← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 117

Sashe 69

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Meye nasabar inda ta fito da iya cire qadangare?" Ya jefa mata tambayar wannan karon cikin matuqar fushi

"To ai......"

"Mtsw common keep quiet!"

"Yaya kowa fa....."

"Will you shut up ko sai na saki a dakin kema kinji yadda akeji?" Ya fada yana tura qofar dakin,wanda hakan ke nuna mata da gaske yake

"Am sorry" ta fada ba tare data shirya ba,don taga bacin ransa qarara.

Wani mugun tsaki yaja kamar xai cire harshensa,ya waiwaya ga jawahir da itama haushi da takaici ya cikata

"Ki tafi da ita dakinki"

"To yaya...." Ta amsa mishi tana kama hannun kaltume sukayi gaba,ya taka a hankali yabi bayansu ba tare da yabi takan matsalar najwan ba.

Bin bayansa tayi da kallo zuciyarta na quna,lallai ya tabbata mutumin nan bai qaunarta shima,tunda har zai barta da abinda take tsoro.yayi tafiyarsa,bayan yasan ko mommy bata a gida,saita juya fuuu tayi hanyar fita zuwa farfajiyar gidan,zata juyewa security nasu rabon.

D/Z
40

A hankali kowannensu yake kaiwa cikinsa a bincin,yayin da kowanne hannunsa yake dauke da wayarsa,table din yau fayau yake,saboda babu kowa a kai,daga mummyn sai najwa.

Wayar hannunta mummy ta ajjiye a gefanta,ta dora idanunta a kan najwa

"Ina jawahir ne?"

"Tana daki" ta amsa mata tana ci gaba da danna waya

"Me yake damun yarinyar nan ne?,kwanakin nan duka ta daina zaman cin abinci?" Fuska najwa ta yamutse ta ajiye wayar itma a gefan plate dinta

"Ina gaya miki mummy yarinyar nan bata da hankali,duk sanda zanyi mata magana saiki hanani,kinsan abinda yasa ta daina cin abinci damu?,saboda waccar banzar 'yar qauyen mai aikin,tare suke cin abinci cikin daki,kuma kina zaune an maida miki yarinyar baiwa,ita kewa yarinyar can karatu,ni wallahi badan badan ba da sai nace jawahir ba jinina bace"

"Ke!....kul!..." Mummyn ta fada cikin hanzari da muryar tsawa tana duban najwa

"Kada na kuma jin irin wannan furucin daga bakinki,jawahir jininki ce halak malak" baki najwa ta sake tana bin mummy da kallo

"Bakiji abinda nace miki ba?,nace kada na qara jin wannan kalmar daga bakinki"

"Naji" ta amsa,fuskarta ta fara nuna fushin nan nata da bata iya boyeshi duk sa'adda aka bata mata rai,tana daukar cokali taci gaba da cin abincinta,yayin da mummy ta sake daukar wayarta tana laluben number jawahir.

A daidai lokacin suna zaune saman carpet din dakin jawahir din,wanda tun ranar da saraki yace suje dakinta bata bar kaltumen ta koma dakinta ba,anan suke kwana,saidai jawahir din tana boyewa bata bari mummy ta fuskanta ba.

Mayukan data siyawa kaltum take daddagawa,sai data gama ta waiwayo tana dubanta,cikin yanayin jin haushi tace

"Ai wallahi tunda na kalli fatarki naga bata fara komai ba nasan baki amfani dasu,kinsan tsada da kyan mayukan na kaltum?" Kai ta girgixa

"Ni wallahi tsoron koilin nake,banason bilicin,masu yima qyanqyaminsu nake,asiyata tana yi,amma ko hanya banason mu hada,tasha yimin ba'a da tsokanata,wai ni baqa ce,amma ni bana damuwa kwata kwata,saboda nasan haka Allah yakeson ganina,kuma tunda ya bani baiwar ji da gani,ya bani hankali,ya bani idanu da qafafuwa to nafi mutum miliyan dasu wannan ma suke nema" murmushi jawahir tayi,sau tari tana tsintar kyawawan dabi'u daga kaltum din

"Maganarki haka take, black is beauty ni a wajena,ke kyakkyawa ce kaltum" ta fada tana kallonta,zaro idanu kaltum tayi itama tana duban jawahir,fuskarta da zuciyarta cike fal da mamakin kalamanta,saboda ita din ce mutum ta farko data fara gaya mata wannan kalmar,ko da yaushe saidai ace habiba ko asiya sune masu kyau a gidansu,saboda sun fita hasken fata,amma itakam bata taba jin wanda ya gaya mta hakan ba sai yau.

Ta lura da tarin mamakin dake qunshe a fuskar kaltume,saita sanya dariya kafin ta tsaya

"Wai mamaki kike?,da gaske nake ke kyakkyawa ce"

"Ki daina fada don Allah,sai naga kamar kinamin ba'a ne" ta fada tana shafa 'yar kewayayyar fuskarta,tare da shafo zara zaran gashin idanunta masu tsaho,da a wadansu lokuta take jin suke rage kyan fuskarta

"Kaltum,irinku ne masu boyayyen kyan da ba kasafai aka fiya ganinsa ta farat daya ba,sai sanda suka sake girma,suka kula da kansu,a sannan kyau mai ban mamaki yake bayyana daga jikinsu,fari tsaho ko sirantaka ba shine kyau ba,kowacce mace kyakkyawa ce ta irin hanyar da Allah S W T ya halicceta,amma ina me tabbatar miki ke.din kina daga sahun kyawawan mata,ina kuma da yaqinin nan gaba maza sai sunyi gware a kanki"

Idanu kaltum din ta sake fiddowa,wadanne mazan?,badai mazan irin wannan garin da take gani ba,saidai mazan qauyensu. Jawahir ta sake katse mata tunaninta ta hanyar cewa

"Wannan man dana siyo,bana komai bane,baya saka hasken fata,bazan ma yarda ki shafa ba idan muna tare,saboda ya saraki ya taba gayamin shafa man da zai sanya mutum hasken fata haramunne haramunne haramun ne......,kuma duk wadda takeyi ta shirya gamuwa da fushin ubangiji matuqar bata tuba ta daina ba,kuma dabi'a ce da shaidan yayi alqawarin dama sai ya sanya mata sun yita ita da qarin gashi" saita miqe ta soma bare ledar jikin mayukan tana dorawa saman mudubi

"Daga yau sune man shafawarki.....gana gyaran gashi ma.....wait...." Ta fada tana waiwayowa

"Ni ban taba ganin kanki bama fa kaltum,ya kike iya wuni ki kwana da dan kwali?" Murmushi tayi tana sake janyo dankwalinta tana rufe kanta,batason kowa yaga kan nata,saboda tsufa da kitsonta yayi,ranar da taso tsefewa a ranar suka tashi da kai bilalu asibiti,abinda ya hana tsifar kenan har yau,sai taji qwalla ta cika mata idanu

"Allah sarki bilalu,yana can qarqashin qasa a kwance" wannan tunanin ya qara yawan qwallarta,sai tayi qasa da idanuwanta,wanda kiran wayar mummy ya hana jawahir ganin hawayen

"Gani nan" ta fada tana katse wayar,saita duba sashen da kaltum ke zaune

"Zanje na dawo mummy na kirana,shima man wankin kan nan yana sake gyara gashi,idan ya karbeki ma har tsahon gashi yake qarawa,Allah kafin lokacin shigarki makaranta dole ki fara amfani dasu don kada su rainaki,nasan ya samir private zai kaiki,ba kasafai yakesaka mutum a government school ba" daga haka ta fice daga dakin.

"Ni dinma ba kowa bace,yadda kika daukeni jawa(haka take kiranta) ba haka bane,ban samu dukka wannan darajar a gidan uban daya haifeni ba,saidai na gaji,na gaji" ta fada tana kifa kanta saman cinyarta,hawayen da take riqewa suka fara zuba,jinta take a wani irin takure,ta gaji da zaman gidan,ta gaji da kewar ummanta da takeyi da habibanta,tana kewar dakin kwananta duk da nan ya ninka shi sau babu iyaka,amma tana kewarsa,tana kewar qauyensu qwarai.

Yadda mummy ta zuba mata idanu har ta qaraso ya tabbatar mata akwai damuwa,tun kafin takai ga zama ta balbaleta da fada,abinda ta jima bataji tayi mata ba

"Izinin waye kika nema da xaki fara koyawa yarinya karatu haka siddan,daga zuwanta gidan,ba'asan wacece ba ita?,ko yau ta cutar dake ta gudu babu inda zamu sameta,saboda bamu da tabbacin asalinta?da zaki dauketa ki kaita dakin kwananki ku dinga kwana tare,dakin kwananki fa jawahir?,anya kuwa kina tunawa da waye ubanki da kike hada matsayinki dana wasu?" Fuskar mommy take kallo tana mamakin yau kalaman dake fita daga bakinta,baya koda yaushe ita mai son taimako ce da jan mutane a jiki gami da faran faran dasu,gwiwa a sanyaye tace

"Mommy kece kuwa?" Idanunta ta lumshe tana qoqarin cooling down kanta,tare da controlling fushinta,batasan ta fidda maganganu haka ba

"Tunzurani kike son yi jawahir na soma aikata halin da ba nawa ba" ajiyar zuciya jawahir din ta sauke,ta gyara tsaiwarta

"Mummy,ya samir ne yace na koya mata karatu,kuma shine yace na kaita dakina,kuma mummy itama ta fara koyamin karatun islamiya,tana da karatun addini,zaki mamaki sosai idan kikaga yadda ta iya....."

"Ya isa,jeki" mummyn ta katseta sanda samir yake takowa cikij falon

"Thank you mummy" ta fada tana jin dadin yadda bata ja abun da yawa ba,tafi zargin ma najwa ce ta zugata,don haka ta wuce najwan tana yar waqarta.

Yana isowa wajen kwarjininsa ya mamaye gurin,fuskarta da mayalwaciyar fara'a kamar kullum tace

"Barka da fitowa son" tana gyara masa kujerar dake daura da ita,yana gyarawa kansa wata kujerar tare da shirin zama ya amsa

"Yauwa mummy" saiya soma gaidata bayan ya zauna,najwa ta gaidashi tana sauri ta kammala tabar wajen,abu guda dayan da take mtuqar jin haushinsa shine yadda kwarjininsa yake bugar da ita,sau tari shike mata burki kan abubuwa da yawa da take da burin aiwatarwa.

Umarni mommy ta bata tayi saving dinsa,ta miqe ta hada masa komai,sannan ta kwashe wayoyinta tabar wajen

"Samir,me yasa ne kwanakin nan kamar kana aiwatar da abubuwanka gaba gadi ba tare da sanina ko izini na ba?" Ta jefa masa tambayar data sanyashi daga kai ya dubeta,idanuwansa daya zuba mata ya sanyata gyara maganar

"Duka masu aikin gidan nan qarqashina suke,nice ahaqqu da cinsu shansu da suturarsu,to amma ita wannan yarinyar ka dauki kudinka da kanka kayi mata abinda nice zanyishi,why son?" Ta qarashe tana fidda boyayyen numfashi,yau batasan mene yahau kanta take sakin magana haka anyhow ba.

Ci gaba da cin abincinsa yayi kafin yace

"Ita na daukota ne daga gaban iyayenta da sunan amana,so dole kinga nima na kula da wasu abubuwan,amana ba abune qarami ba"

"Qwarai kuwa son,kayi gaskiya,dole ne kowanne mutum ya dinga kula da amana,kuma tunda haka ne nima zan tayaka in sha Allah" ta fada tana murmushi sosai kan fuskarta,saidai can qasan zuciyarta tana kallon haka kamar ragin matsayine a gareta,amma koma meye zatayi amfani da fikirarta kamar kullum,komai yaci gaba da gudana a qarqashinta.

"I called daddy several times amma bana samunshi,akwai wani specific line daya kiraki dashi?" Wayarta tadan kalla sannan tace

"Oh god.....tunda yaje bakuyi waya ba son?" Kansa ya gyada,fuskarta cike da damuwa tana jawo wayarta gabanta tace

"Bai kamata ba, that's why ko yaushe yake kallonka a matsayin wanda bai damu da al'amuransa ba,pls put the digits ka kirashi yanzun nan" ta fada tana buda wasu shiryayyun numbers ta fara gaya masa yana rubutawa.

Sai daya gama jerasu tsaf ya sake kallonsu,kaman zaiyi magana sai kuma ya fasa ya fara gwada kiran,a take na'ura ta gaya masa cewa a kashe wayar take

"Maybe he is busy shi yasa ya kashe wayar,but please try to call him again"

"Ok"ya amsa yana yunqurin aje wayar,dai dai sanda amiru ya shigo,a shirye tsaf dashi,kamar yadda ta lura shima samir din yayi ado ne cikin wata shadda da suke iri daya sak data amiru,dinkin matasan yanzu qaramin hannu,haka tsahon rigar bai wuce cinyarsa ba.
Chapter 69 · 0% Book details