← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 117

Sashe 51

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwana biyu a tsakani da yammaci,suna tsakar gida,kaltum tana yiwa inna tsaiba kitso,umma na saman tabarma sanye da hijabinta,da carbinta a hannu tana jan lazumi suna hira jifa jifa,kawu ado da bai jima da fita ba yayi sallama ya shigo

"Amadu ne shida iliya,ke karimatu" ya qwalawa diyarsa kira,wadda ke daki zaune,saita fito

"Dauko tabarma ki kawo dakin soro" ta amsa masa ta juya,ta fito da tabarmar takai musu ta dawo,sanna tace da umma taje inji kawun,bismillah tayi ta yunqura ta miqe ta fice soron.

Kaltum na yiwa inna tsaiba kitson tana saqe saqe cikin ranta,rabi da rabin hankalinta yana ga soron,saidai ba huruminta bane zuwa idan ba kiranta akayi ba.

Suna gama kitson kuwa kawu ado ya leqo ya kirayeta,ta saka nata hijabin tabi sahun ummansu.

Shida kawu iliya dinne kamar yadda kawu ado yace,sai cika yake yana batsewa,ummansu na daga gefe ita da kawu ado.

A sanyaye ta tsugunna ta gaidasu,ita dai bata kula ba baban nasu ya amsa ko bai amsa ba,ta samu waje kusa da mahaifiyarta ta rabe,sanda kawu ado yace

"To gata nan" gyara zama baban nasu yayi yana gyara zaman babbar rigarsa dake saman kafadarsa tare da cewa

"Yauwa.....to gata nan,tana daya daga cikin matsalolina na rayuwa,ta samu miji ta koreshi,kwanaki duk inda nabi sai naga ana nuna ni da baki,ana cewa diyata tayi cikin shege shi yasa aka fasa aurenta,kuma babu dama yayyensu din nan su muzammulu su saka hannu da zummar hukuntasu,sai ta haike musu tace bataso.....to yanzu dai duka ba wannan ba,na yarda zata koma dakinta,amma bisa wasu sharudda,idan ta amince falillahil.hamdi,idan bata amince ba taci gaba da zama,don ni bansan da wanne zanji ba,magana ta gaskiya ehe" ya qarashe maganar yana daga hannayensa sama.

Gyara zama kawu ado yayi yana qoqarin tausar zuciyarsa

"Sharudda kamar wanne da wanne kenan?" Ya tambayeshi yana zuba masa idanu

"Yauwa" ya ambata yana gyara zamanshi

"Na farko....duk sanda yaron nan bilalu ya sake dauko wani abun maganar,zan wanke masa hannu aka,sannan zan sallameshi daga gidana" wani kallo kawu ado ya bishi dashi,ya yunqura zaiyi magana umma ta dakatar dashi da idanunta

"Na biyu kuma....ita kattume,dama ma deba mata kwanakin fidda miji,to tun suna gidan nan kwanakinta sun cika.....zan mata adalci daya,zan qara mata sati biyu kacal ta kawo miji,idan ba haka ba,zan aura mata dan uwanta auwalu kowa ya huta"

Ba kawu ado ba kawai,wannan karon gaba dayansu suka daga kai suna duban baban,wala'alla maganarce tayi musa nauyi,sai ya waiwaya yana kallon dan uwansa

"Ko ba haka ba iliya?" Kai ya gyada

"Wannan haka yake,banda ma lalacewar zamani ai gida bata qoshi ba ba'a kaiwa dawa,sannan duk lalacewar naka ai naka ne,da a zamanin kakannu ne da saidai aji sanarwar daurin aure ma kawai,daga uwa har 'yarta sai a sannan zasusan da batun" ya fadi kamar gaske yana wani tsume fuska.

Wani abu ne yazo ya tsayawa umma a wuya,kaltume kuwa tuni ta fara ruwan hawayem baqinciki da takaici,don ji take kamar ma an daura auren da auwalun,tunda dai a zahirin gaskiya ta sani cewa a yanzun bata da wanda zata bugi qirji tace shine maneminta,kawai sun qulla bata shi,shine za'a ce an bata sati biyu ta kawo mijia,ummanmu na ganin sanda kawu ado ya buda baki zai magana kan wannan hukuncin,tuni ta rigashi,ta bude baki da sauri tana fadin............

30
D/Z

30

"Mun amince indai wannan shine sharadin" da mamaki kawu ado ya kalleta,amma duban data yi masa ya sanya yayi shuru baice komai ba,ya tabbatar akwai sauran bayani a bakinta

"Shikenan,wasalam wa kitabihi,kina iya komawa dakinki" baban ya fadi yana miqewa yana kade babbar rigarsa,kawu iliya shima ya miqe,suka bawa kawu ado hannu,baiqi ba ya basu hannu sukayi musabaha kana suka fice daga dakin.

Shuru neya biyo baya,sai tashin kukan kaltum,wadda ta kasa haquri jin umman batace komai ba,kamar yadda kawu ado yayi shuru,cikin muryar kuka tace

"Yanzu ummanmu,da bakinki zaki amince na auri auwalu?"

"Abinda ya bani mamaki kenan,dukkan wata doka da sharudda da naso gindaya masa sun rushe,saima shi daya bada tasa dokar da qa'idar,bansan meye mahangarki ba zuwaira" kawu ado ya fada cike da mamaki kamar yadda kaltum itama ta cika da mamaki,dukkansu suka zuba mata idanu suna jiran jin abinda zata fada

"Ba zaki auri auwalu ba kaltume,ba zaki auri auwalu ba da izinin ubangiji,ado......kasan gayawa jini na wuce?" Saiya gyada kanshi yana mamakin tambayar data yi masa.

"Sallar dare nada tasiri mai ban mamaki,tasiri mai matuqar yawa,hakanne uasa kadanne daga cikin bayinsa ke ribantarta,take da wahalar da kuma wuyar jurewa,duk kuwa da cewa dukkanmu akwai buqatun da muke nema wajen ubangiji,wanda da zamu tsaya mata.....ba shakka dukka kuka da damuwarmu ta qare,saidai idan har qaddarar hakan bai qare ba cikin kundin qaddararmu,kamar dai qaddarar aurena da amadu.......zanta gayawa ubangiji,....zanta roqarsa,zanta masa magiya game da lamarim kaltume,ina ji a jikina ubangiji zai mata musaya mafi alkhairi,inaji a jikina ubangijina xai share min hawayena,inaji a jikina kukana na shekara da shekaru watan watarana zai zama dariyata,danme zan bata wannan lokaci mai tsaho?,don me zan yanke doguwar tafiyar da jikina ke bani na kawo qarshenta?" Sosai maganganunta suka shigi kawu ado,amma ga kaltum bata fahimci komai ba,bataga wata mahanga ko mafita dange da auren auwalu ba,wanda idan har ya tabbata batajin zata ci gaba da rayuwa a duniya gaba daya,bama iya cikin qauyen ba.

Kawu ado ya shirya musu komawarsu gida,gidan da suke masa kallon wani kurkuku mai tarin qunci takura da kuma tsanani,saidai a hakan ummansu ta zabar musu su koma ciki,basu kuma da wani sauran zabi ko ta cewa.

Sayayyar kayan abinci masu yawa kawu ado yayi mata,sannan ya damqa mata kudi

"Wannan jari na baki,ki nemi abin sana'a don Allah yaya zuwaira,kada ki yarda wannan karon ya amshe miki jarinki ya karyaki bayan bai taba doraki ba" murmushi tayi,ta karba ta kuma yi godiya,tana godew mahaliccinta daya bata 'yan uwa dake qaunarta saboda Allah,ya kuma sanua hadin kai a tsakaninsu,duk da tushiyar bata so ba.

Tun daga sanda suka koma kaltum ta lura da wani binbininta da auwalu yakeyi,bini bini saiya mata siyayya ya faki idanun laure ya aiko mata dash,abun yana bata mata rai da kuma ci mata tuwo a qwarya,da alama an fesa masa cewa shi za'a baiwa nan da sati biyu.

Idan ya aiko da kayan bata ko kallonsu,saboda ummansu ta hanata ta dinga maida masa,saidai idan bilal ya dawo,ya dauka abinda yakeso a ciki ya qara gaba abinsa,don ya riga ya gayawa kaltume

"Yaaya,ki dauka kici,wahalar banza yakeyi kawai,waye zai bashi ke?ni tun sanda ummanmu ma tace bazai aureki ba hankalina ya kwanta,don ummanmu bata magana biyu" a lokacin gani take ba zasu gane abinda takeji ba,kullum kwanan duniya tana kwana ne sa fargaba ta tashi da ita.

***********Zaune take saman kujera 'yar tsuguno daga can magangarar ruwansu tana musu wanki ciki harda kaya bilal,umma tana daga bakin qofar daki tana tsefe kanta,duk da tsaho da yalwar gashinta bata bari ya dade bata sabunta kitson kanta ba.

Sharaf sharaf sukaji tafiya,duk sai suka maida hankalinsu bakin qofa.

Bilal ne ke shigowa da takalman aikinsa a hannu,ya qaraso tsakar gidan ya sulale ya zauna

"Acici mala'ikun tauna,yunwar ce?" Kaltum ta tsokaneshi,don yau koda safe ma baisa komai a cikinsa ba,data yi masa maganae karyawa ma sai yace zaici saiya dawo,baya jin dadin bakinsa ne.

To a nan ma kansa ya girgiza
"Bana jin yunwa,bakina da cikina ne babu dadi wallahi" ya fada yana yamutsa fuska,tare da qoqarin kashingida kan gwiwar hannunsa

"Wannan neman kudin daka sanya a gaba ne,kullum babu hutu,awa a shirin da hudu amma kana bautar da jikinka?ya kamata dai ka dinga hutawa" umma ta fada tana ci gaba da tsifarta

"Zan huta ne umma,nima sai naji inason na huta" ya fada yana zamewa,tare da kwanciya rigingine,amma ya miqe sambal,yayin da kaltume da umma sukaci gaba da hirarsu,har zuwa sanda kaltum ta gama wankin ta soma shanyawa a gurguje a gurguje,saboda koda kiran sallar la'asar da aka fara.

Har umman ta miqe,saita ankara dashi
"Kai bilalu?,meye haka?,kazo ka wani mimmiqe ka rufe fuska da riga kaman wata gawa,tashi kaje kayi sallar la'asar gashi can ana kira" miqewa yayi ya zauna yana dafe da cikinsa

"Umma zanyi a gida,baza iya zuwa har masallaci ba,ciwo cikin yake min"

"Wannan ciwon ciki Allah ya rangwanta,ya yaye shi,saika tashi ka watsa ruwa a jikinka ka daura alwala kayi sallar,sai kazo kasha sauran magungunanka" amsa mata yayi da to,sannan ya miqe cikin dauriya da dakiya,kaltum ta bishi da kallon tausayi irin na 'yan uwantaka.

A iya kwanakin ta lura har dan fadawa yayi,tana yawan ganinsa da daddare idanu biyu,idan ta nema ba'asi sai yace tashinsa kenan.

********"jiya da yau duka banga hard working boy din nan ba....." Saraki ya fadi sanda yake takawa zuwa inda motarsa ke ajjiye tana jiran qarasowarsa,yana kuma cire lethier hand socks din dake hannunsa,wanda yayi amfani da ita yanzu wajen duba ingancin wani sumunti da za'a qarasa plaster ginin makarantar daya kawo qarshe a yanzun

"Kamar bashi da lafiya fa,don shekaran jiya daga nan aka maidashi gida ma,ya fadi ciwon ciki" dakatawa da tafiyar samir yayi,ya waiwayo yana duban umar

"Amma me kukayi akan hakan?" Dan sosa kansa yayi kadan,don yasan amsar da zaya bayar kuskurece a wajen samir

"Babu komai,munyi magana da murtala yace tunda akaji shuru lafiya ce" kadan adams apple dinsa ya motsa,alamun abun ya masa ba dadi,yadan lumshe kyawawan idanuwansa da Allah yayi musu wani irin yanka mai daukar hankali da kwarjini,kamar zaice wani abu saiya fasa,yaci gaba da takawa zuwa inda motar tashi take umar na biye dashi cikin fargaba har suka qarasa.

Budeta yasa akayi,saiya cire 'yar saman rigarshi ya jefa ciki,ya fidda takalmin qafarsa shima ya maida cikin motar,saiya zari slippers dinsa da yake sakawa idan zaiyi alwala a wajen ya sanya,yana nade hannun lon sleeve shirt din dake jikinsa yace

"Kiramin hannafi" ba tare daya waiwaya umar ba,ajjiye litattafan hannunsa yayi ya juya zuwa sashen da makarantar take da hanzari,don suna daga bayan makarantar ne,inda ba wanda yake iya ganinsu,yawancin lokuta anan yake ajiyar motarsa,hakan yasa har yanzu da gini ke daf da kammala ba kowa ne yasan matsayinsa ko kuma waye shi ba.

Minti uku sai gasu tare da hannafi,takawa ya fara yi sannan ya gayawa hannafin inda zasuje

"Gidansu yaron nan.....bilal"

"To mai gida" hannafi ya fada yana shigewa gaba da hanzari.
Chapter 51 · 0% Book details