Sashe 47
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Bismillahirrahmanirrahim* __________ Har washe gari HUYAAM Bata dawo dai dai ba. Dan da Wani Irin ciwon kai suka tafi suka barta dashi.duk da Tasha maganin nata Amma bamu Wani sauiki aciki, haka Nan dai Ammie ta barta ganin iya ciwon kanne bawai jikin ba, Dan inda sabo irin wannan ciwon kan na Huyaam ta Saba dashi.tun k'arfe 8 na dare tacewa Ammie bacci take ji nan Ammie ta kaita d'akin Huda ta Kwantar ta saida Ammie taga tayi bacci sannan ta bar d'akin tareda da Huda .Dan Ammie tace tareda da Huda zasu kwana saboda ta dinga kula da ita kafin safiya. ahaka ta koma falon downstairs ta barsu tareda Huda....Washe gari da safe wajen k'arfe 7:30am Huyaam na zaune kan sallaya a nan d'akin Huda da tun bayan da tai sallan ASuba tayi azkar d'inta take nan Zaune tana karatun Al'qur'ani ita kad'ai ce zaune Huda Kuma tana kan gadon ta koma bacci.dan tunda ta tashi tajita saka yau kamar Bata tab'a Wani ciwo ba, ciwon kan ma dayak'i tafiya yanzu haka ya tafi Babu shi Hakan nema ya Bata damar yin karatun. knocking d'in kofar d'akin da akayi Tareda turowa aka shigo lokaci D'aya Yasa Huyaam ta juya tana kallon Mai shigowar.Ammie ce tashigo sanye da jihab a jikinta,ajiyar zuciya ta sauke ganin Huyaam d'in Zaune tana karatun Al'qur'ani Hakan na nufin Jikin da sauk'i kenan.sauke idonta Huyaam tai k'asa tana ansa sallamar Ammie tareda gaisheta lokacin D'aya.Ammie ta k'araso d'akin ta tsaya tana kallan Huyaam da kulawa ta ansa mata sannan tace. "Ya Jikin Huyaam?... "Huyaam tace cikin sanyin murya. "Da sauk'i Ammie". Ammie tace. "Allah ya sawak'e , Allah ya K'ara lafiya, yanzu babu ciwon kan?..." Huyaam tace. "Eh yanzu Babu". Ammie tace. "To Alhamdulillah Allah ya K'ara lafiya idan Kina Jin yauwa dai ki taso muje Kisha ko iya tea ne before a gama breakfast d'in". Huyaam ta girgiza mata kai tace. "bana Jin yunwa". Ammie tace. "Kin tabbata Huyaam". Huyaam tai shiru ta Jin jina mata kai alamar eh.Ammie ta sauke numfashi tace. "Shikenan! Hudan Bata tashi bane ba?...." Ta fad'a tana kallan saman bed d'in da Huda ke kwance sai sauke numfashi takeyi.huyaam ta kalli gadon sai Kuma ta kalli Ammie tace."a'a tayi sallah ita ta tashe Nima mukai tare". Ammie tace. "Shikenan Allah ya K'ara lafiya". Huyaam ta ansa da Ameen daga haka Ammie ta fita daga d'akin bayan ta kullo Musu k'ofar..... K'arfe Hud'u da Rabi na yamma, dayake yau Al'hamis babu Islamiya yasa gabad'ayansu basuje ko Ina ba suna zaune a gida. Huyaam da Huda ne kad'ai zaune a falon ita da muneefa Dan muneeb tunda ya tafi masallaci sallahn ASR Bai dawo ba.ya Zarah ma dai tana school Bata dawo ba.Ammei Kuma tana sama tunda ta haura Bata sauko ba.Baba magajiya ce ta fito daga kitchen ta k'araso falon hannunta rik'e da Wani D'an k'aramin tray Wanda ta d'ora jug da cup akai data damawa Huyaam kunu dan tace shi take son Sha.da sallama ta k'araso falon ta k'arasa nan gaban HUYAAM ta ajiye tray d'in tana kallanta tace. "Gashi an dama kunun 'yar gidan Ammie...." "Ta fad'a cikin girmamawa.huyaam ta d'aga ido ta kalli baba magajiya sannan ta kalli tray d'in tace. "Sannu baba nagode". Baba magajiya tai murmushi tace. "babu abinda kike buk'ata Kuma?..." Girgiza mata kai Huyaam tai tace. "Babu komai". Baba magajiya tace. "Allah ya K'ara lafiya ranki Dad'e". Huyaam ta ansa mata da Ameen.mik'ewa Baba magjiya tai ta bar falon ta koma kitchen d'in.huyaam ta d'auki cup d'in ta tsiyayi kunun ta kai Baki ta fara Sha sai taji yayi mata Dad'i sosai abakinta.bayan Kamar mintuna 15 suna Zaune afalon akai Sallama a k'ofar falon, safnah ce da mamansu Hajiya Aysha.Huda da Huyaam suka ansa musu sallamar tasu har suka k'araso falon. Huda da Huyaam suka had'a Baki Wajen gaida Hajiya Aysha.hajiya Aysha ta ansa musu da kulawa tana tambayar Huyaam jikinta.huyaam ta ansa mata a Kun yace.huda ta Mik'e tace. "Ummi ki zauna bari naiwa Ammien Magana tana sama".Daga haka Huda ta nufi stairs d'in.Hajiya Aysha tai murmushi ta zauna nan saman kujera . safnah ta k'arasa ta zauna kusa da Huyaam tana kallanta da kulawa tace. "Huyaam ya jikin?..." Huyaam na D'anyi murmushi tace. "Da sauk'i". Safna tace. "Allah ya K'ara lafiya". Huyaam ta ansa mata da Ameen k'asa k'asa.d'aya daga cikin hadiman Ammie ce tai sallama a falon hannunta d'auke da tray data D'ora ruwa da drink's akai ta ajiye saman table Dake nan gaban Hajiya Aysha sannan ta tsugunna har k'asa ta gaida Hajiya Aysha. Ansa mata Hajiya Aysha tai da kulawa sannan ta mik'e ta koma kitchen d'in.Huda ce ta sauko downstairs d'in tana kallan Hajiya Aysha tace. "Ummi Ammien tace kije falon sama" Mik'ewa Hajiya Aysha tai tana ansa mata da to daga haka ta nufi stairs Wanda zai sadan ta b'angaren Ammien.. Fulani Salamatu ce zaune a cikin d'akin Aziza tana kallan Aziza Dake zaune a falon tun d'azu sai chatting takeyi.Aziza ta d'ago tana kallan mummyn nasu Dake tai mata magana tun d'azu akaro na Babu adadi Amma Kuma batai mata magana ba yanzun ma gajiya tai tace. "wai mommy yanzu Dan Allah Mai kikeso nace miki ne? nifa wallahi banasanshi ko kad'an kuma kinsan ma Karatu Zanyi ba wai soyayya ba ni gaskiya kark'i k'aramin zancensa banaso". Ta fad'a a fusace tana Wani tura Baki gaba.fulani Salamatu kallan Aziza kawai take da mamakin abinda ta fad'a yanzu Aziza so take ta Bat'a mata duk Wani shiri da buri akan abinda take ganin shine kad'ai mafitar ta kome? Ita fa a yanzu babban burinta bai wuce ace 'yarta ta auri D'an sarki mai jiran gado ba tunda ita Bata haifi D'a namijin da zai gaji sarautar gidan ba ai gara ace 'yarta na Auren D'an sarki Koba komai wata Rana 'yar tace matar sarki harma ta haifi yarima .sauke numfashi tai ta k'ara gyara zamanta tana kallan Aziza tai k'asa da murya tace. "Haba Aziza Yanzu ni kenan ban isa na fad'a miki magana Kiji ba? Haba Aziza komai fa da kikaga Inaya danke nakeyi fa badan Komai ba, Amma yanzu ni zaki kunyata ko yaya?.." Aziza tai shiru batai magana tana cigaba da danna wayarta.fulani Salamatu ta cigaba tace. "To Yanzu da kike cewa bakyason sa Dan Allah meye laifinsa da zakice bakyason nasa sai kace bakisan Shiba Aziza? Ga kyau ga kud'i ga Aji to Dan Allah Kiko Aziza me kikeso awurin D'a namiji Wanda shi ba shida shi?..bana tunanin koke zaki fad'a masa kyau. "Aziza ta Kalli mommyn nasu Jin abinda ta fad'a tace. "Wai mommy Dan Allah shine yace Yana Sona ko Kuma kece dai kike son ni na so shin?.ta fad'a tana jiran ansar mommyn nasu.Fulani Salamatu ta K'ara gyara zamanta tai k'asa da murya tace. "Waya ce Miki baya sanki Aziza? Kema kinsan babu Wani d'a namiji da zai ganki baiji kin masa ba". Aziza ta tura Baki gaba tace . "To Dan Allah mommy abar zancen nan kawai yanzu AURE za'a min ko Kuma karatu Zanyi?. Falani salamatu tace. "Karatu zakiyi Aziza, Amma Kuma inaso ne na ga kin amince da maganar nan tawa yadda ko zuwa gaba ne nasan bani da matsala akan wannan Abu Da nakeso ya k'ullu". Aziza ta Bat'a Rai tace. "To Dan Allah tunda sai nayi karatu ki K'yaleni da wannan maganar ki bari har sai lokaci yayi".fulani Salamatu tai shiru tana kallan Aziza tana tunanin ta yadda zata b'ullo mata Dan Kada ta watsa mata k'asa a ido ta Bat'a mata duk Wani shirin ta,Dan Aziza ce kad'ai take tunanin zata had'a ta da shi Wanda take wannan burin akan nasa. Sauke numfashi tai tace. "Shikenan tunda kince haka Amma inaso kiyi tunnani akai". Da k'yar Aziza ta iya ansa mata da to sannan fulani Salamatu ta mik'e ta fita daga d'akin gabad'aya....... _____________ Tun bayan da su Huyaam sukai sallahn magrib suka d'auko Al'qur'ani suke karatu anan falon kamar yadda suka Saba,har yanzu da ake K'iran sallahn isha'i kafin su tsaya da karatun bayan sunkai Aya sannan suka rufe Al'qur'anin .Addu'o'i sukai Sosai kafin su shafa suka Mik'e Jin anshiga Sallahn, jam'i sukabi suka bi sallahn.....k'arfe 8:30pm suna Zaune a falon downstairs bayan sunyi dinner ko Wacce rik'e da wayarta a hannunta daga Huyaam har Huda ya Zarah ce bata a falon tana d'akinta tun bayan da sukai dinner ta shige d'akin Bata fito ba har yanzu.muneefa da muneefa kuma suna zaune a falon suna game. Knocking k'ofar falon akai Tareda Sallama lokaci D'aya a aka turo k'ofar aka shigo.kallan k'ofar sukai Huda na ansa sallamar tasa harya k'arasa shigo falonwa falon bakinsa d'auke da sallama.huda na murmushi tace. "Ya chiroma sannu da zuwa". Ta fad'a tana kallansa har lokacin murmushi ne a saman fuskarta.Aziz chiroma ya zauna anan saman kujera Yana kallan Huda."yace.yauwa Huda." Muneeb da muneefa ne suka juyo suna gaida shi ,ansa musu yayi Yana murmushi Yana tambayar su school suka ansa masa da Alhamdulillah. Yace. "Good,Masha Allah! Ya Fad'a Yana kallan Huyaam ta gefen ido data sunkuyar da kanta idonta na kan screen d'in wayar ta kamar Batasan Yana wajen ba.Huda tana kallansa tace. "Ya chiroma Ina wuni?" Yana murmushi yace. "Lafiya lau Alhamdulillah ya huta?. Huda tace. "Lafiya lau". Huyaam ta d'ago da kanta tana kallansa ta D'an saki fuskarta kad'an tace. "Ya chiroma Ina wuni". Ya juya ya kalleta ya ansa mata da kulawa har lokacin idonsa yana Kanta yace. "Ashe Kuma anyi waya shine ko fad'amin?...." Huyaam ta sauke idonta batai magana ba sai Huda ce tana Murmushi tace. "To muma mun Dad'e bamu gankaba ai shiyasa bamu nuna Maka ba". Ya shafa kansa Yace. "Eh wallahi two days bana zama idan na fita tun safe sai bayan 8 nake dawowa". Huda tace. "Ayya". Ta mik'a masa wayar Hannunta tace. "To gatawa ka Gani " yasa hannu ya karb'a Yana juya wayar a hannunsa yace. "Wow Masha Allah! lallai yarima Yana ji daku irin haka wannan latest phone". Huda tai murmushi Amma batai Magana ba ya d'ago ya Kalleta yace. "To abani contact ko ba'a badawa?..." Huda tace. "Mai zai Hana kuwa ya Aziz bari na Karanto Maka". Yana murmushi ya Mik'a mata wayarsa yace ungo kisamin taki". karb'ar wayar tasa Huda tai.itako Huyaam na