← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 117

Sashe 41

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sati gida cur tayi tana jinyar jikinta kafin ta warware,a tsahon satin bata ga koda gilmawar mai kama da wasila cikin gidan ba bare ita,sai tarin qawayenta da kullum ke kaw mata zancan abinda wasila keta yamadidi dashi.

Dakatar dasu tayi,ta kuma shaida musu batason ji,saboda jin bashi da wani amfani,hakanan babu wani magani da zaiyi mata,face baqin wasila da zata dinga gani.

Randa ta cika satin misalin sha daya na rana,tana tsakar gida tana tsince musu busashshen zogale da suke shirin yin miyar zogale ayau din,cikin shinkafar da yakumbo indo ta ajjiyr musu,har zuwa yau kuma suke amfanarta.

Alamun sauti kamar na kuka datake jiyowa kamar daga nesa kadan da inda take yasa tayi sak,ta kuma dakata da abinda takeyi,tana jiran taji daga ina kukan ke tahowa.

A hankali taji alamun sashensu yake yowa,kuma kamar muryar habibanta,abunda yasa babu shiri ta dangware farantin dake kan cinyarta ta miqe tsaye,gabanta da wani irin mugun faduwa,ta zubawa qofar shigowa sashen nasu idanu,tana jira tagani shin ita dince?,idan itace da wacce tazo?,me kuma ya faru,bugun zuciyarta na daduwa har batasan ummansu ta fito tana tsaye daga bayanta ba itama tana jiran shigowar habiba,dukkaninsu kowa ya kasa motsawa daga inda yake tsaye bare yaje ya tarota.

D/Z
23

*_Littafin kudi ne,ki guji shiga haqqin wasu ta hanyar yadawa,ki tuntubi wadan nan numbers din don biyan naki ki karanta cikin aminci_*

08184017082
Ko kuma
09134848107

Ba'a dauki wani dogon lokaci ba habiba ta bayyana a tsakar gidan,zani daban riga daban,idanuwanta sunyi jazur dasu,da alama kuka tasha take kuma kanyi har yanzu.

Sai a sannan kaltum ta samu qarfin halin tunkarar habiban,hankalinta a matuqar tashe duba da yanayin data shigo dashi,riqeta kaltum tayi tana jaddada tambayar

"Lafiya?,habi lafiya?".

Bata iya magana ba sai da suka isa gaban umma da tayi mutuwar tsaye,cikin qarfin hali itama ta sake tambayarta

"Umma.....anacan ana yamadidi da yaaya a gari wai tayi cikin shege,dalilin kenan daya sanya wai ya munzali yayi mata dukan tsiya".

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda ummanmu ta ambata,a tunaninta cikin zuciyarta tayi,saidai tsabar rudanin data samu kanta a ciki baisa ta fahimci a fili tayi ba har sai da sautin ya fito,saita nema jikin katangar dakinta ta jingina tana kamo hannun habiba gami da zaunar da ita cike da qarfin hali,wanda kaltume ma da taji tana niyyar faduwa saita sulale ta zauna kusa da 'yar uwarta.

Duk wani yawun bakin umma ya bushe,ta qaqalo wani da qyar sannan ta samu damar yiwa habiba bayanun yadda komai ya faru

"Na sani ummanmu,yaaya ce fa,ni nasan ba zata taba aikata wani abu mara kyau ba,bansan iblishin da yaketa yada zancan ba,har gida aka sameni tun shekaran jiya ake gayamin,baaba ce take korarsu fata fata,tace batason gulma su tashi su bamu waje,to umma daga shekaran jiya zuwa yau karo na hudu kenan ana zuwarmin da zancan,wannan wanne irin bata suna ne umma?,me muka yiwa mutane?" Sai kuka ya sake kubce mata,wanda a wannan karon ita kanta umman bata data cewa,ta rasa dukka kalama bakinta.

A daidai lokacin inna laure tayi sallama a tsakar gidan nasu cikin nuna hali na gigita,shigowarta yasa habiba saurin boye kuka ta tare da goge fuskarta,don ta sani ba alkhairi bane ya shigo da ita ba.

Diri diri ta fara yi,kafin daga bisani tace

"Zuwaira lafiya habiba ta shigo tana kuka?,ko daga gidan aurenta ne?" Idanu umma kawai ta zuba mata tana dubanta,tana kallon zallar rashin alkhairi daga laure,wadda a kullum bata fatan musu alkhairi sai sharri

"Ba komai sai alkhairi" shine amsar da umman kawai ta bata,saita juya tana cewa

"Au too.....to Allah yasa,koda yake idanma ba'a gaya mana ba idan tayi tsami zamuji,kamar yadda mukaji na dayar muna daga zaune"

Wani mugun kallo kaltum ta bita dashi,duk da cewa a yanzun takanta take da mummunan baqin sharrin da aka laqaba mata,tabbas da zata samu dama da saita maidawa inna lauren martani dai dai da maganarta.

"Saurareni habiba da kyau......" Umma ta fada tana yunqurin baiwa kata qearin gwiwa,saboda ta hangi rauni a idanun dukkaninsu,kuma ta tabbatar cewa qwarin gwiwar da zasu gani a idanunta itace zata motsa tasu jarumtar

"Kowanne bawa da kalar qaddararsa,wani tasa tafi wanna muni,dukkaninmu mun sani hatta da annabawan Allah an jarrabesu,halitta mafi soyuwa ga wanda akayi duniya da lahira saboda shi annabi Muhammadu wato nana aisha an jefeta da qazafin zina,ko kin manta?,kina tunanin indai hakane akwai wanda zai tsallake?" Kai ta girgixa a hankali,daga ita har kaltum din suna jin nutsuwa ta fara saukar musu,hakan ya bata qwarin gwiwa naci gaba da maganar da takeyi,duk da ita kadai tasan abinda takeji a zuciyarta.

"Duk wanda ya jefeku da sharri ko qazafi,ku barwa Allah komai,shi baya zalunci,kuma baya yarda a zalunci bawa,da sannu zai fitarwa da dukkan me haqqi haqqinsa komai daren dadewa" cikin hikimar iya zance,da qwarewa irin ta uwa ta gari ta sauke rudu da dimuwar da suka shiga,sannan daga qarshe ya dubi habiba

"Yanzu yusufa yasan kin fito?" Kai ta jinjina

"Ya sani ummanmu,shine ma ya rakoni,baaba tace ya rakoni saboda jikina babu dadi" sam sun mance da batun ma lalurarta saboda wannan yanayin da suka shiga

"Alla ya sawwaqe,saiki tashi ki koma gida ai ko?"narkewa habiban tayi

"Ummanmu ya barni fa,yace na zauna har dare,zaizo ya daukeni".

Zaman nata ya yiwa kaltum dadi sosai,ya debe mata kewa fiye da kima,tayi rashin 'yar uwa a kusa,wanda bata sake gasgata hakan ba sai yau da suka wuni tare cur da habiban,tsoro da fargaba dake ranta kaso mafi yawa ya ragu a ranta.

A nan babansu ya dawo ya taddata,ya fara zabga sababi kenan kan ta tashi ta tafi gidanta,shi ba mahaukaci bane da zatazo ta zaune masa.....saiga yusufa dan halak,harda tsabar kayan marmarinsa,lemo,kan kana da ayaba harda biredi.

Ita dai umma ta sani cewa,ubangiji kawai ya dubi irin rayuwar dasu habiba ke ciki ya bata miji na kerewa sa'a,hakanan itama ya dubeta,ya duba darajar addu'ar da take musu ya hadata da surukai na gari,fatanta ubangiji yasa 'yar uwarta kaltum ta dace kamar yadda itama ta dace din.

Suna kewar habiban itama tana kewarsu yusufa ya tasa kayarshi a gaba suka tafi gida,saidai ba wata damuwa bace mai yawa a ransu,saboda sunsan tana samun kulawar da bata taba samun irinta ba cikin gidan mahaifanta.

*******WASHEGARI********

Ƙarfe goma na safiya tana duqe tana sake sharen wajen da bilalu ya gama dabdalarsa bayan sun gama karin safe,tana yi tana mitar sai tayi maganin bilal din,yayin da shi kuma yake shirin fita aiki abinsa yana dariya

"Haba yaaya kattume ta wajena,kasa kisa a ganmu a rana mana ayi mana dariya" umma dake kwance cikin daki saboda zugin da qafarta takeyi mata ta tabe baki,saman fuskarta kwance da murmushi,dramer din kaltum da bilal sai su din,ka gansu nan ka qyale kayi wucewarka abinka.

Kayan ummansu da babansu data jiqa ta nufa ta soma daurayewa,tun bayan ciwon da tayi sai yau zata fita,zata zagaya bayan katangarsu ta yiwa wata amarya da aka kawo daga qauyen kusa dasu kitso,shi yasa take aikin da hanzari hanzari,tayi ya gama taje,don tun jiya ta aiko amma bata samu zuwa ba.

Sallamar da aka rangada ce ta sata waiwayawa bayanta inda qofa take,duk da bata dago daga abinda take ba,ta amsa tana ci gaba da wankin,saidai yadda aketa koda sallamar a jejjere yasa ta saki zanin ummansu dake hannunta,ta miqe sosai tana amsa sallamar,zuwa sannan har sun iso filin tsakar gidan dake sashen nasu.

Mata ne su su uku,kowacce sanyi da hijabi,suna rarraba idanu gami da kallon kowanne lungu da saqo na gidan,hakan ya sanya kaltum sake amsa sallamar,ga zatonta ko basuji ba,ko kuma basu gan bilal ba,idanma haka ne gata ita dake tsaye tana kallonsu.

Sake amsa sallamar saiya zamana kamar kiran jan hankali kuwa a garesu,gaba daya suka waiwayo suna kallonta.

Idanunta suka haska mata fuskar daya daga cikin matan,kamar ta santa,kamar lantai babar nasuru,duk da cewa sai daya tabtaba ganinta,amma bata da saurin mance abu,tabbas ita dince,sai kunya da nauyi suka kamata,da sauri ta jawo hijabinta dake ka igiyar dake daura dasu ta zura tana fadin

"Baaba sannunku da zuwa" kafin a hankali ta nufi gabanta,ta durqusa a saman gwiwarta tana gaidasu,yayin da bilal dake gefe shima yake tayata gaisuwar.

Babu wanda suka amsa gaisuwarsa a cikinsu,sai daya daga cikinsu ce ma ta taushe gaisuwar da tambayar

"Babanki yana nan?" Kai ta girgiza cikin mamakin lafiya?

"Bai jima da fita ba"

"Babarki fa"

"Tana daki,tada kwanta ne batajin dadi"

"Ba wannan muka tambayeki ba,kira mana ita maza maza,sauri mukeyi" mamaki sosai ya sake kamata,amma duk da haka bata fasa qarasawa ta dauko musu tabarmar kaba ta shimfida musu ba,dai dai lokacin da taji daya daga cikinsu na cewa

"Lanti itace?"

"Eyi.....itace".

A kwancen ta tadda ummansun,bacci ya fara daukarta,motsin shigowarta ya farkar da ita
"Yaya akayi?,bilalun ya tafi?" Kai ta kada,rabin hankalinta yana ga tsakar gida

"Baqi kikayi"

"Baqi.....ganinan" ta fada taba miqewa zaune,saita daura dankwalinta ta rufe gashinta da har yanzu yake da santsi sannan ta miqe cikin qarfin hali tabi bayan kaltum wadda bayan ta shaida musu gata nan,saita kasa zama tsakar gidan ta wuce dakinsu,su kuma suka rakata da kallo,kasa zama tayi,ta rakube bakin windownsu,tana jin gaba daya qafafunta sunyi sanyi da laushi,kamar ba zasu iya daukarta ba.

"Sannunku da zuwa,ya kuke tsaye ga shimfida anyi,ku zauna mana" cewar umma cikin fara'a da faram faram

"Ba zama mukazo yi ba,duk gidajenmu akwai wajen zama,hasalima saqon daga tsaye sai yafi tafiya" dan dumm umma tayi mamaki yana daureta,har ta gaza daurewa tace

"Tooo,ikon Allah"

"Ikon gaske......" Suka maida mata,sannan daya daga cikin ta matso gaba,ta yadda ta fita daga jerin matan

"Gwara na matso sosai yadda zakifi ganeni.....sunana lanti,nice nan na haifi nasuru da kaina,ba doguwar magana ko jan zance ya kawo mu ba,don haka baro baro za'a yita.....mun samu labarin cikin shegan da 'yarku tayi,sahihin labari kuma daga majiya mai tushe,wato daga bakin mafiya kusanci da ita har mutum biyu,saboda haka mukazo mu shaida muku cewa.....mun yanke igiyar alaqar auratayya da akazo aka tambayawa dana,babu shi babu 'yarku,kudin aure da muka kawo kuma nan da anjima manyansa zasu zo su karba a mayar masa da abinsa....."

Duk da rudanin da umma ta shiga,amma tayi namijin qoqarin dannewa

"Shikenan saqon naki?,inason komawa daki?"
Chapter 41 · 0% Book details