← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 85

Sashe 76

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

k'ofar falon b'angaren, k'ofar ta tab'a taji a Bud'e take Hannu tasa ta Bud'e a hankali yadda k'ofar bazatai K'ara ba ta shiga ahankali cikin sand'a take tafiyar harta shigo tsakiyar main falorn gidan.kalle kalle ta farayi ganin Babu kowa sai k'arar AC data fan yasa ta nufi stairs d'in da zai SADA ta da b'angaren gimbiya Aysha ta haura da sauri cikin sand'a tana waige waige harta gama haurawa gabad'aya.a corridor ta tsaya tana Sauke numfashi kafin ta nufi inda d'akin gimbiya Aysha yake .tana Isa ta Tsaya a bakin k'ofar ta kasa shiga tana waige waige.tafi mintuna biyar a bakin k'ofar ta kasa shiga kafin ta iya tab'a k'ofar ta sa hannu ta Bud'e a Hankali datai Sa'a ma k'ofar ba'a rufe take ba saboda Wani lokacin Hajiya inna tana shigowa duba gimbiya Aysha lokaci lokaci acikin dare, shiyasa yauma Anty Amina Bata rufe k'ofar ba.Ahankali shakundum ta shiga Bud'e k'ofar ta yadda bazatai K'ara ba harta gama bud'ewa gabad'aya. Nan ta fara lek'awa cikin d'akin.babu haske a d'akin sai dumb light blue Wanda baida haske sosai nan ta hango iya gimbiya Aysha ce kwance saman gadon sai Anam a D'aya gadon Anty Amina Kuma Bata nan. k'arar ruwa da shakundum taji a toilet yasa ta Gane Anty Amina ce aciki cikin sauri ta shiga d'akin gadan gadan kan gadon gimbiya Aysha ta nufa Babu Bat'a lokaci ta fito da wani Abu ta watsa mata a fuskarta da duka jikinta gabad'aya .take gimbiya Aysha ta Bud'e ido jin Wani Irin zafi ya ratsa ta, tana kallan shakundum Bata ko kiftawa, kafin ta farga daga zafin daya ratsa ta tuni shakundum ta haye saman gadon ta d'agota ta zuwa jikinta nan ta fito da layar da tazo da ita zata cusa mata a cikin Bakinta. adai dai lokacin da Anty Amina ta Bud'e k'ofar toilet d'in ta fito.taku D'aya tai taji wani Irin nishi da K'aka Kari Had'i da kamar kokawa na tashi a Cikin d'akin nan da nan gaban ta ya yanke ya Fad'i ta d'aga kanta ta fara dube_dube a d'akin nan ta hango mutum ne a saman gadon gimbiya Aysha tana k'ok'arin cusawa gimbiya Aysha Abu a Baki,ai da Wani Irin speed ta nufi gadon tasa K'ara cikin kid'imewa tana cewa waye? shakundum da tayi nisa a San cimma burinta har Batama son lokacin da aka Bud'e k'ofar toilet d'in ba sai K'ara taji, cikin rud'ewa ta sauko daga saman gadon fuskarta a rufe da Wani Bak'in Abu da bama ka iya ganin komai sai k'waryar idonta.ganin Anty Amina ta nufo gunta zata kamata yasa ta nufi k'ofar fita a Wani mugun speed.da gudu Anty Amina tabi bayanta ganin tana k'ok'arin fita ta shak'o wuyan ta baya. Sha kundum ta rik'e hannun Anty Amina Dake wuyanta na ganin Anty Amina na k'ok'arin yage mata abinda ta rufe fuskarta dashi.nan dai suka fita daga d'akin Anty Amina na ihun a tai Maka musu, shakundum Kuma nata k'ok'arin k'wace kanta Dan kada Azo a kamata.Anty Amina kuwa tak'i sakinta saima Kara shak'eta da take tamau. nan Shakundum ta shiga kokawa da Anty Amina ita ko ta rik'eta gam tak'i sakinta tana cewa azo a taimaka mata ga Wani ya shigo musu d'aki .adai lokacin da Hajiya inna ta hauro stairs d'in tana tambayar meya faruwa cikin tashin hankali Jin hayaniyar tak'i k'arewa, kawai taga yadda mutum yay shigar b'adda kama baka gane shin macene ko namiji. ai shakundum ma ganin Hajiya inna ta zo ta kuma tasan tsaf zasu had'u su kamata kar asirin ta ya tonu, tuni tai k'ok'arin d'aga hannunta ta bugawa Anty Amina guiwar hannun a gefen cikin ta, Babu shiri Anty Amina ta saketa da sauri jin wata iriyar azaba ta saukar mata nan ta fad'i a k'asa.shakundum tai hanyar stairs d'in da gudu zata sauka Hajiya inna ta ruk'ota Aiko nan ma shakundum ta juyo ta hankad'a Hajiya inna nan itama ta fad'i ta baje a k'asa har tana buguwa da k'arfen stairs d'in. ganin duk ta gama dasu Babu mai iya tashi ya biyota acikinsu yasa ita Kuma ta fara saukowa stairs d'in cikin sauri sauri har tana had'awa da gudu _gudu.ganin guduwa fa zatai yasa Hajiya inna ta mik'e da k'yar Jiri na d'ibanta tabi bayanta tana ihun a taimaka musu ga wani yashigo musu b'angare a kama shi.mik'ewa Anty Amina itama tai tabi bayan Hajiya inna suka sauko stairs d'in. Nan suka tadda har shakundum ta kusan fita daga falon gabad'aya. adai dai da Wani dogarin ya farka agigice Jin ihun su Hajiya Inna nan shima ya yashigo falon sukai kicib'us da shakundum Dake k'ok'arin fita daga falon.Hajiya Inna ta ce cikin ihu "ka kama shi gashi nan zai fita" ganin wadda yaga Hajiya ita na nunawa tana ihun cewa ya kama shi yasa ya fisgota da k'arfi Hajiya inna ta ce "yauwa lurwanu Maza rik'e mana ko waye da k'arfi karya k'wace...... *End book one* K'arshen littafi na D'aya.bazance komai akan rayuwar gidajen sarautar nan guda biyu ba. Amma ke daga Jin tafiyar labarin Kin san yanzu aka fara ta. Amma bari na Dan Baku tsokaci kad'an daga ciki. *Tofa masu karatu Mai ke Shirin faruwa ne?shin wacece Huyaam acikin masarautar kano? shin da Gaske ne Huyaam ba 'yar gidan bace ma'ana ba Ammie da Mai martaba ne suka haifeta ba kamar yadda fulani Salamatu tazo tai baran bararma ta fad'a ko ya ya abun yake ??* *Mai Cece makomar Huyaam a gidan idan Hakan ta kasance?* *shin Wani Hali Ammie zata shiga?* *Wani mataki Mai martaba zai d'auka akan Fulani Salamatu?* *Shin yaya soyayyar HUYAAM da AZIZ CHIROMA da Kuma ABDALLAH SHATTIMA harma da LAMID'O duk da dai shi har yanzu ta bayan fage yake Bai fito ya bayyana mata kansa ba kamar yadda Sauran sukayi BA? Shin acikinsu waye zai iyi samun soyayyar Huyaam harma ya samu nasarar auren ta?* *Shin burin Hajiya Lubabatu zai cika na ganin Salima ta auri Afeef ko Kuma bazai cika ba*? *Shin burin Fulani Salamatu zai cika na ganin ta aurawa Aziza Wanda take cewa zata had'a ta dashi ko bazai yuba*? *Mai zai faru idan akaje Egypt*? *Shin asirin shakundum na tunowa ko bazai tonu ba*? *Shin gimbiya Aysha da sultan zasu samu lafiya ko Kuma baza su samu ba* *Shin ya labarin jaririyar gimbiya Ayush da Sha kundum ta sace ta, da Gaske ta mutum ko Kuma tana raye? shin Idan tana raye ayina take rayuwar,shin zasu had'u da iyayenta gimbiya Aysha da Mai martaba sarkin masarautar zazzau ko Kuma basa had'uwa? *Suwaye Razik'a da maina? Duka amsoshin wannan tambayar suna cikin littafin HUYAAM book 2. 'yan uwa karku bari ayi wannan tafiyar Babu. Kamar yadda na fad'a muku Littafin HUYAAM na kud'i ne a man hajar WhatsApp regular group akan naira 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in 2270127432 Naja'atu umar zenith bank Evidence of payment 07066508376 *Yan Niger _zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA 07066508376 Alhamdulillah! Anan na kawo k'arshen Free pages na littafin HUYAAM book one.Book 2 Kuma na kud'i ne. akan naira dariyar 700 kacal. Amma akwai discounts ga Wanda suka fara biya zasu Bada naira dari biyar kacal daga yanzu zuwa ranar da zamu cigaba da paid book idan ya wuce Kuma Zaku biya normal price wato 700. Ga masu bukatar magana da Marrbuyar Kuma zakuyi tun tubarta kai tsaye ta wannan number 07066508376. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ __* *__(MRS SARAKIES )__* *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 4 _____________ Tun bayan dasu HUYAAM suka kai Anty khadija airport suka dawo gida har yau kimanin sati d'aya kenan Afeef baiyiwa Huyaam maganar komai ba Daya dangin wai ya ganta da Aziz ko Kuma yay mata tambayar Mai yasa ya gansu tare shi.ko kad'an ko da wasa Bai mata Hakan ba, tun tana b'oyewa idan ta ganshi tana 'yar wasan b'uya dashi na karsu had'u har ta dawo da daina ta saki jikinta ta cigaba da sabgoginta ganin shi ko kallo ma Bata ishe shi ba, tun tana tunanin wata rana zai iya Mata maganar har ta dawo ta daina Damuwa da hakan ta cigaba da harkokin ta a gidan harma watarana su zauna tare dashi a main falon gidan ya gama zamansa ya tashi batareda da ya nuna mata alamar wai Yana rik'e da ita ba.Hakan yasa itama ta manta da zancen..A b'angarenta da Aziz chiroma kuwa tun tana basar dashi idan ya K'irata a waya har ta dawo tana picking call d'insa.yay ta janta da hira Wani lokacin ta tanka masa Wani lokacin kuwa tai Banza dashi ta k'yaleshi har ya gaji Dan kansa ya k'yaleta. daga baya Kuma abinda ta Gane idan tak'i tankasan Huda yake k'ira ya fadawa ya rok'e ta akan tazo ta rok'ar masa Huyaam ta dinga kula shi.to ita Kuma Huda idan taji haka saita ce masa karya Damu zata shawo masa kan Huyaam, haka zata to tai ta rok'ar Huyaam dayi mata rik'o da magiya da nasihu kala kala akan ta dinga kula Aziz ko yaya yane tana sakar masa fuska. tun Huyaam Bata sauran ta yau da gobe har ta dawo take sauraran Huda, ta yadda take D'an Kulashi sama sama harma ta dinga D'an bashi ansa a hirar da sukeyi. tun Huyaam Bata saki jikinta dashi ba harta dawo ta fara saki suke hira abinsu.to tun daga wannan Wani al'amari ya fara d'arsuwa azuciyar Huyaam game da AZIZ bawai taji tana sonshi bane sannan Kuma bawai Bata son shi ba, Haka dai take Jinsa a zuciyar ta a Wani sashe na Daban inda da Bata bashi wannan matsayin ba.ga wata iriyar shak'uwa da suka fara Yi ita dashi har mamakin kanta take Wani lokacin... tsakaninta da Abdallah shattima ma kuwa Shima dai kamar yadda take Jin Aziz haka Shima take Jinsa.sai dai har a zaciyarta bawai sonsu take ba kawai dai ta d'auke su ne matsayin masu Bata kuluwa da Kuma da d'ad'an maganganu da suke Yi a gareta.... Yanzu haka Zaune take a d'aki saman gadon ta wajen k'arfe 12 da Rabi ne na Rana. gama wayar su kenan da Aziz
Chapter 76 · 0% Book details