← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 85

Sashe 12

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gari wato Ranar Tuesday. Aranar kan suna da paper zasuyi second to the last paper itama ta safe ce Danma yau D'aya zasuyi ba biyu ba,Dan haka da wuri suka Tashi sukai shiri suka tafi makaranta.basu suka dawo ba sai wajen k'arfe biyu da Rabi na Rana Shima suna dawowa sukai shirin islamiya k'arfe uku da 'yan mintuna Kuma suka tafi..... Ranar Wednesday Basu da paper sai ranar Friday itace last paper kenan aranar kuma zasuyi candy.da yamman Ranar su Huda suka shirya ya haidar zai kaisu suyi siyayyar kayan graduation d'in da zasuyi Mai martaba ne da kansa yace akaisu kowa ya zab'i abinda yake so duka su biyar d'in harsu ikleema tunda dama sune zasuyi graduation d'in a duka gidan ,Shine a matsayin gift d'in Da Mai martaba zai Basu . kuma ko Wacce dama uwarta tayi mata gift na graduation . itama Ammie tayiwa su Huyaam d'in Kuna musu bala'in tsada kala hur hud'u less da atamfa.dama tun jiya su Huda suka fad'awa su ikleema akan cewa yau za'a kaisu shopping....yanzu haka k'arfe biyar ne Saura na yamman ranar su ikleema already sun fito daga part d'insu suna tsaye nan harabar gidan itada safna ko Wacce cikin shiri sunyi kyau ba kad'an ba suna tsaye suna k'ok'arin zuwa part d'in su Huyaam Aziza ta fito daga part d'insu ta k'araso har wurinsu tana kallansu tace. "Ina su ishashshu mulkakku Daman suke basu fito ba koh?..."Ta fad'a tana kallon hanyar part d'in su Huyaam. ikleema ta Kalli Aziza wacce ta Wani had'e Rai tace . "Haba Aziza Dan Allah ki daina abinda kikeyi Babu Dad'i,yanzu me zaisa ki Fad'i Irin wannan maganar yanzu idan agabansu kikayi fa? Ai kema kinsan fad'a kika takalo ko?..."Aziza zatai magana ya Haidar ya fito daga part d'insu sanye yake cikin shigar k'ana nun kaya Wanda sukai masa bala'in kyau sai baza k'amshi yake hannunsa Kuma rik'e da key d'in motarsa su Huyaam Kuma suna bayansa .tun daga nesa Aziza take kallansu Huyaam Ganin yadda sukai bala'in kyau ba kad'an .gabad'ayansu sanye suke cikin shigar doguwar rigar abaya maroon color wacce ta fito da ainihin kyansu sai Wani d'aukar ido kayan suke saboda duwatsun da akai adon rigunan dasu sai kawo haske suke ta ko Ina.Ai take Aziza ta d'auke kanta tare da tsuke fuska ta Maida gefe ganin yadda kallo ya koma kansu HUYAAM Dan hadiman gidan nan sai kallansu suke suna musu kirari,har suka k'araso wajen motar. ya haidar ya danna remote d'in Dake jikin key d'in motar take motar ta Bud'e da Kanta ganin haka yasa Aziza tai saurin shiga can bayan motar Dan Bata so ma su hadu dasu HUYAAM bare tai musu magana, ikleema da safna suka shiga suma suka zauna kan seat d'in Dake gaban Aziza su Huyaam ne suka karaso Suma suka shiga inda su ikleema ke zaune HUYAAM ce k'arshen shiga tana Zaune daga bakin murfin motar. Ya haidar ya juyo Yana kallansu fuska d'aure yace. "Nine driver ku da duk zaku shige baya?wa kuka barwa front seat d'in?...". Sukai shiru basuyi magana ba suna sunkuyar da kai k'asa.yace. "ba magana nake muku ba?..."ya fad'a a D'an tsawace. Huda ce tai k'arfin halin kallan Huyaam Wacce ta tura Baki gaba tai k'asa da murya tace. "Kije tunda kece a farko HUYAAM"...HUYAAM ta d'ago zata harari Huda sukai ido hud'u da ya haidar Wanda shima kallanta yake yay mata Wani kallo take ta Bud'e Murfin motar ta fito daga wajen ta koma gaba ta zauna tana K'ara tura Baki gaba .ya haidar ya juya ya ta-da motar suka fice daga gidan bayan an wangale musu gate fadawan nan sai kirari suke musu. Awani K'aton mall Wanda ake ji dashi a garin kano ya haidar yay parking motar ya fito Suma suka fito ya rufe motarsa yay gaba suka bishi a Baya Huda da ikleema sune a gaba sun jera suna tafiya Huyaam kuma da safna wacce ke ke tai mata surutu itadai sai dai ta bita da uhmm ko a'a sai Aziza wacce ta ware kanta ita kad'ai tana tafiya cikin Isa da tak'ama sai Wani Shan k'amshi take .tun kafin su shiga cikin Mall d'in nan kallo ya koma kansu saboda Babu k'arya ko Wacce tayi kyau Kuma keda kin gansu kinsan hutu Had'i da Jin Dad'i sun samu muhalli ajikinsu.Ahaka suka shiga cikin Mall d'in ya haidar ya Kallesu bayan sun shiga yace. "kuje ku zab'i duk abinda kuke so".yana fad'ar haka samu waje ya zauna ya zaro wayarsa. ikleema da Huda suka tafi wajen trollories d'in Dan d'aukar musu.D'aya ikleema da safnah Huda Kuma ta d'aukar musu itada HUYAAM Aziza kuwa dama sun San halinta itama haka ta K'arasa ta d'auki nata trolling tai nata wurin HUYAAM ta k'araso kusa da ya haidar tai k'asa da murya tace. "Yaya! ya ka zauna Kuma?..." Ta fad'a tana tura Baki gaba. Batare da ya haidar ya d'ago ba Yana duba wayarsa yace. "Da kukai Sa'a ma na rakoku shine kike tambayar ya na zauna ko? to ki zauna tambayata Karki bisu kuyi abinda zakuyi nidai ina gajiya tafiya ta Zanyi "ya fad'a Yana cigaba da kallan wayarsa. HUYAAM ta tab'e Baki tabi bayan su Huda. B'angaren dogayen riguna suka fara zuwa nan suka fara zab'a kowa biyu biyu kafin su d'auki Wasu iri D'aya Guda biyar suka ce anko zasuyi gabad'ayansu .duka su biyar d'in harda Aziza suka d'aukawa da tai nata wurin,daga wajen dogayen riguna Kuma wajen hands bag da takalma suka nufa nanma kowa ya d'auki biyu biyu sai Kuma sukai wajen cosmetics suka d'auki turaruka masu bala'in kyau da tsada da kayan kwalliya,bayan sun gama da nan Kuma sai sukai wajen kayan graduation d'in da zasu d'auka nan ma dai sun d'auki abubuwa sosai daga nan Kuma sukai wajen payments. A cikin Mall d'in nan inbanda Kallansu Babu abinda akeyi ganin sun gama yasa ya haidar ya mik'e ya karasa wajen payments d'in shima bayan anyi counting kud'in ya Mik'a musu card d'insa suka cire kud'in sannan aka zuba musu cikin Manyan bags ma'aikatan wajen suka rakosu dashi har boots ya haidar ya Bud'e musu suka sa kayan ya zaga driver seat ya shiga ganin su Huda har sun shiga ya ta-da motar suka nufi palace. K'arfe shida Saura suka shiga palace bayan ya haidar yay parking motar nan harabar gidan ya Bud'e musu boots kowa ya d'auki ledarsa Dan dama tun a wajen payments aka sawa kowa nata unlike su Huyaam da nasu ke had'e sai bayan kowa ya d'auki ledarsa Sukai wa ya Haidar godiya kowa ya nufi part d'insu bayan sunyiwa juna sallama.Amma Banda Aziza data Saka kayan a gaba tana K'iran Wani dogari Mai suna bala akan yazo ya kai mata nata kayan b'angarensu. Gabad'aya su ikleema sai da suka juya suna kallan Aziza saboda mamakin abinda tai, Amma sai basuyi magana ba Suka juya suka cigaba da tafiya ganin ya haidar ya juya Yana kallanta alamar zai mata magana suko su Huyaam tuni sun shige part d'insu. Ya haidar Yana kallan Aziza da bala yazo ya zube agabanta cikin rawar jiki Yana cewa. "Gani ranki Dad'e" ya fad'a cikin girmamawa. Aziza ta juya masa ido tace. "Kayan nan zaka biyoni dasu". tana fad'ar haka ta juya zatai gaba ya haidar ya k'ira sunan bala da k'arfi wanda ya juyo da sauri Yana zare ido ya haidar yace. "Kai bala karka sake ka d'auki kayannan idan ba zata iya d'auka ba ta barshi " ya fad'a Yana kallan Aziza data juyo da sauri tana kallansa Jin abinda ya fad'a. Aziza ta Marai raice tace. "Yaya haidar da nauyi fa kayan,Dan Allah ka barshi ya tayani d'auka mana".ta fad'a kamar zatai kuka. Ya haidar yay mata Wani kallo yace. "Su sauran 'yan uwanki da suka d'auki nasu kayan kin fisu ne? ba Kai D'aya kuka Siyo ba nawa kayan yake da Dan Rashin tausayi zakisa mutumin Daya kusan haifarki d'aukar miki kaya?..." ya fad'a atsawa ce.sai Kuma ya juya Yana kallan bala Daya k'asa tafiya yace. "Bala ko baza ka tafi bane?..." Bala ya mik'e da sauri yace. "A'a rankai Dad'e wane ni,Allah ya huci Zuciyarka".Yana fad'ar haka ya tashi ya bar wajen.Aziza ta fashe da Kuka ta d'auki kayan tai part d'insu tana rusa uban kuka kamar wacce akayiwa Wani mugun abu.ya haidar yay tsaki yabi bayan su HUYAAM...... 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__* *__(MRS SARAKIES )__* *PAID BOOK *FREE PAGES* *Tallah! Tallah!! Tallah!!!* *Ina kuke hajiyoyin gidan nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zo muku har inda kuke *Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma akanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka *Atamfofi da lesses* *Abaya* *Shadda* *Hand bag* *Shoe* *Veil na manya Dana Yara* *Socks rin hands made d'in nan masu net*. *Hula ta 'yan Gayu* *Siyan D'aya ko sari* *Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki* *Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka* 08135305790 *Sai mun jiku *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 1 __________ Da kuka Aziza ta k'arasa b'angaren su.Ramla da walida ta rara a falon suna Zauna suna kallo Baki Bud'e suka bi Aziza da kallo ganin yadda ta shigo cikin falon tana zunduma uban kuka kamar wacce akayiwa Wani mugun abu.tun daga sama Fulani Salamatu Dake cikin d'akinta ta d'auro alwala ta fito daga toilet kenan zata ta-da sallah tajiyo kamar kuka d'aukarta ma ko walida ce yasa babu shiri ta fito daga d'akinta cikin tashin hankali ta sauko downstairs. Mamaki ne ya kamata ganin yadda Aziza take kuka ta k'araso Gaban Aziza tana kallanta tai k'asa da murya tace. "Aziza meyasa meki kike wannan uban kukan haka? Ina daga shopping kuke?...."ta fad'a Tana kallan Aziza tare da k'arewa falon kallo da mamaki. Aziza da tun shigowarta ta dire kayan nan kan tiles tana
Chapter 12 · 0% Book details