Sashe 78
Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har suka shiga suka zauna yana duba wayar hannunsa,shuru yaci gaba da ratsa office din,lokaci lokaci tana satar kallonsa,abinda ke fado mata a rai kawai shine....maganar mubina data tabbatar tana da alaqa da shi,sai kuma yarinyar yanzu,mamaki ke kai kawo a ranta,me yasa kowa sonshi yakeyi?,idan bata manta ba mata kusan uku tana gidan sunzo ne kawai saboda shi,wasu su wuni su tafi,tana nazartarsa tsaf,tun asali mutum ne mai girmama kowa musamman mace,bashi da wulaqanci saidai ya iya jan aji da kuma mutunta kai,hakanan sauqinsa baisa ya zama me daukar raini ba.
Bata tsammata ba ya dago kai sai suka hada ido,da sauri ta janye idanunta ta mayar kan wani dan qaramin frame dake dauke da certificate of honor da aka baiwa asibitin.
Karamin murmushi ya saka,ya gane cewa ta iya basarwa itama,saiya maida wayarsa aljihu a hankali,yaji yana son qureta,don haka ya kafeta da idanu,so yake ya kamata red handed,ya kuma tabbatar mata da kallonshi takeyi,abinda ya fuskanci tana avoiding kenan,don tun dazu da idanunsa ke kan wayarsa jikinsa ya tabbatar masa da kallonsa ake.
Wasu mintuna ta diba da take da tabbacin ya koma sabgar da yakeyi,zuciyarta naci gaba da raya mata ta sake juyawa ta kalleshi ko zata gane abinda yasa mata ke sonshi.
A hankali take juyar da kanta kamar me ciwon wuya,caraf ya sake kamata,ta kuma dauke kanta da sauri tana jin kunya fiye da dazu,wannan karon murmushi yayi mai dan sauti,sannan ya hade hannayensa a tsakiyar qafafunsa,cikin lallausan muryarsa yace
"Me yasa kuka gwanance wajen iya satar kallon mutum,sai kuma an kamaku kuji kunya.....amma ke me yasa bakya son na kamaki kina kallona?"
Daburcewa tayi sosai,nauyi da kunya suna cikata,karon farko da taji wasu kalamai da suka samu matsugunni a ranta har suka rudata,itama batasan tsautsayin da yasa ta nace saita kalleshin ba,kame kame ta fara yi,tahau gyara fuskar hijabinta,gyaran da bashi da tushe bare makama,hakan yasa ya sake kafeta da ido.
Sosai ya lura baqin fuskarta dukka a yanxu babushi,sai wata kala da fatarta ke fitarwa ta daban.
Sauko da idanunsa yayi saitin qirjinta,har yau bai gasgata jawahir data ce wai ta isa saka breezier ba,cikin wani mugun sauri ya kauda da idanunsa sanda ya rage qiris ta ganshi,ya sauke boyayar ajiyar zuciya yana godewa Allah da bata ganshi ba,da girmansa ya zube.
Kafin wani a cikinsu ya sake wani motsi an turo qofar dakin anshigo.
Dogon likita baqi,mara jiki sosai,saidai akwai alamun nutsuwa sosai a tattare dashi.
Hannu ya bawa samir sukayi musabaha,sannan yaja kujerarsa ya zauna yana amsa gaisuwar kaltum.
File din dake gabansa wanda da alama sabone ya bude,ya fara yiwa kaltum din tambayoyi.
Da qyar take iya amsawa saboda nauyin da takeji,kusan tunda ta girma ba'a taba sakata gaba ana mata tambaya irin makamanciyar wannan ba,samir na zaune kam kujerar yana monitoring nata har likitan ya gama.
"CT scan za'ayi mata,shine zaifi nuna dukka abinda nake buqatar gani,saidai akwai 'yar tsada" ya fada yana qarasa rubutunsa jikin file din.
Tunda suka shiga dakin scan din gaba daya tsoro ya kamata,musamman data kalli machine na scan din,har batasan sanda ta tara qwalla a idanunta ba,ta waiwayo tana duban samir dake tsaye a bayanta,hannunsa daya cikin aljihun wandonsa,yayin da daya hannun nasa yake dan saman kanshi yana shafawa a hankali gami da karanta wani rubutu dake manne a farar takarda jikin bangon dakin.
A hankali wata nurse ta tura qofar dakin tashigo,hannunta dauke da wata riga da tafi kama data marasa lafiya,ta ajjiye rigar saman wani dan abu,sannan ta isa wajen machine din tana goge gadon dake maqale dashi,gami da gyara shimfidar kai.
Sai data gama tsaf kaltum na tsaye tana kallonta,ji take kamar ta zura da gudu tabar dakin saboda tsoro,gefansu nurse din ta tsaya tana ajjiye wasu allurai,sannan ta fara hadesu waje daya a syringe
"Idan na gama miki wannan allurar,zaki cire abinda kikasan akwai qarfe a jikinsa da yake jikinki,kamar bra da rigarki da kuma skert tunda akwai zip a jiki,saiki sauya da wannan rigar" ta fada tana nuna rigar da yatsantsa.
"Bismillah qaraso" ta fada tana duban kaltum sanda ta gama hada ruwan allurar waje daya.
Kanta ya daga sai suka hada idanu da samir wanda ya kafeta da ido,tuni ya hangi tsoro muraran cikin idanunta,saiya taka a hankali,ya isa wajen,yaja wata kujera dake gefan nurse din zuwa gabanta,sannan ya yiwa kaltum din nuni kan tazo ta zauna.
Narai narai ta sakeyi da idanu ba tare data ko motsa ba,wani qaramin murmushi ne ya subucewa fuskarsa,ya gane tsoron allura takeyi,abunda ya bashi mamaki,saboda ya tuna tsiwarta,baiyi tunanin zatayi tsoron allura ba
"Hala madam din taka tsoron allura take,anya basa an riqe mana ita ba?' matar ta fada tana murmushi hadi da miqewa riqe da allurar tata.
"Bari na taimaka miki" yace da matar
Hannunsa ya cire daga aljihun nasa,ya qara taku biyar zuwa inda take tsayen,ya tsaya daga bayanta,,dab da ita sosai,har tana jin hucin lallausan turarenta
"unhummm......remove it" ya fada a hankali kamar me rada,abinda yasa taji gaba daya ta diririce kenan,kusancin dake tsakaninsu tana jin yayi yawa,saita sanya hannu a hankali ta dage hijabin nata,ta kuma miqawa nurse din hannunta,gami da rintse idanunta sosai saboda tsoron tsinin allurar.
Wani qaramar qara ta saki sanda aka saka allurar,ta yamutse fuska sosai tana jin wani iri har zuwa sanda ta zare syringe din tana cewa
"Muna gab da tashi,da sauri madam ki canza kaya sai kuyimin magana"tana kaiwa qarshen maganar ne sanda take bude qofa ta fice.
Kanta a qasa tana mulmula wajen da aka yi mata allurar,tana tsammatar jin ya fita amma bataji ya motsa ba,harta gama ta cire audugar
"Be hurry" ya fada muryarsa qasan maqoshi yana kallonta,batasan ya zata ce masa ba,amma hannunta ya qage,batasan da yadda zata cire kayan ba.
Kamar ya karanci matsalarta ganin bata da niyyar motsawa saiya sake takowa zuwa inda take,ya saka hannu a hankali ya zare hijabin jikinta,wanda ya hado da dankwalin dake kanta gaba daya ba tare da yasani ba.
Sassalkan gashinta data matse da dan qaramin band ya ware gaba daya ya bazu daga baya zuwa fuskarta.
Idanunsa ya dauke da sauri yana lumshe idanunsa,saiya bude ya sake maidawa kan sumartata dake qyalli a hasken fararen qawayayen dake dakin,jiya jiya jawahir ta tirketa aka tsefe ta sake wankeshi,ta kuma sanya streacher ta ja mata shi,ita tana mitar bai tsufa ba kuma baiyi datti ba,jawahir din kuma tana mitar dama masu gashi basason kitso ko kuma a taba musu kansu,inama itace keda suma kamar tata da anyi kallo.
Hannunsa biyu ya sanya ya tattaro gashin dake qamshin man da akayi oiling dinsa dashi dake dukan fuskarsa,daure mata shi yayi,sannan ya sake qara taku biyu yana rage tazarar dake tsakaninsu,ya sanya hannuwansa duka biyu ya juyo da ita tana fuskantarsa.
Hannunsa ya dora saman zip din rigarta ya zuge mata tun daga sama zuwa qasa,idanunsa na kallon wani waje na daban,saboda qamshin turarenta da yake shaqa sosai,wanda baisan me yasa yake sauya bugun zuciyarsa ba.
Sai da yakai zip din qarshe sannan ya saketa a hankali,yayi taku biyu baya sannan ya juya yana takawa a hankali cikin wani mutuwar jiki zuwa bakin window din dakin,bayan ya maida hannuwansa cikin aljihun wandonsa,daya hannun kuma yana duba agogon hannunsa yana cewa
"Ki canza da sauri karmu bata musu lokaci" ya dage labulen yana kallon farfajiyar asibitin.
Bude qofar akayi,amma duk da haka bai waiwaya ba,har zuwa sanda ya sake jin muryar nurse din
"Sir,she need your assistance,allurar tana dan riqr hannu" gaban kaltum yayi mugun faduwa,wannan matar zata jiqa mata aiki,riga a bude tana kokawar cire bra,ta samu ya kalli wani wajen kuma tayi calling attention dinsa,a hankali ya waiwayo,idanunsa suka sauka a kanta sanda ta tsaya cak da abinda takeyi din,zuciyarta na harbawa a jajjere,bata iya sake daga kanta ba harya sake iskota,wanda taji kamar ya bace bat daga dakin,zuciyarta ta qara nauyi sanda dumin hannunsa ya ratsa fatar bayanta,ya saka yatsuntsa guda biyu ya balle damammiyar bra din jikinta,wanda hakan ya baiwa abinda ta takura din damar sakewa.
Ajiyar zuciyar data kusa fita ita ya subuce mata sanda yake sabule rigar daga jikinta,yanayin komai ne yana tsaye daga bayanta,ya dauki rigar ya zura mata yana cewa
"Hurry up"
Da saurinta ta saka rigar wadda take ta yadice,a tsaye kamar ta masu aikin shara a asibiti.
"Ya salam!!" Ya fada qasan ransa har sai da labbansa suka motsa,da wani irin amo mai nauyi sanda kaltum ta juyo ta soma takowa zuwa wajen machine din kamar yadda nurse din ta bata umarni,tana jin kamar zata fadi da saboda nauyi,tana iya jin yadda rigar ta lafe a jikinta,ta kuma bayyana surarta dukiyar fulanin da Allah ya mata baiwarsu,take kuma boyesu tun daga sanda suka fara bayyana kansu,saboda kunyar hakan da takeji,har da yawa suke mata kallon qwaila.
Wani irin laushi da yaji qafafunsa sunyi suna shirin gaza ci gaba da daukan nauyin tsaiwarsa sai yaja kujerar dake dakin ya zauna,yana kallonta har zuwa sanda ta kwanta saman gadon kwanciyar rigingine kamar yadda nurse din tace mata,hakan saiya zamana kamar dama ce suka samu ta bayyana kansu sosai ta cikin rigar,gaza ci gaba yayi da kallonta ya zare idanunsa ya maida ga machine din sanda gadon ya dagata sama ya kuma turata tsakiyar machine din.
Shuru ne ya ratsa dakin,babu komai sai qarar machine din daketa wasu bayanai,ko sau daya bai qara daga idanu ya dubeta ba,yayin da kaltum tsoron machine din da kuma abinda ya farun ya karya duk wani kuzari nata,tanajin wani nauyi na ratsata,tunda take wannan shine karon farko da wani ya taba ganin ainihin surar jikinta,saita lumshe ido tana tuna yadda taji hannunsa saman jikinta,zuciyarta naci gaba da bugawa da sauri da sauri.
Duba takaddun likitan yayi ya ajjiye CD plate din da suka hado dashi,tsahon wasu mintuna sannan ya dubi samir
"Gwajin da nayi mata a nan,da kuma wannan scan din ya nuna komai,akwai qarancin sinadarai a jikinta wanda zasu taimakawa zuwan period a jikinta,kuma hakan zai zamana yana da alaqa da matsalar haihuwa,so amma ba wani damuwa in sha Allah,akwai magunguna da zata fara sha daga yau zuwa sati biyu,suna da kyau magungunan sosai,zasu taimaka wajen samuwar sinadaran isassu da zasu kawo mata al'adar a kusa,kuma ina saka ran insha Allah tana kammala shansu period dinta na farko zaizo"