← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 85

Sashe 40

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Egypt d'in tunda naga abun ya dawo". Afeef yace. "Bari na d'auko waya ta na kira doc". Ammie ta gyad'a masa kai batace komai ba harya fita daga d'akin. Babu dad'ewa ya dawo yace. "Doc yace min gashi nan zuwa". Ammie tace. "Shikenan" daga haka afeef ya fita daga d'akin gabad'aya...bayan fitar sa Babu dad'ewa baba magajiya tai knocking k'ofar aka Bata iznin shiga, tashigo d'akin Bakinta d'auke da sallama suka ansa mata ta tsugunna ta gaida Ammie cikin girmamawa, Ammie ta ansa mata da kulawa.baba magjiya tace. "Ranki Dad'e ya Mai jiki". Ammie tana kallan ta tace. "da sauk'i". Baba magajiya tace. "Allah ya sawak'e bari naje zan dawo anjima". Ammie ta gyad'a mata daga haka ta fita daga d'akin...... ___________ *Masarautar Zazzau* "Ko baka fahimci Abinda nake ce Maka bane eh Abdallah da yaran Hausa nake maka magana fa?..." Hajiya inna ta fad'a tana kallan Mai martaba Dake zaune a falonsa . sarki Abdallah ya d'ago Yana kallanta sai Kuma yay k'asa da murya yace. "Eh inna da sanina ya tafi school d'in kuma abunda yasa ma na barshi naji yace suna da test d'in da zasuyi 11:30am kuma Kinga yau Friday da wuri ma zasu gama 12 ma zakiga ya dawo in Sha Allah".Haka sarki Abdallah ya fad'a Yana kallan mahaifiyar tashi. Hajiya inna tace. "Amma wallahi kaidai Abdullah bakai tunani Mai kyau ba ya za'ayi ka biye masa kawai ka Barshi ya tafi wata boko bayan kasan shekaranjiya yadda muka ga Rana haka mukaga wannan dare da yaran nan yadda yadinga ihu Yana wasu surutai tsakiyar dare badan Allah yasa duk muna kusa ba munjiyoshi da wuri da haka zai gudu cikin dare bamu sani ba". Hajiya inna ta fad'a cikin b'acin rai.. Takawa yay shiru Yana kallanta sai kuma yace. "To Yanzu dai Inna na fahimceki Amma kuma Dan Allah kiyi hak'uri tunda yanzu dai test zasuyi kuma nasan ma yanzu haka sun kusan zuwa school d'in koma sunje,saboda haka Dan Allah ki kwantar da hankalinki in Sha Allah Babu abinda ma zai sa meshi in Sha Allah tunda kullum muna addu'a sannan ba shi kad'ai ya tafi ba,harda rakiyar fadawan gidan nan Kuma kinga hakanma ai mugodewa Allah tunda har Yana iya zuwa school d'in harma ya fuskanci Abinda ake koya masan, da da baya iya zuwan fa?...". Ya fad'a Yana kallan Hajiya inna.Hajiya inna tai shiru sai muka ta sauke numfashi tace. "Gaskiya ne wannan to Allah ya K'ara masa lafiya Amma wallahi ni abinda yay daren shekaranjiya ne shiya tsoratani , Amma tunda kace haka Allah ya K'ara tsareshi ya kuma Kara musu lafiya Baki D'aya". Mai martaba yay murmushi ya ansa da Ameen ,yace. "nima yanzu Zanyi shirin tafiya masallacin juma'a naga lokaci Yana kusantowa". Hajiya inna tace "Eh kuma Hakane to bari Nima na koma wajen su Ayshan duk da itama dai jikin alhamdulillah".daga nan Hajiya inna taiwa Mai martaba sallama ta fita daga falon nasa gabad'aya.a k'ofa sukaci karo da shakundum zata shigo falon cikin shiga ta Alfarma Hakan yasa tai saurin matsawa baya ganin Hajiya inna zata fito daga falon tana sunkuyar da kanta k'asa tace. "Barka da wannan lokacin Mai babban d'aki".ta fad'a kanta a k'asa.hajiya inna tace. "Yauwa" atak'aice tana yin gaba.shakundum ta bita da Harara kafin ta shige cikin falon takawa..... k'arfe Sha biyu da Rabi na Ranar anty Amina ce zaune a kusa da gimbiya Aysha waya ce a hannunta vedio call suke da Gimbiya Bilkisu wacce ke tambayar ta jikin gimbiya Aysha.anty Amina tana Murmushi tace. "Da sauk'i Yaya Bilkisu bari ma na Kara mata wayar a fuskarta ki ganta ko zaki fi yarda Dani". Daga haka ta kai wayar dai dai fuskar gimbiya Aysha Dake kwance akan gadon kamar yadda take a Koda yaushe.gimbiya Bilkisu tace tana kallanta cikin sanyin murya. "Ya jiki Yaya gimbiya " lumshe ido gimbiya Aysha tai alamar ansawa.gimbiya Bilkisu tace. Allah ya K'ara lafiya Allah yasa kaffarane, Allah ya tashi kafad'unki Yaya gimbiya".. ta fad'a cikin rawar murya Gimbiya Aysha na Jin ta hakan yasa nan ma ta K'ara lumshe idon nata .ita dai gimbiya Bilkisu zuba mata ido kawai tai tana kallan yayarta tana tunowa da shekarun Baya a lokacin da yayar tata take cikin k'oshin lafiyarta take rayuwar ta cikin walwala da farin ciki Amma lokaci D'aya komai ya sauya take ta runtse idonta hawaye ya soma ziraro mata a saman fuskarta,ganin haka yasa anty Amina da tasan dama dole hakan saita faru shiyasa Wani lokacin ko gimbiya Bilkisu ta k'ira zataji ya jikin na gimbiya Aysha Anty Amina take ce mata tayi bacci saboda Kukan da take aduk lokacin da zasuyi waya harma Wani lokacin tasa itama gimbiya Aysha tai hawayen, juyawa anty Amina tai taga hawaye ya kawo idon gimbiya Aysha harya soma zirarowa zuwa Kuncinta, nan hankalin anty Amina ya K'ara tashi ga ta kasa kashe wayar shigowar da Anam tai d'akin yasa ta Mik'a mata wayar tace. "Jeki ku gaisa da Yaya Bilkisu" Anam ta karb'i wayar ta fita daga d'akin zuwa falo. Anty Amina Kuma ta zauna gefen gadon tana lallashin gimbiya Aysha da kalamai masu Dad'i....... Family doctor d'in nasu da Afeef ya k'ira Bai samu zuwa da wuri ba sai k'arfe Sha biyu da kusan Rabi saboda go slow Daya tare shi a hanya. Bayan ya gama treatment d'in raunin da Huyaam taji ya d'ago yana Kallan Ammie yace cikin ladabi. "Ranki Dad'e angama Babu Wani abun dama kawai D'an yankewa tai kuma munyi treating d'in wajen in Sha Allah Babu Wani abun ".Ya fad'a cikin girmamawa. Ammie ta Kalli k'afar Huyaam sannan ta Kalli doc tace. "Doc kaga fa tasa k'afar ta tane cikin kwalaban data fasa,ka tabbatar Babu Wanda ya mak'ale mata acikin k'afar tata?..." Doc ya Jin Jina kai yace cikin girmamawa. "Eh Babu ranki Dad'e na duba ko ina Banga Wani Abu ba" Ammie ta Sauke numfashi tace. "Shikenan mungode Allah yasaka da Alkhairi" Doc yace. "Babu komai Allah ya Bata lafiya ranki Dad'e bari naje zan bawa yarima takardar magun gunan da za'a Siyo matan". Ammie tace. "Shikenan Babu damuwa". Daga haka doc ya fita daga d'akin Afeef Dake tsaye a gefe yabi bayansa Ammie Kuma ta zubawa HUYAAM ido ita tareda Huda suna kallanta da tausayawa har lokacin su muneefa Basu dawo ba Amma tasan suna hanya tunda lokacin tashin nasu yayi harma ya wuce...... HUYAAM LAMID'O AZIZ CHIROMA AFEEF 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__* *__(MRS SARAKIES )__* PAGE 2 *TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!* *Assalamualaikum mutanan arziki.yauwa Ma dai na K'ara Zuwa muku da Wani sabo albishir d'in* *Ina kuke manyan mata masu capacity ? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."* *To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* *1,Atamfofi* *2, lesses* *3, Abaya* *4, kayan kwalliya ko Wani iri ne* 5,*D'an kunnaye(jiwelleries)* *6,takalma* *7,hand bag* *8, mayafai* *9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*. *domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka +234 811 190 1302 /09020337676* *Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta* *Sai mun Jiku
Chapter 40 · 0% Book details