← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 85

Sashe 14

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'yarta tai tsaki tana Jin zuciyarta na mata zafi..... Suko su ikleema Koda suka shiga b'angaren su murna suke tayi har ikleema take bawa mamansu labarin gifts d'in da aka bawa su Huyaam.bud'ar bakin Hajiya Lubabatu sai cewa tai. "Dalla rufe min Baki ke baza kiyiwa kanki fad'a ba kiyi Karatun da kema za'a Baki gifts d'in saidai kizo kina Bada labarin yadda aka bawa wasu". Ta fad'a cikin Jin haushin itama Dan itama ta tsani ace komai 'ya'yan Ammei ne akan gaba . Jikin ikleema Yay sanyi ta tashi ta bar wajen ta shige D'aki tana mamakin halin maman nasu. Ita ko safna data fad'awa umminsu Hajiya Aysha itakan murna ta Tayasu tace zata k'ira Ammie ma tai mata murna...... 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *PAID BOOK *FREE PAGES* *NA* *__(MRS SARAKIES )__* *Littafin HUYAAM littafin kud'ine so please get ready to start payment Dan Free pages would be end soon* *So Karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku masoya *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 1 ____________ Da sallama a bakinsu su HUYAAM suka shiga falon su. Koda suka shiga ciki gabad'aya suka tadda su ya Zarah a falon da muneefa sai muneeb zaune kan kujera da dukan alamu suma zaman jiran dawowar tasu suke yi. Da gudu muneefa ta taso daga zaunan da take ta nufesu, Huyaam ta fara rumgumewa tana Murmushi da cewa. "congratulations ya HUYAAM".ta fad'a tana fad'a murmushi....HUYAAM ta rumgumeta itama tana cewa . "Thank you so much Auta".kafin ta saki muneefa .nan muneefa ta k'arasa ta rumgume Huda tana Murmushi da cewa . "Congratulations ya Huda". Ta fad'a tana k'an k'ame Huda. Huda tai murmushi itama tace "Thank you muneefa".ta fad'a tana shafa kanta Kafin su saki juna.Nan muneeb shima yay musu congratulations Yana zaune kan kujera.huda ta ansa masa Huyaam kan da sauri ta k'arasa wajen ya Zarah Dake mata murmushi ta zauna kusa da ita tace . "Ya zarah yau Dai Allah ya cikamun burina na zama candidate". Ta fad'a tana k'an k'ame ya Zarah cikin farin ciki. Ya zarah tai murmushi itama ta rumgume Huyaam tace . "Congratulations sis Allah ya Baku good results". ta fad'a tana murmushi.huyaam ta rik'o hannunta tace . "Thanks you so much big sis kafin ta mik'e tsaye daga kusa da ya Zarah tana tattare gifts d'in data zubar a falon. Ammie ce ta sauko downstairs jin hayaniyar yaran. Huyaam tana tsaye da gifts d'in da aka Basu zata je d'akin Ammie ta nuna mata kuma sai ga Ammie ta shigo falon da sallama abakinta tana kallansu, ai tuni HUYAAM ta zube kayan hannunta nan k'asan falon ta nufi Ammie ta rungumeta tana cewa. "Alhamdulillah ya Allah, yau dai mun zama candidate Ammie". Ta fad'a tana Wani k'an k'ame Ammie. Huda ma ta taho da gudu ta rumgume Ammie tana dariyar farin ciki tace . "Ammie munyi graduation yau". ta fad'a tana murmushi haka suka rungume Ammie kamar zasu kada ta suna murna.Ammie tai murmushi ta had'a hannayenta duka biyun ta rumgumosu jikinta kafin tace. "Alhamdulillah ya Allah, Allah mungode maka daka nuna mana wannan ranar,I congratulate you once again daughters wishing you good results". Ta fad'a tana murmushi. Gabad'aya suka had'a Baki wajen cewa Ameen.ya Zarah dai kallan su take tana murmushi haka su muneefa.Ammie ta rik'o hannunsu suka dawo cikin falon kafin ta saki hannun nasu ta zauna nan kan kujera sukuma suka d'auko gifts d'in da aka Basu da wata envelope Wadda ke d'auke da certificate d'insu aciki suka nunawa Ammie da cewa gifts d'in da aka Basu ne a school .Nan Ammie ta karb'a tana Gani tare fa tayasu murna Sosai.su ya Zarah suma duk suka Karb'a Suna Gani tare da Yi musu fatan alkhairi. Ammie ta dube su tace. "To Kuje kuyi wanka ku sauya kaya sannan ku tafi da gifts d'in ku ajiye idan Mai martaba ya shigo anjima saiku nuna masa". ta fad'a tana kallanasu. Suka ansa mata da girmamawa sannan suka kwashi kayan sukai sama zuwa d'akinsu dashi. Da daddare Mai martaba yana d'akinsa Yana shiryawa su Huyaam suka shigo falonsa bakinsu d'auke da sallama. Babu kowa a falon sai k'arar AC da fan.Dan haka suka k'araso cikin falon suka zauna nan k'asan carpet d'in falon suna zama jiransa Dan k'ila daki ya shiga.babu dad'ewa kuwa Mai martaba ya fito cikin shigar manyan kaya sai Hirami Daya yafa a kansa Irin shigar sarauta dai yayi ,bakinsa d'auki da sallama ya k'araso cikin falon Yana kallansu. Su Huyaam Dake zaune nan k'asan carpet d'in falon batare da sun d'ago da kansu ba suka ansa masa kansu a K'asa.mai martaba ya samu waje a inda yake zama ya Zauna Yana kallansu suka had'a Baki wajen gaida shi.mai martaba ya ansa musu da kulawa. Huyaam tana Murmushi tace. "Abba yau dai munyi final papper mun zama candidate"ta fad'a tana murmushi. Mai martaba ya Kallesu ganin yadda fuskokinsu ke d'auke da farin ciki ya Jin Jina kai Yana sakin murmushin shima yace. "Masha Allah i congratulate you dears Allah yasa albarka". Fuskarsa na bayyanar da farin ciki shima..suka had'a Baki wajen cewa Ameen,nan suka Mik'a masa gifts d'in da aka Basu suka ajiye anan gabansa HUYAAM tace . "Abba ga gifts d'in da aka Bamu a school for the best students of the year". Ta fad'a tana murmushi. Mai martaba yace . "Masha Allah yaran kirki congratulations once again". ya fad'a yana d'aukar gifts d'in da suka ajiye anan gabansa yana Gani D'aya bayan D'aya. Bayan ya gama ya d'ago Yana kallansu yace . "I really appreciate daughters Allah ya Bada good results". Ya fad'a for happiness.suka had'a Baki wajen ansa masa.Nan dai sukai ta ta hira tareda da Mai martaba daga k'arshe dai Ya K'ara congratulations d'insu tareda Yi musu nisaha. Su kuma suna sauraransa ,Basu Dad'e a falon ba sukai masa sallama suka tafi Mai martaba ya bisu da kallo Yana Jin k'aunar yaran nasa na k'aruwa acikin zuciyarsa .dama acikinsu su ukun nan Huyaam da Huda suna da k'ok'ari sosai yadda ya kamata Amma Banda Aziza,d'azu fa da yaje b'angaren fulani Salamatu danyi mata sallama da Kuma duba yaran kafin ya shigo b'angaren Ammie Dan Kwanan tane har ya gama abinda zaiyi Amma baiga Aziza ta bashi Wani gifts da sunan ambata a school ba ,iya ka kawai data ce masa Abba munyi graduation yay mata Allah ya Sanya alkhairi kuma harya ya fito baiga Wani Abu Mai kama da gifts ba yoda ace ma ambata aida uwar tace zata fara fad'a masa saboda yasan halinta da fariya.kuma dama can yasan Aziza Bata da k'ok'ari huda da Huyaam ne kawai masu k'ok'ari Dan kan Aziza Kamar dusa haka yake Bai tab'a ganin ambawa Aziza Wani special Abu ba wai Dan tana da k'ok'ari a school ba ,kullum sai dai a bawa su HUYAAM yadda ya fahimci Aziza Bata da aiki sai shegen girman Kai da buri Irin na uwarta ya sauke numfashi Yana amsa sallamar Ammie data shigo falon....... ____________ Washe har k'arfe Sha biyu Saura Huyaam Bata tashi daga bacci ba. itakan Huda tun K'arfe goma ta shi tai wanka ta fito Dan ita Bata Saba bacci Irin na Huyaam ba Wanda yake kamar na mutuwa tai tayi bata tab'a gajiya.dayake basuda islamiya yau Babar shugaban makarantar tasu ce ta rasu shiyasa aka Basu hutun one week kafin su koma .ganin haka yasa Ammie da Taga kowa ya tashi Amma Banda HUYAAM yasa tace tunda babu inda zasu yau a k'yaleta ta huta saboda karatun da suka Sha na exam.... k'arfe Sha biyu da kwata HUYAAM ta shi bakinta d'auke da addu'ar bacci tana Mik'a ta sauko daga saman gadon ta nufi toilet zatai wanka.babu dad'ewa ta fito ta k'arasa gaban mirror ta fara Shafa lotion d'inta masu dad'in kamshi da tsada bayan ta gama ta nufi wardrobe d'inta ta d'auko wato doguwar rigar abaya blue black Mai tsadar gaske wacce ta fito da ainihin kyanta ta k'arasa gaban mirror ta yafa mayafin a saman kanta fuskarta ta fito tayi kyau sosai ba kad'an ba,duk da bama Wani make up tai ba Amma ba k'aramin kyau tai ba ta shafa lips bolm a lips d'inta sannan ta feshe jikinta da turaruka masu Dad'in k'amshi sannan ta fito daga d'akin bayan ta jawo k'ofar ta rufe, d'akin Ammie ta lek'a taga Bata ciki ta rufe k'ofar ta sauko k'asa... Da sallama ta sauko downstairs d'in ta Tarar da gabad'ayansu suna zaune a falon ga TV a kunne. Ammie tana zaune kan kujera 3 seater muneefa na kwance kusa da ita ta d'aura kanta saman cinyar Ammie ,sai muneeb Dake zaune k'asan carfet Yana rubutu acikin littafinsa da dukan alamu assignment yakeyi sai ya Zarah kuma Dake zaune itama kan kujera one seater tana latsa wayarta da dukan alamu chatting takeyi , Huda Kuma tana zaune tana kallo... gabad'aya suka juya suna ansa sallamarta tareda kallonta lokacin D'aya. HUYAAM ta saki murmushi ta k'arasa wajen Ammie ta zauna kan kujerar da Ammie take zaune ta gefenta ta D'ora kanta saman kafad'ar Ammie tana cewa. "barka da safiya Ammie". Ta fad'a tana lumshe idonta.Ammie ta kalleta ta gefen ido tace. "Awurinki ne haryanzu safiya koh? Yanzu fa past 12 ai Rana tayi HUYAAM Safiya kuma ai saita gobe idan Allah ya kaimu". ta fad'a tana shafa kan muneefa.HUYAAM tai murmushi ta d'aga Idonta tana duba rantsatstsan agogon bangon Dake falon kafin ta rik'e Baki tana kallon Ammie da mamaki tace. "Wallahi Ammie I think yanzu baifi 12 Saura ba fa?.." Ammie tace. "dama kina can kin samu abinda kikeso bacci Ina zaki San time ya tafi?. HUYAAM tai murmushi tana D'ora kanta saman kafad'ar Ammie Amma Batace komai ba. Ammie tace. "Oya tashi kije kiyi breakfast time na tafiya". Huyaam ta mik'e zata nufi dining d'in muneefa ta kalleta tace. "Ya HUYAAM kinyi kyau" ta fad'a tana murmushi.huyaam tai mata fari da ido tace. "nagode sis". Ammie ta kalleta ta girgiza kai tana murmushi halin Huyaam sai ita .har Huyaam ta nufi hanyar dining sai Kuma tsaya a inda take tsaye tana kallon ya Zarah tace. "Ya zarah barka da Rana."ta fad'a tana murmushi. Ya zarah ta d'ago da kanta daga latsa wayarta da take tana kallan Huyaam tace. "Sannu maji Dad'in kano Wato sai yanzu kika ga
Chapter 14 · 0% Book details