Sashe 13
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kallan Fulani Salamatu tace tana sheshshek'ar kuka. "Mummy ba ya haidar bane Dan nasa bala dogari ya d'aukar min kayan nan ya tayani shigowa dasu ciki Shine ya Haidar ya hanashi wai bazai kawo ba idan hazan d'auka ba na barshi. kuma Bai tsaya nan ba Saida ya wulak'anta ni a gaban gabad'aya bayin gidannan sai kallo na suke Dan dai kawai su Raina ni".ta k'arasa fad'a tana K'ara sautin Kukanta. Fulani Salamatu da tunda Aziza ta fara magana take kallanta da mamakin abinda haidar yay mata . gabad'aya ranta ya gama B'aci tace cikin D'aga murya da b'acin Rai. "Shi Haidar d'inne ya hana Wani bawa Irin dogari ya d'aukar miki kaya sannan Bai tsaya iya nan ba ya wulak'antaki agaban su saboda shi ya isa yake nufi kome?...." Ta fad'a da k'arfi har Saida hadimanta biyu Dake kitchen suna mata girki suka lek'o suna kallan iKon Allah. Aziza ta gyad'a mata kai tana cigaba da murza idonta tana Kuma sheshshek'ar kuka.Fulani Salamatu ta gyad'a kai kafin cigaban tace . "Wato tunda yayansa baya nan shine shi Kuma zai D'ora daga inda ya tsaya ko me yake nufi? To wallahi Bai isa ba bazai yuba yace sai takurawa Yara na agidan nan ba, ko yayansa alokacin da yake kan ganinyar Rashin mutuncinsa Baya min haka bare Kuma shi ki K'yaleni dashi Dan wallahi bazan zuba ido ana tsangwamarku ana wulak'anta Kuba kuda gidan ubanku bari Mai martaba ya shigo zan fad'a masa idan zai d'auki mataki gara ya d'auka idan kuma bazai iya d'auka ba toni zan d'auka da kaina sai dai ayi duk wacce za'ayi agidan nan Dan bazan d'auka ba". ta k'arasa fad'a tana huci Aziza dai sai share hawayen idonta take Yi Ramla koh da walida sun nan Zaune kan kujera sun zuba musu ido kawai suna kallansu . Fulani Salamatu ta kalli Aziza tace. " ki wuce ciki ki wanke fuskarki ki barni dashi ai zai K'ara idan halin sane dama can shima ba mutunci ne dashi ba,ki dai na kukan nan haka Aziza". ta fad'a tana kamo hannun Aziza ta kaita har d'akinta ta cigaba da lallashinta kafin tace tai alwala tai sallah . Aziza ta gyad'a mata kai bayan ta goge hawayen fuskarta Fulani Salamatu ta fita daga d'akin ta koma nata danyin sallah. Suko su Huyaam suna shiga part d'insu suka nunawa Ammie kayan da suka Siyo.Ammie tai godiya tace idan Mai martaba ma yashigo anjima suje suyi masa godiya suka ansa mata da to sannan suka shige D'aki Dan d'auro alwala suma suyi sallah. Wajen k'arfe na daren ranar Mai martaba yana Zauna a falonsa tare da ya haidar suna magana su Huyaam suka shigo bakinsu d'auke da sallama suka k'arasa suka d'urkusa har kusa Mai suna suka had'a Baki wajen gaida shi. Mai martaba Yana kishin gid'e jikin tuntun sarautan dake falon ya ansa musu da kulawa Yana gyara zamansa. Sannan suka juya suka gaida ya haidar.ya haidar ya ansa musu . Suka juya Suka fuskanci Mai martaba huyaam tai murmushi tace . "Abba munga Sak'o munje munyi shopping d'in d'azu mungode Sosai Allah ya K'ara Bud'i Allah ya K'ara girma". ta fad'a tana murmushi.itama Huda ma tai masa nata godiyar.mai marataba ya Jin jina kai Yana kallan su Yace. "Babu komai Allah ya Bada good results". Ya fad'a Yana kallansu .sukai murmushi gabad'ayansu suna sunkuyar da kansu k'asa Basu Dad'e a falon ba sukai masa sallama suka tafi Dan zasu suje suyi karatu ne Saboda exam d'in gobe..... Bayan fitar su Nan Mai martaba ya cigaba da maganar da yakeyiwa ya haidar.... ____________ *Graduation day* Washe gari Friday ranar data zamto the best Rana awajen su Huda more especially ma Huyaam. wannan ranar ta zamto D'aya daga cikin ranakun da Huyaam take ganin bazata ta tab'a iya mantawa da ita ba saboda ayau idan Allah ya yarda zatai graduation na SSCE...karfe 8:30am dai dai a makarantar taiwa su Huyaam Dan exam d'in ta k'arfe 9 ce suna zuwa hole d'in exam d'in suka Wuce direct suka zauna nan zaman jiran a fara exam d'in. K'arfe 11 dai dai su Huyaam suka gama paper su ta k'arshe.gabad'ayansu suka fito kowa sai murna yake gwanin ban sha'awa Babu Dede'wa Kuma suka wuce assembly ground Dan za'a Bada gifts d'in the Best students na this year Wanda suka fi cin maki tun daga first term har zuwa second term dama haka suke ko wanni year sukan bada gifts ga best students d'insu to wannan Karan ma hakace ta kasance.A cikin subjects d'in da sukeyi aka ware 3 sciences subjects including English wanda a shine za'a Bada gifts d'in.Assembly ground d'in ya cika mak'il da students kowa ka kalla fuskarsa tana bayyanar da farin ciki Yana yin da yake ciki... SS 3A fannin Biology HUYAAM M BELLO itace over role student wacce making ta yafi na kowa a b'angaren biology take wajen nan ya kaure da tafi da ihu haka ana congratulations Huyaam m Bello.Huyaam ta fito cikin jin kunya har gaban assembly ta tsaya ta sunkuyar da kanta k'asa.sai a fannin physics kuma aka K'ira Huda M BELLO sai wata 'yar SS 3B itace tai over role a fanning chemistry wacce k'awar su Huyaam ce itama Mai suna jidda . A fannin English ma dai Huyaam ce dai still over role nan ga akai ta tafi ana mata congratulations. take a wajen aka hau yi musu pictures Had'i da malamai sannan aka basu gifts d'in bayan anyi raping d'insu D'aya text book ne aciki wanda a kai rapping d'insa Wanda zasu musu amfani daga nan har jami'a sai agogon bangon da graduation gown da aka Basu sai enlargement pictures da akai musu tun tuni Wanda ke d'auke da pictures d'in ko wanne students a cikinsu haka aka bawa kowa nasa sannan aka K'ara Yi musu pictures kowa rik'e da gifts d'insu bayan an gama akaiwa graduate d'in addu'ar samun kyakkyawan saka mako daga k'arshe akai addu'a gabad'aya students d'in aka sallamesu..tunda suka baro assembly ground d'in ikleema da safna suka karb'i gitfs d'in suna Gani sai kace su aka bawa gifts d'in nan dai sai Wani murna suke suna Taya su Huyaam murna Amma Banda Aziza data had'e Rai Dan ita ba'a Bata ba k'iras ya rage ta saki Kuka kai tama Yi a b'oye Bata bari bane sun Gani ba,suko su Huyaam Basu ma San tana Yi ba har aka zo d'aukar su Aziza Bata Bud'e Baki tai musu magana ba bare Kuma tai musu murna Sukuwa Basu damu ba saboda sun riga da sun San halinta.. Driver Yana yin parking bayan an Bud'e musu motar duk suka fito fuskokinsu d'auke da mad'aukakin farin ciki saboda yau Rana ce ta musamman agaresu da suka Dad'e suna fatan Gani .safna da ikleema sukaiwa su Huyaam Sallama Suma sukai musu sannan kowa ya wuce part d'insu farin ciki bayyane a saman afuskarsu, na suma sun zama graduate, Amma Banda Aziza da ta cika tai fam k'iris ya rage ta fashe saboda haushi. Aziza tana shiga part d'insu ko sallama batai ba su Ramlat suna zaune falon suna jiran dawowar Aziza su tayata murnar gama exam d'inta da kuma Murnar zama candidate da tai .ganin ta shigo falon yasa su walida duk suka mik'e sukai kanta suna K'iran sunanta tareda cewa. "congratulations ya Aziza".suka fad'a suna k'ok'arin zuwa su rungumeta fuskokinsu d'auke da murmushi,Bayin Allah Basu kula da yadda Aziza ta shigo falon ba.... Aziza data daka musu wata uwar tsawa muryarta na rawa Basu San lokacin da suka tsaya a inda suke ba kowa ya k'ame ya kasa motsawa kusa da ita .. Fulani Salamatu da itama da fuskarta take d'auke da farin cikin yau 'yarta ta zama candidate Amma sai fuskar ta Disha she ta maye gurbin farin ciki da damuwa ta tsaya tana kallan Aziza da Kuma tunanin Mai yasa meta haka da ita dai a saninta d'azu da safe da farin ciki Aziza ta bar gidan tana Murna tana komai Amma Shine yanzu Kuma ta dawo da b'acin Rai.fulani salamatu ta Mike ganin Aziza nata masifa ita kad'ai ta k'araso har gabanta ta kamo hannun Aziza ta zaunar ta kan kujera itama ta zauna kusa da ita tana kallanta tai k'asa da murya tace cikin lallashi... "Meyasa meki Aziza?....", ta fad'a tana kallan Aziza. Aziza ta fashe da Kukan da take son tayiwa Wani ko zataji dad'i tace cikin rawar murya. "Mummy su Huda aka bawa gifts tsabar san kai Amma ni ba'a bani ba"ta fada tana sheshshek'ar kuka. Fulani Salamatu ta dafata tace . "Ayina aka Basu gifts d'in?..." Aziza tace. "A school ne mummy". Fulani Salamatu tace . "Wai harda su ikleema aka bawa ne?.."Aziza ta girgiza mata kai tace. "A'a banda su iya su biyu kad'ai aka bawa".ta fad'a cikin b'acin Rai. Fulani Salamatu tab'e Baki kafin tace. "Ki kwantar da hankalinki indai gifts ne kema zaki mallakeshi ai Babu Wani abun da zasu mallaka Wanda ke baza ko iya mallaka ba, saboda ki kwantar da hankalinki Dan ambasu Wani gifts d'in da Bai taka Kara ya karua ba ,Dan dai wannan D'an abinda da aka Basu ki bari kema zan aika asiyo miki iri D'aya da nasu sak babu abinda zai ban banta. next week kuma by this day kema saiki had'a party ki gayyato su ki nuna musu duk su Gani su San cewa ba wata tsiyar aka Basu ba Wanda Wani bazai iya mallaka ba bare su d'auki kansu amatsayin Wani Abun kinji ai ko?...".ta fad'a tana kallan Aziza...Aziza ta gyad'a kai. Fulani Salamatu tace. "karki Wani sawa kanki Damuwa Aziza kinsan banason ganin ki cikin damuwa,ki kwantar da hankalinki Babu Wanda ya isa ya fiki a gidan nan". Aziz ta k'ara gyad'a mata kai .Fulani Salamatu tace. "yanzu dai ki tashi kije kiyi wanka idan kika huce ki sakarwa 'yan uwanki fuska Kinga tun d'azu suke Zaune suna zaman jiranki ne ki dawo Dan suyi miki murna". Ta fad'a tana murmushi. Aziza ta gyad'a mata kai ta kalli su Ramlat tace cikin dashashshiyar Murya. "Am sorry sister's". sai kuma ta mik'e ta haura sama zuwa d'akinta su walida suka bita da kallo fulani Salamatu Kuma ta Sauke numfashi tana Jin Wani Bak'in ciki na K'ara ruruwa aranta wato komai sai yaran nan sunfi