← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 117

Sashe 90

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kaltum....bakwa sha'awar komai ne?" Ta fadi tana ajjiye wani paper plate dake hannunta

"Get out malamarsu" samir din yadan fada a kausashe,da alama akwai abinda ya taba rashi,ba zata iya tuna yaushe ne na qarshe daya mata hakan ba,don haka ta dauke plate dinta tana boye fuskarta tabar wajen.

Da kadan da kadan ake raguwa awajen,duk da ruwan saman daya fara sauka bai hana mutane tafiya ba,saboda kusan kowa da motarsa yazo shida iyalinsa,wajen ya qayatar sosai,babu hauka babu baragada,kowa da matarsa yake,masu setup irinsu jawahir kadanne,sai zuwa sannan ya daga kanshi yana maida wayarsa aljihu yana kuma dora kansa a kan kaltum.

Kwalliyarta na nan kamar sannan aka yita,dan qaramin bakinta da yasha jambaki yana motsawa kadan kadan,baisan me take fada ba,daya tsura mata idanu sanda aka yi tsawa sai ya lura addu'ar tsawa take,ta dan rufe idanunta kadan,wanda hakan ya fito da zara zaran gashin idanunta da zaka tsammaci sa mata akayi,saidai mascaran da aka sanya musu ya sake fitar da kyau da tsahonsu,ya fuskanci tsoron tsawa take sosai,saiya miqe a hankali ya miqa mata hannunshi.

Jin tsaiwarsa saman kanta yasa ta bude idanuwanta,suka sauka akan lallausan tafin hannunsa da yake miqa mata,karo na biyu kenan daya taba bata wannan damar,tana jin kunya tana kuma jin nauyi,yana kuma sanyata shiga wani yanayi,amma haka ta dora masa nata hannun a hankali ya rumtse cikin nasa ya kuma jirayi tashinta kana suka nufi hanyar fita.

Dukka akan idanun jawahir,mamaki yana sake kamata,bata taba ganin haka daga yayan nata ba,hannunsa cikin na wata?,me aikin gidansu?,kuma ba muharramarsa ba,shida kullum maganarsa itace su kare mutuncin kansu,kada su yarda koda wasa su hada jiki da wani da namiji?,binsu tayi da idanu har suka fice daga hall din.

Dakatawa yayi da tafiyar yana kallon ruwan,ya soma qarfi sosai,wanda mutane da yawa dake ciki basusan da hakan ba,waiwayawa yayi kadan ya dubeta,sai yaga ruwan ta zubawa idanu itama,da alama tana wasafta ta yadda zata shiga cikinsa.

Yana riqe da hannunta a hankali suka fara taka cikin ruwan suna dosar motarsu,idanuwanta ta runtse sanda sanyin ruwan yake ratsa jikinta,saukarsa ta farko ji tayi kaman numfashinta zaya dauke,tunda can ita me tsoron ruwa ce,shi yasa kaf rayuwarta bata taba shiga rafi wanka ba,saidai tayi rakiya wa su wasila,tana tsaye kuma har suyi su gama.

Qarfin ruwan ya sanya kafin su isa motar ta jiqe,duk da bame yawa ba amma tana jin sayin har cikin qashinta.

Takurewa tayi sosai a sit dinta,tana kallon singalilin hannunsa da ruwa ya jiqa yana kashe ac ya maidata zuwa heater,sumar gargasarsa itama tayi luf,ta rufe idanunta sanda akayi wata walqiya,ta tabbatar tsawa ce zata biyo baya don haka ta sake curewa guri guda.

Binta yayi da kallo,saiya saka hannunsa ga seat din baya,ya dauko hiramin daya siya dazun a store din da sukaje siyayya shida amiru,ya farke ledar ya wareshi ya soma rufa mata,abinda ya sakata bude ido,idanunsu ya shiga cikin na juna,eye lashes dinta sun jiqe sosai sunyi wara wara,sai tayi qas da kanta tana jin dadin rufetan da yayi

"Na gode" ta samu kanta da fada,ya tada motar yana amsa mata da

"You are welcome".

Tun basuyi nisa ba ruwan yayi wani irin qarfi naban mamaki,tituna suka fara cika saboda rashin kyakkyawar magudanar ruwa,tsaki samir din yaja yana kallon yadda titi ya shafe da ruwa,ya rasa aikin me gwamnati keyi?,ruwa a saman titi kamar layukan unguwanni?" Baka bambace titi da kwata?,yana daya daga cikin abinda yasa ya tsani siyasa iyaka kenan,babu komai cikinta sai yaudara da daukan alqawuran dako kusa ko alama basa iya cika koda kaso daya cikin ukunsu.

Ji yayi bazai iya ci gaba da tuqin ba,don baisan yadda zai tadda unguwarsu ya dikkon ba,bugu da qari ma ya tabbatar idan yaje zaiyi horn ne ya taso me gadin da a yanzu yake cikin dakinsa ya samawa kansa mafaka daga dukan ruwan saman,wannan tunanin yasa ya gangara a hankali hannun da yake tuqi qofar wani katafaren guest in,ba tare daya tuna inda zai ajjiye kaltum din ba.

Umarnin fitowa yayi mata bayan ya bude mata murfin motar,ta fito a hankali tana sake hade jikinta waje guda,saiya saka hannunsa saman daya kafadartata ya janyota zuwa jikinsa,abinda ya rage mata dukan ruwan,saidai kuma hakan da yayi mata tamkar ya sake jefa abun fashewa ne cikin zuciyarta,ta dinga sauke qaramar ajiyar zuciya a hankali.

Da tarba ta mutunci receptionist din ya karbeshi,ya buqaci daki biyu

"Saidai kayi haquri yallabai idan babu damuwa kuyi squatting a daki daya,babu dakuna sai wannan da ka karba yanzu guda biyun da suke ba kowa a ciki gyara ake musu,babu damar iya zama a ciki"

"Ba matsala" ya fada a hankali.

Sai daya bude mata dakin ta shiga sannan taga ya sake fita ya dawo bada jimawa ba,hannunsa dauke da wani irin akwati dan qarami me dauke da tambarin wani store,wanda manyan customers dinsu da sukayi siyaya da yawa ko me manyan kudi suke zubawa kaya a ciki.

Tana daga zaunen ya kunna heater din dakin,ya rage haske qwayayen,sannan kuma ya kunna water heater ta bandaki ya shige bayan ya tara ruwa me zafi sosai.

Har sanda ya murda qofar toilet din ya fito tana zaune a wajen jikinta a hade,duk da dumi ya fara ratsata,saidai hankalinta ya rabu biyu,ta yaya zasu kwana a dakin nan daga ita saishi?,me zata cewa jawahir idan ta tambayeta ina sukaje?,zatace mata ne sun kwana tare bayan babu wanda yasan alaqarsu?.

"Ki cire wadan nan kayan kafin sanyi ya kamaki,ki shiga toilet ki dumama jikinki da ruwan zafi" ya fada sanda yake fitowa daga toilet din sanye da sabuwar rigar wanka ta towel har qasa me budadden qirji,abinda ya bayyana tarin sumar dake kwance a qirjinsa baqa sosai mai kuma santsi.

Numfashinta ta dauke gaba daya tana sake qanqame jikinta,ruwan da yayi wanka ya sanya kowacce suma ta jikinsa kwanciya,hatta da qawataccen sajen fuskarsa mai kama da qasumba,saidai baikai qasumba fadi da cika ba.

Wani abu ta hadiye,cikin dakiya tace

"Da zaka qarasa dani gida....saboda su jawahir....." Kasa qarasawa tayi saboda ji da tayi a jikinta ita ya zubawa ido,ilai kuwa haka ne,har baisan sanda murmushi ya subuce masa ba,yana da tabbacin batasan waye samir ba,wannan rayuwar ba irin waddanya fasaltawa kansa ko yake sha'awarta bace,inda tazo masa a matsayin matar aurensa da suka fahimci juna,duniya tasan da aurensu da ba wannan zancan ake ba a yanzu,kwata kwata wannan ba irin rayuwar auren daya tanadarwa kansa bace,saidai akwai wani qwaqqwaran bond da yakejin yana son gilmawa a tsakani,duk da haka aure duka aure ne,zai tunasar da ita abinda takeson mantawa,duk da cewa baison ya wuce gona da iri,saboda yanajin cewa gaba kadan xai bata dukkanin zabi ne.

Batasan ya tsaya a gabanta ba sai da idanunta suka dauka kam xara zaran yatsun qafarsa da gashin ke kan kowanne dan yatsa ke akwance shima,kafin tayi wani motsi ya kama dukka kafadunta ya dagata,sai ya saka hannu ya zare hiraminsa ya aje gefe,jawota yayi jikinsa ya mata sasssuqar runguma,abinda ya kusa sanyata daukewar numfashinta kenan saboda jikinta daya gogi nashi,shi dinma yaji,amma ya dake,yanason ya mata tuni ne kan abinda ta manta,saiya kama zip din rigarta ya saukeshi qasa gaba daya,duk da cewa a iya nata qarfin fa cukuikuye rigar a jikinta amma hakan bai hanashi sabule mata ita ba ya hada harda bra dinta,adalci daya yayi mata tana jikinsa bazai iya kallonta ba saidai duk wata fata ta jikinta da hannunsa ya taba yana jin aiken saqo zuwa kowanne sashe na jikinsa,sai ya dauko hiramin ya rufa mata,ta kamashi kuwa tsam ta riqe tana sake lullube jikinta,ko ina na jikin nata yana rawa,qafafunta kamar ba zasu iya daukarta ba

"Akwai ruwa me zafi kije kiyi wanka kixo ki kwanta,idan sun tambayeki gobe,kina iya gaya musu mijinki kika biyo,naki da zunubi ko dis a wajen Allah" ya fada yana juya mata baya yana takawa zuwa gaban madubin dake fuskantosu,saidai yana iya hangenta ta madubin sanda take takawa da sauri kamar zata fadi ta durfafi bandaki.

Ta dade a tsaye tana haki tare da sauke numfashi,gaba daya ya aza mata wani irin nauyi da tsoro,bata taba kawo haka a tsakaninsu ba,duk da cewa tana jin abubuwa masu yawa dangane dashi cikin zuciyarta.......

*_A WANNAN DAREN_*

Su biyu ne rak zaune cikin dakin,duk da suna saka ran shigowar mutum na uku wato najwa.

A hankali hajiya jidda ke qarewa dakin kallo,tana qiyasta yawan dukiyar da aka sake narkawa dakin,kafin maganar hajiya shuwa ta shiga kunnenta

"Idan bakiyi wasa ba hajiya jidda kwabarki tana dab da tayi ruwa,dava tafiyata ace babu wani ci gaba da aka samu?,saima tarin koma baya dani na hango?,me yasa ba zaki kawo qarshen komai kowa ya huta ba kema ki huta?,tun kafin akai lokacin da zaki dora hannunki aka?" Murmushi mummy ta saki tana duban hajiya shuwa

"Akwai abinda nake jira da dako,banason garin sauri naje na aikata kuskuren da kika kusa aikatawa" murmushi hajiya shuwa ta saki

"Iya gidan nan kadai amma ya isheki amsa ko?" Maida mata murmushinta mummy tayi

"Eh qwarai,saidai akwai banbanci,banajin zan iya qarasawa bigiren da kike kai a yanzu" dariya sosai hajiya shuwa ta saki

"Kijimin mata.....da wanda yaci alade,da kuma wanda yaci mushe meye bambancinsu?"kai mummy ta girgiza

"Banbanci me tarin yawa kuwa,tunda ko banza shi mushe ai yankan Allah ne......".

A hankali najwa taja da baya hannunta riqe da cup din tea data hado da niyyar sha,ta taka kuma zuwa dakin da aka sauketa cikin gidan hajiya shuwa tun bayan zuwansu garin azare,wanda sukaqi zama gidan ya dikko.

Katafaren dakin da sai ka zaci dakin wata hamshsqiyar ne,ranta a bace take duban tvn dake aiki a dakin,duk da cewa bata tvn take ba,hirarsu mummy ke dawo mata,ko daya bataji sun tattauna kan matsalarta ba.

shedan ke dake zafafa mata zuciya,ta fuskanci mummy tana slow ne kan abubuwa da dama,to itakam a yanzu tanajin qarfinta ya kawo,zata shiga nata yaqin,zata aiwatar da abubuwan da mummy ta kasa aiwatarwa,bata jin xata yarda ta amince....tasha dukka wata wahalar karatu saboda cikar buri da muradinta,sannan a qarshe daddy yace taje tayi aiki da kamfanin saraki a qarqashin sarakin?ba zata iya ba,kuma da sake.

Miqewa mummyn tayi tana tattaki gaban hajiya shuwa,maganganun da suka sakeyi suna mata yawo akai,hajiya shuwan kuma na binta da kallo.

Tsayin wasu mintuna mummyn ta dawo gabanta ta tsaya
Chapter 90 · 0% Book details