Sashe 34
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
haka tace. "Yaya Nima na biyoka sai mu dawo tare ko juyowa Bai yi ba balle ya ansa mata.ya Zarah tabi bayansa da Sauri bayan tai ma Ammie sallama.bayan fitar su Ammie na kallan Huyaam tace. "To idan ya tafi Dake d'in Ina zai kaiki?..."Huyaam tai shiru tana kallan Ammie". Ammie girgiza tace. "Wuce ki k'iramin Huda idan ta gama akwai aikin da zan saku". Babu musu HUYAAM ta haye sama da sauri.Ammie Kuma ta samu waje ta zauna a falon tana jiransu........ K'arfe biyu sauya fulani Salamatu ce tsaye a Wani k'aton store Dake b'angaren Hajiya Lubabatu inda aka ajiye kayan tarb'ar Bak'in anyi packaging d'insu an kammala komai tun Wajen k'arfe D'aya ,sannan an ajeye komai a inda ya dace komai yayi Masha Allah Bak'in kawai ake jiran zuwan nasu ta bakin na Hajiya Lubabatu Dake cewa ayi komai cikin girmamawa aikuwa anyi d'in Dan Babu laifi sunyi abu cikin girmamawa anyi Abun fita kunya sosai.Fulani Salamatu ta juyo tana kallon hajiya Lubabatu bayan ta gama ganin Komai tace. "K'awata komai yayi yadda ya dace Babu Wanda ya isa ya Raina mu gaskiya mutanan nan sun iya aiki sunyi komai yadda ya dace". Ta fad'a tana kallan Hajiya Lubabatu... Hajiya Lubabatu tace. "Babu laifi Nima naga k'ok'arinsu gaskiya sun iya aiki". Fulani Salamatu tace. "sosai ma kefa su suke yiwa gidan governor kano duk Wani kwangila da za'ayi indai anan government house d'in ne taro ko biki ke duk Wani Wanda yake ji da kansa a garin kano indai Yana so ya fita kunyar Bak'i na b'angaren abinda zai tarb'esu to ya k'irasu Dan sun iya aiki". Hajiya Lubabatu tace. "Gaskiya nima na shaida Kuma na Yaba musu". Fulani Salamatu tace. "To ni dai bari na koma tunda dai naga abinda ya kawonin anjima kafin suzo zan dawo saboda mu shirya komai yadda ya dace". Hajiya Lubabatu tace. "Gaskiya ne to Dan Allah ki dawo da wuri". Tace. "In Sha Allah da wuri zan dawo". Daga haka ta fita daga store d'in Hajiya Lubabatu na biye da ita har zuwa falon hadimar ta karima da tai mata rakiya ta mik'e daga zuben da take a falon tabi bayan ta bayan taiwa Hajiya Lubabatu sallama cikin girmamawa....... ___________ K'arfe Hud'u da Rabi na Ranar Ammie ce ta fito cikin shiga ta Alfarma itama tayi bala'in kyau ba kad'an ba Dan kamar ba wacce ta haifi yara d'ai d'ai har bakwai ba . sanye take cikin Wani ubansun less Wanda yalashe mak'uden kud'ad'e ta D'ora alkyabba akai Mai tsadar gaske sai Wani walwali take kamar wacce zata gasar kyau tana kallan su Huyaam Dake zaune falon su biyu sai muneefa shi muneeb Bai dawo ba tunda ya fita sallahr ASR ya haidar kan dama Yana wajen aiki nan companyn Mai martaba Dake jihar kano, ya Zarah ma tunda ta fita school Bata dawo ba .garama Afeef ya dawo d'azu Dan Bai Dad'e da sake fita ba.tana kallansu tace. "Huyaam ku zauna zanje b'angaren Hajiya Lubabatu zamu tarb'i Bak'in nan".so banaso na ganku ko a compound ne kunji ai?.." duk da tasan ba fitar suke ba, kuma baza su fara yanzu ba amma dai tana musu worning ne.dayake yau alhamis babu Islamiya Kuma Babu inda zasu yasa suke Zaune a falon bayan sun gama karatun Al'qur'ani d'azu da sukai ASR prayer.har Suka had'a Baki wajen ansa mata da to kafin HUYAAM tace. "Ammie Kinga yadda kikai kyau kuwa?..." Ta fad'a cikin zuzu tawa .Ammie tai mata murmushi tace. "Ni bangani ba kece dai kika Gane min". HUYAAM tace . "Ai kuwa kinyi kyau sosai sai Kin dawo". Tace. "Allah yasa" ta fad'a tana gyara zaman alkyabbar jikinta.hadimarta baba magajiya itace take tsaye daga Bayan Ammie Dan ita zatai mata rakayi har b'angaren Hajiya Lubabatun .Ammie tai gaba Baba magajiya na biye da ita da Jakarta a hannunta tana ansawa muneefa Dake mata adawo lafiya.huyaam sukabi Ammie da kallo har ta fice daga falon gabad'aya.. Ammie da taje b'angaren Hajiya Lubabatu ta iske Fulani Salamatu tare da k'awar tata dukansu suma cikin shiga ta Alfarma kowacce Tasha less sai Wani walwali sukeyi. Fulani Salamatu sai Wani jiji da kai take da k'yar ta iya ansa sallamar da Ammie tai musu har suka gaisa Amma ita Hajiya Lubabatu da yake ita tasan ta kan duniya faran Faran suka gaisa da Ammie har take cewa "Fulani nayi fushi Kuna manyan iyaye sai Yanzu kuka zo? Ammie dai murmushi tai tace ai mata afuwa haka nan tai ta janta da zance kamar ba ita bace take zaginta idan suka had'u da Fulani Salamatu ba .itama kanta Fulani Salamatu kallan Hajiya Lubabatu take da mamakin yadda ta sakewa Ammie Amma Kuma batai magana ba tai shiru tana kallan iKon Allah.k'annenn Hajiya Lubabatu da 'yan uwanta da sisters d'in ta duk sunzo dasu za'ai tarb'an bakin suka risina suka shiga Gaida Ammie cikin girmamawa, Ammie ta ansa musu itama da kulawa, sisters d'in su baba turaki dai suna hanya Basu k'araso ba Amma ance saua k'iris su k'araso iya k'anwarsu ce D'aya da ba'a nan take AURE ba bazata samu damar zuwa ba.Ammie na nan zauna kusa da antyn su Ikleema Babu dad'ewa saiga Hajiya Aysha nan wato maman su safna, nan suka zauna suke gaisawa.ita dai Hajiya lubabatu ta juyar da kanta gefe sai faman latsa wayarta takeyi....... K'arfe Hud'u da mintuna arba'in Bak'in suka iso bayan 'yan uwan su Mai martaba sun zo .take dogarayen Dake Bakin gate d'in suka mik'e aka wangale musu gate d'in. wasu Manyan Manyan motoci ne suke ta shigowa k'aton compound d'in kamar bazasu k'areba Dana k'irga su d'ai d'ai har guda biyar hud'u Bak'in da suka kawo lefan ne sai d'ayar Wacce itace k'atuwar ciki nai K'irar limozing wacce a itane aka sako lefen aciki.bayan drivers d'in sunyi parking haka suka fito suka bud'e duka motocin tareda matsawa baya Dan bawa wad'an da suke ciki damar fitowa sannu a hankali naga wasu manyan mata suna fitowa daga cikin motar D'aya Bayan D'aya har suka gama fitowa gabad'aya.Dana k'irgasu su su goma sha hud'u ne cif cif dukkansu cikin shiga ta Alfarma Babu K'arya gaskiya sun Sha suturu keda kingansu kinsan badaga k'aramin gida suka fito ba.drivers d'inne suka fiddo da manyan boxes d'in suna shiga dasu inda aka ce nan zasu kai. Ka'nnen Hajiya Lubabatu ne su biyu suka fito zasu shiga da Bak'in nan b'angaren nata. Bayan sun iso sukai musu barka da zuwa tareda Yi musu jagora har zuwa b'angaren.da sallama abakinsu suka shiga falon lokacin har angama kawo akwatunan suna nan an ajiye anan tsakiyar k'aton falon. Ammie da fulani Salamatu duk suna zaune saman kujera guda biyu ajere sai su Hajiya Aysha da antynsu safnah harda ma ita Kanta Hajiya Lubabatun duk suna zaune. Bak'in ne suka shigo bakinsu d'auke da sallama gabad'aya aka ansa musu da kulawa ana basu wurin zama suka k'arasa suna k'arewa mutanan Dake falon kallo ko ba'a fad'a musu ba sun San Ammie dai itace matar sarkie ita da fulani Salamatu saboda yadda shigar su ta fita daban dana sauran mutanan Dake falon Basu zauna kan kujerar da ake tai Musu tayin su zauna ba sai da suka zo har gaban su Ammie suka kwashi gaisuwa a wajen su.duk suka ansa musu da kulawa sannan suka mik'e suka k'arasa wajen zamansu Dama a gaban sarakai duk mun kud'inku da mulkinku kune dai a k'asan su dole sai ambasu wannan Girman. Zama sukai akan kujera wasunsu Kuma a k'asa kan k'aton carpet d'in da aka shimfid'a musu awajen.K'ara gaisawa sukai cikin girmamawa aka kawo musu ruwa da drink's da abincin da kai musu mu duk babu abinda suka tab'a.sannan akai addu'a aka shiga Bud'e kaya. Akwatuna ne guda 24 cif cif Wanda kowanne suke shak'e da kaya mak'il .Gud'a ce kawai ke tashi a falon nan Dan ko Wacce a kwati da za'a Bud'e sai anyi Gud'a kayane Wanda suka ansa sunansu kaya Wanda aka kashe mak'udan kud'ad'e wajen siyan su Masha Allah! kawai ake ta furtawa. haka aka gama Bud'e kaya da naiya million Daya kud'in D'inki nan ma wata gud'ar ce ta K'ara tashi Dan suma Dangin angon suna da sarauta Kuma 'yan kasuwa ne Dan baban angon shattiman kano ne suna da kud'i Babu laifi .haka aka gama Bud'e kaya aka rufe Taro da addu'a kafin nan Bak'in suka fara shirin tafiya suma an Basu kud'in takuici naira dubu D'ari takwas Wanda Ammie ce ta ciro acikin Jakarta ta Bada, kuma karkice Rance a'a kyauta ta Bada .Dan Da million Daya tai niyyar bayarwa to taga su sun bada million Daya kud'in D'inki yasa tace kawai karsukuga anrainasu yasa ta Bada dubu Dari takwas d'in.mamakine ya kashe kowa ganin Ammie ta Bada wannan uban kud'in kafin Hajiya Lubabatu ta d'auko ta Basu . Fulani Salamatu kamar ta mutu Dan haushi Dan ta tsani ace Ammie tai Abu ita batai ba musamman ma agaban bak'uwar fuska .da tasan hakane da ita zata Bada wannan kud'in Amma sai gashi Ammie tai mata kisan gilla agaban mutane tasan duk inda akaje haka za'a ce matar saiki tai kaza tai kaza ita batai ba, Amma Haka nan ta shanye ta nuna farin ciki itama Batasan Hajiya Aysha na lura da ita ba.da k'yar suka Karb'a suna ta godiya Ammie tasha kirari Wanda k'iris ya rage Fulani Salamatu tai bindaiga saboda haushi. Sai Kod'a Ammie ake kamar me.kayan da akai musu da Wanda Basu ciba da wanda za'a Basu su tafi dashi aka d'auko aka Rakasu dashi har gaban motarsu sun rabu cikin aminci suna ta godiya suka shiga motocin da suka zo acikinsu bayan sun shiga drivers ma haka aka Bud'e musu gate suka fice daga gidan D'aya bayan D'aya har suka gama fita gabad'aya..bayan tafiyarsu suma su Ammie duk tafiya sukai bayan sunyiwa Hajiya Lubabatu sallama tareda da Bak'in nata sai aka Bar iya k'awarta Fulani Salamatu sai sisters d'in su baba turaki Wanda suka ce zaso zo b'angarensu Ammie kafin su tafi zuwa anjima........ HUYAAM LAMID'O # AZIZ CHIROMA AFEEF *Muje zuwa mutanan MRS SARAKIES .ke daga Jin salon labarin kinsan zai k'ayatar ya Kuma fad'akar.akwai chakwakiya sosai anan gaba Dan labarin ma yanzu muka fara shi*. *ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu