← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 117

Sashe 65

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A dan zabure ta dago jin an turo qofar dakin,har jawahir data shigo cikin shirinta tsaf na tafiya makaranta ta ankara da hakan,saita sake mata murmushi

"Yi haquri,na tsorataki ko?,sauri nake,ina biba zuwaira?" Qofar bandaki dake budewa ta kalla,dai dai sanda biba ke fitowa

"Diyata an fito?"
"Eh wallahi....don Allah biba zoki zubamin.....zan makara Allah,ya saraki na samu zai saukeni" da kallon mamaki kaltume ki binta,da alamu tana da kirki sosai a fuska,saidai kuma yadda take magana a shagwabe ya bata mamaki,ita bata taba ganin inda babba kamarta ke shagwaba ba,wanda inda a karkararsu ne tana da yara uku ma.

Nauyi taji ya kamata sanda suka hada idanu da jawahir,ta kamata tana kallonta,ga mamakin kaltume saita sakar mata murmushi

"Baquwa ya sunanki ne?"
"Kaltume ce" biba ta amsawa jawahir sanda jawahir din tayi gaba,biban na biye da ita a baya suna surutu.

Tana hakimce saman dining din tana breakfast cikin salon da zai nuna izza mulki da kuma iko da take dashi,falon baby daya cikin yaran gidan,sai masu aiki daketa kai komo suna gudanar da hidimar gidan ta yau da kullum wadda ta zame musu jiki.

A irin haka kaltume suka fito tana biye da biba,a mugun darare tana raba idanu tana kallon yadda Allah ya zuba ruwan kyau cikin falon da batasan wanne suna zata bashi ba.

Sai data kusan gama cin dankalin gabanta sanda suke duqe suna gaidata sannan ta ture farantin

"Lafiya lau....ita zaman me takeyi da baki shiga da ita cikin ma'aikata an bata aikin daya dace da ita ba?" Mommyn ta jefawa biba tambayar,kasancewar itace shugabar duka ma'aikata mata na gidan,saboda dadewar da tayi cikin gidan

"Ai dama bansan wanne aiki ya kamata a bata bane,nace ne bari na fara tambayarki tukunna" shuru ne ya biyo baya tana nazari,akwai abinda takeson aiwatarwa,saidai batason wanzar dashi da kanta lallai saita hannun professor,duk da tana hangen lokaci xai mata tsaho kafin komai ya mata yadda takeso,amma zatabi lokaci bisa takatsatsan da rashin gaggawa kamar yadda ta saba

"Kije ki bata duk aikin daya kamaceta.....amma tayi qazanta da yawa,banason a bata aikin daya dangancin abincinmu" ta fada fana dan qarewa kaltume kallo

"To hajiya" biba ta fada tana miqewa.

A hankali kaltume dake duqe itama ta miqe kanta a qasa,ita sam bata gane abubuwan da suke faruwa da ita,tun daga sanda aka daura mata aure zuwa yanzu,ita ba haka tasan ana zaman aure ba,shi wanda yake a sunan mijinta har yanzu jikinta da zuciyarta sunq amsar kalmar,a kallon ma datayi masa a jiya gaba daya sai taga wani irin bahagon dacewa tsakaninta dashi,tunda ya kawota gidan ya ajjiye bata ganshi sau biyu ba,na biyu an kawota wajen wannan matar dake tsareta da wani irin kallo dake sanyata fargaba da tsoro,kuma taji ana maganar a bata aiki,har tana qyamarta,bayan ko kafin ta fito ma sai da tayi wanka,to meye abun qyama a jikinta,to ko su a tasu duniyar haka ake zaman aure?,ta kasa warware wannan zaren,amma dai....koma meye zata zuba ido taga iya gudun nasu ruwan.

Babban kitchen ne,wanda duk girmansa an yishi bisa tsari na zamani,tsari me qawatarwa,kowa dake cikin kitchen din aikinsa yake gabatarwa,sai biba ta dinga bi da ita gurin kowa tana nunata suna gaisawa,kana daga bisani ta nuna mata waje tace ta zauna.

Bata musa ba ta zauna din,tsahon lokaci idanuwanta suna biye dasu,duk da rabi da rabin hankalinta naga gidan wajen ummanta,tare da tunanin a wanne hali take ciki,amma ta cika da mamakin yadda za'a ce wai wannan qawataccen wajen wurin an tanadeshi ne kawai saboda dafa abinci,tabdi,lallai wani aikin sai binni,ashe duk labarin maraya da sukeyi basusan ma komai game da ita ba,tunda hasashensu bai taba hasko musu irin hakan ba,to waishi mijin nata wayeshi ne,kuma me suke a wannan gidan?,a nan zasu dawwama ko zasu tafi?.

Ganin zaman ya soma tsaho ba tare da biba ta waiwayeta ba saitace da ita ta bata aikin da zatayin

"Ki zauna abunki,babu wani aiki me yawa yau,sai gobe idan Allah ya kaimu,idan kin gaji zaki iya komawa dakinki ki zauna" zata iya gane hanyan komawar amma bata da sha'awar ta koma din,don haka taci gaba da zama a wajen,har zuwa lokacin da najwa ta fito yin breakfast,ta kuma aiko cewa biba takai mata kayan karinta dakinta.

Kaltume ta baiwa wasu qananun kofunan qarau masu kyau da wani plate tace ta tayata dashi,tana biye da ita,suka wuce wani qayataccen falon kafin su dangana da dakin najwa din.

Tana zaune saman sofa ta miqe qafafunta da alama wayarta dake saman cinyarta take amsawa,kanta babu dankwali,tana sanye da wasu kayan bacci masu kauri da zasu iya tare mata dan sanyin da aka fara busawa,sai gashinta da bai wuce tsayin dan yatsa ba,saidai kuma a kwance yake yasha gyara.

Suna shigowa ta katse wayar,fuskarta a murtuke ta sauke qafafunta qasa tana bin kaltume da kallo sanda ta qaraso tana dire kofunan kamar yadda taga biba tayi

"Move dalla malama,matsa nace!" Ta fada cikin tsawa kamar zata sanya qafa ta buge kaltume,tsoratar datayi yasa taja baya da sauri,saura kadan kofunan da bata gama ajjiyewa ba su daki qasa su fashe

"Zuwaira meye haka din?,zaki kwaso min yarinya tana wari ki shigomin da ita?,tana tabawa mutane kayan abinci?" Kan biba a qasa tace

"Kiyi haquri"
"Fita ki bani waje,kin tsaya kina dumamawa mutane waje....idan ta fita ki dauka freshner ki fesa min".

Da sauri kaltume taja da baya sannan ta juya tana hada hanya saboda sauri ta nufi qofa,tana jiyo sanda biba ke fasa freshener din,saita lumshe ido tana sakin ajiyar zuciya,tana jin yadda bugun zuciyarta ke qaruwa saboda tsoratar da tayi,su wadanne irin mutane ne wadan nan?,wacce iriyar rayuwa suke?.

"Kiyi haquri kinji?,haka take bata da kirki,nan muma kowa haquri yakeyi da halayenta" biba ta gaya mata bayan fitowarta daga dakin,kai ta kada,ta motsa labbanta a hankali

"Ba komai" saidai tana ji a zuciyarta,tunda har ya tabbata haka halayyarta take,ya zame mata dole ta nisanceta,duk da cewa ta girmemata,haka nan yanayin sukuni da muwalati na rayuwa sun bayyana banbancin dake tsakaninsu,to amma fa zuciyar nan tata har yanzu itace a qirjinta,ba zata juri cin mutunci da wulaqanci ba,bayan ba wani abu ta aikata mata naba dai dai ba.

*********Cikin takun dake qara nuna qasaitarsa,hannyensu biyu duka soke a aljihun Blazer din dake jikinsa ya isa bakin babban gilashin daya mamaye bangon yamma na office dinsa,wanda hakan yake bashi damar hangen ilahirin makekiyar harabar kamfanin dama wasu sassanni na unguwar,hannu yasa ya yaye dan wani abu da aka zuba daga gaban glass din me madadin labule yana furzar da iskar bakinsa,idanunsa ya sauka parking lot dake cike da motocin ma'aikata,can ya hangi fawwaza gaban tata motar,ta sanya muqulli tana bude motar,duk da ka gane yanayin fuskarta sosai,to amma daga nam yana iya karantar yanayinta.

Daga bakin office dinsa take,ya tabbatar ranta a bace yake,saboda hanawa da yayi a barta ta shigo wajensa,gaba daya yau ita da ire irenta babu wanda ya bari ya shigar masa office,shi yasa ya zaunar da umar daga waje,saboda yana da tabbacin shi din zai iya yadda yace masan.

Bai bar wajen ba har sanda ta shiga tabtada motar ta fice daga kamfanin,ya sani cewa ba lokacin tashi bane,kuma fitar tata tamkar ta karya dokar kamfani ne,saidai yana sane da komai,zai kuma yi maganin matsalarta.

Sauke labulen yayi,ya juyo a hankali yana duban saman table dinsa dake cike da files wadanda dukkansu shi suje jira,ga alamun gajiya da kasala sun bayyana qarara cikin kyawawan qwayar idanunsa.

Gaban teburinsa ya qarasa,ya dauki wayar landline yayi magana ta sakanni da basu wuce takwas ba sannan ya sauke wayar,ya koma ga files din yana buda wasu daga ciki,har zuwa sanda qofarsa tayi 'yar qara alamun ana neman izinin shigawa,sau daya ya danna wani abu dake gefansa,qofar ta bude aka shigo

38

Dauke da babban faranti mutumin dake sanye da uniform irin na ma'aikatan cikin kamfanin ya shigo,ya qaraso cikin girmamawa ya ajjiye zazzafan coffe din,ya juya ya fita dai dai sanda saraki ya fara kai cup din coffee din bakinsa,yana sake kiran waya da wayar landline din dake gabansa

"What are you waiting for?...... file na office dinsa kawai nake jira fa,u r wasting my time" ya fada cikin fushi,dan jim yayi,da alama yana sauraren abinda ake fada daga daya bangaren ne,ba tare da yace komai ba ya sauke wayar

"Kai da waye?" Ya tsinci muryar amiru dake shigowa office din kansa tsaye,wanda kusan shi kadai keda wannan ikon,sai ya waiwayo yana riqe da cup din yana dubansa

"Fawwaz.....already na gaya masa ya tattara dukkan wasu bayanai dake offices din dakw qarqashinsa na qarshen shekara,kusan na karbi ko wasu bayanai amma nashi ya gagara zuwa?".

Baice komai ba,sai daya ajjiye file din daya shigo dashi kan sauran dake wajen,yaja kujera ya zauna sannan yace

"Not surprisingly" cira kai samir yayi ya dubeshi,yana nazarin fuskar amirun na wasu sakanni,shima amirun shi yake kalla,kafin daga bisani ya dage masa gira,sannan ya tashi ya zauna sosai yana fadin

"Aje wannan a gefe......ya kukayi da daddy?" Kujerarsa ya koma ya zauna,ya hade hannayensa duka waye daya,sannan ya fara gayama amirun yadda ake ciki.

Shuru ne ya biyo baya na wasu sakanni kafin amiru yace

"Yanzu....what next?.....tunda kaqi yarda da shawarar mayar da ita?" Bayansa ya mayar ya jingina da fuskar kujerar

"Ko wajen hajiya qarama zata koma?" Amiru ya sake fada kafin yaji amsar samir.

Kansa ya kada

"A nan din dai zata zauna tare damu,duk da sabanin ra'ayi da muke yawan samu.....kusan nafi kowa karanta da sanin waye daddy,so i wil do my best naga nayi duk abinda nasan cewa zai hanashi sauya komai" kai amir ya kada,shi kansa tsayin shekaru har yau ya kasa sabawa da wasu abubuwan dake gudana a tsakanin samir din da daddy,hajiya qarama tasha gaya masa cewa, professor rashid nason samir fiye da duk wata halitta dake doron qasa,saidai kuma ayyukansa sun qaryata hakan,wannan abun ya sanya shakku a zuciyar shi kansa amir kan sahihancin maganar.

Neman izini da kuma shigowar fawwaz ita taja hankulansu dukka su biyun,babu wanda ya cewa komai a cikinsu,ya qarasa gaban table din saraki ya sakar maaa file din yana daga tsaye,sannan ya juya yana gyara suit dinsa zai fice,amiru yayi motsi da niyyar maida martani,samir ya masa nuni da hannu kan kada ya tanka
Chapter 65 · 0% Book details