← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 117

Sashe 4

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hakanan zakayi haquri bilal kaci,idan yaso ko zuwa anjima idan babanku ya shigo sai a sarrafa wani abun"
"Ai wallahi kawai ku rufe garin nan,umma bari naje na samo mana shinkafa....an biyani kudin aikina na shekaran jiya jiya da yau"
"Bilal" umman ta kira sunansa
"Amma shine zaka barnatar da kudin a wunin yau kawai?" Fuska ya narke yana kallon umman
"To umma dama ba don aci ba ake neman?" Sai a sannan kaltum data dauko kofuna ta kalleshi,koda yaushe tunanin bilal din daban yake,abinda ya dameku sau tari shi bashi ya dameshi ba,babbar damuwar bilal din yaji yunwa cikin cikinsa,koda ace bashi da kudi....matuqar zai qoshi to yayi maganin dukkan matsalarsa,abu daya takejin dadi,kamar yadda suke zuwa makarantar allo da sassafe haka shima ke zuwa,duk da karatun nasa baya sauri kamar nasu,amma yana bakin qoqarinsa wajen zuwan da bibiyar karatun.

"Ba saboda ciki ba kawai ake nema....bilal baka sha'awar karatun boko?,kamar yadda yaran kowa keyi?,tunda su 'yan uwanka duka mata ne,kuma su basu samu damar yi ba?" Kai ya rausayar yana nufar qofa
"Wanne karatun boko umma......kawai....kawai....." Bai qarasa furta abinda ke zuciyar tasa ba ya fice daga sashen nasu,kai kawai ta girgiza tana dauke idanunta daga kanshi bayan ya fice,ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana sauke idanunta qasa,tsahon wasu sakanni tana saqar zuci,kafin ta tsinto muryar habiba na fadin
"Umma...an gama" muryarta na nuna ba kiran farko kenan data yi mata ba,kanta ta daga da sauri,da kaltume suka fara hada idanu,tun dazun da tabar musu gangar jikinta,ta dauki zuciyarta ta lula duniyar tunani kaltume ke nazartarta,kullum kwanan duniya cikin damuwa zuciyar mahaifiyar tasu take,damuwa ta zama daya daga cikin abubuwan dake damfare da rayuwarta,takan jima cikin rauni tausayi da wani irin narkewar zuciya a duk sanda ta daga idanu ta kalli mahaifiyarta,macace mai tarin haquri nutsuwa ibada da hangen nesa,saidai matsaloli sun taru sun dabaibaye mata rayuwa,suka kuma hada harda tasu rayuwar sukayi tafiyar ruwa da su.

Duk da nata kofin na riqe a hannunta amma ta kasa shan garin,sai juya cokalin ciki kawai da takeyi,kamar yadda ta karanci ba wani ci sosai umman tasu takeyi ba itama,ita kadai tasan tarin abubuwan dake cunkushe cikin qirjinta,wanda girma da nauyinsu yake sanyata wani lokaci kamar ba zata iya dauka ba.

Bai jima ba bilal din ya dawo da shinkafar hausa gwangwani uku,dai mai da barkono da dunqulen maggi,sai kuma ya zauna ya amshi garin shima ya soma sha,yana yi yana basu labarai wadanda duka kusan abubuwan da suka faru ne a wajen aikin da yakeyi.

Kaltum ce ta karbi shinkafar ta juye saman faranti ta soma tsince dattin dake ciki,tana yi tana sauraren hirarrakin bilal din,wanda a ciki take nazartar abubuwa da dama da suke da alaqa da rayuwar bilal din,wanda wala'alla shi din qarancin shekaru ya sanya hankali da tunaninsa baika ga hango hakan ba.

Kakkaurar muryar data karade filin tsakar gidan nasu zuwa sassan nasu cikin furucin sallama ya sanya kowanne cikinsu ya tsaya cak,yanayin kowannensu ya soma sauyawa daga ainihin yadda yake a dazun zuwa wani nau'i na daban.

Ga kaltum dai sake duqar da kanta tayi sosai ga farantin da tak tsintar shinkafar bayan ta sake riqeshi da hannu daya,habiba wadda ke a kashingide saita tashi ta zauna sosai,ta jingina bayanta da katangar dakinsu,yayin da bilal wanda ke riqe da kofin garinsa,wanda surutu ya hanashi gama sha da wuri ya soma kai garin bakinsa sannu a hankali kamar me tsoron tauna wani abu,ummansu kuwa saita janye qafafunta dake a miqe a dazun,duk da cewar akwai mai ciwo a ciki,amma bata kula da wannan ba.

Dattijo ne wanda a qalla shekarunsa zasukai hamsin da bakwai zuwa da takwas,yana sanye da wani farin yadi da kana masa kallo daya na tsanaki zakasan ba farin Allah da annabi bane,ko ince ba farinsa kenan na ainihi ba,hadda farin dadewa da kuma yadda yake shan wanki,qafarsa slippers ne da ake kira dan madina,wanda wa'adin rayuwarsa yakai tsakiya,ba wani tsufa yayi na azo a gani ba,amma ya dauko hanyar tsufan.

Tun daga yanayin fuskarsa zakasan cewa ba ma'abocin wasa ko sakin fuska bane,wala'alla haka yanayinsa yake?,ko kuma shine ya maida kan nasa hakan?.

Kusan a tare kamar hadin baki suka amsa sallamar daya sake kwadawa,a qoqarin da kowa yake na ganin cewa ya kaucema zama mai laifi na farko a wajensa daga isowarshi cikinsu.

"Sannu da xuwa baaba" habiba da bilal suka hada baki wajen fada
"Yauwa" ya amsa yana sauke kallonsa mai kama da harara kan bilal
"Kai....." Da sauri bilal din ya daga kai yana dubansa hadi da aje kofin hannunsa,don ko bai gama cin garin ba hakanan yakejin ya qoshi
"Uban waye ya daure maka gindin daukar min takalmi ka saka?" Ya fada cikin fada,dukkansu suka kai dubansu ga takalmin dake qafar bilal din,takalmi ne da dadde wanda mahaifin nasu ya jima yana cin duniyarsa dashi,ya kuma kakkatse saboda gajiya da yayi da yadda ake morarsa fiye da kima,dalilin da ya sanya baban nasu ya jefashi cikin tarin shirginsa dake aje dafa'an gefan qofar dakinsa,baiko sake bi ta kansa ba,har sai dazu da bilal din zai fita aiki,bashi kuma da takalmin da zai sanya din,ya dauki takalmin ya fita dashi aka diddinke masa,ko kudin bai samu sukunin biya ba,sai daya dawo daga aikin aka biyashi,sannan ya biya ta rumfar shu'aibun ya biyashi kudin gyaran,amma shine a yanzun daga shigowarsa,ko kyakkyawar iskar gidan bai gama shaqa ba,idanunsa suka sauka kan takalmin,ya kuma dira masifarsa akai.

"Wato kana jina ma ina magana kayimin shuru ko?,ga dan iska yana baloqoqo....koda yake....ba laifinka bane,laifin uwarku ne,ita ta sanya kuka rainani,saboda bani da komai ban mallaki komai ba,to duk tsiya dai nine ubanku,bata isa ta canza muku wani uban ba".

A hankali umman ta saukar da idanunta qasa,tana jin yadda idanunta keson tara ruwan hawaye su fito zuwa saman fuskart don rage radadin da take ji cikin zuciyarta amma ta hana hakan faruwa,kome amadu zaiyi mata,koda yankar naman jikinta zaiyi zata iya jurewa ta shanye,abu daya ne da bataso,takejin tarin tozarci,rashin daraja da qimarta na ratsa har cikin qashinta shine ya tashi wannan tijarar gaban yaransu,yaran da ako da yaushe take tattalin tarbiyyarsu,take yaqi da fadin tashi tsaida martabar ubansu daram cikin idanunsu,koda basu so hakan ba,saidai a kullum shi dinne mutum na farko dake fara hawa kan kyakkyawan gini da tubalin data azasu ya rusa komai da komai,ba gaban yaran ba....hatta da faccalarta kusan haka ne,daya daga cikin abinda ya zamo tushe na zallar raini qanqanci da kyara da take mata ita da yaranta ba dare ba rana,kuma babban makamin gori da tayi riqo dashi,take gallazawa da gasa zuciyarta dashi
"Ahaf....aiki cika mace har a wajen miji shine kika ci sunan mace" wadan nan qayyadaddun kalmomi ta dade tana amfani dasu wasu cutar da zuciya da tunaninta,batakai ga fita daga wannan ba ta sake jin muryarsa yana fadin
"Saboda tsabar iskanci da ganin dama keda 'yarki ban isa kuyimin sannu da zuwa ba ko?,gaku riqaqqu tatattu.....ke dama sababbiya ce cikin yarana kaf kin fita zakka...." Bai sauke numfashi ba bare ya basu damar furta komai ya dora kan gaba ta biyu ta zancansa
"Wannan shinkafar kuma a ina aka samota?,ko yauma anje an saidamun mutunci ne aka baku sadakarta?" Yayi tambayr idanunsa akan kaltume,kamar wanda ke jiran qiris yakai mata bugu,itace mutum ta biyu data fi kowa karbar bahagon halayyarsa baya ga mahaifiyarta,sau tari idan yana wasu halayen a kanta sai taji shakka da tantamar kasancewarsa mahaifinta yana shigarta,cikin sanyin jiki data murya tace
"Bilal ne ya kawo.....,sannu da zuwa" ta hada harda gaisuwar da yake mita a kanta,duk da cewa dama ce bai basu ba da zasu marabceshin,maimakon ya amsa duk da ya nuna muradinsa na yi masa maraban....a'ah....saiya waiwaya ya sake duban bilal wanda ta miqe tun dazu yana jiran ya gama fadan ya shige daki,shi kuma ya samu ya fice,don ya tabbatar ya kuskura ya fitan yana tsaka da fada,ya sake jawa kansa wani sabon al'amarin
"Wato kai na fuskanceka,mugu ne kai wani lokacin,ni ina can ina fafutukar sama muku abinda zakuci,kai kuma kana nan kana kashewa uwarka da 'yan uwanka duniya,tunda kake nemanka qwandala baka taba kawomin na sanya albarka ba,saboda tsabar baqin hali irin naka,shegen yaro dan iskan banza da wofi,fitarmin daga gidana kafin na sanya itace na sauke maka gwiwoyi"idanu umma ta rintse sosai,tana jin wani zafi yana ratsa qirjinta,koda zaiyi sala sala da namansu 'ya'yansa ne,bata data cewa,bata kuma da wani iko saman nasa,saidai bata qaunar kalaman da yake yawan furtawa akan bilal da kaltume,kalamaine da duk yadda takai ga jurewa dauke kai da alkunya amma sai sun taba can cikin zuciyarta,tana tsoro....tana tsoron wani abu.....wani abun da bame kyau bane da zai iya faruwa watan watarana,ko ba komai shi din mahaifi ne,daya kamata ace shi ya zama garkuwa ta farko a garesu.

Bin bilal yayi da kallo.harya fice sannan ya dauke idanunsa,ya taka ya nufi dakinsa dake a kulle da muqulli,dakin da dukkansu haka suka taso suka ganshi,koda yaushe a rufe,baya barin kowa ya gitta ta qofar dakin bare akai ga batun shiga ciki,koda mahaifiyarsu kuwa tana da geji a dakin,baresu karan kada miya da basusan komai ba,banda kalar labulen dakin babu abinda zasu iya dorarwa a cikinsa.

Suna jin sanda ya wulla taliya qwaya biyu daya shigo da ita a baqar leda cikin dakin,wadda dama bai taba basu sama da hakan ba yana mitar
"Tunda kunyi gaban kanku kun samowa kanku abunci aini gaba ta kaini" sannan ya dauko butarsa daga cikin dakin ya wuce bayi.

Shuru ne yaci gaba da wanzuwa a tsakaninsu,kowanne da irin tunanin dake kai kawo tsakanin qwaqwalwa da zuciyarsa.

Sosai wani irin bacin rai yake ratsata,har bata qaunar koda motsawa ne ma tayi bare tayi tozali da fuskar mahaifiyarta,fuskar data tabbatar babu abunda ke yawo a samanta illa bacin rai wanda ke cike maqil a zuciyarta,duk da kasancewarta jaruma,mai qarfin hali juriya da jumurin cinye duk wani bacin rai,saidai kasancewarta cikin 'yan adam da aka halitta da ajizanci....qoqarinta wani lokaci yakan gaza kaiwa ga gaci.
Chapter 4 · 0% Book details