← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 85

Sashe 8

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya Zarah. ya Zarah tai Murmushi tace. "eh mama tafiya zamuyi" .ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa tsaye. Hajiya Lubabatu Tace . "To nagode Ku gaida fulanin idan kun koma" Suka ce in Sha Allah zataji daga haka suka nufi k'ofar fita daga falon Hajiya Lubabatu tabisu da kallo tana tab'e Baki kafin ta Mik'e itama tabar falon.....Har k'ofar part d'in ikleema ta rakosu tai musu rakiya bayan ta rakosu ta koma ciki. Daga b'angaren su ikleema part d'in antynmu su ikleema suka nufa .wato kishiyar hajiya Lubabatu Mai suna Hajiya hauwa itakan 'ya'yanta biyu mace da namiji ,namijin shine Babba Mai suna sayyid Sa'an muneeb ne sai macen Kuma maybe suna husna itace autar ta ita kuma sa'ar muneefa ce bayan sun shiga sun sameta a falon tana zaune tareda da yaranta .ta karb'e su cikin mutuntawa tana Basu wurin zama,bayan sun zauna kan kujerun falon suka gaida ta,ta ansa tana tambayar su Ammie sukace tana lafiya,daga haka Kuma falon yay shuri Babu me magana acikinsu.nanma dai Basu fi mintuna biyar ba saukai mata sallama suka tafi. Daga b'angaren Hajiya hauwa b'angaren Baba wambai suka nufa wato b'angaren su safnah. shi kan matarsa D'aya Hajiya Aysha itakan tana Sansu sosai tunda k'awar Ammie ce kaf gidan itace suke mutunci da Ammie, take Kuma zaune da Ammie da zuciya D'aya.ita kan 'ya'yanta hud'u.babban d'anta namiji ne Mai suna Bello Amma ana ce masa lamid'o Saboda sunan Marigayi Mai martaba Wanda ya rasu yaci ,shekararsa 28 Dan yafi ya haidar,baya nan Yana Lagos Yana Aiki a componing Mai martaba Dan shike kula Dana can sai zulaihat yayar safna Mai shekara 25 sa'ar bahijja ce sai namiji D'aya sannan sai safnah sai autarta Aneesa....basu tadda kowa a falon ba sai safna da Anisa ya zulaihat Batanan taje unguwa.da murmushi a fuskar safna ta ansa musu sallamar su ta taso ta rumgume Huyaam da Huda bayan ta gaida ya Zarah tana kallan Huyaam ta rik'e baki tace. "Uhmm! wato jiki ya ware koh? shiyasa akaci wannan gayun kenan?..." Ta fad'a tana murmushi. HUYAAM ta Maida mata da Martanin murmushin Amma bataci komai ba suka k'arasa har cikin falon suka zauna suna zama Hajiya Aysha wacce suke K'iranta da ummi ta fito daga kitchen tana kallansu tai murmushi tace. "A'a!! kuce yaran Ammie ne agidan kenan?...." ta fad'a tana k'arasowa har cikin falon ta zauna kan kujera . Sukai murmushi dukansu kafin su had'a baki wajen cewa. "Ummi Ina yini" ummi ta ansa musu har lokacin murmushi Bai gushe Daga saman fuskarta ba.tana kallansu tace. "Lafiya lau Alhamdulillah Ina Ammie?...."sukace lafiyanta lau" ta Jin jina kai kafin tace . "to Masha Allah,ya juma'a Kuma?...".suka ansa da Alhamdulillah nan ta fara Tambayarsu school suna Bata ansa.kan kace me safnah harta cika musu gabansu da ruwa dasu drinks da fruits sai abinci da ummi tasa aka kawo musu duk da dai Baci zasuyi ba haka suka zauna suke ta hira tare da ummi da yake ita macace da Babu ruwanta ga safnah itama da suke ta hira da ita sai Aneesa Dake tare da muneefa suna ta wasansu a falon .sun Dad'e a part d'in Dan Sai wajen k'arfe shida suka koma part d'insu. Lokacin Ana K'iran sallahn magrib.... suna shiga b'angaren su basu tsaya a ko Ina ba sama suka haura Dan suna shiga ya Zarah ta wuce d'aki ita da Huda Dan cire kayan jikinsu Dan Wani Irin damunsu sukaji kayan yanayi ita ko Huyaam d'akin Ammie ta tafi Dan zuwa ta sanar da ita sun dawo Tunda Basu tadda kowa a falon ba. ____________ Da daddare wajen k'arfe 9 na dare bayan su HUYAAM sunyi dinner. Mai martaba yana zaune a falonsa Dake nan part d'in Ammie ,Dan shima b'angaren daban a part d'in ya Zarah ta shigo ta gaida Mai martaba Dan dama haka sukeyi indai Yana b'angarensu ,to sai sunzo sun gaidashi .bayan ta fita HUYAAM da Huda ne suka shigo falon sanye da jihab har k'asa bakunansu d'auke da sallama. mai marataba dake kishin gid'e jikin tuntun sarautan dake babban falon nasa Yana hutawa.ya d'ago yana kallansu bayan ya ansa sallamar tasu cikin nutsuwarsa da kamewarsa har suka k'araso cikin falon. Suka d'urkusa suka zauna nan saman carpet d'in Dake malale a tsakiyar falon ,bayan sun zauna Suka had'a Baki wajen gaida Mai martaba suka ce. "Abba barka da dare, ina wuni".. suka had'a Baki wajen gaida shi. Mai martaba ya Dan d'ago Yana gyara zamansa Yana kallansu da kyau kafin yace. "Barka dai 'yan biyun Ammie ya kuke?..."ya fad'a Yana murmushinsu na manya. sukace "Lafiya lau Alhamdulillah Abba".Mai martaba ya Jin Jina kai Kafin yace . "Masha Allah ,ya exam kuma?yau ba'a je school ba koh?...."ya fad'a Yana kallansu.dan NECO da WAEC suke zanawa sune zasu fita this year yanzu haka sun zana kusan 5 papers Saura 4 su gama . HUYAAM ta gyad'a kai kafin tace . "Eh Abba yau bamu jeba saboda bamu da exam". Mai martaba ya Jin Jina kai sai Kuma ta cigaba tace. "Abba kasan yaushe zamuyi graduation kuwa?..."Mai martaba ya Dan Bud'e ido Yana kallan HUYAAM yace. "Bansani ba HUYAAM. HUYAAM tai murmushi ta k'ara gyara zamanta tace. "Saura 4 papers mu gama, idan mukai ranar Monday to baza mu K'ara yiba sai next week by Tuesday idan Kuma mukai to bazamu K'ara yiba sai ranar Friday ,A ranar kuma zamuyi graduation Abba"ta k'arasa fad'a tana murmushin Jin Dad'i dan tana so ace yau tayi Candy. Mai martaba yace. "Masha Allah, Allah ya Bada sa'ar sakamako Mai kyau"wannan Karan gabad'ayansu suka ansa da Ameen. sun Dad'e suna hira Da Mai martaba a falon ,Dan Mai martaba ya kan ware wa 'ya'yansa Wani time indai Yana gida yayi hira da iyalansa harma ya tambayi Matsalolinsu tahakane yake sanin matsalolinsu dukkansu. Idan har yaga sun Wuce time d'in da suke zuwa yaga Basu zoba tofa shida kansa yake aikawa a k'irasu suzo su zauna tare dashi suyi hira Hakan ba k'aramin Dad'i yake jiba .to yauma hakane sun dad'e suna hira kafin suyi masa sallama su tafi ganin lokacin baccinsu yayi. Mai martaba ya bisu da kallo Yana Jin k'aunar yaran nasa na mamaye masa zuciya har suka fita daga falon gabad'aya... Bayan tafiyarsu Babu dad'ewa Ammie ta shigo falon bakinta d'auke da sallama Mai martaba ya d'ago yana ansa mata ,har Ammie ta k'araso falon hannunta d'auke da tray Wanda ta kawowa Mai martaba fruit da green tea ta durk'usa har gabansa ta ajiye masa tana murmushi tace. "Barka da dare rankai Dad'e". Ta fad'a tana ajiye kayan hannunta.mai martaba yay murmushi Yana yiwa Ammei Wani Irin kallo Wanda su kad'ai sukasan Ma'anarsa yace. "barka dai Fulani,sannu da k'ok'ari Allah yayi albarka".ya fad'a Yana murmushi Shima. Ammei tai murmushi tace. "Ameen thumma Ameen rankai Dad'e" nan ta tsiya ya masa a cup sannan ta mik'a masa cikin girmamawa bayan ta had'a masa Irin had'in da yake so mai marataba yasa Hannu ya karb'a bayan ya Zauna dai dai Yana yiwa Ammei godiya Ammie tai murmushi ta zauna nan kusa dashi Yana Sha suna hira Irin nasu na manya ....... 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *Paid book *Free pages* *NA* *____(MRS SARAKIES ____* *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 7 ____________ Haka Huyaam sukai weekend d'insu Wanda gabad'ayansa a karatun exam ya k'are Dan Karatu suke kamar Babu gobe. Yau Sunday gobe Kuma Monday ya kasance gobe suna da exam ,Dan haka wunin yau karatu suka Sha Yi ita da Huda suna cikin study room d'insu Dake nan kusa da d'akinsu. Bayan Azhar HUYAAM ta sauko downstairs wajen k'arfe 2 : 30pm na rana lokacin sunyi sallahn Azhar ta fito zataci abinci dan wata Irin Yunwa takeji ,Dan rabonta da abinci tun na safe shima ba Wani na kirki taciba tun safe da suka fara karatu ita da huda Bata tsaya ba sai yanzu datai sallah Shine ta sauko k'asa zata Nemi abinda zataci.ta k'arasa har dining bayan ta a zauna ta bubbud'e warmers d'in ta d'ibi abinda zata iya ci ,bayan ta gama ta fito falo a dai dai lokacin da ya Haidar shima yake saukowa k'asa zuwa downstairs zai fita Huyaam ta k'araso wajensa da sauri ta Taya a gabansa tana murmushi kafin tace. "Ya haidar albishirinka" ta fad'a tana kallansa har lokacin murmushi ne shimfid'e a saman kyakkyawar fuskarta. Ya tsaya yana kallanta kafin yace. " goro" Huyaam tace . Na kusan zama candidate na gama secondary school na shiga university kamar yadda ya Zarah takeyi" ta fad'a tana Wani fari da ido tare da murmushi. Ya haidar ya gimtse dariyarsa Dan shi wallahi dariya ma ta bashi wai murna take Dan zata gama secondary school sai Kuma yace a fili. "Hmm yarinyar nan bakida hankali naga alama,yanzu ke Dan ZAKI gama secondary school shine kike wannan murnar". Huyaam ta tura Baki gaba jin abinda ya fad'a ya cigaba Yace. "to idan zaki daina murna ma gara kindaina Dan a b'angaren boko dai babu abinda kikayi" daga haka rab'a ta gefenta ya fice daga falon gabad'aya.huyaam ta bishi da kallo jin abinda ya fad'a jiki a Sanyaye ta haura sama zuwa d'akinsu Dan ta D'an kwanta ta huta kafin bayan ASR Kuma ta cigaba da karatunta. Har bayan sallahn isha'i su Huyaam suna studying room d'insu suna karatu sallah ce Kawai da a Abinci yake ta-da su . Yanzu ma Hakan ce ta kasance bayan sunyi dinner suka koma d'akinsu .Mai martaba Kuma Yana zauna a falonsa da Ammie da Kuma ya zarah wacce tazo gaidashi,mai martaba ya kalli ya Zarah yace. "Zarah Ina su mamana suke ne?....." haka yake fad'awa su Huyaam Wani lokacin. Ya zarah ta d'ago ta Kalli Mai martaba kafin tace da ladabi. "suna can d'aki suna karatu gobe Monday suna da exam" kafin ta rufe Baki su Huyaam suka shigo falon bakinsu d'auke da sallama.su Ammie suka ansa Musu ,har suka k'araso falon suka zauna nan saman carpet d'in suna gaida Ammie Kafin nan suka juya suna gaida mai marataba . Mai martaba ya ansa musu Yana kallansu yace. "Ya Karatun?...suka ansa da Alhamdulillah ,Mai martaba ya Jin Jina kai Kafin yace. "Allah ya Bada sa'a". suka ansa da Ameen .sun D'an Dad'e a falon suna hira har ya haidar ma ya shigo kafin daga k'arshe
Chapter 8 · 0% Book details