← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 117

Sashe 10

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

**********
Shuru gidan yake sakamakon dare daya shigo,bayan sallar isha'i ne,bilal baya nan ya fita,wanda dama yawanci bai shigowa gida da wuri,barci ne kawai yake maidoshi,kamar ma bayajin dadin gidan sam,fadi ne kawai da baiyi ba,habiba kuwa na zaure ita da yusufa,wanda tuni ya aiko aka nema masa izinin zuwa wajenta,cikin ikon Allah kuma sai Allah ya hada kansu da hankalinsu gaba daya,yusufa da iyayen nasa ma gaba daya ba wasu baqi ko boyayyu bane,kowa yasan gidansu halayyar mahaifansa dama na yaran gidan,dalilin da yasa baaban baiyi wani musu ko goce goce ba ya bashi izini kai tsaye,don dama shi din kamar yana neman hanyar da zai rabu dasu ne.

Tsakar gidan daga ita sai umman nata,ita ta dasa farantin dake dauke da ragowar wata guntuwar shinkafa tasu tana tsinceta,don ita ce kadai abinda ta rage musu cikin gidan,itama cikin kudin da kawu ado ya basu ce suka siyota suketa ci da kadan kadan,sam abincin da mahaifinsu yake basu baya daga cikin abinda suke lissafa ko sanya rai,saboda babu tabbas din samuwar abincin,idan yaga dama ne ya kawo,idan baiga dama ba kuma ya barsu haka,sa nema suci.

Hira suke jifa jifa da umman,tana magana ne kan bikinsu idan ya taso,ta sani bata da komai,kuma bata bawa kowa ajiya ba,juyayin da take nunawa kenan,kaltum dake tsintar shinkafa kanta a qasa tace
"Babu komai umma,kiyi addu'a,Allah zai kawo da ikonsa" tana rufe baki suka hangi inuwa daga bakin qofar shigowa sassan nasu,hakan ya sanya kowa yaja bakinsa ya tsuke suna duban inuwar,ba'a cika minti daya ba wanda ke laben ya fado,mahaifinsu ne,duk da tsakar gidan babu wadatar haske amma suna iya ganin yanayin fuskarsa
"Munafukai....zancan wa kuke?,munafurcina ko?" Waike zuwaira me yasa kullum ta Allah baki da qoqarin da ya wuce ki barar min da mutuncina a idanun yarana?....ke kuma annamimiya muna fuka,tashi ki koma daki!"ya dakawa katum tsawa,wadda batasan hawa ba batasan sauka,saita sauke farantin kawai ta miqe zuwa dakinsu kamar yadda ya buqata,batasan me yasa ya tsani yazo ya ganta tare da mahaifiyartata a zaune su biyu suna hira ba,koda yaushe yana ganin kamar idan suka zauna kamar hakan hirarsa sukeyi,abinda bai sani ba shine,umman tasu bata taba tattauna kuskurensa ko sakacinsa dasu ba,bata daga cikin irin wadan nan matan,hasalima kosu basu iya suyi qorafi a kansa ba,duk yadda suka kai ga shaqar baqiciki ko bacin ransa,tana horarsu da suci gaba da kyautata masa,ubansu ne,mahaifinsu ne,kamar jiya,datayi kitso ta samu kudi,ta siyo sabulu,ta dawo gida tana tattara kayan umman tasu da sukayi datti,amma ba'a samu damar wankewa ba saboda babu kudin sabulu,amma sai umman ta dakatar da ita
"Kibar nawan,a wanke a gaba,ki debo na babanku,naga wankakkun nasa sun kusa su qare" bata isa ta musa ba,haka taje ta debo kayan nasa,duk da cewa dama can itace mai wanke masa kayan nasa,saidai ko idan wani dalili yasa bata yin ba,bilal zai dauka ya wanke masa,haka ta debo nashin,ta kuma qarar da sabulun kaf a kansu,saidai taci alwashin da zarar tayi wani kitson koda nata ba'a wanke suke,zata fara wanke na umman nata.

Daga cikin dakin tana iya jiyo sababin da baban nasu yakeyi,wanda ita batasan dalilinsa ba,idanunta ta rufe gaba daya ta kwanta rigingine,tana jin yadda kullum kwanan duniya rayuwa ke sake musu nauyi da kuma tsanani,a zuciyarta....bilal da habiba su tafi tausayawa fiye da kan kanta,sai kuma mahaifiyarsu,tana jin da tana da iko da su zata fara tsamewa daga wannan rayuwar da suke ciki,ta kowanne fanni babu dadi,babu wata walwala babu farinciki,batasan iya tsahon lokacin daya kwashe yana sababinsa ba,sai shigowar habiba taji,hannunta riqe da baqar leda,ta aje gefan kaltum tana dubanta
"Yaaya,kada dai ace har kinyi bacci" bata amsa ba sai miqewa da tayi ta zauna kawai tana duban habiban
"Idona biyu,baba yana nan?"
"Eh.....kamar yana dakinsa"
"Umma fa?"
"Tana bakin rijiya,ruwa take ja masa" ajiyar zuciya ta sauke,bakinta ya kasa furtawa habiba dake kallonta komai,har sai da ita habiban ta magantu
"Baba ne ko?" Bata iya amsa mata ba,sai kai kawai data gyada mata,bakinta ta tabe
"Ni ai gwara mutum kawai yayi aurensa ya huta da wannan rayuwar,yaaya gwara kawai muyi aurenmu,ko itama umma ta samu sauqin wasu abubuwan,tunda kinga ko banza zamu dinga taimaka mata da wasu abubuwan,sannan yusufa ma ni yace babu matsala,koshi xaya yimun kayan daki,don shi a nan kurkusa yakeso ayi komai" daga haka ta janyo.ledar ta bude,awara ce mai zafi mai uban yawa,sai qunshin tsire,sai rake wanda aka gyarashi fes,aka yankashi qananu
"Kinga abinda ya kawomin" ta fada tana turawa kaltum ledar,kalla kawai tayi,saita saki murmushi tace
"An gode" yusufa yana da qoqari,yana kuma da hannun kyauta,hakanan yana da kirki kamar yadda ake cewa mamansa ma haka take,sosai kaltume ke yiwa habiba sha'awar aurensa,a yadda kowa ke yabon halayyarsa,tana sanya mata ran cewa zata dace da gidan aure in sha Allahu.

Matsantawa kaltum tayi,har sai data raba abun kashi hudu,nata dana umma dana kaltum din saina bilal,basuyi tunanin su raba da baban ba sam,saboda sun riga sunsan halayyarsa,yanzu akan wannan sai qilu ta jawo bau.

*******

Karfe biyu da minti talatin da uku na azahar ta dage labulen dakin ummansu,wadda suke ciki ita da habiba sunata sauke kayan kwalla na mahaifiyar tasu,da tayi shawarar gwara ta saukesu ta saidasu tun yanzu saboda bikinsu,tunda ba wani abu suke tsinana mata ba
"Umma na gama zan tafi"
"To Allah ya kiyaye,kina gama mata ki dawo gida,kada babanku ya rigaki dawowa"
"In sha Allahu umma bazan zauna ba"
"Saikin dawo yaya" habiba ta fada,ta amsa mata tana sauke labulen kana ta doshi qofar fita daga gidan.

A farfajiyar data hada sassan nasu ta samu baabar asiya da suke kira da baaba laure,a zaune saman tabarma,qaqashin inuwar bishiyar data baza rassanta a filin tsakar gidan,da alama sassan nata ya dauki zafi,da yake shi rana yake kallo,hatta da rumfar dake sashen idan rana ta take zafi take dauka,a nan kawai suke xama su samu iska da inuwa mai kyau,sabanin nasu sashen,da ya bawa rana baya,saidai dakunansu kawai su dauki zafin,amma banda tsakar gidansu,duk da cewar tun asali kowa a muhallinsa yake a zaune,amma baba laure sai data qalubalanci hakan,tace anyi ne da gayya ana sane aka bata nan din,saboda rana tayi mata lahani ita da yaranta.

"Yar baqa mayya" taji baba lauren ta ambata,ta sani sarai da ita take,ta tsani sunan iyaka,kuma ita ta sanya mata shi,duk sanda ta tashi taji 'yan wulaqancinta a kusa haka take kiranta,tasha ce mata
"Baba laure,ba suna bane me kyau,malam na makarantar asuba yace babu kyau mu dinga kiran junanmu da laqabi mummuna fa" saita rafka salati,tace tana son kiranta da jahila,ita zata yiwa kiɗifiri da iyayin banza da wofi,suna ne tun tana tatsitsiyarta ba xata fasa kiranta dashi ba,takan qara da cewa
"Wannan inda kinyi karatun boko Allah ne kadai masanin abinda zaki dinga yi,to sai Allah yasa wadanda ba'a so din su sukayi bokon,kuma sha maka Allahu su zasu zama madubin gidan nan,ehe" baba laure wata irin macace mai.matuqar son kanta,da son 'ya'ya,son 'ya'yan ma har yayi mata yawa,itafa duk duniya yaranta sune kawai 'ya'ya,na kowa ma ya mutu,nata ya rayu,tunda ta taba zuwa cikin gari,taga yadda ake karatun boko,gidan da taje gidan qanwar qawarta ne data haihu,taga yadda suke karatun boko,taga manyan yaran gidan yadda suke,akace mata kowanne ma'aikacine,kuma boko sukayi,shikenan tunda ta dawo ta tasa baba iliya a gaba,ta dinga shirya masa zance,tare da nusar dashi romo da amfanin karatun boko,babu jinkiri ya gamsu,ya kuma yarda,suka ganganda dukkanin kudadensu suka tasamma sanya yaransu a makarantar boko ta cikin gari.

Tun ba'aje ko ina ba suka ga ba zasu iya ba,basu da sauran zabi illa su dawo dasu makarantar boko ta cikin qauyen,wadda a qalla shekara ashirin da wani abu da ginata,fiye da rabin ginin makarantar ya zube,a qarqashin biyu suke karatun,nan fa manyan yaranta maza guda biyu,munzali da muxammilu suka ce sufa ba zasuyi ba,a barsu kawai suje kudu neman kudi,juyin duniya sukaqi fafur,dole ta haqura,saita karkatar da akalar burin nata zuwa kan babbar diyarta mace wato asiya,burinta shine asiyan ta zama wata tauraruwa kuma ta musamman abar kwatance akaf fadin karkarar tasu,a lokacin da suna qananunsu,idan kowa yana fadin abinda yake sha'awar yi ko xama tsakaninsu kaltum da asiyan,idan kaltum tace zane takeso,kuma fannin zane zane takeson karanta,baba laure kan karkace tayita ɓaɓɓaka dariya,babu ma sanda taji ummansu na cewa
"To Allah yasa,Allah yasa ya zame miki alkhairi", takan ce
" ban taba ganin mutane marasa sa'a a rayuwa ba irin zuwaira da yaranta,komai.naku ku a cabe yake zuwa?,banda tohewar basira me za'ayi da wani zane?,zanen 'yan aljanu fa?tabdi,da alama a haka zaku qare ko,ni ai asiyata babu abinda ya dace da ita sai karatun aikin banki gidan kudi,ko karatun inda za'a dinga haqo man fetur,tunda ance shima abune mai daraja"umman bata taba daga kanta dai dai da rana daya ta dubeta kota dubin maganganunta ba,ko sau daya ita wannan baya a lissafinta,addu'arta.....burinta dare da rana shine su samu mazajen aure na gari,shine tabbas!.....shine dahir!....dahir din da babu gaibu a cikinsa.
Chapter 10 · 0% Book details