mik'e ta koma ta cigaba da aikinta.Afeef na kallan Ammie yace. "Ammie bari na tafi". Ammie tace. "shikenan Allah ya kiyaye ka gaida lamid'o idan kaje". Afeef ya ansa mata da in Sha Allah! Dan dama lamid'o ya Dad'e da komawa tun time d'in da AFEEF yazo lokacin Baifi 4 days da dawowar AFEEF d'inba ya koma. Ya zarah ce da Huda suka sauko falon dama tun 7:30 su muneefa suka tafi school.suna kallon yayan nasu Dayay hanyar k'ofar zai tafi sukai masa Allah ya kiyaye ya ansa musu Yana fita daga falon.drivern da zai kai Afeef Airport d'in Dake tsaye can gefe dama Bai tafi ba Yana tsaye Yana jiran fitowar sane yay Maza ya k'araso wajen sa ya karbi trolling hannunsa cikin girmamawa yake masa barka da fitowa. Ansa masa Afeef Yayi at the same time Yana tafiya bai tsaya ba yana kallon time ganin da D'an sauran lokaci yace. "Kaji rani ina zuwa". Daga haka yay Hanyar fad'a gun Mai martaba.cikin girmamawa driver ya ansa masa Yana yin gaba wajen inda yayi parking motar... k'arfe 9:50am taiwa su Afeef airport d'in,fitowa yayi daga cikin motar bayan an Bud'e masa back seat ya fita dogarin na kallansa cikin girmamawa yace. "Allah ya dawo dakai lafiya magajin masarautar kano". shidai Afeef Bai ansa ba har driver ya k'araso da trolling a hannunsa Yana kallan Afeef yace. "A raka ka da akwatun ciki rankai Dad'e?... Afeef yace. "No! badamuwa ku wuce kawai".daga haka yasa hannu ya k'arfi trolling ya bar wajen ya wuce inda ake boarding classes da har an fara dan ma shi Yana VIP ne ba Wani layi zaibi ba.driver da dogarin nan da sukai masa rakiya suka shiga motar suka koma palace.... Tun bayan tafiyar Afeef dasu HUYAAM sukai breakfast suke Zaune a falon ita da Huda.ya Zarah kan ciki ta koma zatai shirin tafiya school Dan k'arfe shad'aya suke da lecture. Knocking akai a k'ofar falon tareda turo k'ofar aka shigo lokaci D'aya.. ikleema ne da safna kowa da wayarsa a hannunsa suka shigo falon bakinsa a washe kamar gonar auduga.. mamaki ne ya kama su Huyaam ganin su Ikleema Amma Kuma sai suka kauda tunanin nasu tunda dai sun San bazai wuce akan wannan wayar bace ta kawo su.k'arasowa falon sukai cikin sand'a kamar wasu marasa gaskiya suka zauna nan k'asan carpet.huda ta rik'e hab'a tace. "Meye kuke Wani sand'a kamar wasu marasa gaskiya?..." Ikleema ta Saka yatsanta abakinta alamar tai shiru".Huda tak'i yin shiru sai ma cewa da tai ".Yau Kuma kune da wannan lokacin". Ta fad'a tana musu Hararar Wasa". Ikleema ta k'ara k'asa in da murya tace. "To ko mu koma ne?...." Sai Kuma ta rik'e baki tai k'asa da murya tace. "Yaya Yana nan ne? shiyasa fa nake tai Miki alamar kiyi shiru Amma kika k'i,Dan kan naje na saki baki ina ta suturu ya fito ya sameni".. Huyaam tai murmushi tace. "Baya nan matsora ciya".. ikleema tace. "Au! Tunda baya nan shikenan ai gara na saita bakin nawa kar naje na saki layi". Huda tace. "Kima Saki bakin mana". Ta fad'a tana murmushin.ikleema tace. "A'a gara dai nai shirun duk da baya nan" Sai kuma tace." Uhmm Kinga zuwa mukai fa mu karb'i contact D'inku tunda dai yanzu muma mun samu 'yan cin kanmu". Ta fad'a tana Wani fari da ido.Huda tasa dariya tace. "Yanzu karb'ar contact d'inne har sai kunzo? ah lallai ko yanzu munsan kunyi waya farin shiga". ikleema tace tana hararar Huda. "ke Banda kenan?...". Huyaam tai murmushi tace. "Ina ko harda ita mana to jiya in Baku labari Huda kasa bacci tai saboda murna". Mai ikleema da safna zasuyi inba dariya ba .Huda ta harari Huyaam tace. "Wallahi kairya take itace ma batai baccinba.Safnah tace. "Kinga malama bama San borin kunya idan bazaki bamu contact d'in naki ba ita Huyaam sai ta bamu ai ba'a dole". Huda tace." Keda wasa nake muku bari na fara Baku tawa". nan ta fara karanto musu duk suka shiga adding numbers d'in Cikin wayoyinsu haka nan dai sukai exchanging numbers a tsakaninsu,har ya Zarah ta fito zata tafi school ta Tarar suna ta hauka da wayoyinsu suka Gaida ta da fatan mata dawowa Lafiya ta ansa musu Sannan ta fita daga falon nan fa Abun NEMA ya samu sai faman latsa waya sukeyi ana dariya ana shewa har Ammie ta fito itama ta samesu..... _____________ Hajiya inna na Zaune nan main falon b'angaren gimbiya Aysha tana kallan TV da ake haska wa'azi daga bakin Wani babban malami a k'asar nan a tashar Sunnah TV sallama akai Tareda da shigowa falon . ta d'aga kai
Chapter 43 · 0% Book details